Barka da zuwa wannan shafin namu mai albarka inda muka kawo muku abubuwan dake karya azumi a musulunci
Abubuwan Dake Karya Azumi a Musulunci
Akwai abubuwa da dama wadanda kesa azumi ya karye, anma mafi yawancin mutane basu sansu ba kokuma suke wasa dasu.
Ka wasu daga cikin abubuwan dake karya azumi a musulunci kamar haka:
1. Rashin Yin Niyyar Ɗaukar Azumi.
Wanda Bai Ɗauki Niyyar Azumin Sa ba Tun a Farkon Dare ya Ƙwana da Niyyar Sa har Alfijir ya fito Bai Niyyar ba, toh Ɓa shi da Azumi wannan yinin, Kuma ba zai Ci Abinci da Rana ba zai Yi abun da ake Cewa ka mun Baki.
Sabida Haka Matukar Ba ki
Ƙwana da Niyyar Ɗaukar Azumi ba toh Baki da Azumi.
Saboda Haka ana Ɗaukar Niyyar Yin Azumi Ne daga Farkon Dare, Misali Ace toh Ana Sa Ran Cewa Gobe Za’a tashi da Azumi Ko Kuma Sarkin Musulmi ya bayar da Sanarwar Ganin Wata da Magriba ko Bayan Sallar Isha’i.
Toh da Zaran An Yi Isha’i Sai Ki Ƙulla Niyyar Ki, In Ma Sarkin Musulmi Ya Bada Sanarwa Ce Za’a tashi da Azumi a Gobe, Shikenan Daman Ke Kin Yi Niyyar Ki tun farko.
Kawai Kina Tashi Sai Ki yi Sahur naki Ki Wuce da Azumin ki idan ko ba ki samu damar yin Niyyar ba a Farkon Daren ba, toh za ki iya yin sa kafin Alfijir ya fito, idan hakan Bai samu ba har Alfijir ya fito ba kiyi ba toh Babu Azumin a wannan Yinin gare ki.
Sa’annan shi Niyya a Zuciya ake Yin Sa. Zakiyi Niyyar Yin Azumin Watan Ramadan, Idan kin tsaya a hakan yayi In kin So za ki Ce Kin Yi Niyyar Yin Azumin Watan Ramadan 30 ko 29.
2. Warware Niyyar Azumi ko Fasawa. Wanda Yayi Haka ba Shi da Azumi.
3. Duk Wanda Yana Yin Azumi Ya Ci Abinci da Gangan.
Bawai da Mantuwa ko Kuskure ba. toh Bai da Azumi idan da Gangan Ne Zai Yi Kaffara Azumi 60.
4. Duk Wanda ya Sha Ruwa da Gangan Alhalin yana Azumi, toh Azumin Sa ya Ƙarye Akwai Kaffara kuma.
5. Duk Wanda ya ke Azumi ya Sadu da Matar Sa da Ganganci, Azumin Sa ya Ƙarye. Kada Ki Yarda Mijin Ki ya Miki Haka Har Kema Ki Biye Masa Wajen Mika Kanki Yayi Jima’i da ke, da Rana kuma Kuna Azumi Dukkan Ku. Haramun ne Akwai Kaffara Shima.
6. Duk Wacce tana Cikin Yin Azumi Sai Jinin Al’ada ya Zo mata da Rana to Azumin ta ya Ƙarye.
7. Duk Wacce take Yin Azumi Naƙuda ya Kamata Jinin Ɓiki ya Zubo mata, Ko Jinin Haila, Azumin ta ya Ƙarye.
8. Duk Wanda Yake Musulmi Sai Yayi Ridda ya Fita daga? Musulunci da Gangan ba abisa Mantuwa ko Kuskure ba, Duk ibadar Sa Sun Rushe a Cikin Su Har da Azumin da Yake Yi.
9. Duk Wanda Yake Azumi ya Ƙwakaro Yin Amai Ko Ƙumallo da Haraswa Azumin sa, ya Ƙarye.
10. Duk Wanda aka Yiwa Allurar Abinci. Azumin sa ya Ƙarye. Saboda Haka Sai Mu Kiyaye Su. Wallahu A’alamu.
ALLAH YA SA MUYI AZUMI KARBABBE.
Ku Biyomu a Fitowa Na Gaba Insha Allahu.
KARANTA: Kalaman Barka Da Shan Ruwa 2023