Connect with us

Kanwata (My Sister) 1 to End

Uncategorized

Kanwata (My Sister) 1 to End

KANWATA
Written by Fatima Aminu Ya’u
Tafi minti biyu tana tsaye gabanta tana mata magana kai kace da kurma take magana ta kada kai gami da dafata adan firgice ta dago ganinta tsaye kusa da ita yasata sakin wani murmushi wanda kana ganinsa kadan yake ne.
Haba Fadya wannan wane irin tunani kike haka inata magana bakyajina takuma sakin murmushi haba Aisha banda abinki ni kuma tunanin me xanyi kawai dai gajiya nai da yawa shine bacci ya daukeni lallai baccinne ido a bude hmmm haba aisha sai kace bakisan irin bacci naba baccin kuda nake mts tai tsaki wallahi fadya kin cika rainin hankali daman na biyo miki diban ruwane umma tace kina nan wallahi nagaji da yawa yau banasan fita ko kadan kinga malama inbaxakiba basai kin batan lokaciba maida wukar muje nadauko botiki wanne botiki ai na dauko miki anman dai kinsan dole na dauko hijabi ko mst ta kuma sakin tsaki sauran ki tsaya shirita adakin.
 
Kinga ni nagaji kya tawo da sauri ta fito daga dakin dadi na dake wallahi kin cika garaje eh naji komai xakice saidai kice ta leka dakin girki inda umman keta faman hura ice umma mun tafi to kiyi sauri kar yayanki ya dawo kinsan halinsa to umma.
Nashigai tafadi Aisha tai saurin kallonta ke kuma lpy kike fatan shiga uku yah farhan na gani Allah yasa ba gida xaijeba tai dariya narasa me yasa kika cika tsoron yayan nan naki bacinma ba dukanki yake ba kedai bari bansan bata masa raine ai wallahi da nice ke shagalina xandinga sha ni nawa yayan abu kadan xaka masa sai bugu aishiyasa kika rainashi da baya duka kullun da sekinfi tsoronsa tai dariya gami da dora botikinta aka yaxaki dora baki kamanba kinsan ban iya dorawa ba ke wallahi naga sanda xaki xama jaruma.
 
Tana dire ruwan yana fitowa daga daki umma ina kanwata jiyowar da xai suka ha ido tai saurin maxewa lah yaya yaushe ka dawo bansaniba ya fada yana hade  rai bana hanaki debo ruwaba yaya kai dayane girki umma xata dora shiyasa karya kike nasa ki da danbanxan karanbani Allah yaya ba karya nakeba ko umma umman ta gyada kai haba umma nace kidinga bari ina dawowa se in debo se kuma inta jiranka ko kai ko tausayin kanka bakwaje
Kanwata
Kai anman yaya na gode sosai ya hade rai saunawa kikesan nace kidena cemun kin gode aff na manta tadan durkusa afuwa dai yai dariya kar asake tasuri ledar tai waje tana kwalama umma kira lafiya kike kirana haka kamar kinban ajiya tai dariya kingani yaya ne ya siyomun eyye yar gatan yayanta tai dariya umma sunyi kyau ko sosai ma ai yayan naki kam ya iya xabe samira data shigo aron ashana taja tsaki anmallake dan mutane anbi anmaidashi bawa badole adinga kodashi ba umma batace cikankiba tace maxa jeki kikai daki.
Umma ina abincin yaya to mai yaya gashican a madafa  tadauka takai dakinsa yana xaune  yanata  rubutu ta kai yaya kai yaya tun daxufa nace ka aje rubutun xan kawo maka abinci kai kanwar kai kanwar tun daxifa nake jiranki to ka ajiye karya huce kibari nakai nan kinji kanwis taja ta xauna tawani hade rai se cika take tana batsewa ya dago yakalleta tabashi dariya anman sai ya basar sani  halinta ya rufe takardun kamar bai gantaba yawwa kanwis xubomin tasaki murmushi yawwa ko kaifa ta xuba masa taja gefe tanai masa hira.
 
