Maman Teddy Hausa Novel

Maman Teddy Hausa Novel

A wannan shafin mun kawo muku maman teddy hausa novel masu dadi wadanda suka kunshi romantic hausa novel, funny hausa novel, love hausa novels da sauransu.

Wacece Maman Teddy?

Aisha muhammad wadda akafi sani da Maman teddy shahararriyar marubuciyar littafan Hausa novel ce wadda tayi fice a arewacin najeriya.

Maman teddy yar asalin garin zariya ce a jahar Kaduna, tana da dimbin masoya dakuma mabiya inda Mata dayawa ke kaunar littafan data wallafah.

Tayi birthday dinta a 2nd October 2022 na wannan shekarar. Muna tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Maman Teddy Hausa Novel

Ga wasu daga cikin littafan da maman teddy ta rubuta takuma wallafah:

 1. Bafullatanan ruga
 2. Ƴar aikina
 3. Walijaam
 4. Ƴar waye
 5. Gidan kwarata
 6. Gidan zaurawa
 7. Ƙwaryar sama
 8. Bintoto
 9. Ƴar maula
 10. Habibi da’iman
 11. Dijama ƴar fulani
 12. kawaliya
 13. Ƙwartn manya
 14. Zuma da maɗaci
 15. Taɓarah
 16. Siyasata
 17. My Lady boss
 18. Zuma Da Madaci Hausa Novel Complete
 19. Yar Tsaakar Gida Hausa novel
 20. Budurcina Hausa novel da sauransu.

=================================

Ga Wani Sabon Littafin Maman Teddy datake kan Rubutawa yanzun.

Budurcina Hausa Novel by Maman Teddy

BUDURCINA! Love, romance, sympathetic, and erotic story.

New Hausa Novel Written by Aunty Aysha Mamanteddy

Shafi na farko 01

Dedication

This book is dedicated to the Almighty ALLAH, my creator, who in his infinite mercy on me make me to be born in this world, in the family of Prof. Muhammad Bamalli and my beloved mother Haj. Safiya.

Finally, this book is also dedicated to my darling husband Alh. Usman Umar Tukur. Love you always.

About the Author..!

Da dama na tambayar wacece Maman Teddy? A taƙaice dai, Aysha Mohammed (Maman Teddy) haifaffiyar Garin Zariya ce, a Jihar Kaduna. A nan take rayuwa tun daga ƙuruciya har zuwa girmanta. A matakin karatu tana da shaidar karatu kan ilimin haɗa magunguna, wanda ta samu a shekarar, 2014. Sannan ta yi Polytechnic a Zaria, while now she’s biologist, wato dai ta samu ƙwarewa kan ilimin halittu. She’s is a teacher, business woman, and advertiser, tana yi wa mutane talla game da kasuwancin su ta ɓangare da dama, musamman a social media da sauran wuraren kasuwancinta.

# Scientist
A peak in to my life.

#Author #teacher #Advertiser #Biologist #Bussiness Woman #Smilemaker.

Free page 1

*Wannan littafin na kuɗi ne. ₦300 for regular payment, VIP payment ₦600, Special Payment ₦1000. Na yi ƙasa da kuɗin littafina ne duba da halin matsatsin da ake ciki, financial challenges, da sauran ƙarance ² na abubuwa da suka sha kan mutane. Don haka masu buƙatar fara payment ga account number na 6037312299 Mohammed Aisha Keystone Bank ko katin MTN ta wannan lambar 08081202932 . If it’s direct VTU transfer ga lambar da za ku tura ta nan 09061466409 sai ku yi min magana ta lambar farko .*

