Connect with us

Auren Sirri Hausa Novel

Hausa Novels

Auren Sirri Hausa Novel

Barka da zuwa shafin mu na littafan hausa novels, inda muka kawo muku littafin auren sirri hausa novel Wanda Aisha bagudo ta rubuta takuma wallafah.

Auren Sirri Hausa Novel

Compiled by Umar Dalha Funtua

AUREN SIRRI

 

Bismillahirahmanurrahim

Aysha A bagudo

 

Page 12

Lekki Unguwace mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta a silent place saboda bata cika hayaniya mutane ba dauke da tarin sanyin niima mai dadi sakamakon kusancinsu da ruwan teku unguwace da tattara kan manya maaikata da kusoshin gwanati hade da manyan masu kudi ga tarin yan yahoo boyz domin mafi yawancisu sunfi shaawar zama acikinta rayuwar mutane unguwar abin shaawa bbu ruwan wani da wani domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje

PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE

Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta hadin kai tattare da zaman lfy Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu

Let alh Muhammed bello khaliyal haifafen garin Lagos ne Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi sananne mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance sannan kuma take zaman lfy marigayi Muhammed bello soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan
ya rike mukamai da dama a wancan lokacin ya rasu yabar tarin dukiya da da yaya da jikoki bila adade
gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu

kafin rasuwarsa dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da enuwan dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din mai mazan kanta
ya tattara kan yanuwasa suna zaune a ciki yana da mata hudu hjy shemau wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da yaya goma Sha biyu mata takwas maza hudu sai hjy hauwa mai dauke da yaya goma maza biyar mata biyar sai hajiya rabi mai yaya takwas maza biyar mata uku sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy shuwa itama tana da yaya takwas mata bakwai namiji daya
bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama an ginashine saboda taron sada zumunci wanda zasu dinga yi a duk karshen wata

haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu
anan cikin dangi mazan suka zabi matan suma matan suka zaba akayi bikinsu anan cikin estate din suka zauna tare da iyalinsu har zuwa sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire
yayinda yayansa da yayan en uwa suka cigaba da kula da estate din
a lokacin aliyu da habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda karatu

Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu ya dukufa gurin juya dukiyarsa ba abinda yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya yayiwa sauran yanuwansa zarra aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba hade da tarin compenis a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da gidaje a abuja da sauran garuruwa
tsananin neman kudinsa ne yasa bai ajiye iyali da wuri ba burinsa bai wuce ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba

Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila a india tun daga lokacin da aliyu ya daura idanunshi akanta ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne ahmed ne babba sai ita sai farida kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince da auren
koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba
kasancewarta mace mai tsananin son jamaa da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da mahamud yaya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar yayan data haifa acikinta
suma kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke kiranta da ummi duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu

shekarata biyar da aure mutuwar mahaifiyar ta risketa zuwan datayi indiya ne dazata dawo tazo da kanwarta fadila ta hada dasu Mahmoud tacigaba da rikonsu
sai da fadila ta dauki sama da shekara takwas da aure sannan tasamu cikin murna a wajen wannan family bai faduwa
cikinta na da wata tara cif ta haifi NASURUDEEN daga ita har aliyu suna matukar son DEENI tamkar numfashinsu DEENI yataso cikin gata da kulawar iyayensa da dangi gabadaya suna nuna masa tsansar gata da soyayya fiyye da tunanin mai karatu
shiyasa yataso a shagwabe a sangartacce saboda kaf estate din kowa yasan da zaman DEENI babbar matsalar da suka fara fuskanta da deeni shine rashin magana da bai yi da farko fadila ta dauka ko kurma ne sai daga baya tagane tsabar miskilanci ne kawai yayi masa yawa
duk tarin yayan dake cikin wannan estate din DEENI yafita dabam acikinsu bashida aboki
gabadaya baya yarda da kowa koda yaushe yana tare da umminsa ko farida ko su Mahmoud tun tasowarsa yake da burin son zama soldier yayinda ummi take bashi goyon baya wajen kiransa soja
Domin wani lokacin zai je yatasa hotonta marigayi kakansa dake manne a falonsu gaba yayi ta kallo yana shafa fuskar tsohon yana murmushin Sam shi bashi da faraa ballanantana sakin fuska koda yaushe fuska nan tashi a hade take tamkar hadari DEENI Nada shekara takwas byn yakare primary school aka sai mishi form din shiga makarantar sojoji baawani samu wata matsala ba yasamu sakamakon matsayin mahaifinsa da kakansa sabanin wayanda basu da gata
domin a wanan lokacin idan dai kai bawani bane ko dan wani ba ko bakada hanya a military school sunanka sorry
Domin kuwa kana ji kana Gani military school zai gareka shiga

byn wani lokacin farida ta samu miji anan cikin estate din wanda shima yakasance Dane ga marigayi Muhammad bello wato habibu ubansu daya da aliyu mahaifin ga DEENI
duk da fadila ta nuna rashin amincewarta matuka da nuna wa eruwartata illar aurenta da Habib Amman sai taga yarinya ta nuna tana so abunta dan haka ta kyaleta kuma da kunya dai ta fito fili tace batason jinin aliyu wanda itama kanta tasan hakan ba mai yiwu bane itama ba wai shi din ne bataso ba halinsa ta tsana
Amman shi babban maaikace gwanati ne director of land and housing same na Lagos state gabadaya yana da mata biyu da yaya bakwai farida ce ta uku
Ko alokaci daya auri farida takasance mace ce mai tsananin hakuri
duk da mijin nata Vai kasance mutun mai adalci ga iyalansa ba Amman bata taba kawo kararshi ga ummi ba domin tasan halin ummi Sam bata son raini

Shekarar da aka yiwa sulaiman da mahamud aure shekarace Allah yayiwa mijin ummi rasuwa wato alh aliyu Muhammad bello sunji matuwar farar daya mutuwar tayi matukar gigita ummi dan byn ya dawo daga sallah asuba ne yayi irin kishingide nan yana lazimi koda ummi taji shiru shiru bai sake fitowa ba Sannan bai nemeta ba kmr yadda ya saba wanda aldarsa ce da zarar gari yayi sha yake fitowa ko yakirata a waya Amman taji shr
tashiga dakin nasa ta tarar dashi kishingide da carbi a hannunsa
da fari ta dauka ko bacci yakeyi sai tayi nufin ta tasheshi yakoma kan gado
Ammai sai taga alamun rashin motse atare dashi takai hannuta wajen hancinsa da karjinsa a lokacin daya taji baya numfashi
take ta zube anan ta sume
har a kashare zaman makoki ummi batasan a wani hali take ba dan bata cikin haiyacinta koda ta farfado ma sai da akayi ta hadawa da addua Sannan aka samu kanta ta dawo daidai dan mutuwar ta girgiza har ta kusan zarar daita

