Tubali Hausa Novel Complete Book 1, 2 and 3

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku tubali hausa novel complete book 1, tubali hausa novel complete book 2 dakuma tubali hausa novel complete book 3.

Tubali Hausa Novel Complete

 

TUBALI
PAGE 1
NA

AYSHA ALIYU GARKUWA

Bismillahi rahmanirahim Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani rai da lfy da damar fara rubuta wannan littafin nawa mai suna TUBALI Ya Allah ka bani aron rai da lfy da konciyar hankali ka bani ikon rubutashi har arshe bisa lfy alfarmar Annabi da alurani Allah kayi min tsari da abin hani ka tsare min hannuna tunanina idanuna alalamina yatsuna da rubuta wani abu da zai zamewa alummar Annabi sharri ko ya zama cutarwa ga tarbiyarmu

 

GEMBU MEMBILA Taraba State

Wani irin hadari mai masifar arfi da duhu ne ya yiwa illahirin yankin Gembu Membila awanya tako wani sashi gabas da yamma kudu da arewa yake ta gangami
Yayinda Ya hae da duhun dare mai gauraye da duhun damina
Hakan yasa babu abunda ke tashi a yankin sai wasu irin tsawa da rugugin da aketa yi babu aautawa kana kuma wata iriyar iska mai an karen arfi da sanyi ne ke ci gaba da kaawa da arfi

A daidai ya irin wannan lokacin kuma gaba aya bani Adam mazauna cikin gidaje sunyi nisan bacci kasan cewar arfe aya na dare ta gota

Wata kyakkyawar mota ce mai masifar kyau da tsadar gaske wanda take nuni da mamalakinta wani ne ko wane ta faso kai
Gudu yake shararawa cikin motar tamkar zai tashi sama
Maana gudu irin na ceton rai shiyasa shi kansa bai san irin tuin da yakeyi ba
Gaba aya jikinsa kyarma yakeyi duk da azabebben sanyin yanayin wurin da kuma sanyin ACn dake cikin motar amma hakan bai hanashi haa fitinanniyar zufa ta fargabar ganin alamun rabuwa da rayuwar duniya ba

Tui yakeyi yana juyowa yana kallon wata zungureriyar tirela dake biye dashi a baya haikanadaran
Da nufin bi ta kanshi ya takeshi ya gane hakane ganin duk inda yayi binshi tirelar takeyi tana binshi

Cikin tsananin tashin hankali yasa hannunshin ya sharce zufan goshinsa kana yasa hannunshi aya ya ruggume yaron dake bisa cinyarsa yana karkarwa ganin irin azabebben gudun da sukeyi
Daidai lokacin kuma suka iso kan babban tsaunin dake saman zuzzurfan kwazazzaan kogin Gembu wanda yake hae da kogin Numan Adamawa Dadin Kowa Gombe kana da binuye
Sannan hanyar tana nan tamkar tafiyar macijiya zizza

Wayarshi ya zaro a cikin kiima ya fara magana da wanda ya kira in yana maganar muryarshi na rawa magana irin ta ban kwana da duniya da barin wasiyya da bada amana
Sun zo gab da Rugar Rumo dake asan hanyar can gefen kwazazzaan
Daidai lokacin kuma tirelar nan ta cim mishi

Cikin tsananin mugunta ya danna motar da arfi ya ingizata cikin ramin dake hae da manyan Koguna wanda zurfinsa ya zarta zaton mai zato

Ji kakeyi kuuuuuuhhhh motar ta bada wani irin gigitaccen sauti
Sai kuma ta an tsaya daga gangarawar sabida karon da tayi da wata bishiya hakan yasa bata faa ciki kai tsaye ba
Da arfi ya kuma matsowa ganin bishiyar ta are aramar motar
Ingizata yayi ta tafi cikin ramin
Ji kakeyi fuuuuuuhhh zinim Ta faa cikin ruwa

Wanda sautin faawan yasa mafi akasarin mutanen Rugar Rumo farkawa

Suna alhini da tausayin sanin duk wanda ya faa ciki ya faa abarinsa kenan

Shi kuwa mai tirelar wani irin masifeffen dariya mara dain amo yayi kana ya wuce cikin garin dan babu damar yin kwana a wannan wurin

Tuin yakeyi wayarshi saale a kunne shi yana cewa
Sir na gama dashi babushi a duniya
Yayi ban kwana da duniya yanzu zan wuce cikin Gembu kuma zamuje mu kashe matarsa da yaranshi kab
an jim yayi jin yadda Sir in ke dariyar cin nasara tare da cewa

kuna kashesu
Sauran cikon 2 million din ku zai shigo hannunku
Cikin zauwa matukin tirelan yace
Yanzu kuwa
Kana ya katse kiran ya nufi cikin Gembu a cikin daren da wannan duhun damunar

Bayan wasu shekaru A kamar Ashirin da biyu 22

Kano state
Shiru hall in taron maaikatan tashar Arewa 24 TV dake birnin Kanon Dabo yake yayinda maaikatan ke zaune bisa kyawawan kujerun dake zagaye da babban table mai kujeru sama da hamsin
Yayinda gaban kowa goran ruwan Faro mai sanyi ne da kuma Nutrimilk sai maltina da chii exotic baya ga haka kuma glass cheers cups ne a gefegefe
Kana sai abun sautin magana dake gaban kowa mai an tsawo
Gefen dama duk manyan maaikata ne
Kana gefen hagu mabiyansa
Can baya kuma ananun maaikata
Babban ogansu ne ke musu bayanin canjecanje tsarin aikin da suke shirin kafawa na forkon shekarar
Gyara zamanshi yayi tare da kallon gefen damanshi
Murya ya an gyara tare da cewa
Ina mai Shirin baon mako
Cikin nutsuwa Jannart Idris Saleh Dakata Ta ago kanta cikin tattausan muryarta mai cike da nitsuwa tace
Im here Sir

Sautin daddadan muryarta ne kuma yasa mafi akasarin mutanen dake wajen suka juyo suna kallonta
Tabbas Nitsuwarta na daya daga cikin dalilan da suka sa aka bata ragamar wannan shirin
Kasan cewar manyan mutane masu kamala da shahara ake gayyatowa so ana buatar mai nitsuwar da zata martaba musu manyan bain su
Cikin kula Uban gidan nasu yaci gaba da cewa
Shirin baon mako yana da manufa mai girma ta samo manyan mutane ta tattauna dasu su sanarwa duniya nasarorin su da kuma irin alubalen da suka fuskanta domin
Su kasan cewa matasanmu masu tasowa Maduban gina TUBALIn rayuwarsu ta yadda zata inganta su tsare kansu da lalatacciyar tarbiya suyi karatun da sanaa domin watanwata rana su zama abun koyi abun so wa yan baya
Shiru ya anyi tare da kurar ruwan Lemun exotic din dake gabansa

