Connect with us

Kalaman Barka Da Shan Ruwa 2024

Love and Relationship ship

Kalaman Barka Da Shan Ruwa 2024

Yakai mai azumi, muna maka Barka da zuwa wannan shafin namu mai albarka inda muka kawo muku kalaman barka da shan ruwa dakuma kalaman soyayya na barka da shan ruwa.

Aika kalaman barka da shan ruwa zuwa ga masoyi ko masoyiya nada matukar muhimmanci gurin kara dankon soyayya.

Buda baki ko ince shan ruwa na daga cikin lokutan da Allah madaukakin sarki yake karban addu’oin bayinsa.

Yiwa masoyiyarka ko masoyinka addu’a a irin wannan lokacin yanada matukar tasiri.

Muna rokon Allah yakarbi ibadun mu baki daya, Ameen.

Kalaman Barka da Shan Ruwa 2024

Ga wasu tarukan kalaman barka da shan ruwa masu matukar tasiri a soyayya:

1. Barka da shan ruwa masoyiyata, Ina miki fatan Allah yakarbi ibadun mu yakuma albarkaci rayuwar mu baki daya.

2. Ina maka fatan Allah yakarbi ibadunka yakuma karbi addu’oin ka masoyina. Barka da shan ruwa!

3. Ni’imar Allah ta cika zuciyarki da gidanki da farin ciki da yalwa.  Barka da shan ruwa.

4. Yakai masoyina, ya azumi kuma ya ibada, Ina maka fatan barka da shan ruwa.

5. Naso muna tare a gidan auren mu domin muyi buda baki a tare kuma acikin farin ciki. Barka da shan ruwa masoyiyata!

6. Ina ma ace an daura auren mu, namaka girki mai dadi, na hadama kayan buda baki na zamani kuma masu dadi na shayarda kaisu lokacin buda baki. Ina maka barka da shan ruwa.

7. So wani abu ne mai kyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya damke. so shi ne yanayin da kan sa ka ji ka a raye.

Ina fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshen rayuwata, saboda ba kin kasance budurwata kadai a gareni ba, kedin aminiyata ce kuma abokiyar rayuwata. Barka da shan ruwa masoyiyata. – kalaman barka da shan ruwa

8. Akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta.

Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Barka da shan ruwa masoyiyata.

9. Tsuntsaye na bukatar fukafukai domin tashi, kifi na bukatar ruwa domin yayi rayuwa, ni kuma ina bukatarka domin na yi rayuwar farin-ciki.

Ina son ka masoyi na, kuma ina maka barka da shan ruwa. – kalaman barka da shan ruwa

10. Nakan raba dare ina mai rokon Allah don neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko danake rokon samu?

Inasonki kuma ina maki barka da shan ruwa.

11. Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin dana kalleki, sai naga cewa kamar babu kyakykyawar mace sai ke. Ina miki barka da shan ruwa!

Karanta: Ramadan day 1 to 30 Quotes And Pictures 2024

12. Zuwa ga zabin zuciyata, ina fatan ka Sha ruwa lafıya? ina fatan izuwa yanzu nutsuwa ta game jikinka, kishirwa ta gushe daga makoshinka?

Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka Sha ruwa lafıya? Ka Huta Lafıya.

13. A dukkan lokacin da na ga daren Lailatil kadari, zan kasance mai rokon Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar burinmu? ina Son Ka.

14. A lokuta da wurare daban-daban ina ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a bude. Ba na iya yin komai ba tare da tinaninka ba. Fatan Ka Sha-ruwa Lafıya.

15. Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan lokacin da idanuwana ke kasancewa a bude. Barka da shanruwa masoyina

16. Irin kulawar da kake nuna min a kullum na saka ni tinanin irin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Barka da shan ruwa masoyina!

17. Zanzamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo şarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka Habeebi na.

18. Zuciyata ba za ta taba canja matsayin da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taba yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taba goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Shan Ruwa Masoyina!

19. Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman kumatunka, na mace a saman labbanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da Shan ruwa baby!

20. A dukkan lokacin da kake bukatar wani ya taya ka hira, karda ka manta kana da ni, ka nemo ni domin debe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Ka Sha Ruwa Lafiya?

21. A lokacin da na tino irin rayuwar da na yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kadai ba tare da kai ba , yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada. Barka Da Shan ruwa nurul qalbi na!

22. Ba zan taba mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka. Barka Da Hutawa. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya?

Ku kasance da wannan shafin namu inda zamuci gaba da kawo muku kalaman barka da shan ruwa na soyayya. – kalaman barka da shan ruwa.

Wasu Na Karanta: Sakonnin Barka Da Sallah 2024 Messages, SMS & Images

Barka da shan ruwa text messages

1. Zuwa ga muradin zuciyata, ina fatan kasha ruwa lafiya? Izuwa yanzu nutsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta
gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka sha ruwa lafiya masoyina

2. A duk lokacin da na ga daren
Lailatilkadari, zan roki Allah Ya mallaka min kai a matsayin mijina kuma uban ‘ya’yana. Ina fatan kai ma zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar burinmu? Ina maka barka dan shan ruwa Habeebi na.

3. Jin muryarki na sakwan daya, na jefa ni cikin kogin tinaninki, na tsawon
lokacin da idanuwana ke kasancewa a
buɗe. Barka Da Shan ruwa masoyiyata!

4. Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin
da kike da shi ba a cikinta. Murmushina gare ki ba zai taɓa yankewa ba. Son ki a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Shanruwa my heart.

5. Da a ce zan iya zama komai, da na
zama ruwan hawaye a gare ki, a haife ni a cikin idanuwanki, na rayu a saman
kumatunki, na mace a saman laɓɓanki.

Ina son ki so mara misaltuwa. Barka Da
Shan ruwa masoyiya ta.

Falalar Azumi

1. An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, Allah mai girma da daukaka ya ce, dukkan ayyukan dan Adam nasa ne, amma ban da azumi, domin azumi nawa ne, kuma ni ne zan yi sakayya domin azumi garkuwa ne.

Duk ranar da mutum yake yin azumi baya zina, baya daga murya, kuma ba ya yin wauta don idan wani ya zage shi, ko ya neme shi da fada lallai ya ce, ni ina yin azumi (sau biyu).

Manzon Allah (SAW) ya ce, na rantse da wanda raina yake hannunsa, warin bakin mai azumi ya fi kamshi a wajen Allah ranar kiyama daga kamshin turaren Almiski, kuma mai azumi yana da farin ciki guda biyu da zai yi farin ciki da su, lokacin da yake yin buda baki, zai yi farin ciki da lokacin da zai hadu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa.

(Bukhari ya ruwaito hadisi na 1904 da Muslim Hadisi 1151). – kalaman barka da shan ruwa

2. An karbo daga Sa’ad dan Sa’ad (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, lallai a cikin aljanna akwai kofofi guda biyu ana kiransu da suna Arrayyan, babu wanda zai shige su sai mai azumi, babu wani wanda zai shige su sai su (wato masu azumi).

Za a ce ina masu azumi sai su mike, sai a ce babu wanda zai shige ta wanda basu ba, idan suka shiga sai a rufe kofar aljannar. – kalaman barka da shan ruwa

Ba mai shiga wannan }ofa ta Arrayyan sai masu azumi, (Bukhari ya ruwaito hadisi na 1896 da Muslim Hadisi 1152).

3. An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, duk wanda ya azumci watan Ramadana yana mai imani, yana mai neman lada, to, an gafarta masa zunubansa wanda ya gabatar (Bukhari ya ruwaito hadisi 1900 da Muslim 760).

Wasu Na Karatun: Sunayen soyayya masu dadi na mata da maza 2024

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Love and Relationship ship

To Top
× Chat Zamgist on WhatsApp