The beginning of 2000s…

Hateeem Ezdaan estate House.
Gidan Larabawa . Kaman yanda Mutane ke ma wannan Estate laƙabi dashi kenan . Kasantuwar mai gidan Asalin su ba cikakkun ƴan Nigeria bane A takaice Halfcast ne , larabawa ne daga ƙasar Lebanon . A salin sunan wannan Familyn ya fara ne da Ezdaan family inda a yanzu suna ɗaya daga cikin wannan a hali ya doke sunan kowa , ba’a Jin na kowa sai na Mutum ɗaya Kasantuwar yafi su haske da suna da Girma ɗaukaka a karkatakaf iyalin Ezdaan Wato Alh Hateeem Ezdaan. Wanda Suke masa laƙabi da Abbie Hateeem . Mutum ne shi mai tsauri da zafi baya da Wasa sam , kuma duka a Familyn Ezdaan Shine Ɗa na uku . Suna da yawan gaske don sun hayayyafa mata da Maza sannan a yanzu har da yara . Sai dai wannan Familyn suna da wata Ɗabi’a guda , duka matan su Da suke Aure yan gida Nigeria suke aure , wannan yasa yaran nasu suke samun tarbiyya sosai duk da hakan ya samu nasaba ne daga Ɗaya daga iyayen nasu Wato Abbie Hateeem . Abbie Hateeem su goma sha ɗaya ne a wurin mahaifin su Ezdaan da kuma mahaifiyar su wanda jikokin ta ke kiran ta Jiddat a hausance wato Kaka . Yaran su maza taƙwas ne duka mata uku . A mazan babba shine Abbie Saleem Ezdaan, Abbie Yaseer Ezdaan, Abbie Almustapha Ezdaan , Abbie AlHayat ,Abbie Ahmadu, Abbie Hateem, Abbie Saifullah ,Abbie Abdullah . Sai kuma mata akwai Hajiya Nafisa, Aƙwai Adda Safnat , sai Autar su Mama Nuwaira . Bara mu shiga labarin kai tsaye . Kar ku manta wannan tamkar gabatarwa ne ba’a fara mafarin tafiyar ba . Muna magana ne akan shekaru na 2000s bamu shiga 2023 ba kun san kuwa da kallo a gaba wannan family haka Hateeem Ezdaan Estate muka Shigo kai tsaye a yanzu .

A hankali yake sauko da ƙafafun sa daga Arabian Stairs ɗin Falon, fuskar sa sam babu Walwala bare annuri daga Ni kasan wannan bai kama da masu daukar wargi ko raini ba , dogo ne Sosai kuma yana da dan cika haka yana da ƙiba duk da ba sosai ba , zamu iya kiran shi Tall and Handsome boy da ashekaru a yanzu ba zai haura 17 ba. Kallo ɗaya zaka masa kasan wannan cikakken Half cast ne ba sai an faɗa maka ba duba ga yanayin sa Fari ne Tassss kalon madara hasken sa ba mai ja bane , gashin kan sa mai yawa da cika don har kame ta yayi da Wani ribom irin nasu na maza yanda yaran larabawa keyi . Kasantuwar wannan lokaci ƙarfe baƙwai ne da Mintuna Goma na safiya ya zama yana Sanye cikin shigar Sport wears na yara matasa yan makarantar secondary yanda yake sauka daga Stairs din yana haɗe giran sa wanda gashin su suka kusa haɗewa , Humm Deeyaan Hateem kenan izza mulki sarauta ficci hohoho rashin ji kankat tun a yanzu haka yake to ina ga kuma mun kai shekara ta 2023 ya abun zai kasance Na bar maku ku Hasko da kan ku Masoya…Gyefen sa na kalla inda na hango Wata mace daga bayan sa ,tana Ɗauke da Ƙatuwar jakar makarantar sa ,a daya hannun ta kuma Jakar Laptop ce alamu duka nasa ne shi take biye masa dashi .

Rohaan ne yayi saurin kallon inda Yayan nasa ke saukowa cikin mulki da taƙamar nan nasa yasa shi kallon Ammie Salmat wacce take Hidimar haɗa masu Karin kumallo . Ammie Ga Akhy Deeyaan ya sauko kawai ki bamu Lunching Box mu tafi dashi zamu makara . Ƙarikawa inda suke Deeyaan Hateem yayi yana zama a Mazaunin sa na kullum wato kusa da Kujeran Ammien nasu. Muryar Rohaan ne ya kuma katse su yana faɗin “ Sabahul khair Ya Akhy Deeyaan ” . Kallon ɗaya Deeyaan yayi ma Ƙanin nasa Rohaan kana ya juya a Miskilance a kuma izzance yana karkaɗa ƙafarsa da gani kasan da aƙwai fitinan da yake son yi . Ita dai Jawahir Gyefen sa ta tsaya don ita ce mai kula da koman sa da yake buƙata ,ba ƙaramin Wahala take sha da Halin Deeyaan Hateem ba . Kallon sa Ammie Salmat tayi tana aje food flask din hannun ta mai Shegen ƙyau wanda tsadar irin wannan sun kai 200k . Ɗan takawa tayi tana kai hannun ta tare da shafa suman kan Deeyaan kana ta sumbaci Saman Goshin sa tana sakar masa murmushi irin na nuna soyayya ta Uwa da Ɗa . Kamin tayi masa magana ne Rohaan ya kuma katse su da cewa “ Akhy Deeyaan zamu yi late ka taso mu tafi , driver na jiran mu . Wani irin kallo Deeyaan ya watsa mawa Rohaan wanda hakan yasa Rohaan saurin yin ƙasa da idon shi , jikin sa na sanyi don yasan halin Yayan nasa shi kan sa bai bar sa ba ,naci ne dai da soyayya irin na jini ɗaya yasa duk baƙar wahalar da yake sha nasa yana nan manne kuma tare da shi .