Ita kuwa Jannart naurar maganar dake gabanta take an sa fararen yatsunta wanda sukaji red henna tana sama tana asa dasu a hankali
Yayinda duk saura kuma sukayi shiru
A nitse yaci gaba da cewa

But now Im sorry to say Jannart shirin ya raunata sosai Yananin tsaron da kike ciki yasa bakya sakewa ki samu ki gayyato mana manyan mutane shahararrun masu nagartan da zasu burge mutane
Shiyasa shirin yayi rauni mafi akasarin ranaku sai dai aita maimaita program in daya gabata
Wannan dalilin yasa muka samu umarni daga sama
Aka bamu zai biyu

Da sauri Jannart ta lumshe idanunta kana tayi asa da kanta saboda fahimtar inda kalamanshi suka dosa
In ta gane ana gab da sallamarta daga aikin Wanda nanne kaai duniyar farin cikin ta in ta shiga cikine kadai take samun ta sake tayi raha tajita mai eanci babu Escort ba Yah Junaidu a kusa
A hankali tasa yatsarta ta an ara saala naurar dake saale a kunnenta wanda shike arawa jinta arfi yadda take an taune lips in ta na asane ya bawa kyakkyawan Dimple in ta damar lotsawa yayinda jajayen lips din nata suke shei dan lasarsu da ta anyi
A hankali Aisha Lawal dake gefenta tasa hannunta ta kama nata tana an murzawa alamun bada arfin guiwa
Salman kuwa dake fuskantar ta idonshi ya rumtse
Da sauri ta bue idonta jin shugaban nasu yaci gaba da cewa

Umarni na forko wannan karon an bamu sunan mutumin da ake son mu gayyato yazo ayi hira dashi
Domin shi kadai ne zai aga darajar shiri
Sai kuma cewa in har bazaki iya samun dama da lokacin sakewa ki nemishi ba to dole a saueki kan shirin
A nemo wata ko wani da zasu iya
Cikin nitsuwa ta an kalleshi kana a hankali cikin tsoron rasa aikinta tace

In sha Allah zan iya
Da sauri ya kalleta
Kai ta jinjina alaman
Yess zan iya
Kai ya jinjina kana yaci gaba da cewa
Sai umarni na karshe dole a nemishi ya zama next 2 weeks dashi zaayi hira Kinga kenan yau saura kwana goma kenan
Asiya ce dake masifar son amsar ragamar program in daga hannun Jannart
Ta gyara zamanta tare da cewa
Sir waye ne shi A ina yake
Cikin an aga sauti yace

Dr Rayyern Bashir Muhammad Mainasara ne

Da sauri duk suka fara kallon juna cikin kauwa Aisha Lawal tace
Sir Rayyern Bashir Muhammad Mainasara shifa

Hannunshi ya aga mata tare da cewa
Na sani shi ba mutum ne kamar kowaba raayin shi da banne
Ko BBC bata taba samun nasarar yin hira dashi bako
Da sauri kab suka amsa da
Yess Yesssss
Ajiyan numfashin ya saue tare da cewa
Toh wannan itace nasararmu in har an samoshi
Zai zama mujallar Arewa ce zata taa fidda hirarshi da hoton fuskarshi kana Arewa 24 TV ce zata taa haska fuskarshi da surar jikinshi bayan sunanshi daya zama sananne a Africa baki aya
Wannan shine zai ara aga darajar shirin
Shin Jannart zaki iya Ko dai kai tsaye asa Asiya
Da sauri Asiya tace
Sir Ni zan iya tunda bani da wani tsaron nuna isar cewa ni ar wanice aikina shine isata
Mafi akasarin mutanen wurin ido suka zuba mata ganin yadda take mgna tana watsawa Jannart harara
Ita kuwa Jannart glass din idonta ta gyara tare da agowa jin shugaban nasu na cewa
Jannart zaki iya ko dai yanayin tsaron da mafahifinki ke baki bazai barkiba
Cikin sanyi da danne fargabarta tace
Sir zan iya in Sha Allah A bani kundin bayaninshi

Ajiyan zuciya Salman ya saue jin cewa ta amsa zata iya baya son rasa abokiyar aikinsa sabida yana jin dain aiki da ita
Aisha Lawal kuma ajiyan zuciya ta saue
Shi kuwa MDn su wani file mara girma ya tura gaban Jannart tare da cewa
Gashi sai dai babu komai nashi a ciki sai sunanshi da sunan Companys inshi da garuruwan da suke Da Hospitals inshi Da kuma foundation in sa mai suna Mainasara Foundation

Jin yayi shiru ne yasa ta an kalleshi kana a hankali tace
Ba phone number insane ba picture dinsa Ba address in sane
MD ne ya an gyara zamanshi tare da cewa
Toh Jannart ai da akwai waannan abubuwan a ciki toh da bazaiyi wuyar samuwa ba kuma da bazai zama mutum na musamman ba kunsa duk abinda yake killace shine special
Sai kuma ta juyo ta kalli mai kula da shirin nasu dake cewa
Babu number sa ba hotonsa ba adireshinsa Kana ko akwai number sa ko sau 1000 zaki kira da layuka 1000 mabanbanta bazata shigaba sabida yana amfani da App in nan da in dai bawai yayi saving number ki a wayarsa bane kiran bazai taba shigaba
Kuma koda ya ajiye ya shiga zaki kira a alla sau goma bazai amsaba sai dai ace mikin ki ajiye mishi voicemail
Sabida yawan aiyuka da uzurrukan da mahaifinshi ya aura masa yasa bashi da isashen lokacin kansa ma da yawan mutane suna matuar jinjina masa da mmakin kwazonsa sabida aiyukan sun mishi yawa kana matashine a tsakiyar dattijai
To shiyasa bai cika samun lokacin amsa kiraba
Sai dai a ajiye mishi sao so nanne zakiji muryarsa idan abinda ke tafe dake mai mahimmanci ne kuma kinyi hikimar faa mishi number ki to shida kanshi zai kira

Mafi akasarin su ajiyan zuciya mai nauyi suka saue
Cikin karaya Jannart tace
My Aunty to Ina kikaji duk wannan bayanin
Dariya Hajia Rabiah tayi tare da cewa
Jannart yar jaridar gaske wato tuni har kin fara binciken tun yanzu a kuma kaina
Murmushi tayi tare da gyaa kai
MD kuma kai ya jinjina sabida gamsuwa da hikimarta da nitsuwarta wurin aikinta
Cikin girma Hajia Rabiah tace
Toh gsky nima wurin PAnsa na samu wannan bayanin
Ba kuma wurin PA din kai tsaye ba
Akwai an yayata abokin anin PAn nashi ne so nan naji wannan

Cikin sauri ta miawa Hajia Rabiah wayarta tare da cewa
Samin number an yayar taki
Murmushi tayi ta amsa tasa mata number
Kana tace
Sunanshi Mahmoud
To tace kana ta adana number

Shi kuwa MDn gyara zamanshi yayi yaci gaba da tsara musu sauyesauyen programs in nasu

