Kurkukun kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Barka da zuwa wannan shafin namu na littafan hausa novels inda muka kawo muku littafin Kurkukun kaddara Book 2 Hausa Novel Complete.

Kurkukun kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Zaro ido su Parveen su ka yi bakunansu a sake, yayin da su ke kallon ƙofar, Wani irin farin Ciki ne Mara misaltuwa ya bayyana akan fuskokinsu Har sun wage baki zasu Fasa ihu Angel Tai saurin Dakatar da su ta hanyar cewa”Kun manta abunda na faɗa ma ku? Komi za ku gani ku ja Baki ku yi shiru idan ba haka ba asirin mu zai tonu har su gane abunda mu ke ƙoƙarin yi’ Fuskokinsu Haris da alamun ruɗu donsu basu son kan me ta ke magana ba, sun dai ga murfin ƙarfe jikin bango, bayan haka sunji batul tace ƙofar da su ke nema.

Naufal ne yai ƙoƙarin buɗe baki Yace”Angel Kun bar mu a duhu, bamu san kan me ku ke magana ba” ya ƙarasa maganar idanunshi akan fuskarta, har lokacin bata daina sakin murmushi ba, Haka zalika su parveen Bakin su awashe ya ke Kamar Gonar audugu Ji su ke kamar ma Har sun fuce daga Cikin kurkukun.

“Ki yi mana bayani mana, Wannan murfin ƙarfen na menene a jikin bango”? javed ne yai maganar, sautin Muryoyin su daƙyar ya ke fita saboda rashin ƙarfin jikin su, har ƙwara sauran mazan akan mubeen ko da su ka shigo toilet ɗin kan shi na asaman Kafaɗar Hannah, Sam babu kuzari a jikin shi.

“Na ruɗe Angel Ki fada mana mun ƙosa Mu ji,” acewar Gabriel.

duk wanda yai magana acikin su idanuwanta na akan la66ansa, Sai bin su ta ke yi da kallo, farin Ciki Ya hana ta yi magana.

“Idan ba zata Iya yi mana Bayani Ba, Deeja Ku faɗa mana Meke faruwa ne’? Haris ne yai maganar idon shi akan su Deeja dake a tsaitsaye Cirko Cirko.

Ganin sun fara fusata Yasa ta haɗiyi yawu tare da sauke nauyayyar Ajiyar zuciya, Cikin sanyin murya ta soma kora masu jawabi sannu a hankali ta fayyace masu komai dangane da ƙofar sai dai ta 6oye masu Game da tattaunawar da su ka yi  Ita da Salsabeel.

Tsabar mamaki yasa su ka dinga jefawa junansu kallo Lokaci ɗaya wani irin Annurin farin Ciki Mara misaltuwa ya lullu6e zukatan su, Har basu san lokacin da suka ƙarasa gaban Angel suka ɗago da ita daga zuƙunnan da take abakin Bango, gaba ɗaya su ka rungumeta, Kamar zasu Karya ƙasusuwan Jikinta, Musamman Gabriel da ya fi kowa burin son ku6uta daga kurkukun ƙaddara, zafafan hawaye ne su ka soma gangarowa ta saman fuskarta, ta rasa gane hawayen menene? Shin na farin Cikin da ta ke yi ne ko kuwa na baƙin Ciki? Ɗaya bayan ɗaya ta ke kallon su Bayan sun sake ta, Maganar da ke yi mata yawo acikin kanta itace”kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku za ku Rayu! wannan maganar ta yi matuƙar tsaya mata aranta, ta ta6a zuciyarta, fatan ta Allah yasa Mutuwar kada ta rusƙe su agidan kurkukun ƙaddara, ba zata so wani daga Cikin su ya ƙara rasa ran shi a wannan Ƙazamin Ginin ba, Duk idan ta tuna Matasan Yaran da ta gani awannan ɗakin lokacin da ta dura taga taje ta gane ma idonta su Rataye Saman igiyoyi kamar dabbobi sai ta ji duk jikin ta ya mutu, Haƙiƙa ta yi matuƙar girgiza ganin yadda Suke feɗe Cikin mutun mai rai su kwashe sassan Jikin shi……..”

Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda Angel ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita har wani jiri ta ke gani acikin idanuwanta, Daƙyar ta jingina bayanta Jikim bango, taci gaba da riskar kukan ta Fuskarta jaga jaga da hawaye.