Byn wani lokacin su sulaiman suka cigaba da tallafawa ummi da DEENI a lokacin farida na dauke da tsohon ciki duk da itama ta dan jima bata haihuwa ba kuma har lokacin ummi bata san eruwarta tana cikin matsala ba sai byn data haihu lokacin ne ummi taga komai bbu alhalin ga tarin dukiya kmr zai kashe habibu gashi yasake kara wani sabon auren matansa sun cike hudu cif
ummi tayi kuka kmr may gashi tana cikin danginsu da suke tamkar tsiya madauri daya
ba daman tace zata dauki wani mataki akan haka
dan tasan yadda kansu yake a hade
dan haka taci kukanta takoshi ita da er uwarta ahankali take furta kalmar shiyasa tun farko naki amincewa da auren nan naki da habibu ba dan komai ba sai dan irin haka Amman kika nace ga irin abinda nake gudar miki kennan Amman kika kiji sai kuma ta tsagaita da kukanta ahankali tace ba yadda zamuyi da ikon Allah sannan ga rabo a tsakani
Amman duk da haka sai da ummi tayi masa tatas saboda daman ita bawani sakar masa fuska take ba kuma yana shakkata
kullum ummi acan take wuni har ranar suna yarinya tace sunan mahaifiyarsu ummi wato muzeenat shima habibu yayi hakan ne saboda ya wanke kansa a wajen ummikuma yayi nasara domin hakan da yayi yasa ummi taji dadi Sosai aranta har ta dan rage jin zafinsa
sannan bakaramin kudi ummi takashewa bby ba haka ma ranar suna ummi Tayi rawar Gani sosai
byn anyi suna ne ummi tasamu habibu akan dan Allah ya dinga kula da farida dan ita kadai gareta bata da kowa duk fadin Nigeria sai ita idan ma bazai damu ba zata bashi Rabin dukiyarta yakara akan nashi da duk wani abinda yake so ita dai burinta kawai ya kular mata da eruwa yayi murmushi kawai hade da ce mata yaji

Byn wani lokacin farida ta kuma samun wani ciki wanda tun yana karami take fama da laulayi tun lokacin ummi tadawo da zeenat wajenta
a kwana a tashi bbu wuya a gurin Allah har cikin farida ya isa haihuwa gurin haihuwar ne taji jiki sosai
koda ta haifi yaron ma bbu rai sannan itama tace ga garinku
mutuwar ta shigi habibu matuka yayi kuka tamkar ransa zai fita dan shi kansa yasan yayi babbar rashin da ba zai taba maida irinsa ba
yayi rashin mata mai tsananin kirki da hakuri da sanin darajar miji Allah sarki ummi kusan har tafi habibu jin mutuwar tilon eruwarta ta
a wannan Lokacin ne rikon zeenat ya dawo dindindin gurin ummi ta dauki soyayyar duniya ta daurawa zeenat tana mugun ji da Yarinyar tamkar ranta kwata kwata bata son abinda zai rabata da zeenat Sannan kuma tana debe mata kewar eruwarta
lokacin shi DEENI na ss1 a NMS Nigeria military school dake zariya
yayinda DEENI Sam ba halinsu daya da ummi ba koda yaushe kagansa fuskar nan tasa a daure a cunkushi bbu wani faraa ga shegen miskilanci tsiya sai dai mugun kyakkyawa ne na karshe ajin farko wato first class gashi da maseefar iya sa kaya kallo daya zaka masa ya gigitaka kaji yashiga ranka farar daya saboda tsabar kyawunsa sai shegen shiga ran mutane domin kusan yanmata cikin estate din suna maseefar son sa yayinda yake girma kyawunsa na sake bayyana hade da miskilancinsa

Tunda zeenat ta dawo gidan magana bata taba hadasu ba ko gaisheshi Tayi baya amsawa in dai bayaga idanun ummi ba yana da matsanancin tsafta wanda kusan a wajen ummi yagada
Cikin haka ya kammala karatunsa na secondary school ya wuce NDA burinsa kennan nason zama cikakken soja itama ummi kuwa nasake karfafamasa gwiwa da bashi goyon baya yana karantar science ne wato likitan soja
bansan yadda zan kwatanta muka halinsa ba Amman yakasance mutun ne shi mai bambanci raayi
byn yakare karatunsa ya fito da mukami second lieutenant star biyu kennan

Zaune zeenat take a falo tana kallon wani serisfilm a zeeword my let home Tayi zurfi cikin kallon film din gabadaya attention dinta naga kallon ita kadai ce ummi tashiga cikin estate din yin barka taji karar Bell wanda shine kusan karo na hudu da taji ana dannawa cikin jin haushi ta mike dan bata son abinda zai dagata daga kallon datakeyi tana bude door din bata tsaya ganin kowaye ba ta juya abinta takoma mazauninta sallama taji hade da shigowa ta dago kanta kennan da niyar amsa sallama sai taga mutun tsaye kikam sanye da sabon kayansu na sojoji gabadaya zeenat ta gigice hade da rikicewa tsabar tsoro dan ita Allah yayita da maseefar jin tsoron soja take cikinta ya dauki kugi Amman still idanunta na kansa ta tsaresa da kallo
in ina tasoma yi wawa waalaiya dakatar daita da hannushi yana zabga mata wata uwar harara muryasa a kwasashe yace yau ne kika fara ganina da har zaki wani tsareni da idanu Kona canza miki ne da sauri tasoma girgiza masa kai Kai tsaye dakin ummi ya nufa tunda bai ganta a parlour ba yasan tana dakinta tana kallonsa ta kasa dauke idanunta daga garesa har sanda ya dawo fuskar nan tasa a hade yace kedan iskanci kina kallon mutune bazaki iya cewa ummi bata nan ba kin wani tsare mutun da idanuwa tamkar na maciji dayake bawani manyan idanu gareta da sauri bakinta na rawa tace dan Allah kayi hakuri mantawa nayi ko kallonta bai sake yi ba yaja tsarki yayi hanyar dakinsa ta tabe baki hade dacewa jarababbe kawai ai yadawo kennan itama taja tsaki ta juya tacigaba da kallonta

MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI

 

Aysha A bagudo

 