Sai kusan arfe shida saura suka tashi a taron

Suna fitowa mafi akasari suka kama hanyar parking lot insu dan daukan ababen hawansu

Wani irin kallo mai cike da tsana Asiya ke bin Jannart dashi lokacin da suka fito a take Escort in ta suka mie suka mara mata baya
A hankali ta an juyo jin Aisha Lawal na kiranta
Jannart Jannart
Juyowa tayi tare da bin tsakiyar hanyar da suka bua matan
Da sauri Aisha Lawal ta iso cikin sanyi tace
Zaki iya
Cikin jin tsoron rasa aikinta ya zama dole taita zaman gidan da yafi na kurkuku muni da zafi
Tace
Naam Aisha zan iya in sha Allah In ban iyaba naci gaba da zaman gida Yah Junaid zai karasa kurmatani da marukan da yake yayyarfa min a cikin ko wani mintuna wurin aikin nan shine duniyata shine TUBALIn an yancina ya zanyi sakacin rasa aikina
Cikin rauni da ara yin asa da murya Aisha tace
Okay Salman yace ince miki in sha Allah zaku iya kuma zai roi a baku cikekken dama da zai biyoki sai ya tuna waannan kattin dake zagaye dake wanda suke shirye da ilkata duk wani na miji in yazo kusa dake
Kai ta jinnina kana sukayi sai anjima

Wasu dalladallan motoci ne guda uku
Ta tsakiya itace a baya
Ta baya kuma an tsaronta hakama na gaba
Tana baya a zaune
Yayinda drivern ta ke janta
A haka suka nufi gida tana mai jin tsoron me zata riska a gida kasan cewar ta wuce lokacin dawowarta

Anguwa ce mai zaman kanta Janbulo tsit anguwar ba hargitsi da hayaniya da kwata kamar ba cikin kano ba sabida manyamanyan gidaje ba irin gidajen kanawa mitsimitsin nan ba
A bakin wani tamfatsetsen gida mai an karen girma da kyau suka tsaya tare da danna hon
Jiki na rawa mai gadi ya bue musu
Nan suka ratsa cikin gidan

Suna isa parking space ana kiran sallan magriba
Wanda yayi daidai da fitowar Alhaji Idi Sale Dakata daga cikin gidansa tare da zaratan samari uku Junaid Azeez Abdul a bayanshi
Da wani mutum wanda suke kama da juna Barrister Kabir Saleh Dakata kaninsa kenan
Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ta saue fahimtar Yah Azeez zai koma wurin aikinsa dan taga ana sa kayansa a mota alamun ana idar da salla zasu wuce Airport dashi
Murmushi Barrister Kabir yayi tare da cewa
Masha Allah Ammina kin dawo kenan
Da sauri ta matso kusa dashi tare da kaucewa mugun kallon da Yah Junaid ke watsa mata cikin sanyi tace
Eh Abba na dawo ina Aunty Dija
Ta kare mgnar tana kallon fuskar Yah Azeez din da yakeyi mata kallon mai cike da tausayawa
Barrister Kabir kuwa wanda ta kira da Abba Cikin kula da tsananin tausayinta da danne wani abu can asan zuciyarsa yace
Suna ciki shiga bari muje masallacin
Da sauri tace to
Kana tayi cikin gida su kuma suka nufi masallaci

Ethiopia Addis Ababa

Wani kyakkyawan matashine mai wani irin tsabtaceccen kyau mai masifar aukar hankali matashine mai jini a jika

Wani irin kimtsestsen taku mai cike da nagarta nitsuwa kamala haiba yakeyi yana mai fitowa habarar wani kyakkyawan Asibitin
Tikur Ambess Teaching hospital Addis
Yayinda wasu manyan likitocin da asar Ethiopia ke ji dasu ke biye dashi a baya kana da Nurses
Taku yakeyi cikin kamala da haiba a hankali yake motsa lips inshi bisa dukkan alamu gajiya ce ta sashi hakan in

Fari ne mai masifar kyau irin farin mutanen asar Ethiopia sai dai fatarsa tana da haske fiye data sauran dake biye dashi a baya bimaana ya an fisu fari
Yana da wani irin hanci mai an karen kyau da tsini idanunsa masakaita masu masifar kyau da fari irin idanun nan ne da in sun cicciko da hawaye in akwai abu a gabansu kalar idon kan iya komawa haka wani irin kekkyawan saje ne mai masifar kyau ne kwance lib a fuskarsa yayi mishi awanya lips inshi an sirara jajaye masu kyau sai girarsa masu kyau
Wani irin askine mai an karen kyau bisa kansa
Sosai kamanninsa da DheerajDhoopar suka fito ras hatta tsawonsa da an jikinsa kamar na DheerajDhoopar ne komansa daidai misali
Daga shigarsa zata nuna wanene shi
Wani irin masifeffen Suit ne a jikinsa mai an karen tsada red colour mai maio riga da wondo sai igon farifari kana necktei in wuyanshi shima fari sai igon jajan
Haka takalmanta sau ciki toms farare ira companyn Italy sai harafin RM da akayi da red color irin ta matasa Masu kima da daraja sai agogon hannunsa irar Gucci shima da harafin RM a gefe da gefe Shigar tayi masifar mishi kyau da kamala
Taku yakeyi suna biye dashi a baya
Har suka iso inda motocinsu ke jere

DR Rayyern Bashir Muhammad Mainasara kenan

Cikin nitsuwa ya juyo yana mai mia wa Dr Adeym hannu cikin nitsuwa suka an yi mgna kana duk sauran ma suka bashi hannu
Kana ya shiga mota Drivernshi dake ciki yaja
Suka fita cikin asibitin
Kai tsaye
Hera Addis hotel Ethiopian suka nufa
A kan hanyarsu ne suka bi kusa da wani babban masallacin
Cikin saue numfashi ya cewa Drivernshi
Tsaya A taaice
Da sauri yace to
Kana suka tsaya ganin ya nufi cikin masallacin ne suka fahimci me zaiyu
Nan suka mara mishi baya dan yin sallan ishai kasan cewar lokacin ta yayi daga nan kuma suka wuce

A hankali ya maida kanshi ya jingine jikin kujerar idonshi ya lumshe tare da motsa lips inshi a hankali yana sauke numfashin gajiys
Yana jin wayarshi na ringing Amman ko idonsa bai bueba sabida tsananin gajiya kayan jikinsa kansu nauyi sukeyi mishi bacci yakeji da kuma yunwa
Shiyasa bai amsa kiranba
Sai dai cikin zuciyarsa yace
Sulaiman
Sai kuma ya an mirgina kanshi gefe
Ganin sun iso
Da sauri mutanen dake cikin motar dake biye dasu a baya suka fito aya daga cikin sune ya matso
Bue mishi marfin motar yayi kana ya matsa gefe
A hankali yace
Bismillahi
Numfashin gajiya ya an fesar
Kana ya zuro afarsa woje
Sai kuma ya an kalli Usman PAnshi dake tattaro System in shi da wayoyinshi
Kana a hankali yace
auko small bag in can
Da sauri Usman yace To
Kana ya auko an jakar leda mai auke da tambarin Edna Mall Addis Ababa Ethiopian yabi bayanshi suka nufi cikin HOTEL in
Kai tsaye inda masauinsu yake suka nufa