Murnar da su ke yi ce ta koma Ciki, Damuwa ta bayyana Akan faces ɗinsu, Har suna haɗa baki wurin furta Sunanta.

“Angel! Why are u shedding ur tears? Dan Allah kada kisa zuciyoyin mu su karaya, Baki ji irin farin Cikin da mu ke yi ba, saboda Kin gano mana ƙofar da zamu bi, don mu ku6uta daga kurkukun ƙaddarar,  Gidan da aka ƙuntata rayuwar mu aka hana mu sakat, Shekara da shekaru tun muna jarirai har zuwa lokacin da muka fara mallakar hankalin mu, Angel dukkan mu nan babu wanda bai haura shekara sha wani abu ba a gidan kurkukun Nan, Ta ya ya ba zamuyi farin Cikin Ganin ƙofar nan ba? muna so mu tsira kodan Muga ya wajen kurkukun nan ya ke, Muna so muga hasken dake awajen shi, koda da numfashin mu na ƙarshe ne, mu dai burin mu, shi ne mu ga mun ku6uta, Idan ma kina tunanin ba zamu Iya tsira mu dukkan mu ba, Zamu roƙi Allah da ya ara mana lokaci mu bar kurkukun nan wlh bamu fatan mu yi wulaƙantacciyar mutuwa acikin  shi! Mun fi so Mutuwar ta risƙe mu acan inda zamu je koma akan hanyar Guduwar mu ne…….”  Kalamansu sun ƙara karya mata zuciya, kallon da take binsu da shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka canza launi kallo ne da ke nuni da tsantsar ƙaunar su, tausayin su da ta ke ji, Ko ɗaya daga Cikin su ba ta son ta rasa, sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba, Mutuwa dole ce!

Tsawon lokaci Suna ta shan kukansu musamman Batul da su Azeeza in ka cire mazan da ke a cikinsu, hawaye ne kwance acikin fararen idanuwansu.

“Muna 6ata lokaci Angel, Ni zan fara jaraba 6alle ƙofar,” Gabriel ne yai maganar, Shi da ba ƙoshin lafiya ba. A haka ya nufi ƙofar  ya zuƙunna yana tatta6a Jikinta.

“Nima zan ta ya ka” acewar Naufal, yai maganar tare da matsawa kusa da Gabriel Ya zuƙunna, Atare suka dunga bugun ƙofar da niyar ta buɗe, sun haɗa uban gumi akan fuskokin su, murfin ƙarfen ko motsi bai yi balle su sa ran zai buɗe.

Matsawa Haris yai kusa dasu Shima ya sanya hannun shi, Hada matan kowa Ya shiga gwada ƙarfin shi akan ƙofar don ta buɗe, Duk wannan budurin da ake yi Jemimah Tana acan cikin ɗakin su kwance saman gado, ta lullu6e kanta da bargo baccin ne bai ishe ta ba.

Sun ɗauka cewa abun wasan yara ne shiyasa su ka dage akan sai sun buɗe ƙofar, Mayen ƙarfe ne murfin da ke ajikinta Yana da ƙarko Shekara da shekaru wurin yana adatse ta ya ya zasu iya buɗe shi? Yaran da ba lafiya gare su ba, Ganin yadda suke ta gabzar ƙofar ko sautin bugun da su ke yi mata bai fita sun Dage sun nace akan dole sai sun buɗe ta..

“Haris! Gabriel! Ku daina wahalar da kanku, Ƙofar ba zata ta6a buɗewa ba, saboda babu babban mukullin da  zamu Iya buɗe ta da shi,”. Jin wannan maganar da Angel ta yi ne yasa su ka mimmiƙe tsaye sai nishi suke fitarwa ta ko’ina sufa ke tsastsafo masu a jikin su.

Atare suka haɗa baki wurin faɗin”Makulli? A ina zamu same shi? Dan Allah ki faɗa mana inda ya ke”

Zuciyarta ba ƙaramar karaya ta yi ba a yayin da su ke tambayarta ina makullin , wani abu da ta lura dashi gaba ɗaya hankalin su ba’a kwance ya ke ba, duk sun furgice burinsu kawai su bar kurkukun.