Page 34

Sai da tagama kallonta tsab Sannan ta canza Chennal hade da tashige kitchen dan daura abinci abincin dare
bakin kofar kitchen din ta dawo Tayi tsaye abunta tana cigaba da kallonta Chennal data canza ajima ajima tana zuwa tana duba abinda ta daura
Karar bell taji ba kaukautawa shiyasa da sauri taje ta bude gudun maseefar DEENi dan tasan muddin yana gida baya son yawan hayaniya yanzu ne zai gama daita Maryam tagani tsaye da wasu en school dinsu su biyu tuni murna yakama zeenat ta rungume su daya bayan daya tana musu sannu da zuwa hade da basu hanya suka shigo har cikin main parlour din hade da Sallamar su
waje ta nuna musu da hunnu kuzauna mana suka zauna ita kuma takoma kitchen ta duba abinda ta daura taga yayi ta kashe gas din sannan ta dawo inda tabarsu hade da kawo musu drunks mai tsanyi da snacks ta ajiye agabasun
gabadaya hayaniyya ce ta barke a atsakaninsu da murna ganin juna zeenat ta kalli su Sumy hade dayin kasa kasa da muryata tace kuyi magana ahankali fa sannan tace kun kyauta sai yau kuka ga damar zuwar mana Sumy tace ba gara mu ba muna zuwa time to time
kufa sai aikin sa rana kullum hira suka shiga
a inda Maryam ta dube zeenat tace wai nan fa IV suka kawo mana na birth din rukky zeenat ta zaro idanu waje I me Maryam tace IV
zeenat Tayi dariya hade da cewa uhmm badani ba kema kinsa sarai bazaa taba barinmu zuwa wani birthday party ba Sumy Tayi murmushi sannan tace ai sai da nagaya rukky Amman tace ga zance ga magana gashi nan ni ai nasan bazakuyi attending birthday party dinta ba da day itace sarkin shishigi da neman suna zeenat tace kmr kinsani duk abinda ya wuce cikin gidan nan namu ta girgiza kanta bazaa taba barinmu ba ki bata hakuri kawai Amman wlh har ga Allah naso zuwa ko dan rukky Sumy tace to why nut ku sace hanya kuje a boye batare da kowa yasani ba zeenat ta kalli Sumy fuskarta a hade tace kefa kin cika matsala fa wlh
kmr bada hausa nake miki magana ba
ta bude bakinta kennan da niyar sake balbale summy
sai ga DEENi ya sake fitowa parlour jikinsa sanye da jallabiya marun colour may maseefar kyau sai kyalli take zuwa ga kamshin turarensa mai mugun sanyi dadi wanda tun tasowar zeenat ta sanshi da auren Hamilton har yanzu fuskarsa a daure take tam kmr koda yaushe take ta hadiye maganarta batare da tasan Tayi hakan ba ta zuba masa idanu tana kallon kwayar idanunshi sai data ya hararata sannan ta dauke idanunta ta maida kallonta da hankalinta kacukam a kansu Sumy dake zaune surusuru Yayinda gabadaya Maryam duk ta fisu tsurewa ko dan ita Yar gidan ce oho
cikin wata irin murya mai sanyi dadi tamkar ba soja ba yace keta juyo ta ahankali ta sake zuba masa idanunta dan tasan dai daita yake dan haka tabada duk attention dinta garesa
bakisan kibawa mutun abinci bane Dan iskanci sai an roka zatayi magana ya katseta a fusace ai ba tun yanzu nasan ke muguwar rowa ce dake ba Tayi surusuru da idanu da sauri tace kayi hakuri dan Allah nayi zaton ko kana azumi ne naga kullum kana yi
yace oh dama kinsa min ido ne har kinsa cewa azumi nake kullum
Jikin Maryam har rawa yake a hankali tace wayoo Allah ashe ya dawo bari in gudu tun bai gama daita ya da kanmu ba zeenat tayi shr har sanda ya sake maimaita tambayarsa hade da cewa dan ubanki bada ke nake ba kike bina da idanu kmr zaki cinyeni ta sake girgiza masa kai Tana bashi hakuri
marowaciyace banza kawai mai mugun gado shiru yayi na dan wani lokaci hade da sauke numfashi
Sannan can kuma yace ai idan bakiyi rowa ba sai Allah ya tambayeki km bazaasan keYar uncle Habib bace
kin taba ganin barewa Tayi gudu danta yakasa rarrafe zeenat ta sake girgiza kai da sauri yace OK ashe dai kema kinsa gaskiya dole kiyi gadon rowa
Ganin haka yasa su sumy suka nemi sulalewa duk yana kallonsu sai daya ga Maryam na shirin gudu itama dan har summy ta daura hannuta kan handle din kofar ya dakatar dasu da hannusa sannan yacigaba duban zeenat yace barikiji da kyau yana mai nuna da yatsansa nan ba gidan marowata bane gidan masu bayarwa ne aci yace menace Da sauri tace gidan masu bayarwa ne
yace gud daga yau bama ni ba ko wani ki kaga yazo gidan nan ki bashi ruwa da abinci yaci dan ba naki bane
ya sake jiho mata wata tambayar yace ko abincin naki ne da sauri ta girgiza masa kai dan gabadaya ta sure ta kasa kwakwaran motsi sai ajiye zuciya kawai take yi yace baki da baki ne kike kadawa mutane kai tace naji kayi hakuri dan Allah Sannan ya juya kan Maryam da kadan ya rage ta fashe da kuka ya zuba musu ritattun idanunsa da suka fi kama da mage masu saurin raunana mutun kai tsaye yace ku kuma en iskanci banza kun wani cikawa mutane kunne da hayaniya tamkar kuna club kallo daya yayi musu kowace tabawa kafarta iska yaja tsaki ya juya ya nufi dakinsa

ahankali zeenat take sauke ajiyar zuciya hade da dafe kirjinta batasan meyasa ba idan har Yaya DEENI yana guri Sam bata samun cikakkiyar natsuwa sai tarinka ganin duk yacika guri ga tsananin tsoransa da take ji yana mamaye zuciyarta Maryam har da kuka tayi byn sun fita dan daman can ita haka take shegen tsoro gareta aiko su sumy suka ce mezasu ba dariya ba dariya suka dinga yi har da rike ciki suna nuna ta aiko tace yau sai da suyi ta zama a estate din dan bazata rakasu gun securities ba sai da sukayi ta bata hakuri sannan suka jera suna hirar abunda ya faru

Ko lokacin da ummi tadawo tuni murna da farinciki Ganin tilon dan nata yamamayeta zuciyarta nan suka zauna a parlour suna hira cikin hirar ne ummi take masa maganar aure in da tace masa yakamata yanemi mata yayi aure kasan shekararka nawa kuwa yanzu yayi murmushi ai dole nasan shekaruna muke nan kullum cikin rubuta date of birth talatin da biyu ne kawai fa ummi Tayi dariya 32 din ne kawai kusan duk saannin haihuwar ka duk sunyi aure acikin estate din nan gasu yasir nan ma duk ansa musu rana dan haka kaima ka fidda mata kafin azumi DEENI yazaro idannu yana bin ummi da kallo a shagwabe yace haba first love dan sunan da yake kiranta dashi kennan tun tasowarsa ni din guda nawa nake da zakice inyi wani aure yanzu Dan Allah kiyi hakuri my first lov zuwa wani lokaci duk hirar da suke zeenat na zaune tana jinsu haka kawai taji gabanta na faduwa lokacin da taji abinda ummi tace Amma jin amsar da yaya DEENI yabata yasa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta
kmr ance ya dago idanunsa suka sauka cikin nata harararta yayi yace kallon fa kin wani tsare mutun da idanu ummi tace uhmm kafa dawo kennan karka takuramin yarinya
ya langwabar da kansa yana maida idanunsa kan ummi cikin sanyi murya yace haba first lov baki ga irin kallon da take bin mutune dashi bane kmr bata san mutun ba ummi tace kai da wani idanu ka kalleta har kasan tana kallonka kuma ma ni banga komai ba kai dai ta kurace kawai dakai indai kana gida baka barin yarinya nan ta huta ta sarara ya dubi ummi ya tabe baki Sannan yace kekawo min coffee ta mike taje ta hado coffee din takawo masa gabanta na wani irin faduwa ta durkusa har kasa ta ajiye masa