Suna shiga ya juyo ya kalli Usman daya ajiye mishi kayyakin nasa bisa kujera
Sai da safe bazanci komai ba kada Sulaiman ya dameka kace zaka zo ka dameni Yayi mgnar cikin gajiya
Cikin sauri yace
Okay Sir
Yana mai kunce net inshi yace
Toh jeka
Toh yace tare da juyawa zai fita
Sai kuma ya an juyo yana kallonshi jin yana cewa
Ramadan ya kira azu
Kai ya gyaa mishi kawai
Ganin haka Usman ya juya ya fita

Yana ganin ya fita ya matso ya rufe ofar
Yana juyowa yana cire Suit in bisa kujera ya cillata kana ya cire ta cikin
Sunkuyowa ya anyi yana kunce belt in ugunshi
Yana daga tsaye ya zare wando

Yana son sakewa shiyasa yake jin dain rayuwar kaaici
Sabida yana masifar kunya da suturce surar jikinsa
Ko dan yanayin halittar jikinsa mai gargasa ne baya son koda Ramadan ne yaga koda damtsen hannunshi bare sharaarsa bare aje ga cinyarsa da tattausan gargasa yayi masu awanya
So Amman in shi kaaine yana sakewa wasu lokutan daga falo yake fatali da kayyakinsa kafin ya shiga bedroom ma daga shi sai boxes zai shiga
Tattare kayan yayi ya wuce dasu Bedroom bisa gado ya ajiyesu
Kana ya wuce Bathroom

Bayan ya fitone ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wondo iya guiwa farare al

Turare ya an fesa kana ya ara gudun AC sannan ya koma parlon ya auko ar jakar da yasa Usman ya auko mishi wanda yake cike da chocolates kala dabandaban
Masu sanyi a daskare

Sosai ya ci Galaxy Chocolate mai an karen dai kamar yadda ya saba taammali da kayan zai
Bayan ya gama ne kuma yasha tea mara hai wato coffee Bayan ya kammala ne kuma ya dawo Bedroom rie da system a hannunshi

Kashe wutan akin yayi kana ya kwanta
tare dasa l system innasa a gaba

Ajiyan zuciya ya saue Allah ya sani yana jin wani irin nishadi da sanyi na musamman in yana jin waazin Dattijon nan Malam Mainasara yana son tafsir din shi
Baya gajiya da kallon fuskar tsohon
Wannan yasa yake bibiyar shafin shi na You tube inda yake saka tafsiransa
Lallatsa system in yayi
Jim kaan sai ga hoton ya bayyana
Fuskar dattijon ya zubawa idanu
Har bai jin abinda ake magana a kai
Sai da yaji iska na an cika mishi ido ne ya an lumshe idanun tare da saue numfashi kana ya bue su
Kan rubutun dake asan hoton Dattijo ya kuma kalla Malam Mainasara
Cikin sanyi can asan zuciyarsa yake magana
arshen sunanmu iri aya Ni dai nasan Tubalin nawa sunan Toh shi kuma menene TUBALIn nashi sunan Mainasara menene asalin sunan
Wa zai amsa mishi waannan tambayoyin da zuciyarsa tai dena mishi su
Numfashin gajiya ya saue kana ya kauda tunanin yaci gaba da jin tafsir in nashi

Jin bacci zai kwashesa ne yasa ya rufe naurar ya kwanta yana mai bue tafin fararen hannunshi yana adduoin
Yana idawa ya shafa ya kwanta

 

Kano Nigeria

Sulaiman ne zaune bisa kujera matarsa Sumayya na gefenshi
Da sauri yace
Ikon Allah
Juyowa Sumayya tayi tana cewa
Lfy
Da sauri ya matsota tare da cewa
Kiji ikon Allah wai Riyyamnsra wannan an Ethiopia da nake ce miki yana masifar kama da Rayyern wai zaizo Nigeria
Leowa tayi ta kalli fuskar wayarshi inda yake TIKTOK yana bisa shafin Riyyamnsra
Kai gsky kam Ni kaina ina taajjudin kamanni Rayyern da yaron nan kamar ta azanta

Uhumm ni kaina na gaza daina mmakin kamanninsu
To amman kin kuma ji wai zaizo Nigeria
Rion da tayiwa yarsu ta gyara tare da cewa
Abban Nihal me abun mamaki don zai zo Nigeria kasan celebritys da yawo kamar jirage
Kanshi ya jinjina tare da cewa
Sumayyah ba zuwansa Nigeria bane abin mamaki
Toh menene abin mamakin
Ta tambayeshi cikin kulawa
Juyo mata fuskar wayar yayi
Da sauri ta zsro idonta waje cike da mamaki tace
Dama H

 

TUBALI
NA
AYSHA ALIYU GARKUWA

 

ASSALAMU ALAIKUM Masoyana ma karantan littattafaina ina mai farin cikin sanar daku yau din nan MON 18 OCT 2021 zaa fara biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauki Biya 500 karamin farashin na karamin group kana sai Special people Group akan farashi mai sauki 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake zaku biya ta asusuna

ACCOUNT NO 0661110170

BANK NAME AISHA ALIYU GARKUWA

BANK GTBank

sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276

PLS TAKE NOTE BAND VTU
kada kiyi min VTU ko transfern katin ta wannan numben etisalat din idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fadi miki Please and please in dai da hali kada ki turo min katin kiyi min transfern ruwan kudi ta bank account na in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy numbers in katin ki turo min ta whatsApp

Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntubi Mommy akan layinta 22790899076 ta wurinta zaku biya hoton katin zaku dauka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp Special people group 1k ne 1000 karamin group kuma 500 kacal
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da yayan jikoki mu kyautata lafazi da muamala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki

Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa
Tausayi Sarkakiya jan hankali Fadakarwa Nishadantarwa ilimantarwa alajabi Saar rayuwa rion amana cin amana ribar kyautatawa kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya

Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani kasa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min In Kuma karamin Group kike so ki sayi katin MTN ki copy numbers din ki turo min ta whatsApp numbern na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfern katin 9mobile dan layin nada matsala

Zaayi tsawon mako aya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane zaa fara biya yau MON 18 OCT 2021 Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy

Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kudinki kiji tausayin marainiya kada ku cutar da marainiyar Allah

Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar Please ina neman alfarmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba na tuba kiyi hauri ba raini bane ko wulakanci face yawan mutane wata kil ban isa kan Chart naki bane Amman muddin na isa na kuma bude na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi hauri da min mgn sai na dan samu salama