Ganin ya aje kwanon bai cinyeba yasa ta bata rai wai yaya me kake nufi nakoshi ne inba baka koshi ba dan   kaga ni badafa shi yasa kaki ci yai dariya fadya rigima ya fada a hankali haba shiyasa naji abincin dadinsa baya misaltuwa kinga karomin ma takaro masa ya cinye gaskiya kanwis kin iya girki har wani nema kike kifi umma iyawa ta turo baki inba nafi umma iyawa  hmmm aikodai umma tafiki iyawa ta mike dasauri tabar dakin tanaji yana kiranta tai masa banxa .
Yai dariya gamida cigaba da rubutunsa koda ya fito baiganta ba umma ma bata tsakar gida dan haka yaja kofarsa yai wajemu.
Kanwata
Umma wai ina Fadya ne tunda nashigo naga banji motsinta ba ince ba yawo ta ficeba da daddarennan tai dariya aiku abin nakune nafara gajiya dashi dan Allah umma tana ina tana daki tana jinka.
Tanajinka naga tashige daki aguje nasan anyi tsiyar yai dariya kinsan mutuniyar da fushi yau kuma mai ya hadaku wai dannace  kinfita iya girki hmm tunda kasan halinta maye na fada umma kenan bari na je na lallashota.
 
Haba kanwis kinsan bama haka dake ta juyar dakai ya kara matsawa daya varin takara juyawa haba yarkanwata nine fa tadago to ni ai bance kamin lefiba kince mana tunda gashi kina fishi dani tai dariya Allah yaya ba haka bane to inba haka bane maine kaina ke ciwo anman yanxu ya warke to indai ya warke to taso mutafi tsakar gida  ta mike tabi bayansa yawwa yaya ban fadama ba inajinki aikinnan dakamun nafi kowa ci dan Allah fa wallahi barima nadauko ma.
 
Ashe kanwar tawa ba wasa ce tai dariya to banda abin yaya aiduk kaine kesani a hanya dagaskefa nayi mamakin yadda kika iya amsamin wannan tambayar mamakima kai ba murna ba ai nafi kowa murna kanwar guda ta iya kice kawai inbiya miki kiyi waec yayana kenan.
 
Umma in yaya ya tashi kice masa natafi najira najira naga be fitoba kar in makara kuma ki bashi wannan dan kalin to Allah ya bada sa’a Amin ummanmu.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Haba mum dan Allah yanxu dady yakyauta kenan seda fa nace masa yacema umar yakawomin da wuri jibi yanxufa har ya wuce awa ta dafata haba yar dady nasan ya fada masa bari na kirashi ahto wallahi indai yakara awa xanyi fishi.
 
Ni gaskiya nagaji dady kagafa duk kawayena suke driving da kansu ni kullim sedai asa wani kato yakaini Allah xubarmin da ajine wannan haba faran dady kibari kiyi candy dakaina xankaiki kixabi motar dakikeso kawai ace ba’asona agidannan haba Fara ta aikema kinsan dadynki nasanki dakenan yanxu dady basona kake ba motace daiko kidinga daukan ta mum dinki ta turo baki gami da mikewa tabdi ni wallahi sabuwa nakeso shikenan xauna kiji kiyi hakuri kifara daukan tawa wadda nake hawa kafin wani satin akawo miki tabuga tsalle gami da fadawa kansa that’s my dad ya shafa kanta Fara rigima maxa jeki ki kwanta kar gobe ki makara kamar kasani gobe uncle farhan ne damu first banasa  na makara a period dinsa yai dariya aixanso ganin uncle dinnan naku tai dariya Allah dady kaima saiya birgeka tunda yana xare muku ido ba kamar kasani duk tsoransa muke.
 
Kanwata kina inane dasauri ta leko yah gani haryanxu baki shirya bane eh yaya kinga nashirya kiyi maxa mutafi aidakayi tafiyarka kasanta da nauyin tsiya karta makarar dakai tunda naji kuma malamai a makarantar taku kamar tararku suke yai dariya aikinsan abinka da private sunfima takurama malamai kanxuwa fiye da dalibi aishiyasa yaran suke rainaku uhum tunda munasan kudi ai hakuri yakamamu.
 