Adaidai wannan lokacin ne zeenat ta kammala karatunta na secondary school ta fito da sakamakon mai kyau domin tasamu almost 7 credit masu kyau
shi kansa DEENI yaji dadi Sosai sanda ummi ta nuna masa Amman dayake miskili ne sai cewa yayi Sam shi bai ga wani kokari da Tayi ba tunda bata cinye duka ba
ummi Tayi murmushin tace kai ne dai bakaga kokarin ta ba Amman ni nagani km nasan Tayi kokarin Sosai
Ina laifi duk cikin wayanda suka rubuta jarabawa tare bbu wanda yakaita marks
yace ok inda ta cinye duka ne zan iya cewa Tayi kokarin ai wayanda suke cinye 9 credit ba finta brain sukayi ba
Ita dai wasa da kallace kallacen banza tasa a gaba
ummi ta hade fuska tana harararsa yacigaba da zagin zeenat ganin yadda ummi Ta canza fuska ne yasa yabar maganar ummi ta sake duba result din tana shafawa hade da kwallawa zeenat data tashi tun sanda taji DEENi yasoma zaginta kira takaraso tazo ta tsaya kusa da ummi DEENi ya dauki wayarsa yana daddannawa ba ko kalli inda take ba ummi ta mika mata slip din tana murmushin tace kinyi kokari sosai zeenat ta karba ta juya ta bar gurin dan bazata iya zama a duk inda yake ba
ummi ta dubi DEENI tace yanzu kuma sai aure zanwa zanwa yarinyata
DEENI ya juyo a sukwane yace wani irin aure kuma first lov da rana tsaka kudai Bari yarinya tacigaba da karatu kawai dan yanzu kai yawaye an daina irin wannan auren ballanantana mata marasa illimi ummi ta dubesa da kyau ta numfasa Sannan tace ni tawa iya secondary zan aurar daita dan ma taki sauraran masu sonta itama shegen iyayi ne daita kuma dai kasan matan wannan family din basa wuce secondary ake musu aure
kuma kasan bazaa fara karatun jamia daga kanta ba uhm nima nafi son na aurar da abita DEENI ya tabe baki Sannan yace Allah ya kyauta ni ko zanyi aure bazan auren Yar secondary ba wlh sai wacce tagama jamia mai tarin illimi kuma ba auren family zanyi ba dan baya birgeni yakarasa maganar yana dan murmushi ummi tace to Allah yabaka saa amman ni tawa aure zan mata da wuri
kai kasan halin big dady bazai taba barinka kayi aure a waje ba
Wlh nasoma a hada aurenka dana su yasir yace uhmmmm su dai yi nasu ni sai nan gaba

A wata yammacin DEENI zaune akan dadduma awajen shakatawa shi da abokansa wayanda duk kusan family ne zagaye dashi gefe guda kuma flasks ne cike da ruwan zafi da kananan cups hira suke sosai atsakaninsu Amman banda DEENI dan gabadaya daukar hirar tasu yake shirme dan duk zance nasu akan maganar aurene wanda shi kuma Sam baya kaunar ji dan haka ya sharesu yacigaba da lasalasar wayarsa ya yinda ya kai hannunsa daya ya dauki cup din coffee wanda orready fk ya tsiyaya masa ya kai bakinsa yasha hade da rufe rikitattun idanunshi wanda yazame masa jiki fk ya kalli yasir da faysal dake tawowa inda suke ya kwashe da dariya har suka karaso bai bar musu dariya ba fk yace sannuku da karasowa Mayan angwane kunsha kamshin kunsha kamshin faysal yace kai dai anyi dan iskan yaro kai baka tsaya ruwan ido ba kana biyewa wannan ya nuna DEENI da yatsa fk yayi murmushi yace yayi an gwanen bana wannan karon gabadaya suka dara hannu suka bawa juna suka gaigaisa har DEENI
yasir ya dube fk yace ai gara muyi aurenmu tunda muna son juna kai ka zauna kar kayi har mahdi ya bayyana fk yace Aa nifa bance saboda me zakuyi aurenku ba Amman gaskiya zaku takura kanku ne kawai yanzu da wani aure wayannan kananan bbys din
DEENI ya tabe baki Sannan ya dube fk yace shiyasa rawar kan yaran ke kara yawa ba dukkansu suka sa dariya suna cikin dariyar ne fk har da rike ciki sai gasu zeenat da suka taso daga islamiyya su biyar suka jero kowace sanye da hijab dinta raudat da shemah da samiha da Maryam sai zeenat dake tsakiyar su dukkansu kyawawane
da hannut fk yake nuna musu inda suke Sannan ya dakata dariyarsa ya kalli inda DEENi ke zaune tamkar bai san abinda ake ciki ba ko kallon inda suke bai yi ba yacigaba daddannawa da sarrafa wayarsa
fk yace kai gaskiya bbys din nan fa su hadu dayawa fa nima ko zan dan shiga daga ciki ne
yasir yace dako ka huta kabar wannan ya nuna DEENi fk ya cigaba Aa ina ai bazan barsa ba tare zamuyi namu auren ko yakace mutumina kaga Shikenan mun huta da surutu jamaa DEENi ya kallesa a kaikaice yace Aa ku dai da kuka ji zaku iya kuje kuyi Tayi
Amman ni ya nuna kansa da yatsansa hade da tabe baki ba yanzu ba har sanda su zeenat suka zo suka wuce Suna hirarsu suna dariya Maryam ce ke basu labarin abinda ya faru jiya bbu wanda bai dara ba har ita zeenat din raudat tacewa zeenat ai ke kika daukar masa wlh kuma yarinka yi miki kennan ina ma nice daya gane kuresan suka sake yin dariya

Tun lokacin daya dawo zance sa da ummi bai wuce DEENI kayi aure fito da mata cikin yanuwanka kayi aure hirar kennan sai dai idan basu zauna ba