Sayan na gari maida kui gida sai kinzo

 

 

Albishirinku Maaurata GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku maaurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MAAURATA

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara Kullum dai magana daya ce akan maaurata fada rashin jituwa mutuwar aure akan kuskure kalilan rashin kula rashin yi wa juna uziri Toh wai duk me ya janyo hakan Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take Shin yaruwa ke macece amma kin san wacece mace ku Kin san me ake kira mace kuwa Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango sanyin idaniyarsa ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da niimar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su

Wannan ita ce mace Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace kaya ne da suke taimakawa sex hormones dinki
Misali kina kallon India hollywood Asian film kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu
Saboda me hakan Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da niima cike da tsukewa kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haine na ingantattun itatuwa da yayansu
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki
Zo ki ji yaruwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace Gubar ciko gumbar tsalle dole gubar da baa baiwa mai kishiya garin mai garin mallaka tsumin goron tula tsumin tsartai tsumin maratsi palapala butar sirri kwanon kasaitacciyar mace furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu
Ina mata masu fama da sanyi Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan
Ina da ciccibi mai kyau Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya

Akwai daya bangaren wato KAMSHI
Kimarki gyaranki da kamshinki Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta akwai shuumar humra sayan na gari maida kui gida banda karanta yayin gyara Hajia

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zainki ko karin bayani zaki tura kuin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn

Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
GARKUWAR MAAURATA

 

By
GARKUWAR FULANI

  • TUBALI PAGE 2 NA AYSHA ALIYU GARKUWA

Hausa ya keyi fa ko Cike da kauwa Sulaiman yace
Eh abinda ya ban mamaki kenan
Sai kuma ya kalleta jin tana cewa
Koda yake ba mamaki wani ne ya rubuta mishi tunda kaga ai yace
Ethiopia Addis Ababa to Nigeria kano State Kanawa zan zo muku
Wata il wani ne ya rubuta mishi
Komawa yayi da baya ya jingina bayanshi da jikin kujera
Numfashi ya an fesar tare da cewa
Kai Sumayyah gsky da mamaki fa
Kalli Comments in mutane fa da amsar da yake basu
Ya are maganar yana shiga comments section in asan videon da ya saka a shafin nasa
Inda wani Abis Fulani yake cewa
Eyyeh Riyyamnsra a Nigeria kanawa nama fatan isa lfy
Cike da mamaki Sumayyah ta kalli amsar da ya baiwa Abis Fulani
Ngd aboki na da alamun musabaha
Sai kuma tayi asa ganin inda wani
Ahmad MG ya fara mgn da zaro ido alamun mamaki tare da cewa
Riyyamnsra da yin Hausa ko mafarki nakeyi
Dariya yayi tare da bashi amsa
Noh Ahmad zahiri ne
Tofa wannan abun yasa comments in mutane zubowa kamar ruwan sama domin shi dai an asar Ethiopia ne kalarsa harshensa cimarsa rayuwarsa komai na canne bai taa koda maganar Nigeria a shafinsa ba sai gashi yau kuma yayi video cewa zaizo Nigeria kuma yana rubutu da hausa yana kuma karantawa
Cikin kauwa Sumayyah taci gaba da bin comments in mutane na farkofarko da ya iya basu amsa sabida yawan mutanen
Cikin mamaki tace
Lah kalli tambayar da wani ya mishi
Amsar wayar Sulaiman yayi
Ya fara duba saon da Imran yayi mishi
Riyyamnsra kasan Nigeria ne Ko Ka taa zuwane Ko wannan ne zuwan da zakayi na forko
Alaman murmushi yasa tare da cewa
Nasan abu da yawa kan Nigeria

Da sauri yace gaya min kaan daga ci

Ok kamar me kake son in gaya maka
Da sauri yace
Ka iya taken asa Ko rantsuwar alawarin asa

Cikin lumshe ido Riyyamnsra dake kwance a akinsa
Ya rubuta mishi amsa da bari in baka amsar a video
Take kuwa ya tashi zaune yayi taken asarmu Nigeria asarmu ta gado kana da rantsuwar alawarin asa
Wannan video da ya saki
Yayi matuar jan hankali alummar Hausawa duniya baki ayansu more Especially an Nigeria bama ya kanawa
Da sauri Sulaiman ya fara rubutu
A karo na forko a rayuwarsa da zaiyiwa wani comment a TIKTOK
Rubutu yayi cikin harshen nasara
Hey Riyyamnsra you knew much about Nigeria you are a patriot
Yayi mgnar da gayya ne dan ya gano ko dai an Nigeria ne basaja ne da karya yasa yake ciwa an Ethiopia ne wata il karatune ya kaishi can
Murmushi yayi tare da rubuta mishi amsa
Baon Nigeria dai mai kishin Nigeria amman ni an Ethiopia ne
Sai dai Nigeria asar babban abokina ne da mukayi karatu tare a US
So daga ganin wannan video akai ta cewa
Haba shi yasa mana
Nasir Ahmad ne wanda shine abokin nashi ya fito yanata mishi tsiya a nashi shafin Nanfa aka gane sanadin zuwansa da kuma inda ya koyi Hausa ras

an gajeren tsaki Sulaiman yayi tare da cewa
Wadannan yaran gaba aya TIKTOK ta haukata mana matasa wanda sune TUBALIn alumma sai gashi kuma muin ma suna shirin haukatamu
Dariya Sumayyah tayi tare da cewa
Dama haka ai Rayyern in ke ce maka in baka dena biyewa social media ba zaka rasa lokacin kanka
Kwaffa yayi tare da rufe datarsa kana yace
Nima fa Ibrahim ne ya sani fara wannan abun sabida kamannin Rayyern da wannan yaron
Daga nan sukaci gaba da hira kan kamanninsu

Washe gari da safe ranar talata

Gidan Alhaji Idi Sale Dakata
Su kusan shida ne cikin falonshi
Wanda huu daga cikin manyan yan kasuwane masu faa a ji masu juya sule ta koma million aya ko tako wanne irin halin aama ko talaka zaiji dai haka ko bazai jiba
Biyu daga ciki kuma usoshin gwamnati ne masu arfin iko daga ta jiha zuwa ta asa