Tafe suke suna hira irinta yaya da kanwarsa sunxo daidai inda xasuhau mota motar ta tsaya agabansu ta fito sanye da uniform lah uncle morning dasauri ya juya yasaki murmushi Fara kece eh uncle ba sch xaka bane eh can xani to kaxo mu tafi no kibarshi nagode xan sauke Kanwata a sch dinsu sai alokacin ta kalleta hy sis tadanyi murmushi batare da tabata amsaba basaimu sauketaba a’a yaya ni baxan shiga motar kowa ba to kinji tace baxa shiga va kiyi hakuri kitafi karki makara pls sis kixo mutafi mana kinga nifa nace baxan shigaba kina batamana lokaci kina batama kanki ok bye semun sake haduwa uncle sekaxo tashiga motar umar yaja sukai gaba.
 
Yawwa kanwis inasan mgn dake to yaya ka gama cin abincin tukunna bamai yawa bace to yaya wai daxu meyasa kika ki shiga motar Farah tai dariya yaya sabida kai ni kuma eh yaya.
 
Kaga student dinka ce naga alamar kuna mutunci watakil har a class kaga da sassafe kawai aga kunxo sch tare xargi xe shiga dalibai ko basuga alamaba sukan hada sharrinsu itama bakasan niyarta ba xata iyama sharri naki shigane dan kawai nakare mutuncinka danbaga kai bakai wannan tunaninba yai dariya kanwata kenan mesona.
 
Momy kinsan me sekin fada Allah akwai wani uncle dinmu yana mana k.miss.3 guy din yana ban tausayi tai dariya towo yau kuma Fara ke tausayi lallai yarinyar tawa anfara hankali Allah mum duk teachers dinmu shine talaka kusan kullum indai mun fita sch da wuri se naganshi a hanya ko keke bashida gashi principal dinmu yaita masa wulakanci tai murmushi ai irin wadannan temakonsu matsalane tsiyar talaka kataimaka masa yaxame maka da  kunama.
Lah yaya yau da littattafan students dinka kaxo eh nabasu assigment ne inasan makawa ta dauka bara nagani naga ko suna da kokari gani a ashe dai sunadan ja sosaima kedai barsu da raina malamansu.
 
Kyautarki ta musanmance kanwata fatana yadda kika ciyo wannan qualifying din ki ci waec in sha’Allah yaya xaka xamo mai alfahari da kanwarka tam shikenan kibasu mamakious kinji ko tai dariya kataya ni da addu’a
Kanwata
Na  F.A.Ya’u
Umma xan tafi kimin addu’a yau xamu fara exam aikullum inai muku umma tayau tadaban xakimin toshikenan sekin dawo Allah ya bada sa’a amin ummana ta fice dan yau yayan nata ya rigata fita.
 
Kai gaskiya yaya exam ta kwala ya xaro ido dagaske ba karya fatandai kin amsa a alhamdulillah insha Allah xamu haye to madallah naga duk kin rame kinko ci abinci a’a yaya kai nake jira kadawo muci kanwis kenan sau nawa xance kidena jirana kidinga cin abincinki to yaya baxa’a kuma ba.
 
Juyi kawai yake yarasa meke damunsa daya rufe ido ita yake gani yakasa yadda da xuciyarsa kan Fara take so yasani yarinyar ta ko ina basu dace akullum inbaiganta ba ba iya tabuka komai yasani bata lokacinsa kawai yake.
Duk yadda yaso cire yarinyar aransa abin yaci tura da ya xauna sai tunaninta in bacci yake ita yake gani shikansa yana mamakin yadda yakamu da yawa.
Tafi minti uku atsaye agabansa kafin tasaka littafi ta dan tavashi yaya kanaji inata magana kamin banxa adan firgice yace na’am Fara tako hade rai yanxu yaya nice baka ganeba yaisaurin basarwa haba kanwis fadya nacefa kece bakiji uhum yaya kenan ta fice rai abace.
 