Kusan mintuna Uku Rohaan yake kallo bai ce masa komai ba har Tsawon wannan mintinan kana ya fara magana cikin Issa yana cewa “ Rohaan Driver kace yana jiran mu? , Ni yake jira ko kuwa kai ne ƙaramin yaro yake jira ? , Uhmmm ina saurenka.

Kasa magana Rohaan yayi yayin da Ammie Salmat ta katse su da cewa “ Ban gane ba Wai wani magana kake yi haka Deeyaan? .

Kallon Ammie Deeyaan yayi kana yace “ Ammie Jiya na faɗa masa Cewar na daina hawa mota da girmana Driver ya kai Ni school, moto nake so nawa na kaina ,kuma ba guda Ɗaya ba ,ɗaya yayi mun ƙaɗan sai dai uku zuwa sama da haka . Waro ido Rohaan yayi yana kallon Deeyaan wanda yake maganan yana cika wuya alamu ba wasa a tare dashi , hancinsa har gumi ke tsatstsafo masa na masifa kai da gani kasan aƙwai zafin zuciya . Cike da ƙasa da murya Rohaan ya kalli Deeyaan yana cewa “ Abbie fa yana nan ,yanzu Zai zo kayi Shiru kar ka jamana . Kaiii Rohaan…..!

Deeyaan ne ya daka masa Tsawa cikin ɗaga Murya kana ya cigaba da cewa“ Na ce moto nake so a bani a yau a yanxu kuma a cikin sababbin can na compound wanda ba’a fara aiki dasu ba . Ba zan shiga moto driver ya Driving Dina ba , i pass that limit na wuce matsayin Mara abun hawa , a dai dai lokacin da Abokaina sun fara nisa millioniers kaje ji iyayen su duk sun basu motoci while me I’m still in a one circle , kullum jiya a yau . Sai ka jira idan kayi arziƙi ka nemi naka ka hau jirgin sama in ma kana so . Amma a yanzu driver zaka bi ya kai ka zuwa makaranta .!

Muryar Abbie Hateeem ya katse su wanda yake isowa zuwa Dinning ɗin . Juyawa Ammie da Rohaan suka yi suna kallon inda Abbie yake , ban da Deeyaan da har a lokacin ran sa ke a zafafe . Sanye yake cikin shigar jallabiya Brown alamu ba ya da Fitan Safe yana wani aikin ne a gida . Zama yayi a daya daga Kujerun Wurin wanda ke fuskantar na Deeyaan kana ya cigaba da cewa “ Ammie Salmat kina zaune yake Wannan maganganun ? Nawa duka duka shekarun Deeyaan suke ne ?.

Wani irin ba daɗi Deeyaan Hateem yaji wannan yasa shi miƙewa daga mazaunin sa yana faɗin “ Abbie Ni ba yaro bane yanzu ,kawai don nace moto Shikenan sai ka fara wannan maganan? Abbie kalli fa kaman mu muna da kudi muna da komai Abbie amma kalli irin karin kumallon da muke yi with this Unpleasant Dishes….yayi maganan yana pointing hannun sa zuwa inda kayan break fast ɗin su suke . Abincucuwa ne kusan kala huɗu sai Cofee da masu buƙatar tea sune cikon na biyar din . Na tsani wannan Rayuwar Abbie na tsani na buɗe ido na Ganni cikin wannan Gidan babu komai sai Wahala . Mashaallh Deeyaan…! Abbie ya furta cike da hikima irin nasu ta manya kana yace “ Idan kana so kayi karin kumallo mai kyau ka nemi naka kuɗin sai Kaci ka sha kaji daɗin ka . Of course yes Abbie zan yi kuɗi ƙudi marasa iyaka . Zan fi ka suna zan Fika kudi Abbie sai naga nayi hakan hankalina zai kwanta . Ba moto zan hau ba Flight ne da jiragen yawo zasu rinƙa ɗauka na ba Driver ba . Zanji daɗin rayuwa ta saboda ina son mulki ina son Mulki Abbie ina kuma son nayi kudi na zarce ka da kowa naka . Kuma zanyi nan kusa …. Deeyaan….! Muryar Ammie Salmat ya katse shi tana saurin isowa inda yake tare da kama shi tana Girgiza shi tare da dakatar dashi da maganganun sa . Idanun ta ne suka fara ciko da ƙwallah Wayyo Ni Deeyaan yaushe zaka daina Wannan zafin zuciyar? Yaushe zaka rinƙa iya sarrafa harshen ka ka koyi yanda ake tauna magana ? Deeyaan wannan fa Abbien ka ne Mahaifin ka , Kasan Girman sa kasan addinin ka sannan mun baka ilimi dama da hagu . Musamman ga addinin ka , Deeyaan shekaru biyu fa kenan da kammala alƙu’rnin ka ka dawo daga Egypt amma me yasa halayyar ka kullum da gyara ne ?. Har yanzu Kai yaro ne Karatu ne ke gaban ka ba son Mulki kuɗi ko wani abu ba.