Alhaji Yawale ne ya gyara zamanshi tare da cewa
Yaron nan fa yanayi mana illa ba tare da mun ankare ba
Gaba aya ya rarake tubalin da mukayi tsawon shekaru muna ginawa muna samun wuri na jawo mana wuri
Cikin tsananin takaici Alhaji Abdu Tababa ne yace
Tuntuni nake gaya muku haka
Mu kauda yaron nan a doron asa shine kawai mafi sauin mu
Kunaga yadda kasuwan cinsa ke haaka kamfanonin sa suna bunasa daga Arewacin Nigeria har ya koma kudanci ya kafu
Uwa uba yanzu duk asashen Afrika yanada rassai
Ya maida kayan abinci da araha tamkar ruwan sama cikin damuna
Duk inda ka shiga a kasuwannin Mainasara race ke cike
A farashi mai saui ta yaya zaayi a saurari kayan kamfanonin mu

aya daga cikinsu ne ya mie tsaye tare da cewa
Ni tambaya ta a kullum ma shine
menene Tubalin kasuwancin yaron nan
Yaushema aka haifeshi Saan yaran cikin mune fa
Ta ina ya samu Wannan tarin dukiyar da har ya samu damar razana mana kasuwanci ya raunata mana Companys
Yaushe yayi ginin duk a lokacin aya menene Tubalin dukiyarsa da matakan ikonsa
Ya are maganar yana kallon Bala Tambari wanda shine shugaban tsaretsaren ginin masanaantu a gwamnatance dole sai yasa hannu zaayi gini ya zaayi ka bashi izini da damar yin gini a duk inda yake so a asar nan
Cikin takaici Bala Tambari ya fesar da numfashi tare da cewa
Tsohon yarjejeniya ne yana da dukkan abin buata yanada sa hannun da suka gabaceni kuma kan tsari suke
Naso in alu balanceshi
Tun shekaru biyar baya lokacin da ya fara gina babban campany dake Nan birnin Kano wanda yanzu yake gab da kammalashi so naga komai da hujja yakeyi
Yaron shegen taurin kai ne dashi gashi da an banzan tsaurin ido
Kana mgna zai tsira maka waannan siraran idanun nashi masu kama da soyayyan gujjiya tsakar idon ka ya baka amsa da hujjar da baka isa kayi mgna ba

DrLukman ne ya fesar da iska a baki tare da cewa
Ni ta ko ina ya tosheni
A fannin likitancin gaba aya yana bi yana rarake privet Hospitals
an banzan komai na asibitinsa mai saui kuma ga kula ya zaayi aje irin namu asibitocin

Alhaji idi Sale Dakatane ya mie a fusacen shina kana yace
Nifa gaba aya ya taazzara min campany na na shinkafa
Sannan kafin kace ka motsa sai ka samu ya toshe ko ina
Hegen yaro mai jajayen kunnuwa
Yana nan tamkar Wahainiya samun ganinshi ma ya zamewa mutun aiki

Dr Lukman ne ya an saue numfashi tare da cewa
Cikin satin nan zai dawo Nigeria yanzu haka yana Ethiopia yaje shugaban kasar can da kanshi da manyan likitocin sune suka karrama shi
Sabida taimakon da yayiwa wasu daga cikin mutanen asar Ethiopia cikin Airport kan hanyarsa ta zuwa US dan karramashi a matsayin an kasuwan da yafi ko wanne sauin farashin kayan masarufi
Kaga yana tafi kuma yazo wai kuma Ethiopia zasuyi mishi wata karramawar
Yaro kamar an ruwa komai yasa kai sai Nasara
Bala Tambari ne ya kalleshi tare da cewa
Toh yanzu dole kai zaka nema mana zama dashi
Yana dawowa muna buatar shi mu gwada sayan farashinsa
Muyi mishi tayin harallarmu yasan irin ribar da muke shigarwa wata il zai amince mu haa hannu in kuma yai tabbas zamu gina mishi gadar zare
Da sauri Alhaji Idi Sale Dakata yace
Uhumm ai In Kuma yai amincewa mu haa hannu
Toh lokacin wasan zai fara dan in taurin kaine da gsky da samun arfin iko bai kai
Maigaskiya da wasu ba da muka gama dasu shekaru ashirin da biyu baya ba danni cinnaka ne ban bar na gida Bama bare shi baare
Haka dai suka tashi a taron nasu
A nufin sai ya dawo su zauna dashi

A cikin gidan kuwa Jannart ce ke
Tsaye a kitchen inda take sanye da wani half gown mai masifar kyau wanda ya dan bayyana fararen legs dinta rigar irin mai kauri da kama fatar jiki dinnan ne wanda hakanne kuma yasa hadaddiyar Surar jikinta dan bayyana kasancewarta yar gayu Tabbas Jannart macece mai matukar son fashion shiyasa hatta suturun da take sawa ya banbanta da sauran na yan Nigeria saboda sometimes tafi yin shiga irin na wasu daga cikin larabawa ko kuma shigar mutanen turkey
Tsaye take a kitchine din cikin kuma nutsuwa take aikinta
Yayinda Mom ke tsaye a gefenta
Cikin kula Mom ta kalleta tare da cewa
Jannart kamar Yayanki ne ke kiranki
Cikin bugawar zuciya tace
Yah Junaid
Da sauri tace
Eh shi dai
Bugawa zuciyarta ya kumayi tare dajin wani iri acikin jikinta saidai kuma babu yanda ta iya haka ta juya cikin sanyi ta nufi falon

Can tsakar falon ta hangoshi tsaye saurayi ne mai murdaddiyar Surar jiki da kuma tarin gashi akansa irin bususun nan duk da cewar kyawun nasa bawani na zarce hankali bane amma bazaa taba kiransa da mummuna ba wata riga
marar hannuce ajikinsa sai kuma wondon dake jikinsa wanda ya tsaya masa iya guywa
Bisa alamu kuma yanzu ya tashi daga bacci
saboda yanda idanunsa sukayi jazir

Kallonta yayi tare kuma da dan cije labbansa still Cikin binta da wani irin mayataccen kallo yace
Kije ki share min akina

Fuskarta ta dan bata cikin kuma tsanar shiga akin nashi tace
Yah Junaid breakfast nake haa mana
A fusace ya juyo kanta cikin takaicin abubuwan dake hae mishi a kanta ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari a kan kunneta na dama saida ya bada wani irin sauti auuuuu Da an karen arfi
A gigice tasa tafin hannunta ta tallabe uncin ta
Yayinda wasu taurari suka fara gilma mata a gani
In da sabo yaci ace fuskarta ta saba da marukan Yah Junaid Wanda tun tana yarinya take shansu gashi sanadin su kunnuwanta sun samu matsala jinta ya raunata
Wasu irin hawaye ne masu masifar zafine suka silalo mata
Ba tare da tace komaiba ta juya ta nufi akin shi
Ta yaya zuciyarta zata samu sauin an uwanta da take bata da wani sama dashi tunda shine suke uwa aya uba aya amman yafi kowa tsanarta a duniya
Ba shauwa ko tausayawa a tsakaninsu
Sannan mahaifinsu babu ruwanshi ko a gabanshi Junaid zai daketa babu ruwanshi sai yayi kamar baya wurin ma
In Mom tayi mgna ya gwatsaleta yace babu ruwanta sunfi kusa

Wannan ne ya ara tsananta zubda hawayen ta
A haka ta fara tattara mishi falon da gaba aya ya birkitashi

