Connect with us

Zuma Da Madaci Hausa Novel Complete

Hausa Novels

Zuma Da Madaci Hausa Novel Complete

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin zuma da madaci hausa novel complete, zuma da madaci 4, zuma da madaci part 3, zuma da madaci part 2 zuma da maci part 1 da dai sauransu.

Anan mun Samar muku link dazaku sauke littafin izuwa wayoyinku. Kuduba link din yana karshen wannan rubutun.

Maman teddy itace ta rubuta takuma wallafah wannan littafin.

Zuma Da Madaci Hausa Novel Complete

Novel Title Zuma Da Madaci Hausa Novel Complete
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 300kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author Maman Teddy
Tags zuma DA madaci novel, littafin zuma DA madaci, zuma DA madaci part 1
Published date 04 – 12– 2022

Karanta: Littattafan hausa novel complete guda 500

Karanta Kadan daga cikin Zuma Da Madaci Hausa Novel Complete

BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIM

“Fadan maganan nakeyi hadi da tsalle ina Rungume Momy na”. itakam kakam ta rungume ni tana mai cemun Maza boye Baby na babu abun da zaiyi maki.

Dariya nake Dimple dina na kara lo6awa,ina mai cewa” Tom Momy ai nafishi iyawa ko?”

Sosai ma kuwa ina za’a had’a”.

Kai Momy maiyasa kk had’ani da Wannan Jaririyan yarinyan?” Plz ki bani naje na cigaba da Drawing dina na”.

Gwalo na masa ina fito da Harshena waje,don nasan A rayuwa babu abun da Yah Huday ya tsana irin aringa masa Gwalo da Dariya”. Ai ko nan ya nufo ni niko na daka taalle na yi bayan Momy na”. Ae ko da sauri ta’axani saman bayan nata ina kara lufff a gadon bayan ta,wanda a yanxu na daina Dariyan dana keyi,tunda na lura ya kufula matuka”. Ganin haka cike da tsoro nace Momy bashi Drawing din ko kyau ma Baiyi ba”.

Momy ne ta mika nasa tana Dungura masa da cewa” Oyah Amsa,kuma bance kafita harkan Baby na bako”.

Dukar da kan sa yy kasa yana mai jin babu dadi,don a yau yaji yayi fishi da Yar anwan nashi,cike dajin Haushi yace” Momy ke kike tare mata,inta cakaleni kaman sa’an ta”. kuma fah Momy na girme mata da yawa. Shekaru Far goma sha na bata”.

Dariya momy tayi tana mai cewa” Haba wa Huday dina,Yar anwa ce fah,inban da Abun ka Suhaimart nawa take?”.

Baiba ma Momy Amsa ba,illah juyawa da yy zuwa Dakin sa dayake falon yana furta Kuma Momy gobe Bazanje da ita School ba,sai dai Driver ya kai ta”.

Dajin haka nayi saurin Sauka daga Bayan Momy ina furta,lahhh Momy wai baxai je dani ba?”

Shi kam tuni yy dakin sa,Momy ne tayimin murmushi hadi da shafa ni tana cewa” Ina ya isah ma,aiko dake zaije,Kyaleshi kiniji,Maza jeki Wurin Nanny ta yi maki Wanka,ta gyramun ke”.

tom Momy na fadi hadi da saurin Nufan sasan Nanny na,wato mai Kulawa dani”.

Shiko Aliyu Huday iyayen y’an Fushi,tuni yacika yy fam,bin Drawing din da ko kammalawa baiyi ba yy da kallo,yana tunanin Abun da zaiyi ma Suhaimart don 6ata Ranta,Don ya lura ita sam bata san ma itace yake zanewa ba”.

Wani murmushun mugunta yy,don tuno da yanda zai lalata Zanen ya mai sheta mummuna,aiko nan ya fara hadi da nannade wani Cup da Leda mai karfi da yayi”.

Itakam Momy da wucewa na ne ta hau bina da kallo,tana mai tunanin Abubuwa,a ranta kam cewa taje inbanda abun Huday maiye nashi na bin Ta Suhaimart? Kanwar ka ta nawa?” Hmmm shiru tayi hadi da komawa kitchen kasancewar Daddy yana hanya”.

Nikam koda naje Sasan Nanny na sam bana da Sukuni Don yau Abokin hirar nawa yana fushi dani,na tsokane sa”. Kasancewar Nanny na na sameta tana Sallah yasani juyawa na koma Barayin Momy, wanda da isana na nufi Bedroom dina dake a falon”.