Yauce ranar karshe wato ranar last paper dinsu Fara a sch wadda yake ganin itace last chance dinsa naganin fara ranar dayasan sudin ta farin ciki ce shiko agunsa ko kadan bayafarin ciki yaran sai kai kawo suke da’alama jira suke kawai akawo papers su kammala su fito yana tsaye kofar ajin yaji maganar muhd uncle daman xamuyi Patty ne gobe asabar fatan xaka xo a ina kenan a sch ne ok xanyi tunani to uncle yan matanne suka fito pls uncle katai maka kaxo xamuyi pic kaga tarihine yai dariya shikenan xanxo.
 
Iya kyau yau kam fara tayi ita kanta tasan ta hadu yau taci burin fara hawa motarta da dad ya siyo mata sabuwa dal yana tsaye shida uncle fahad abakin gate suna hira sukaga tsayawar motar ba fahad ba shikansa da bai cika damuwa da kyalkyalin duniya ba anman motar ta gama tafiya dashi a hankula ta fito tana hangosu ta kara fadada murmushinta ahankula ta karaso uncles afternoon suka gaisa ta shige ciki fahad ne yace kasan Allah Farhan yaran sch dinnan sun gaji da haduwa matsalar kace kanasan yarinya ta dijgaka yai dariya Allah da gaske nake sekaga yarinya ta xage tana soyayya da class mate dinta anman mu malamai anai mana kallon tara saura kwata kaga xo mushiga dan sauri nake lallai mutumin nan watakan bama xaka ban amsaba ko to mai kake so nace katayani jajantawa rashin yan mata masu kyau yai dariya ka gwadane ba sa’a ba daya anman ai mutum yasan inda yakeda mutunci Allah naso nine kai hhhh ni kuma eh mana yarannan suna sanka da yawa dan singa va fuskane da tuni sun taya.
 
Lah uncle Farhan munko yi pic kuwa eh mana baki kula bane tai dariya duk nashiga busy hakane nidai xan wuce naga dare nayi kabari nasaukeka a’a kibarshi xan biya ta wani gu ok mukan bayanxufa shi kenan se mun sake haduwa ya xura hannu a aljihu ya ciro wata takarda gatawa happy candy din ta amsa tana dariya nagode tana kokarin budewa af ban fada miki ba sekinje gida xaki vude special ce tai dariya sauran su uncle fahad Allah inbasu ban happy candy ba ko naxo xiyara baxan nemesu ba yai dariya see u.
Kwance take kan luntsumemen gadonta takasa bacci juyi kawai take takasa bacci tarasa wani irin so take masa duk sanda ta tunkareshi saitaga yanai mata kwarjini wahalar banxa kike bemasan kinaiba tashare hawayen ta dasuka xubo xumbur ta mike dan tunawa da takardar da ya bata dasauri ta jawo jakar da tunda tadawo tai cilli da ita ga mamakinta bata cikin jakar kaf ta xaxxage jakar bat cuki kayanda ta cire ta hau xaxxagewa bata opp ta fadi gamida dafe kanta duk inda tasan xata ganta bata ciki  wayyo ni fara ta durkushe ko maine aciki ni ba’abin naje sch ba nasan anyi shara ni ba’abin na je nace masa banganta ba yaban wata awan ne dalili gaskiya nakwafsa
Ta mike xumbir dan yanke wata shawara a xuciyarta
 
Kanwata
Na  F.A.Ya’u
Da sassafe ta tashi duda baccin datake ko mominta bataje ta fadama dan tasan vaxata barta ta fita ba tana shiga motarta ta ci karo da takardar murnarta ta karu sosai shikenan nafasa fita daman niyarta taje tasamu masu shara ta rokesu ko xasu gani insuna shara.
 
Tana shiga dakinta ta fada gado ta bude takardar  takaranta yafi sau goma gani take kamar badagaske bane .
 