“Angel kin yi shiru baki amsa mana ba” Jan numfashi ta yi tare da sanya tongue ɗinta ta ɗan lashi lower lip ɗinta da ya bushe Cikin sanyi murya ta soma yi masu magana.

“Danish! Shine makullin Da zai Iya 6alle mana ƙofar, gashi baya atare damu Yana acikin kurkuku, Yanzu dole sai mun nemo shi idan har muna son mu ku6uta …….” a matuƙar ruɗe su ke jefa mata kallo, Dole su yi mamaki, Ta ya ya Danish da ya kasance Ragon Namiji acikin su zai zama Makullin buɗe ƙofa? How that can be possible? Ta ina Danish ya ke da ƙarfin yin hakan? ganin irin kallon da su ke binta dashi yasa ta fahimci cewa Basu gasgata maganarta ba. Suna buƙatar ƙarin haske.

“Bazan Iya yi ma ku dogon bayani ba, because you won’t understand me, but definitely Danish is the key to open the door, just believe my words, he can open it,”

Lamarin ya yi matuƙar ɗaure masu kai, Musamman Haris shi da yafi kowa sanin Danish, mutumin da ko ƙwaro Tsoron shi ya ke ji yau shine Angel ta ke kira da makullin buɗe ƙofa.

“Maganar ki gaskice! Ni shaida ne akan hakan! Danish ne kaɗai zai Iya buɗe ƙofar!  kusan atare suka ɗaura Idanuwansu akan fuskar Gabriel da yayi maganar.

“Nasan za ku yi mamaki, Dalilin da yasa nace haka, Saboda kokawar da muka ta6a yi dashi, lokacin da Danish Ya shaƙi wuyana da hannun shi, Shaƙar da bana tunanin cikakken mutunne yayi mini ita, Ni nasan mai naji a lokacin da har yaja na naushi idonshi, ƙarfi ne dashi naban mamaki, tabbas shi zai iya buɗe ƙofar……” tunkan ya ƙarasa rufe baki Haris yace”Kun rikita mini tunani na, Taya mutumin daya rasa idon shi ɗaya zai Iya yin hakan? Bayan ni asani na  Danish bashi da wani ƙarfi,” Fuskar shi da alamun ruɗu yai maganar.

“Danish Ya rasa ido”! Batul ce ta ambaci hakan Idanuwanta azazzare hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba jin abunda Haris yace don ita bata san da zancen rasa ido da Danish yai ba, sun6oye mata don karsu tayar mata da hankalinta.

“Danish bai rasa idonshi ba, Sun samu sa6ani da Gabriel ne, Har takaiga ya naushi idon shi, wanda silar hakan Giant yazo ya tafi dashi, Na 6oye maki hakan ne saboda bana son hankalin ki ya tashi, Kuma Ni da kaina Danish ya faɗa mini cewa Lafiyar shi qalou ba abunda ya same shi, ‘ Angel ce ta kora mata jawabi, Hankalin batul yaƙi kwanciya da kalamanta, jikin ta yayi sanyi, hawaye tuni sun soma yin sintiri saman kuncin ta.

“Shikenan Yanzu ki faɗa mana Taya za’ae mu ga ɗan uwan mu Danish? Idan ma ta kama Ni zan bi ki mu shiga prison ne don mu nemo shi” Gabriel ne yai maganar da ƙwarin gwiwarsa, Har yanzu yana nan da rashin tsoronshi.

Girgiza kai Angel tayi”wannan aikina ne, Ni kaɗaice zan Iya dawo da Danish Cikin mu, In sha Allah, ”

“But how could you do that? Bayan babu wata ƙofa da zaki Iya shiga prison”? Har ta buɗe baki da niyar Ta amsa Ma Naufal tambayar da yai mata, kwatsam! ba zato ba tsammani Kunnuwanta su ka jiyo mata motsin buɗe ƙopar ɗakin su, hakan yasa tai saurin Katse maganarta, Idanuwanta azazzare Take  kallon su.