Yau takama walimarsu zeenat ta saukar alqurani mai girma wanda aka shirya musu anan islamiyyarsu dake cikin estate din su kusan goma anyi taro walima lfy yayinda zeenat ta karbi kyaututtuka da dama saboda kokarinta har kuka ummi Tayi sakamakon tunowa datayi da eruwarta taro ya watse lfy kowa yakama gabansa byn sun gama hirarsu da ya zame musu jiki suka fara hada kujerun da akayi walimar dasu sun fito kennan suka ga Yaya DEENI da wani abokinsa zaune akan kujera biyu suna hira take suka ja birki samiha tacewa zeenat jeki amso wadan can kujerun cikin zolaya tayi mata maganar dan tasan yadda take jin tsoronsa zeenat tace uhmmmm ku dai kuje suka sa mata dariya ke wlh muguwar matsoraciyace wlh ki rage tsoransa shiyasa yabi duk ya renaki Tayi sororo tana kallonsu Sannan tace to bari naje amso Tayi tafiya kmr zata isa gurinsa sai kuna ta juyo da sauri aiko suka sake kwashe mata da dariya
muryashi ce ta katse musu dariyar tasu lokacin daya suke kallonsa a frigice yayinda gaban zeenat yasoma faduwa yace keda hannu ya nuna musu alamun suzo s suka nufo inda
Yake cike da tsoro ya zuba musu rikitattun idanunsa yana kallonsu daya byn daya yana nazarinsu Sannan yace da ganinku akwai alamun rashin gaskiya atare daku ya nuna su da dan yatsansa zeenat Tayi saurin cewa Aa cikin inda inda uhm bbu komai fa Tayi gudun Kar wata cikinsu tafada masa shiyasa Tayi saurin yin magana to menene na inda inda wama ya tambayeki Tayi shiru tamkar ruwa yacinyeta Sannan ya juya ya kalli abokin nasa da ya zubawa zeenat idanu yana kallonta kafarsa yasa ya take kafar manir dashi sannan ya dawo natsuwarsa ya mai da hankalinsa kan DEENi DEENi ya nuna su zeenat da samiha hade da shemah da Maryam yace gasu nan bansa inda sauran suka nufa ba manir yace ina tayaku murna walima saukar alqurani mai girma Allah yasa na tsoron Allah ne suka hada baki wajen cewa Ameen kallonsu kawai DEENi yayi jikinsu har rawa yake suka bar wajen
manir yabi bayansu da kallo yace kai sisters din nan naka fa akwai kyau DEENi ya kallesa yana watsa masa harara ok iskancin naka kuma yau agidanmu zai Kare
manir yayi murmushi yace Allah barin ma wace ta tsakiyarsu gaskiya duk tafiso haduwa DEENi ya kalli inda ya nuna sai yaga zeenat yake nufi take yaja tsaki manir yace dama ita ka zaba wlh dan nasan karshe ma auren zumunci zaa maka DEENi ya sake jan tsaki dan Allah malam karka dameni da wannan shirme bazan manir bai daddara ba ya sake cewa Allah dama tsayawa kayi akayi Yar gida tunda duk tarin matan dake sonka baka kallonsu a fusace DEENi yayi magana dan me zan kallesu alhalin banda abinyi dasu
manir yayi murmushi ina ma ni ne kai wlh tsayawa zanyi na kwashi gara son raina har sai nagaji in more kuriciyata DEENi yace ai kai dan iskanci ne lamba daya wlh ka guji abinda kakewa yayan mutane ko dan gaba
ka dauki neman mata tamkar wani abinci manir ya dan daki kafadar DEENi yace ai sun fi abinci dadi
Amman Allah koni ina son na daina bin matan bazan wlh abun ne da kmr wuya Amma kacigaba da yimin addua DEENi ya nuna sa kai zanwa addua saboda banda abinda zan roka Allah manir ya dage masa gira daya yes meye dan kamin addua kaga idan Allah ya shiryani sai kabani wacce Yar dimadimar sister din taka na aura bai kulasa ba sai canza zance da yayi nan dai suka cigaba da hirarsu har zuwa sanda sukayi sallama da juna

Abinda zai daure maka kai bai wuce yadda ummi ke sake bawa zeenat kulawa ta musamman ba ta kowani part tana iya kokarin ganin ta fito da diyarta ta tsab zeenat bata rasa komai ba tun daga dangin sutura da mayuka shafe masu tsada zuwa kayan kwalliya ana cikin haka tafiya takama ummi zuwa India dan haka ta tasa diyarta gaba suka tafi zeenat taji dadin zuwansu India tamkar karta dawo watan su daya suka tattaro suka diro Nigeria saboda bikin family dinsu yakusa koda ta dawo ma su Maryam sun dinka mata duk anco din da aka fidda tunda damar suna da telarsu ce da yake zuwa har gida ya karba dinki
biki akayi sosai bakama hannu yaro an kashe kudi tamkar baasan ciwonsu ba bidia iri kuma a duk anan cikin estate din akayi komai daga karshe akayi walima washegari ranar Sunday aka daura auren en mata biyar haka ma samarin aka dan kowace gidan mijinta ya saura mutun uku ne cal suka rage da basu aure ba Maryam da shemah sai zeena amaza kuma fk da DEENi sai kamil

 

MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI

 

 

Aysha A bagudo

 

Page 56

 

Zeenat na da kyau sai dai ba can ba fara ce Sol Amman batada dagon hanci wannan bai sa fuskarta muni ba haka idanunta matsakaita ne ita mutun ce mai tsananin son kwalliya wanda ko alwala Tayi sai ta sake yin wata sabuwar kwalliya haka nan ummi bata gajiya da siya mata kayan kwalliya iri iri sannan bata ganin aibunta a duk lokacin da zata bata a gurin yin kwalliyar
abinda kawai bata so kuma bata yarda dashi ba shine a yimata dinkin da zai bayyana surar jikinta nan nefa tace bazata bada goyon baya gurin bata kamasho yada zina ba dan a cewarta shigar da yawancin enamata keyi a wannan zamani itace ke sake haifar da fashadi a doron kasa
zeenat akwaita da saurin sabo da mutane sannan km tana da son kawaye ita da Maryam dan ko yanzu suka san mutun ko km kuka hadu dasu sanadin wata kawar Shikenan sun zama kawaye shiyasa suka fi dukkan sauran enuwansu jamaa dan daga waje ma zuwa ake gurinsu sabanin sauran kullum kaga ana rikinci a bakin get da sune gurin shigo da baki most especially ma na school dinsu abinda ummi tafi tsana kennan daga gareta yawan tara kawaye gata da matukar son gayu da son kallace kallacen film muddin tana gida kuwa bata da aikin yi sai na kallo daga wannan Chennal zuwa wata sai dai duk da wannan halin nata Allah yabata illimi sosai both arabic school

Daidai misali Allah yayi mata farin jinin samari masu sonta daga waje ma biyota akeyi sai dai bata fita dan ma ummi taki yarda tafara zance da wuri sai data kai ss2 kuma duk masu zuwa gurinta da aure suke sonta amman matsalar dai daya ce family dinsu basa yarda da macce Tayi auren wajen Amman sukan bar namiji
kana duk masu son nata bataji son su har cikin ranta har wani lokacin ummi kesata gaba da fada tace maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kirasa kowa kizo kina nema yawan yi mata fadan da ummi keyi ne yasa ta tsaida kamil dan gwaggonta yayar mahaifinta da suke uwa guda uba guda
shima bakowa yasan suna tare dashi ba dan bata gama tantancewa aurensa ba kuma shi bai fiyye zama a garin ba yana aiki ne a abuja haka kawai taji idan bata samu wanda yafi ba zata iya aurensa dan shima ba laifi