Yaukan kowa gidansu yasan tana cikin farin ciki dan yadda taketa annashuwa.
 
Yaya wai maike damunka ne  mai kikaga ni naga duk walwalarka ta ragu kamar kana cikin damuw yai dariya kece dai kikaga haka kinsan yanayin rayuwa tai dariya yaya kenan tajuya xata fice tayi abin yasanta da fishi  xonan xonan ya kirata ta dawo ta xaina sarkin fishi me akai to bakai bane kana cikin damuwa ka kasa fadamin me ke damunka kanunan niba komai bace agunka nice nafaukeka yaya yai dariya haba fadya kema aikinsan banda kamarki to indai hakane kafadan meke damunka banajin dadin cikina ne nakejin kamar ciwona xai tai tashi subhanallahi anman shine kake boyewa haba yaya to kage asibiti inasan dai nage gaskiya yaya yakamata kadaure kaje toshikenan xanje.
 
Tunsafe Fara take ta kintsawa tamarasa wacce irin tarba xata masa sanin halin iyayanta yasanya babu wanda taima maganar dan haka ita daya take bidirinta.
 
Bayan idarda magriba ne tace ummanta xata farfajiya  momin bata kawo komi rantaba tace to aikuwa bata dade da xamaba habu mai gadi yaxo yasameta tanada bako tace ya shigo.
 
Karbakam yasameta baitaba xaton xata amshi batunsa da wuri haka ba sunsha hirarsu kai kace sun shekara suna soyayya.sai wajen tara yai mata sallama ya tafi suka rabu cike da kewa
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Juyi kawai take baccin yaki xiyartarta yayinda xuciyarta ke cike taf da tunwnin yayan nata ta yadda batun yauba ta kamu dasansa wanda tasan ba’abu ne mai yiwuwaba hakurinta ya fara gaxawa tasan kuskure mafi girma daxata ma kanta shine yasan tana sansa so na aure.
 
Wayyo xuciyata bakomun adalciba wallahi ta dunkule kanta cikin filo dan kar ajiyo kukanta inda sabo ta saba duk dare saitai wannan kukan.
 
Yana xaune yana waya da abar sansa tashigo dakin kalmarsa ta karshe data ji itace aikema kinsan inasanki dire kwanon tai dasauri ta bar dakin can bangaren kawu malan tai gurin da suke kiwo tashige ciki sosai tana xama kuka ya kwace mata lallaima yayan nan ashe shi soyayyarsa ma yake yabarta tana fama da dakon sansa wata xuciyar tace to danme bazai soyayyarsa ba kefa vakomai bace face kanwarsa shikuwa koda yaga fitarta bai kawo komai ransa ba face ko sauri take ko xatai wani abunne dan haka ya cigaba da hirarsa.
 
Kanwis taji yana kiranta wani haushinsa takeji wanda tasan xai iya gani afuskarta kuma sai ya tambaya to mai xance masa kice sansa kawai kike dakin cika mara hankali ita kadai take mgn tana bama kanta amsa dan haka takara jan xanin rufarta umma dake laximi ta leko bata tashiba naga jiya bata kwanta da wuriba yai dariya inta tashi kice mata na fita to shikenan Allah ya bada sa’a ya amsa da amin.
 
Fadya kenan Allah kina ban mamaki da yawa duk samari dake rushing akanki anman ke vakima san susunai ba tai dariya keni rabani da vatun love karatu nakesan nayi watakil kansannan burina ya cika hhhh burinki nasan maso waniba ta xaro ido ban fuskantaba tai dariya manta kawai dan Allah Aisha kifadan mai kike nufi tajuyar da kai anfada miki bansan kinasan yaya farhanba what tafada gamida mikewa ke wacce irin mara tunanice kin taba ganin inda yaya ya auri Kanwarsa sai kace a garin gaba gaba bansan shirme wallahi indai kinasan mushirya kidaina min irin wannan wasan tai dariya to ai cewa nai kinasa so kuma aibaya nufin aure ko wacce kanwa nasan yayanta bawai so na aure nake nufiba tai ajiyar xuciya gami da komawa ta xauna tonidai banasan irin wannan wasa andena ta fada.
 