Shigowa yayi ya zauna yana mai Binta da ido duk inda tayi
Wani irin abu yakeji a kanta
A hankali ya mie yabi bayanta lokacin da ta shiga Bedroom
Da sauri ta juyo jin shigowarsa
Gefenta ya matso fuska a murtuke hakan ne yasa bugun zuciyarta ya ara tsananta
Har kana iya ganin yadda numfashin ta ke fita da yanayin tsoro
Fuska ya kuma murtukewa
Kana yace
Munafuka sai kace da gaske haka kike tsoron maza ji yadda kike tafiya ba bra kina wani karkakaa irji irin ke gaki ar iska mai son maza ko

Idanunta ta rumtse da karfi cikin kuma unan ran azafin da Yah Junaid ke jifarta dashi murya na rawa tace
Aa
Cikin hae fuska ya daka mata tsawa tare da cewa
Toh meya hanaki sa bra
Murya na rawa tace
Dr Lukman ne yace in daina sa bra sabida matsalar numfashin da Athsman ina ke jamin In nasa ya matse min irji sai numfashina yayi ta shaewa

Wani irin dogon tsaki yaja tare da cewa
Ubanki zanci in baki dena raina min hankali ba matse irjin da atti keyi bai shae numfashin ba sai saka bra ne zai cushe miki numfashin
Fice min da gani Ya kare maganar a tsawace

Jin hakanne kuma yasa da sauri ta juya ta fita hawaye na zubo mata sabida raain marin daya yarfa mata da zafin kalaman zargi da yake binta dasu

A falo ta samu Mom da sauri ta faa jikinta
Cikin sakin sassayan kuka tace
Mom ki gaya musu wlh ni ba yar iska bace Meyasa Mom Meyasa Ya Junaid ke jifana da mugayen maganganu shifa yaya nane

Jawo hannunta Mom tayi suka zauna bisa kujera a hankali tasa tafin hannunta tana share mata hawaye cikin yin asa da murya tace
Na sani Jannart kuma Allah ya sani ke ba ar iska bace Yaushe ma kika samu sakewar rayuwar duniya kullum kina cikin takunkumi
Ko ina zakije da masu gadinki
Na rasa wannan masifar tsaron na menene kina girma ana ara killaceki kamar abun rashin gsky
Cikin shesshean kuka tace

Mom shi Yah Junaid gani yake su masu tsaron nawa dasu nake iskanci
Daddy Kuma gani yake in ya cire masu tsaron da wasu zanyi iskanci
Wlh na sani Mom bawai dan tsaron lfyata bane yasa Daddy ware min masu tsaro
Shima zargina yakeyi ko Mom
Jin yadda numfashin ta ke fitane yasa mom gyara zamanta kana ta fuskanceta da kyau
Allah ya sani tana son Jannart tamkar ar cikinta
Amman duk yadda zatayi bata burge Alhaji Idi da Junaid gani suke kamar so take Jannart ta lalace ne don ba ita ta haifeta ba
Cikin kula da tausasawa uubar da suke shayar da ita tace
Aa Jannart Daddynku baya zarginki shi ya bada masu tsaronkine sabida larurar ciwonki kina buatar makusanci a koda yaushe tunda abu kaan ke tada miki athsman in wanda kinga tun da yana nimoniya kina girma yana canzawa ya ria har ya zama asman shiyasa yake tsananta kulawa a kanki
Sabida abu kaan ke tada miki shi
Kuma Yah Junaid inki yana sonki
an uwa uwa aya uba aya ya wuce wasa
Sun haa da son da Mamanki zatayi mikine da tana raye
Cikin zubda hawaye tace
Mom kin bani son da ya kamata uwa ta bawa arta ni banyi maraicin kyakkyawan tarbiyar uwa ta gari ba
Kawai dai basa so nane
Cikin kafeta da ido Mom tace
Jannart ki yarda dani tashi muje kici abinci
Cikin nitsuwa tasa hannunta ta share hawayenta kana ta mie
Dinning area suka nufa
Suna zama Daddy ya fito da hakama Junaid da Abdul
Nan suka zauna sukayi breakfast

A hankali ta sauke numfashi ganin Junaid ya mie ya bar wurin

Sai kuma ta an kalli Alhaji Idi Saleh Dakata
Cikin takatsantsan da girmamawa tace
Daddy Ina son zanje gidan Aunty Rabiah akwai wani aikin da zamuyi a can
Ido ya an zuba mata
Ita kuwa da sauri tayi asa da kanta
Tana tasbihi cikin ranta da adduar Allah ya aurata a kanshi
Juyawa yayi ya fara saua kan steps in tare da cewa
Kada ki dae
Kuma afarki afarsu Sunday
Cikin sabo da hakan tace
Toh
Kana ta mie ta nufi akinta Mom kuma ta fara tattara kan table in

Wanka tayi cikin nitsuwa da kuma saurisauri
Tana fitowa ta zauna ta tsane jikinta kana ta busar da tattausan suman kanta
Ta shafa mishi mayuka sannan ta tubkeshi
Mai ta an shafa kana ta Murja farar hoda tare dasa man baki
Sosai tayi kyau duk da bata cika kwalliya a fuskarta ba
Wasu tattausan riga da wondo pallazo farare al ta zaro
Sai wata doguwar riga budaddiya mai igiya a tsakiya
pantie tasa kana ta zira dogon wondon daya kasance yayi tightin fatar jikinta
Dole sa bra baya cikin jadawalin rayuwarta sabida larurar ciwonta
Sai dai takan sa rigunan su an matseta
Rigar ta zura irin mai wuyanan nane wato high neck nae wuyan tayi ta gyarashi
Cibcib rigar tayi mata a jikinta gwanin burgewa irjinta yayi cas a tsaye babu alamun ronofowa bare zubewa
Lafaffen cikinta ya taimaka kwarai wurin bayyana tsayeyyun breast inta

Doguwar rigar kimono blue color mai igon farifarin ta aura saman riga da wondon cib kuwa kimonon yayi mata ajikinta inda kuma har asa yazo mata
Igiyoyin dake sarafe tsakiyan rigar ta kama ta aure
Hakan ya bawa tsakiyar rigar haewa sama can kan irirjin ta kuma gefe da gefen ya rufu har ya samu damar rufe nimples in ta
Sai kuma tsakiyan bai ida rufuwa ba
Sai kuma can asa ta nan zaka gane riga da wondone a asan doguwar rigar farin mayafi rigar ta dauko tayi Rolling kanta fuskarta ta fito a ciki kamar sifili 0 a ciki
Sosai shigar tayi masifar mata kyau
Wanda kuma sune suturunta na yau da kullum wanda tafi so da jin dain sawa kasan cewar rigunan cikin masu taushine suna buuwa daidai jikinta

Turare mai sauin amshi ta fesa sanin sa mai tsananin amshin yana da illa ga baliga in zata fita da kuma lfyarta
Wasu fararen takalma sau ciki masu taushi tasa
Kana ta zari babbar wayarta kiran iphone11promax ta fito