Shiru Deeyaan Hateem yayi a Miskilance ya furta “ Afuwan ya Ammie, Abbie kayi hakuri ” . Juyawa suka ga yayi yana nufar Up stairs din da ya sauko yana komawa yayin da Jawahir tabi bayan sa da sauri itako Ammie Kallon sa take har ya shige tabbas sanin hali yafi sanin kama tasan kafiya da naci irin nasa ,idan yace yess to dole ka bi masa . Hummmm Sauke numfashi Abbie yayi yayin da Rohaan cike da Damuwa ya furta “ Abbie don Allah ku basa Moton Akhy Deeyaan fa ya iya mota , kuma kullum plan din sa ya za’a yi yayi kuɗi sannan Abbie zaiyi kuɗin …. Shashancin Banza .! Maza yi breakfast ka tashi ku tafi . Muryar Abbie cike da tsauri ya katse Rohaan wanda yayi saurin ɗaukar Ƙaramar wuƙar gaban sa da fork yana fara chopping Irish din gaban sa .

Cikin sanyin jiki Ammie ta furta “ Deeyaan yayi fushi Bara naje na Rarrashe sa ” . Kallon ta Abbie yayi yana mamakin yanda take zafin Son Deeyaan duk jikin ta yayi ba daɗi bata son ganin damuwar Deeyaan a Rayuwar ta , duk da shine yaron ta na farko amma ko ƙaramin ɗan ta Rohaan bai samu gatan ta irin yanda take ma Deeyaan .
**
Tun da Deeyaan ya shiga Bedroom din sa rest chair ya zauna abin sa . Ina son mulki ina son nayi kudi na zarce kowa . Ba iyaka familyn Hateeem Ezdaan ba , Nigeria da Duniya nake so taji ta kuma kira sunana . Sai ance Deeyaan Hateem Multi billionaire . Shigowar Jawahir yasa shi juyar da kan sa yana Daura Wuyan sa bisa saman Kujeran . Cikin sauri Jawahir ta tako inda yake tana faɗin “ Deeyaan ko akwai abun da kake buƙata? ” . Ba tare da ya kalle ta ba ,haka ba tare da ya tanka ta ba ya miƙar da ƙafafun sa wanda hakan da yayi mata yasa ta Fahimtar mai yake nufi don tun kamin ya kai haka itace mai kulawa dashi haka sanin hali yafi sanin kama . Tasan shi ciki da waje fiye da kowa sai dai iyayen sa kawai . Durkusawa tayi a gaban sa tana Kai hannun ta tare da fara cire Boot din ƙafarsa. Hannun sa yasa yana cire Rigar jikin sa yana zamana daga shi sai white Singlate. Miƙewa yayi tsaye a gaban ta yana sauke dogon Wandon Jikin sa yana zamana daga shi sai Short nicker kana ya zauna a kujeran yana ware hannun sa idanun sa a lumshe a Miskilance ya furta “ Massage” .
Cikin sauri Jawahir ta matsa inda hannun sa yake tana fara matsa masa tare da masa taussa a hankali yana lumshe ido

Topah yanzu muka fara.

# Deeyaan Hateem yace yana son mulki kudi yaji daɗin rayuwar sa tun a yanzu to ina ga gaba kuma lokacin an zama ƙwallon shege .
Labari ne wanda yake ɗauke da jarumai ma banbanta haka labari ne mai ɗauke da nishaɗantarwa wanda nasan zaku ji dadin shi . Ba’a fara komai ba tukuna . Ku dai ku cigaba da biyo alƙalamin Anty Aysha Mamanteddy .

Don’t forget to share to another groups

Wannan littafin na kuɗi ne. ₦300 for regular payment, VIP payment ₦600, Special Payment ₦1000. Na yi ƙasa da kuɗin littafina ne duba da halin matsatsin da ake ciki, financial challenges, da sauran ƙarance ² na abubuwa da suka sha kan mutane.

Tags: maman teddy wattpad, maman teddy novels, maman teddy hausa novel complete, maman teddy hausa novels