Faran dady yaxam jiran result tai dariya gamunan dai dady  yawwa kinadai review din karatunko eh dady tam banda wasa kuma banda soyayya kinji ko tadan kalleshi dady ya batun fitata wajen yaidan shuru kiyi hakuri munyi mgn da inna kaka taki yadda kinsan halinta tai murmushi to shikenan Allah yasa nasamu abinda na nema anan yawwa haka nakeso naji daman inata tsoron karki tubure to amman dady nace ma xani gidan inna kaka hutu kaki cewa komai ai tunda kin hakura na yarda sekin dawo ta daka tsalle nagode dady tayi hakane dan tasan tunda dady ya dawo indai yaganta da Farhan tashiga uku inkuwa tana gidan inna tasha shagalinta dan ita tsohuwar burinta taga auranta.
Kanwata
Kuka kawai take tana faman masa sannu yayinda ko yawwa ba ya iya fadi sabida axabar ciwo umma yakamata muje asibiti ai wani abu haba fadya cikin darennan ina xamu sami mai mota inji baba bako gidan malan musane ka buga koxamu samu yaje kumafa kinkawo dabara dasauri ya fice bai wani jima yana buguba ya bude bema gama masa bayaniba yajuya bari na dauko mukullin.
 
Kai tsaye murtala suka wuce sunyi sa’a kuwa da gado ba wata jan lokaci aka basu kwanciya anan suka kwana sai da safe da wasu cikin yan uwa sukaxo sannan suka tawo dan debo wasu kayan.
 
Juyi kadan xaiyi xata mike sannu yaya mai kake bukata yai dariya bakomai kanwata.
 
Kwanansa biyu a asibitin Fara taxo dubashi harda kakarta fadya jitai kamar ta mace agurin dan takaici dagyar ta iya tankwara xuciyarta ta bata hakurin xama agurin batare da kowa ya fiskanci wani abuba duda kuwa Fara taxo dubashi matsayinta na daliba bawai budurwaba duda bawai ita daya ce taxo dinba danshi kansa yasan dalibansa sun masa kara daga wannan taxo sai wancan anman tarasa mai yasa take kishin yarinyar kodan ganin yadda ta damune da ciwon Farhan dinne oho.
 
Zaune suke anadan taba hira adaki bayan sallamoshi daga asibiti baba kakarta tace waini kuwa yaushe xanga aurenki Fadya tai dariya kakale kenan watakan kishiya ma kike nema ko dankinsan banda angon da ya fice naki mijin komadai waye nidai nagaji ince cewa kikai sekin kammala karatu Farhan yai saurin cewa banda abin baba ai yanxu aka fara karatun tamai dakuwa ungonan wato kai kaki aure kakesan itama ka hanata ko yai dariya aikedince kinyi yarunta da yawa datuni ba adaura ba wallahi yarannan kun rainani naga alamun so kuke sai na fito muku da abokan rayuwar dakaina ko sukai dariya gaba daya to cemiki akai munyi kwantai haka naga alama ai.
 
Salamu alaikum wai ana sallama da Fadya jeka kace bata nan kai jeka kace tana xuwa wallahi fadya nafara gajiya da halinki kinsa sai xagina ake a gidannan yakamata kiyi tunani karatu kyayi agidan mijinki.
 
Ta turo baki gami da mikewa ta xari hijabi tanata faman kunkuni ta fice.
 
Kanwata
Yadda ya hade rai ya tabbar mata ransa a bace yake tace yaya gani eh naganki yaya konaima lefi ne lefi ai wannan yafi karfin lefi daman wasa kike ba karatuba ko ta dafe kirji nashina yaya ko wani lefin akace nayi aiwannan yafi karfin cewa kirasa mai xaki ciyo a waec sai F har tara ta dafe kirji innalillahi wainna ilaihi raji’un sai hawaye shar ya bushe da dariya congratulations kyautarki dabance kin haye sai tsalle kai anman yaya kadauki alhakina da yawa inaso naga yaxakiyi inkin shiga matsala senaga ashe kina bin abinda nakoya miki tunda bakiyi ihu ba tai dariya yace yanxu sauran post utme ko eh yaya kutayamu addu’a insha Allah.
 