Jiki da jini wata safiya ummi ta tashi da ciwon ciki wasa wasa tun tana daurewa har abun yafi karfinta gabadaya tafita haiyacinta hankalin zeenat yayi mugun tashi dan bazata manta yawan labarin da ummi ke yawan bata na mahaifiyarta da irin wahalar da batasha kafin mutuwarta ciki har da cewa mata Tayi ta bude ido ta zabi miji wanda zai san mutuncinta kar taje gurin ruwan idonta ta kwashi gaibu shiyasa take massefar jin tsoron haihuwa da mutuwa dan ta kudircewa ranta ta amince da mutuwa tunda tasan muddin kwanakinta suka Kare Shikenan amman ita kam bazata yarda da haihuwa ba ganinta garata tasha wahala daya
wunin ranar da ciwo ummi ta wuni can kuma tasamu sauki dare nayi ciwo ya sake dawo zeenat taso zuwa ta sanar da DEENi Amman ummi taki
washegari DEENi yashigo da shirin fita aiki dan bai san bata da lafiya ba koda yashigo dakin yayi matukar girgiza da ganinta kwance cikin bargo da kyar take iya magana a rude yakaraso inda take ya tambayar ba lafiya ne Ummi tace eh tun jiya yace meyasa baki sa an tashe ni ba ya kalli inda zeenat ke rukube kusa da ummi duk tazama wata kalar tausayi
keWace irin sakariyace da baza ki iya zuwa kisanar min ba da kyar ummi ta iya bude baki tace ni na hanata ya furzar da huci ta bakinsa hade da cire hular kansa yayi wurgi dashi gefe take ya Ciro waya cikin aljihun bayan wandonsa yakira family doctor dinsu wanda side dinsu kawai yake dubawa
mintina kadan sai gashi likinta dayake bai da Nisa dasu cikin sauri yashiga duba ummi sosai har drip aka sawa ummi a ranar DEENi kasa fita yayi koina byn likinta ya wuce ne ya kirasu ya Mahmoud ya sanar masu da ummi fa ba lfy idanunta ta zuba mashi tana kallon bakinsa yadda yake maganar ne tamkar wata mace shi yafi daukar hankalinta
ba taba jin DEENi ya birgeta ba irin na yau
duk wunin ranar kusan shi yayiwa ummi komai hatta magani da abinci a baki yabata sai gurin laasar su Yaya Mahmood sukazo tare da matansu sai zuwansu ne ma yasa mutane cikin estate din suka sani dan DEENi bai sanar da kowa ba shi dai ta mahaifiyarsa kawai yake
Ai kafin kace me tuni side din ummi yacika da jamaa haka suka dinga shigowa duba ummi har dare DEENi na tare da ummi yana bata kulawa duk yayi wani iri cikin lokaci kadan yafita haiyacinsa zeenat na zaune a gefe guda tana jiyo hirarsu rokonsa ummi take akan yayi aure ahankali takira sunansa NASURULDEEN abinda yasake tada ma DEENi hankali kennan yaushe rabon dayaji ummi takira complete name dinsa tacigaba ban rasa komai na rayuwar duniya ba inada tarin dukiya da kadaroro wanda ni kaina basan iyakarsu ba burina da muradina ahalin yanzu bai wuce inga aurenka ba Amman na fuskanci kafi son sai na mutu sannan zakayi aure Jikin DEENi ya dauki rawa hankalinsa ya sake tashi matuka ta sake kiransa cikin tattausar muryar hade da rarrashi DEENi banida kowa daga kai sai zeenat sai kuma dan uwana wanda yake wata uwa duniya idan bakayi aure ka taramin jikoki masu albarka ba mezakayi min naji dadi ina ji ajikina sai na mutu zakayi aure a rude yace first lov ki daina cewa haka zanyi inshallahu kina raye Tayi murmushin karfin hali tace kullun haka kake cewa ni tuni na fidda raina ka tashi katafi Allah ya maka albarka Amman yarinyar nan zeenat na rokeka dan Allah ko ban tashi ba kada kabari ta koma hannun mahaifinta na damka amanarta a hannunka bata da kowa duk duniyar nan daga ni sai kai karikemin ita a hannunka har zuwa lokacin da zata samu miji DEENi yakamo tafin hannun ummi cikin nasa ahankali yasoma magana muryasa cike da rauni da fargaba yace haba first lov ki daina maganar mutuwa nan kece zaki aurar daita da hannuki kuma kina raye inshallahu ta girgiza kai ita kadai tasan abinda take ji cikin muryarta irinta marasa lfy tace Shikenan tashi kaje ka kwanta hankalinsa a tashe ya fice daga dakin
zeenat ta mike daga inda take idanunta na zubda hawaye ta taimaka mata suka kwanta tana kuka kasa kasa ummi tace lfy zeenat ummi ummi cikin sheshekar kuka tace banason naji kina cewa zaki mutu kibarni dan Allah ummi tace nafa da kar na fada mutuwa ta zamemin dole sai dai idan ajalina bai zo ba zeenat ta saki kuka hade da kamkameta ummi a jikinta tacigaba da kuka mai cin rai hade da cewa ummi bazaki mutu ba inshallahu da kanki zaki aurar dani ni ga duk wanda kike so da kyar bacci ya dauketa yayinda ummi Tayi nisa a bacci.

Hero Hausa Novel by Maman Teddy

Shi kuwa DEENi tunda ya koma dakinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zariya yake daga farkon dakin zuwa karshe kafin daga baya ya nemi gurin ya zauna
yayi tagumi da duka hannuwansa yayi zurfi cikin tunanin yadda zai yi lallai ya zama dole ya nemo mata domin cikawa umminsa burinta sai dai shi matsalar sa bai san ta ina zai fara ba Bai taba yin buduwar ba ballanantana wata aba soyayya shi duk a tunaninsa raini hakan zai jawo masa idan yaje yace yana son budurwar
ya kamo gefen lips dinsa ya dan cizawa a hankali har daga karshe ya yanke shawara zai nemi fk da zance anan ya sulale ya kwanta rigingine idanunsa na kallon celling dakin
yayinda ya rungume hannushi a saman kirjinsa yana aiyana irin type din maccen dayake son ta mallakesakuma wacce ya dace ya aura cikin sanyi ya runtse idanunsa gam take yasoma zaiyano irin type dinsa kyakkyawa dogowa mai dirin jiki choculate colour mai dara daran idanu sannan educated mai wushiryar haka dai ya rinka yi har dare ya sula bai samu wani ishashen bacci ba koda asuba kafin ya tafi masallaci sai da ya fara shiga Bedroom din ummi ya sameta tana sallah ya sauke ajiyar zuciya sannan ya wuce ganinta tsaye tana sallah yasan Allah yakawo mata sauki