Bin Drawing din da Yah Huday ke mun kullum nayi da ido,ina jin kaunar Zanen a zuciya ta”. Da jin son yah Huday din, A haka na nufi kan gado na na kwanta,don na gaji don tsiwar da na masa ya Wahalar dani Sosai.

A haka sam ban san lokacin da Bacci yy awon gaba dani ba”.

Zaune take Cikin gaggan Daliban Almajiran Makarantan Allo,ta rafka Uwar tagumi daka ganta kasan maraici da damuwa ga kankantan shekaru duk sun isheta”.

Daga Lafceciyar Bulala Mal.Ado yy hadi da lafta mata a gadon baya,wanda yasata saurin dagowa hadi da fashewa da wani irin ihu mai hade da kururuwa”. Yimun Shiru wanda sukayi gadon gulma da munafunci,Zaki cigaba da karanta karatun naki ne ko sai na Kara maki”.

Cikin Sauri Iftyhal ta cigaba da Karatun Allon tana mai zubar da Hawayen Wuya da Azaba,Wanda A shekaru batafi 10 ba a duniya”. Kuka tajeyi tana karatun Allon hadi dajin wani Azababben yunwa don Rabon ta da Abinci tun Jiya da Safe,gashi har anwayi gari da safe. shiyasa gaba daya ta fice daga Hayyacin ta”. Kunsan Abun ka ga yaro karami,shikam Malam Mamman da yake kallon komai kuma shine mahaifin Iftyhal don Ado Shine Babban dan shi,Kuma shida Iftyhal Dan kishiya ne da Amarya,don Mahaifiyar Iftyhal itace Amarya,Sosai tasha Wahalar zama da Mahaifiyar Ado,don Hakurin ta shine kadai ya ceceta a gidan, A haka tayi ta hakuri har ta Haifi Iftyhal wanda a ranan da ta Haifeta tace ga garin ku nan,Sosai Dangin Mahaifiyan Iftyhal suka so Daukan ta,amma sai Mahaifiyar Ado Kulu,tace ita zata Raine ta,wanda A haka dai Sukayi hakuri suka bar Iftyhal, sosai Iftyhal ta taso cikin Gararin Rayuwa da Talauci ga Wahala da Azabtar da ita da sukeyi gidan,sam bata da Dan uwa bare tasamu sassauci ta bangaren sa”. Wannan kenan,muje Zuwa don muji ya abun ya kasance”.

Xaune duka Familyn Alh.Muh’d Harun akan Dirning Area,wanda da’alama suna break fast ne,kutsa kai nayi hadi da nufan Wurin don na baima idona abunci nima”.Bude Baki Hjy.Huwaoila tayi hadi da kirar Sunan Yar Autan nata da cewa” Suhaimart “…Suhaimart”.

Niko danake Zaune Nanny na tana shurya ni don tafy makaranta,tana rataya mun Schl Bag dina”. Jiyo kirar Momy na yasani saurin sakkowa ina Dariya don kullum a haka nake,cikin biyu zaka sameni ina yin Daya,walau dariya ko Murmushi.

Da gudu na nufi Daddy ina Rungumeshi da cewa” Daddy Good morning”.

Morning my dear,Ya Nanny?”

Murmushi nayi ina furta tana lfy Daddy”. Nan kafin yace wani Abu na kuma waigawa ga Momy ina Cewa” Momy Ina Yah Huday?”

Kafin ta bani amsa ne sai ga Huday adole ga Babban nan,nan yafara hura Hanci yana kumburi ya zauna Bai kalli kowa ba yace” Daddy Momy Good Morning”.

Nan duka cike da kulawa suka amshe da tambayan lafyn sa”. A takaice ya basu amsa,ya fara yin break din sa”.

Dariya nayi dacewa” Yah Huday Kasan meye Yau bakayi Zanen ba?.

Wani murmushi yy mun kan yace’Ayyah nayi na zana ki,kinga bari na nuna maki”.

Cikin Isaah da kasaita ya dauko wani Hoton mao kama dana na Goggon biri,Don bakina ya fito dashi wani yy gaba sosai,Zaro ido nayi ina bubbuga kafa dacewa” Wayyo Momy na Daddy,kallah wai wannan mummunan ce ni”. Aiko nan nasaka Kuka,aiko cike da Mugun ta yafara Dariya,Hadi da Cigaba da Yin break din shi”.

