Connect with us

Tarihin Aisha Najamu, Shekaru, da Hotuna

Labaran Kannywood

Tarihin Aisha Najamu, Shekaru, da Hotuna

Barka da zuwa wannan shafin namu inda zaku karanta Tarihin Aisha Najamu, shekaru, Sana’a, Aure dakuma Hotuna.

 

Shin ko kun san Aisha Najamu ta Izzar So? Idan A’a to zan baku shawarar ku karanta wannan labarin har zuwa karshe kamar yadda zan yi bayani dalla-dalla akan duk abin da kuke son sani game da Tarihin Aisha Najamu, Shekaru, Sana’a, Aure Da Hotuna.

 

Izzar so shine Fim din Hausa mai dogon zango nafarko a fadin adewacin najeriya Wanda marigayi Nura Mustapha waye shine daraktan shirin kafin ya rasu. Aisha Najamu da Lawan Ahmad sune jogo acikin shirin.

 

A cikin fim din Aisha ta fito ne (a matsayin hajiya Nafisat) tana kokarin korar Ahmad wanda ya fito (a matsayin umar Hashim) daga kamfanin mahaifinta saboda ya tsaya mata a matsayin cikas.

 

To, ba tare da bata lokaci ba bari in zurfafa a cikin babban maudu’in wannan rubutu.

 

WACECE AISHA NAJAMU?

Aisha Najamu itace sabuwar jarumar da ta fito a Kannywood. Ta shahara a Najeriya saboda rawar da ta taka a wani fim mai suna Izzar So.

 

SHEKARUN AISHA NAJAMU

An haife ta a ranar 8 ga Afrilu 1995 a Jihar Kano. Aisha Najamu tana da shekaru 28 a duniya.

 

KARATU

A’isha ta yi karatun firamare da sakandare duka a Jihar Kano kafin ta shiga Jami’ar inda ta karanci harkokin kasuwanci.

 

SANA’A

Jarumar Kannywood Aisha najamu dai ta fara wasan kwaikwayo ne jim kadan bayan ta kammala jami’a.

 

Ta fara shahara ne bayan ta fito a cikin fim din Izzar So. Fim din Izzar So ya sanya Aisha ta zama jarumar da ta yi fice a masana’antar.

 

Daga baya ta shiga masana’antar saboda kwarewar da ta yi.

 

AUREN AISHA NAJAMU

Masoya sun yi ta tambayar ko Aisha tana da aure a yanzu. A halin yanzu ba ta auri kowa ba amma jarumar ta mayar da hankali sosai kan sana’arta.

 

TAKAITACCEN TARIHIN AISHA NAJAMU

Cikakken Suna Aisha Najamu
Shekaru 28
Kabila Hausa
Sana’a Wasar kwaikwayo

 

Karanta: Cikakken Tarihin Hajara Izzar so

 

HOTUNAN AISHA NAJAMU

Tarihin Aisha Najamu   Hotunan Aisha najamu   Hotunan Aisha najamu 2   Hotunan Aisha najamu 3   Hotunan Aisha najamu 4 Aisha Najamu ko shakka babu ita ce sarauniyar Kannywood. Ita ‘yar wasan kwaikwayo ce mai ban mamaki tare da babbar dama a masana’antar

Jarumar dai ta kusa wuce wasu fitattun Taurari kamar su Rahama Sadau, Maryam Waziri, Maryam Yahaya da Momee Gombe da sauran su.

Ko kuna da wani abun da zaku ce game da Aisha Najamu ta Izzar So? Sashen sharhi a buɗe yake wa kowa.

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Labaran Kannywood

To Top
× Chat Zamgist on WhatsApp