A masallaci DEENi suka hadu da fk byn an idar da sallah yajashi gefe guda da idanu fk yake binsa da kallo abinda bai taba faruwa ba saboda DEENi daya idar da sallah yayi yan adduoinsa yake wuce wa gida
fk ya dube sa da kyau yana nazarinsa kafin daga baya yace lfy kuwa naganka haka Gabadaya fk yagama tsurewa da ganin yanayinsa sai da ya sake maimaita tambayarsa sannan DEENi yace ina fa lfy jiya ummi kwana Tayi ba lfy har tana barmin wasiya burinta da muradinta yanzu bai wuce nayi aure ba
fk yayi shr yana jin DEENi har sanda yagama bayaninsa sannan yace baita kadai ba har big dady ma burinsa kennan dan ko jiya sai daya min maganar nida kai Amman tunda kai ummi ta damu ta tsananta gara kayi kawai kurabu lfy
DEENi yace ai bakasan inda zan nemi matar ba nifa gabadaya enmata family din nan basu min ba sannan kuma sun min kankanta da aure fk yace Aa bawani kankanta mace na kankanta da aure ne kaine dai kawai kake ganin haka ni yanzu na yanke shawarar zan tsaida shemah kawai tunda na dade ina sonta nida zakaji shawarata ma da zeenat ka aura DEENi ya mishi wani irin kallon bakada hankali sannan yaja tsaki yace haba dai zeenat fk yacigaba yarinyar akwai hankali wlh ba kmr wancan banzar ubannata ba dayake duk sun tsani halinsa
kaga kawai sai a hada bikinka da nawa kawai kaga zeenat batada matsalar km ko bakomai ummi zata ji dadin Sosai da wannan hadin
DEENi yace Amma ban taba jin koda alamar digon sonta ba kuma ni gaskiya ina ganin tamin yarinta dayawa duk fa shekarunta sha tara zuwa sha ashirin ne fa nafison mutual girl wace ta mallaki hankalin kanta tasan yadda zata kula dani akan bed amman wannan Yar bbyn maimakon ta kula dani ni ne zan koma renonta
fk ya dubesa a kaikaice yace lallai yaran zamanin da kasani Amman banda na yanzu sai su maka abinda manyan matan baza su iya ba kana rai nata ne kawai sai kaga mararta ta daukeka tsab DEENi yaja tsarki kai ban son iskanci shawara nake so ba wani shirme ka can na bazan ba
fk ya kada kafada yace well tunda kaga bata maka ba kana iya duba wasu acikin gari
DEENi ya kalleshi yana watsamasa harara kaifa dan iskane dan kaga nazo maka da maganata shine zaka rainawa kanka hankali sai kuma yayi kasa kasa da murya yace kasan Allah ni fa ko a waje ba wai ina kallon mata bane fk yace to katsaya akan zeenat din kawai duk inda ake neman macce mai natsuwa yarinyar nan takai DEENi ya sake jan tsaki yace ai inda takaicin yake kennan sai kuma nakirata ince ina sonta ya fada yana tabe baki hade jin takaici da haushin shawarar da fk yakawo masa fk yace inda bazaka iya ba kabi ta sama maana kasamu big dady da maganar kawai kasanar dashi kana sonta nasan zai ji dadi Sosai
DEENi ya sake watsamasa wata harara yace dan Allah malam ka dameni ina ganin fa kmr kafara samun tabin hankali wa yace dakai ina sonta zan dai yi aure badan ina so ba ya juya yabar fk nan tsaye yana binsa da kallon mamaki sannan kuma yace ai kaine babban mahaukacin dan iskan kawai sai iskanci fall ciki shi bai ga laifinsa da yace bazata ya saukarsa a bed sai nawa sai kuma ya kwashe da dariya

 

MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI

AYSHA A BAGUDO

Page 78

Har DEENi yazo gida tunanin yake akan shawarar da fk ya bashi anya kuwa zai iya amince da auren zeenat
Lokacin da yashigo yayi daidai da zeenat ta tabare magani tana mikawa ummi ta amsa ta apa zeenat ta Mika mata ruwa yayinda shi km yake tsaye jingine da jikin kofa rungume da hannuwansa duka a kirjinsa yana kallonsu take zuciyarsa ta dinga ingizashi akan lallai bbu wace ta dace ya aura sama da zeenat bisa ga hujarsa tacewa bazai taba samun matsala daita gurin kula da mahaifinsa saboda irin soyayyar dake tsakaninsu
yasan ko yana nan ko baya nan zata kula daita umminsa zata zamo a karkashin kukawarta tunda zeenat bata da wata uwar da wuce ummi tunaninsa ya katse lokacin da ummi takira sunansa tace son karaso mana yayi frigigit ya dawo natsuwarsa ahankali yashiga takowa har inda ummi take ya zauna zeenat ta gaidashi ta mike zata fice daga dakin bai amsa mata gaisuwar data masa sai dai yabi bayanta da kallo ummi ta kalleshi ta kauda kanta yace first lov yajikin naki ummi ta danyi murmushi hade daura hannuta kan sumar kansa tace naji sauki sosai ahankali sauke ajiyar zuciya ko bai ce komai ummi ta fahimci yaji dadin yadda yaganta yana nan zaune Sam yakasa yiwa ummi zance yana ya auren zeenat din daga karshe ma tunani yayi kawai gara yasamu ya mahamud da zance dan gaskiya kunya yake ji yayiwa ummi maganar da kansa

Da yammacin ranar byn ya dawo daga office yaje har gida yasamu ya mahamud da maganar ya ji dadi kwarai da gaske har yarasa inda zai sa DEENi dan farinciki dan shima da kansa ya matsu yaga DEENi ya ajiye iyali kmr kowani magidanci yace Shikenan sai kasamu yarinyar da zance ku daidaita kanku DEENi yace Aa ina ganin basai na sameta ba in dai first lov ta amince ai Shikenan
yaya mahamud yace ummi bazata taki ba Amman dai kasan kaidar auren gidanmu kennan bbu dole a ciki muddin kuka daidaita kanku na iyayenmu may sauki ne idan Kuma ita ummi ta amince ita yarinyar tace bata sonka fa DEENi yaji haushi da takaici sunkamasa alokaci guda yace ai nima ba wai ina sonta bane kawai dai zan aureta ne
Yaya mahamud yace shirme bazan kennan kai yanzu idan anzo meeting cewa zakayi basonta kake yi ba zadai ka aureta ne DEENi yayi murmushin gefen baki har dimple dinsa ya lotsa sannan yace cewa kurum zanyi ina son zan aure zeenat ne Yaya mahamud yace to Allah ya mana zabi na alkhari kabari zanje gurin ummi tukun duk yadda mukayi daita zakaji DEENi yace Shikenan ya mike fice a office ma koda yaje aikinsa kawai yasa gaba
dan shi gabadaya ya manta da wani zance aure can

Mahamud yasamu ummi cike da karfin gwiwa ganinsa ba wanda zai kai ummi murna tunda daman burinta kennan naganin auren DEENi Amman ga mamakinsa yana gama labarta mata abinda yakawo shi sai yaga ummi tayi kicin kicni da ranta tamkar bata taba sanin wani abu farinciki ba sai da gaban Yaya mahamud ya fadi dan ganin yadda ummi tayi da fuska tamkar yazo mata da zance mugun abu tace kai ne kaga sun dace kaba shi shawara ya nemi aurenta ko Kuma shi da kansa ya sameka da zance
Da sauri yaya mahamud yace Aa shine dai yazo min da zance ummi ta sake daure fuska sannan tace ka koma ka fada masa ban amince ba kace masa akwai sauran mata a gidan nan yana da damar zabar duk wacce tayi masa idan ma ya canza raayinsa nakin auren family to yaje waje ya nemi matarsa can itama Allah zai bata nata mijin Amman Sam ni ban yarda da wannan hadin ba tayi shiru na wani lokacin kana zubawa Mahmud idanunta tana kallon yanayin daya shiga ahankali ta numfasa sannan tace kana iya wucewa idan kana da abinyi ka manta da wannan shirme na DEENi
Yaya mahamud yayi kasa da kansa Sosai cikin muryasa can kasa kasa da alamun km rarrashi yace dan Allah ummi ki amince da auren nan bazan iya tunkarar DEENi da maganar ba
duk da bansa dalilinki nakin amincewa ba ummi ta dan saki fuskanta ba kmr dazu ba tana mugun son mahamud tamkar dan da ta haifa acikinta tana jinsa har cikin zuciyarta