Cikin Sauri Daddy yafara mgn dacewa” Ina sam Bakye ne ba,Mama na,ki bar kuka,Momyn ki zata yi maki me kyau”.

Ehh Baby na Zuwa gobe zan zanaki kiyi kyau sosai,kinji”.

Kuka na kuma sawa ina mai cewa” Nifah na Yah Huday nakeso,in bana shi ba banason na kowa”.

Ganin yanda Su Momy ke ta Rarrashi na yasa Huday saurin matsowa kusa dani,yana mai cewa” Sorry my little bari kigani,wannan sam bakya bace”. Tsagaitawa nayi da kukan ina mai ce masa,Ae wannan Budurwan ka ne ko?”

Daure fuska yy bai cemin ko mai ba,aiko nan su Daddy suka saka Dariya don sometimes lamarina da Huday na basu dariya so Dramatic.

Wasu Cups ya dauko Guda Biyu,ko wanne dauke da Zanen duka mu,daya nawa,sai nashi,da Momy da Daddy”…

Dariya nasa ina daukan na Nawa ina cewa wow Yah Huday, tnc u so much”.

Sai kuma na dauki nashi ina kallon Kykykyawan Fuskan shi da cewa” I luv u Yah Huday… ”

Dariya yymun da cewa Luv you too Suhaimart “.

Dariya duka iyayen namu suka saka,Ganin yanda da anyi fada da an shirya tsakanin mu”.

Momy ne tace” Wow my Son anyah nan da wasu y’an shekaru baxa kafi Momyn ka bakuwa?” Dariya Daddy yy yana mai Dafa Kafadan Huday da cewa” Yy kyau Aliyou na”.

Momy ne ta katse mu dacewa” Kuuyi maza ku kammala kar fah kuyi lattin Zuwa School,tom Momy”.

Muka ce da itah hadi da cigaba da yin break din namu”.

A gaggauce muka gama sannan na rungumi Momy ina mata bye,haka ma Daddy “.

Da fitowan mu Driver ya taho da zanman daukan mu don isa damu School, amma sai Yah Huday yace yau Keken mu zamu tafi”.

Wasu keken mu muka dauko masu kyau don kowa sha’awan su yake,Hawa nasa keken yy,yana mai cemun nazo mu tafi,aiiko nan na dafe kai ina cewa” Oushh…Ash…. Yah Huday I’m Feeling headach.

Kallon na yy yayi Murmushi don ya fahimceni sarai keken ne bazan hau ba,nashi nake nufin Hawa,Dariya yy gami dacemun” Serious…”.

Daga masa kai nayi ina kara langwabar da kai “.

Miko hannusa nayi,nan ko nayi saurin matsowa ina mai Hayewa kai,yana mai fara tukawa ahaka muka bar gidan…..

A hanyan mu kuwa taxuwa School,a hankali yake tfy dani,kaman wanda ya dauko Kwai,din kar wani abu ya sameni,a haka dai muka isah Makaranta don har mun danyi Latti”.

Da isan mu Abokan Yah Huday suka rufar masa,da tambayan Dalilin zuwan sa Latti haka? Amma gani na yasani duka sukayi shuru don ko ba’a fada masu ba sun san nice nasa shi late din”.

Basu hannu yy suna gaisawa,yyn da duka suka rakoni har Section din mu,don kaini Nursery Class din mu”.

A kan hanya kuwa haka yara Student ke gaishe da Yah Huday good morning Senior”. Haka ya dinga amsa masu cikin isah da izzah,Don dama a School din yanxu shine Labour Prefect.

Don a wannan shekaran Zasu fita, Nikuma a wannan shekaran zan shiga Primary 1.

Sai da yaga shiga na Class sannan ya mikomun Lunching box dina,hadi da komawa Secondary Section dinsu”.

Ke Dabba Zonan ki dauki wannan Tallahn kije kisaida mun,kuma kika bari Malam ya ganki wlh sai na zaneki cikin gidan nan”. Innah kulu ne mai mgnan tana faman Hura jibgegen Hancin ta da ya cika fuska tam….ga baki ga muni,abun ba dadin gani”.

 

Download Zuma DA madaci Part 1

Part 2

Part 3

Continue Reading
You may also like...
1 Comment

1 Comment

  1. Ameenatu

    January 16, 2023 at 10:14 pm

    Naji dadin wannan link din

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Hausa Novels

To Top
× Chat Zamgist on WhatsApp