Connect with us

Gyaran Nono Da Tumfafiya

Hausa Novels

Gyaran Nono Da Tumfafiya

Assalamu Alaikum, Barkanku da karasowa izuwa wannan shafin namu na gyaran jiki inda ayau muka kawo muku yanda ake gyaran nono da tumfafiya.

Nono wata kadara ce mai tartare da albarkatu ajikin ya mace, kuma yana daga cikin abubuwan dake daukar hankalin da namiji.

Saboda haka gyaransu nada matukar amfani ga mace budurwa, bazawara dadai sauransu.

Batare da bata lolaci ba, bari mu zurfafa cikin abunda yakawuku wannan shafin namu.

Gyaran Nono Da Tumfafiya

Tumfafiya wata bishiya ce mai matsakaicin tsayi da ke girma a Yammaci da Gabacin Afrika da kuma wasu sassa na Kudancin Asiya. Haka kuma ana samun tumfafiya a kasar Indiya.

Ta kuma kasance daya daga cikin bishiyoyin da cibiyar koyar da hada magani da ke a kasar ta India waton (All India Institute Of Medical Sciences) sun yi nazari na musamman ga wasu muhimman sinadiran da ke kumshe a cikin ganyen tumfafiya inda suka tabbatar da cewa wadannan sinadiran suna maganin gudawa.

Gyaran Nono Da Tumfafiya

A dalilin hakane masana maganin tsirran itatuwa na kasar Indiya waton Ayurbedic pharmacopoeia suka yi umurni amfani da saiwar da kuma ganye ko kunnuwan tunfafiya a magance asma da daukewar sheda da kuma sauran cututtukan da ake dangantawa da cututtukan huhu.

A kasar Hausa, masu maganin gargajiya na amfani da ruwan tumfafiya don warkar da wasu cututtukan fata kamar makero.

Inda ake aske gashin kai ko kuma duk inda makeron yake a jiki sai a karkare gurin da makeron yake har sai gurin ya yi jini sai a tarfa wadannan ruwan na tumfafiya kan makeron, za a dunga wanke wajen a kullum ana sanya ruwan tumfafiya a sama har sanda ciwon ya warke.

Tunmfafiya na maganin dafi kamar na maciji da cizon kunama. Ana amfani da saiwar tumfafiya bayan an konata sai a gauraya garinta da na danyen mai a shafa kan inda cizon ko harbin yake.

A kasar India, suna amfani da furen tumfafiya ga masu farfadiya da kuma ciwon kurkunu.

Ana amfani da kunnuwan tumfafiya a maida basir mai tsiro. Za a nemi kunnuwan tumfafiya kamar kwara biyu ko uku haka sai a dan kara su ga zafin wuta kadan sai a danne dubura da su in sha Allahu nan take duburar za ta koma.

Ana tarfa ruwan tumfafiya kamar digo biyu a cikin kunnen dake ciwo za a yi haka sau daya zuwa biyu. Amma idan kunnen na ruwa to sai a tafasa itatuwan tumfafiyar misalin kofi daya sai a rinka wanke kunnen dake ciwo da su.

Tumfafiya na maganin dan kanoma wanda ya tsananta, shawara, ciwon ciki, yawan ciwon kai na ba gaira ba dalili, tarin nimoniya da kuma cutar kuturta.

Ana kona saiwar tumfafiya a maida su gari sai a hada da dan karamin cokali na garin lalle a daura a kan ciwon kafa ko hannu ko yatsan da ya kumbura ko ya ja ruwa kamar ciwon dan kankare ko wanda ake tunanin na kambun baka ne.

Wannan kumshin zai zuke dafin ciwon a cikin karamin lomaganin. Ana amfani da tumfafiya a kona jinnun da aka turowa mutum ta hanyar sihiri.

A nan za a nemi garin ganyen kaikayi koma kan mashekiya sai a nemi furen tumfafiya a shanya idan ya bushe sai a dake a gauraya su waje daya a nemi allo babba a rubuta abun da ya sauwaka daga ayoyin Alkur’ani mai girma sai a wanke a tafasa a sha tun da safe kamin a karya.

Wallahi sihirin ko wane iri ne zai karye nan take.

Ana tafasa kunnuwan tumfafiya a tunga wanka da ruwan tun da safe dan maganin matsanancin ciwon gabobi da kuma jiyojin jiki

Mata masu neman tagomashi ga mazajensu sai su nemi busashen garin tumfafiya sai su hada da garin lalle da kuma garin ganyen bishiyar birana. Sai dai kuma bishiyar tumfafiya tana da ban tsoro musamman da dare inda takan canza bishiya ce da iskoki ke fakewa a gunta.

Dan haka sai a san yanda aka tinkaren ta. Amma tana da fa’idodi da dama. Duk da yake ba kowane irin ilmi ya dace mu fayyace ba. Saboda fadar wani ilmi zai zamo illa. Da fatar duk abin da muka fada a kan kuskure za a gafarce mu.

Nasan mai karatu zaice baiji inda muka ambaci yanda ake gyaran nono da tumfafiya a cikin wannan rubutun namu ba, to kucigaba da ziyartar wannan shafin namu inda zamuyi muku bayani dalla-dalla akan yadde ake anfani da tumfafiya wajan gyaran nono.

Allah yasa mudace. Ameen

KARANTA: Maganin Girman Nono Na Shafawa

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Hausa Novels

To Top
× Chat Zamgist on WhatsApp