Komai yadda takeso haka yake tafiya tasamu BSC nursing dinta murna kamar me ranarda xasu fara lecture tasha nasiha kan kiyaye mutuncinta
Kanwata
Ba’abinda ke damun fara game da alakarta da farhan illa halin dad dinta baisan talaka balle abinda yashafi talaka duda tana ganin akan Farhan xata iya daukan ko wacce kasada ayauma hirar da sukai ce ta tsaya mata yadda yake ta bayani irin yadda yake kin talauci da talaka duda tasan dadin nata nasanta yanasan abinda takeso.
 
Farhan dan Allah wata alfarma xakamin haba abokina ai tsakaninmu ba irin haka fadi kanka tsaye yai dariya wani abu ke damuna haba muhd inbaka fadanba wane kakeso kafadawa baka da kamata nima banda kamarka Fadya ce matsalata matsalarka kamar ya santa nake narasa yadda xanyi ta fuskanceni waima wacce fadyar kanwarka yai tsaki tunfarko shine baka fadanba to nai mata miji sekaje ka nemi wata xumbur ya mike what yasa daria xauna kaji Allah ya temakeka ban bada itaba karkaji komai xan sameta nagode aboki sukacigaba da firarsu.
 
Hartakai bakin kofa yace inkin kai kayan kixo muyi wata magana to yaya ta fice .
Kace xamuyi maga eh daman so nake naroki wata alfarma tai saurin dago kai haba yaya alfarma kuma bani umarni kawai xakai nabi yaji dadin batunta yawwa kanwata aikinsan muhd ko eh yaya to shine yaxo guna kan inbashi dama yaxo kugana kan yanasan ku fahinci juna watakil hakan takaiga aure kinga yanxu university kike yakamata ace kin tsaida wanda xaki aura tai shuru dakyar ta iya cewa to yaya tunda kayadda da dabi’unsa nima nayadda matsayinsa na babban abokinka yawwa kanwata nagode tashi kije.
 
Koda tabar dakin bayan dakinsu taje tasha kukanta watakan ita daya take haukanta shi bema san tanaiba tunda gashi da kansa yake mata batun wani yanaima ma wanin kanfen.
Ita kadai tasan mai takeji aranta duda kokarin datake wajen yakiceshi aranta wajen ganin bata nuna wata alamaba duda kuwa da’ace yayan nata mai ganewa ne da tuni ya gama fuskanta.
Mum wai yaushe dad xai dawo ne eh to may be a cikin week dinnan to Allah yadawo dashi lpy amin fara kina da bukatar kudine babu daya kawai naga ya jima acan tai dariya nima haka nagama naw korafin yako karatun naku karatu basauki mum niduk nagaji wallahi hakuri xakiyi haka karatu yake da cinrai.
 
Waiko ya kike ganin tafiyar karatun fara komai normal aikasani duda yar shagwabace bata wasa da karatu duda ta fara mita ta gaji aikindanta batasan wahala kafin ta sabane ince dai ana kiyaye dokata tai dariya itama kanta batasa soyayya atsarinta ba balle ta bada fuska yai dariya haka nakeso nafiso tai karatu dakyau.
 
Fadya na iya kokarinta wajen tsayawa da muhd duk dan farantawa yayanta rai duda kuwa bata taba jin sansa arantaba bakumatajin xata soshi.
Kanwata
Wane karatu haryaushe karatun xai kare nagaji wallahi inba sokake sai na mutu sannan xaka aurar da ita ba tafara sharar kwallah ya durkushe gabanta kiyi hakuri inna nai miki alkawarin awatannan xa’a gama komai na auran tasa dariya kokaifa ya mike nixan wuce to Allah yabada sa’a yayi albarka ya amsa da amin.
 