A bakin ofar shigowa falon tayi kiciis da Mom cikin
Yanayin sakin fuska Mom tace
Kai masha Allah iyata kinyi kyau
Cikin yanayin jin dai tace
Ngd Mom bari inje da wuri in samu in dawo da wuri
Toh hamzarta iyata sai kin dawo
Toh tace kana ta fita ta tafi

Tana fitowa harabar gidan
Wadannan garadan marasa kan gado suka mie baki ayansu

A hankali ta matso kusa da Drivern
Cikin kula yace
Jannart yau kuma ina zamu je naga yau ba ranar aiki bane
Cikin jin dain yadda dattijon ke mata mgn ta mutuntaka tace
Baba Ado gidan Hajia Rabiah zamuje
Marfin motar ya kama da nufin bue mata da sauri tace
Baba Ado ka bari zan bue
Murmushi yayi kana ya bude mata ta shiga
Suma sauran suka shiga sauran motocin suka tafi

Suna isa gidan Hajia Rabiah
Bayan sunyi parking ta nufi cikin gida su kuma suka zauna a waje

Da sallama a bakinta ta tura ofar
Da sauri taja da baya ganin Asiya dake fitowa
Sai kuma ta shigo ganin taja gefe tana hararanta
Da sauri tayi ciki jin Hajia Rabiah na cewa
A a Jannart kin iso ko
Maza shigo daga ciki

Cikin jin dai ta shigo
Ta zauna inda Hajia Rabiah ke nuna mata
Cikin girmamawa tace
My Aunty Ina kwana
Murmushi tayi tare da cewa
Lfy lau Alhamdulillah ya an tsaron ki
Cikin yin gajeren murmushi tace
Gasu can a tsaye a bakin gate tamkar dogaran sarki
Dariya ta anyi kana ta kalli wani an matashi dake zaune can bisa kujarar Dinning area tace
Toh Mahmoud ga Jannart in ta iso
Tunda kai bawa Asiya amsa ko aya
Da sauri ta juyo ta kalli inda aka kira Mahmoud
Shi kuwa tasowa yayi ya nufo cikin falon yana mai cewa
Aunty naga kamar hasadace ke cinta kuma ma bada ita nai wayaba
Ita kuma wanna sai saii
Kin san tun safe ina nan kin ajiyeni kamar mara aikin yi
Cikin nitsuwarta tace
Im so sorry Ina kwana
Gefe ya zauna kana yace
Wuni dai tunda 12 tayi

Nan suka gaisa kana Jannart ta fuskanceshu da kyau
Cikin sani makamar aiki tace
Yaushe jirgin Ethiopia zai diro Nigeria a wanne gari aya Abuja ko Lagos ne
Murmushi Mahmoud yayi tare da cewa
Wato zaki nuna min ke yar jaridace tuni kin fara tambaya da wayo
Jirgi zaki tambaya ko shi
Kwae fuska tayi tare da kallon Hajia Rabiah kana a hankali tace
My Aunty menene ma sunan nashi
Cikin zuba mata ido Hajia Rabiah tace
Iyeh wato ma har kin mance sunan nashi Kin manta cewa sunan nashi ne kawai makaminki
Cewar Hajia Rabiah

Ita kuma Jannart takwara kanta tayi bisa kafaa kana tace
Please my Aunty gaya min zan rie

Rayyern Ta bata amsa a takaice
Ita kuwa ido ta lumshe tare da fesar da numfashi can cikin zuciyarta tace
RAYYERN RAYYERN RAYYERN Ta maimaita sunan sau uku kana ta juyo ta kalli Mahmoud cikin nitsuwa tace
Mahmoud ranar yaushe zai dawo Da wanne lokacin jirginsu zai iso daga Abuja ko Lagos zuwa Kano
Gyara zamanshi yayi kana yace
J

free PAGE

 

TUBALI
NA
AYSHA ALIYU GARKUWA

 

ASSALAMU ALAIKUM Masoyana ma karantan littattafaina ina mai farin cikin sanar daku yau din nan MON 18 OCT 2021 zaa fara biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauki Biya 500 karamin farashin na karamin group kana sai Special people Group akan farashi mai sauki 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake zaku biya ta asusuna

ACCOUNT NO 0661110170

BANK NAME AISHA ALIYU GARKUWA

BANK GTBank

sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276

PLS TAKE NOTE BAND VTU
kada kiyi min VTU ko transfern katin ta wannan numben etisalat din idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fadi miki Please and please in dai da hali kada ki turo min katin kiyi min transfern ruwan kudi ta bank account na in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy numbers in katin ki turo min ta whatsApp

Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntubi Mommy akan layinta 22790899076 ta wurinta zaku biya hoton katin zaku dauka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp Special people group 1k ne 1000 karamin group kuma 500 kacal
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da yayan jikoki mu kyautata lafazi da muamala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki

Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa
Tausayi Sarkakiya jan hankali Fadakarwa Nishadantarwa ilimantarwa alajabi Saar rayuwa rion amana cin amana ribar kyautatawa kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya

Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani kasa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min In Kuma karamin Group kike so ki sayi katin MTN ki copy numbers din ki turo min ta whatsApp numbern na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfern katin 9mobile dan layin nada matsala

Zaayi tsawon mako aya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane zaa fara biya yau MON 18 OCT 2021 Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy

Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kudinki kiji tausayin marainiya kada ku cutar da marainiyar Allah

Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar Please ina neman alfarmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba na tuba kiyi hauri ba raini bane ko wulakanci face yawan mutane wata kil ban isa kan Chart naki bane Amman muddin na isa na kuma bude na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi hauri da min mgn sai na dan samu salama.

Tubali Hausa Novel Complete Download

Novel Title Tubali Hausa Novel Complete
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 863kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author Aisha Aliyu Garkuwa
Tags Tubali
Published date 22 – 02– 2023

Karanta: Abban Sojoji Hausa Novel Book 3

Download Novel

Wasu Na karatun: Gidan dadi Hausa novel by Oum Aphnan

 

Tubali Hausa Novel Complete

 

Tags: tubali hausa novel complete,tubali hausa novel complete book 2,tubali hausa novel complete book 3,tubali hausa novel page 44,tubali hausa novel wattpad,tubali hausa novel page 31,tubali hausa novel page 50,tubali hausa novel book 1,tubali hausa novel page 40,tubali hausa novel page 1,tubali hausa novel by aisha garkuwa,tubali hausa novel na aisha garkuwa,tubali hausa novel book 3,tubali hausa novel book 2,tubali hausa novel download,tubali hausa novel complete download,tubali hausa novel end,tubali hausa novel by garkuwa,abu sadeeq hausa novel group tubali 66,http tubali hausa novel,http tubali complete hausa novel,littafin tubali hausa novel complete,littafin tubali hausa novel,tubali hausa novel on wattpad,tubali hausa novels book 2,tubali hausa novel 31 to 40,tubali hausa novel 11 to 20,tubali hausa novel 41 to 50,www.tubali hausa novel.com,Tubali hausa novel