“Kamar buɗe ƙofar ɗakin Mu ake yi? Mun shiga uku, Asirin mu zai tonu, wlh mu gudu daga Cikin toilet ɗin nan,” Parveen ce tai maganar, hankalinsu idan yai dubu toh ya tashi, Gaba ɗaya duk sun bi sun ruɗe, a sukwane Angel ta juya da gudu ta nufi Ƙofar toilet ta buɗe ta, Fucewar ta keda wuya suma suka bi bayanta, garin gudu har suna bangaje juna, Adai dai lokacin da suka faɗo  tsakiyar ɗakin, kowannansu ya  tsaya da tafiya, Idanuwansu azazzare su ke bin benan da kallo, sai faman haki suke yi babu mai sauran kwanciyar hankali acikin su, babban abunda su ke jima fargaba  kada ace Tsohuwa zafreen ce, Ilai ko hasashen su Ya zama gaskiya, ƙofar na ƙarasa buɗewa kunnuwansu suka soma jiyo masu takun takalmanta Har wani sauti su ke badawa ƙwas ƙwas! Jikinsu Ya hau kakarwa zufa ta dinga tsastsafo masu ta ko’ina a jikin su.

Cikin muryar raɗa Deeja tace”Mun shiga uku Angel mun manta bamu maida tukunyar fulawar nan ba! Yanzu idan ta shiga toilet ɗin ya zamu yi?

Ƙasa ƙasa da murya Angel ta ce”In sha Allah ma ba zata shiga ba, Idan ma tai yunƙurin yin hakan zan dakatar da ita,” ita kanta da ta ke yin maganar a tsoroce ta ke furtata, ƙarfin halin ne kawai.

Ahankali ta ke tunkaro in da suke atsaye Cikin shigarta ta jajayen kaya, Yau babu mask a kan fuskarta, Daga bayanta Giants ne Guda Biyu masu ƙirar Samudawa, ko da ta ƙaraso dab dasu saita dakata da yin tafiyar A tsanake ta ke binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Saboda tsabar ruɗu da kama kai, Jikin Angel na 6ari ta russinar da kanta Ƙasa muryarta babu natsuwa ta furta”Ina kwana” Tun da tsohuwa zafreen ta kafe ta da ido sam ta kasa motsawa, Lamarin ne ya ɗaure mata kai, Yadda Angel ta duƙa mata wurin gaishe da ita…..

Da sauri su Haris suka russinar da kansu tare da gaishe da ita Cikin girmamawa.

Babu wanda ta amsamawa a cikinsu, Tsawon mintuna biyar kafin ta ɗan yi gyaran murya tare da basu Umarnin su ɗago da kawunansu, bayan sun ɗago ta tsare fuskar angel da blue eyes ɗinta, Suspicious looking ta ke binta dashi Hatta tsigar jikin Angel sai da ta tashi haiƙam, Sam takasa yarda su haɗa ido da tsohuwa zafreen, ta dage tana ta wasa da yatsun hannunta, ta harɗe su acikin na juna, Su ta ƙurawa ido.

Su Deeja duk sun sha jinin jikin su, ganin irin kallon da tsohuwa zafreen ke bin Angel da shi, Kuskuren da Angel ta tafka shine gaishe da zafreen da ta yi, Mace Dattijuwa irin zafreen wadda taga jiya taga yau, Taya zata Iya yi mata wayau? Yarinyar da bata ta6a gaishe da ita ba, sai yau Hakan ya ƙara sanya mata zargin wani abu na faruwa a ɗakin nasu, A hankali takawar da idanuwanta daga kan fuskar Angel ta soma bin fuskokin su Batul da kallo, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, sam babu alamun gaskiya atattare dasu, duk wani motsinsu akan idonta.

Ba zato ba tsammani suka ga ta tuntsire da dariya mai sautin gaske hankalinsu ya ƙara ɗugunzuma, a firgice su ke bin ta da kallo, Lokaci ɗaya ta dakata dayin dariyar ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri.

“Meyasa ki ka yi gaggawar gaishe dani tun kafin in buƙaci hakan? Kamar daga sama Angel taji ta jefa mata tambayar.

Yawu ta haɗiya kutt a maƙoshinta, Idanuwanta na kallon Ƙasa azazzare ta soma magana Cikin rashin natsuwa

“Nagane kuskure na, kuma Na yi danasanin rashin kunyar da na yi maki a kwanakin baya, inaso na gyara tsakanina dake ne saboda nasan ban kyauta ba..” tunkan ta kai ƙarshen maganar tsohuwa zafreen ta soma sakin bazawarin murmushi, wanda silar hakan yasa ta kasa ƙarasa zancen da ta kamo.

ALSO READ: Auren Sha Awa Hausa Novel by Oum Aphnan Pdf

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*