tace bawai ina kin hadin bane duk duniya idan akwai wanda zai so auren DEENi da zeenat a bayana yake na farko dai kaima kasan halin DEENi da dan bazar zuciya ga saurin fushi ga maseefar miskilanci tsiya ga jin kai sannan da bakinsa yasha gayamin cewar shi bazai taba yin auren family ba sannan shi mai digiri yake so ya aura shine km yanzu zai zowa mutane da wani salo
ni da tawa iya secondary kadai ta tsaya ai kai da jin zancensa ma kasan akwai wani makirci daya shirya dan nace yayi aure ai bance lallai sai ya aure tawa yarinyar ba Muhamud yace ummi ki duba lamarin abun tunda shi da kansa ya furta cewa ita ta masa ba zaa samu wata matsala ba
ummi tace Sam bata yarda da wannan tsarin ba ita dai yaje gaba ya nema hakurin duniya nan bbu wanda yaya Muhamud bai bawa ummi ba amman taki amincewa duk ta inda ya bullo mata sai itama tabiyo masa ta wata hanyar har ran yaya mahamud yasoma baci yaji haushin abinda ummi tayi dan haka ya hakura ya fice ransa abace

DEENi zaune a office dinsa ya dukufa wajen tura sakwanni a yanar gizo hankalinsa kwance yake bin komai daki daki yaji daya daga cikin wayoyinsa daya ta dauki karar sauti mai dadi ya dauke idanunsa daga kallon system din yasa hannu ya dauki wayar yana dubawa ganin sunan dake yawo akan screen din ne yasa yayi sauri dagawa yakara a kunnenshi hade da yin sallama kana ina muryar Yaya mahamud yaji ta daki dodon kunnenshi cikin sanyi murya DEENi yace ina office yace ok idan katashi kabiyo inason ganinka sannan ya kashe wayar

DEENi zaune a gaban Yaya mahamud kansa sunkuye a kasa yayinda idanunshi ke kallon zarazaran yatsun kafafunsa yana sauraron sakonshi da ummi tabayar a sanar dashi
a gurin Yaya mahamud sam bai tsammaci jin haka daga umminsa ba ga mamakin Yaya mahamud sai yaji deeni yace Shikenan babu komai Allah yasa haka shine mafi alkhari
ya mahamud yace ka hakura kennan Nashi ganin bazai damu dan ummi ta hanashi auren zeenat dan haka Yace eh tunda daman ba wai yana sonta bane nan dai suka bar zance aure suka shiga wata hirar daban a inda Yaya mahamud ya tashi yaje ya kwaso wasu takardu da file files ya zubesu nan a gaban DEENi yace yasa masa hannu ciki kai tsaye DEENi ya zaro wani hadadden Biro daga gaban aljihun rigarsa yasoma cike gurraren da akeso yayi sign dan gabadaya dukiyar DEENi sulaiman da Muhamud ne akai su suke kula daita kuma komai na tafiya daidai domin dukkannisu abu guda ne a gurin ummi dan ma idan baagaya maka ba
zaka dauka duk ummi ce ta haife su

Sai da DEENi yagama sign din sannan yaya mahamud hada da mishi bayanin companies din da suke son budewa a kasar American sun turo musu da sako akan suna da bukatar mutun daya daga cikin masu company din yazo interview dan haka shi ya wakilta sulaiman yaje DEENi yayi murmushin yace Shikenan bbu komai duk yadda kukayi daidai ne Allah ya taimaka

To byn DEENi yakoma gida ya dingawa ummi wani irin kallon wanda shi kansa yakasa gane dalilin yin haka yana son yi mata magana Amman yayi shr yayinda zuciyarsa ke kwabarsa akan ya share kawai ai baita kadai bace mace a duniya daman ai dan ita yake son ya aure zeenat din da yaje waje ya aure wata wacce bai san halinta na boye ba ai gara zeenat din Amman tunda bata so shima ya hakura

Da misalin karfe goma na dare DEENi sanye da rigar wanka dan fitawarsa kennan daga bathroom ya tsaya gaban dress mirrow yana karewa jikinsa hade da zare rigar wanka dake jikinsa ya saura daga shi sai boxer yabi koina a jikinsa da turaren Hamilton 27 sai daya kammala da komai na aladarsa da yasaba yi kafin ya kwanta sannan ya hau kan royal bed din ya lumshe rikitattun idanunshi alamun yana son yayi bacci sai dai baccin yaki zuwa kawai ya tsinci kansa da tunanin zeenatya rinka jinta ajikinsa yadda yake jinta a halin yanzu bai tsammaci abin har ya zai haka ba
Sosai ya tsinci kansa cikin damuwa ko baya son yarinyar hakika ya tsananta da son aurenta yayi shr yana tambayar kansa abinda ummi take nufi da kin amincewa datayishi ya guji big dady da maganar a tunaninsa sai umminsa tafi kowa murna da jin dadi ya dauki tsawon lokacin kwance kafin bacci barawo yayi gaba dashi

Byn kwanaki DEENi yakasa hakuri da maganar zeenat din kmr yadda yaso shima ta share da zance kawai ya manta dasu
Amman yakasa ya samu ummi da kansa a wata safiya dayazo gaisheta byn yayi shirinsa na zuwa aiki cikin kakinsa dake kara masa kyau tamkar dan shi kadai akayi sai kamshin yake zubawa ta koina gashin kan nan nasa kwance luf luf luf dasu duk da bacika yawa sukayi ba saboda yanayin aiki Amman dayake Allah yayi mishi suma takoina ajikinsa ko yayi askin ma baya wani dadewa gashin zai sake fitowa sosai yayi kyau matuka ita kanta ummi satar kallonsa take har ya tagota ya sakar mata murmushi tace son kayi kyau sosai fa uniform din nan nakara maka kyau ya dage mata girarsa daya yace Allah first lov yace ai daman can nj may kyau ne sannan duk maccen datayi dacen samuna ta gama samun duniyarta sai dai ta nemi lahirarta kawai ummi tayi dariya sosai ya kamo hannun umminsa cikin nasa muryasa a shagwabe hade da dan karyar da wuyansa yace first lov da kanki ma kin yaba dani tace uhmm yabon gwani yazama dole yace to meyasa bazaki bani auren zeenat ba.

Auren Sirri Hausa Novel Download

Novel Title Auren Sirri Hausa Novel
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 1.1MB
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author Aisha Bagudo
File format TXT
Published date 24 – 06– 2023

 

Tags: littafin auren sirri hausa novel, auren sirri hausa novel page 1, auren sirri hausa novel page 2, auren sirri hausa novel page 75, auren sirri hausa novel page 90, auren sirri hausa novel page 76, auren sirri hausa novel page 129

 

DOWNLOAD

 

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Hausa Novels

To Top
× Chat Zamgist on WhatsApp