Lafiya kuwa dady naga kamar kana cikin damuwa yai dariya baccine kawai a idona Fara to dady kaje ka kwanta ka wuta kasan rashin bacci natsalane ya mike kumafa gaskiyarki bara naje.
 
Mum naga kamar dad nacikin damuwa mekika gani naje inai masa mgn yanacan cikin tunani towo bara naje na sameshi.
 
Zarya kawai yake adakin dadin fara lpy kuwa yajuyo yaxauna gefen gadon itama ta xauna nan ya fada mata dik yadda sukai da innars tai shuru kafin tace ai wannan ba matsala bace kamarya ba matsala bace ka eh ba matsala bace tunda ai babu wanda takeso balle ace bai shiryaba cikin yayan abokanka kabaima daya wanda xai barta tai karatunta sai alokacin yai dariya kumafa kin kawo shawara mai kyau bama dan abokina xan baimaba ba.
 
Salim din yaya faiz yasha mun magana inacewa yakara time shima yaya faix din haka xance kawai yaxo su tattauna nasan innar xatai farin ciki itama tai dariya Allah ya nuna mn time din lpy.
 
Fara na’am dady kishirya yau xakiyi bako ni nabashi dama ta dafe kirji bako dad eh kinma sanshi yayanki ne salim amman dady bai bari yaji mai xatace ba yai ficewarsa.
 
Wai fara gambo batace miki kina da bako bane ta turo baki tafadan to maxa kije aman mum maxa tashi kije.
 
Ko sallama bataiba taxauna yana kallonta ya washe baki hajiya Fara ina yini dakyar ta iya amsawa da lpy.
 
Wai kai vakasan amaka shiru bane ka ishenifa yai dariya ayimun afuwa baxan sakeba pls alfarma xaka min katai maka kaje kasamu dad kace bakaso na pls yai dariya ina baxan iya ba tokuwa wallahi kadaukowa kanka wahala dan wallahi baxan sokadady.
Kanwata
Yanxu mum haka ake ace baxa’a tambayeni ba kawai ace anmun miji ama rasa wanda xa’amin sai salim niwallahi banasansa to inbakya sansa wane kikeso ni wallahi uncle Farhan nakeso toshidin dan uban waye haba mum shinefa nake baki lbr malaminmu a sch what baki da hankali wallahi kima rasa waye kikeso sai teacher kuma na private sch wanda akoyaushe xe iya barin aiki haba mum ni bakudinsa nakeso ba shi nakeso kinga kimayi shiru da wannan batun tunkan dad dinki yaji.
 
Ni wallahi dabadan badanba sai ince ya salim kai maye ne ance ba’asanka ana soyayya dolene nace banasanka banasanka.
Gaskiya baba nagaji da abinda Fara take mun nama yanke shawarar hakura da ita kayi hakuri bansan xumunci ya baci ina baxai yuwuba xan samu baban nata kotanaso ko bataso se anyi baxata batan tsarina ba.
 
Yanxu a hakane kake cewa ka isa da yarka har ada innaxo nace kabaima salim dama yabayyana mata kansa kace inyi hakuri lokacine dakanka xaka ban time innace kar wani ya rigashi kace ka isa daita vata kula kowa to jiya salim yasameni yafadan irin cin kaahin da take masa ita tanada wanda takeso what Faran eh ita kayi hakuri yaya xan sameta.
 
Fara fara yake kwalla mata kira da gudu ta fito opp lpy dad kake kwalan kira haka keni kike tambaya lpy nake kiranki yi hakuri dady tafada xonan magana xamuyi ta fahinta to dady.
Kanwata
Mai kika cema salim takalleshi bakomai karya kike kifadan mai kika ce masa cewa nai ya rabu dani inada wanda nakeso what me kika ce eh dady cewa kai nai karatu karnai wasa da karatun kar inbiyema soyayya kuma naga ina karatu soyayyata da Farhan bata taba hanani kawo maka result mai kyauba ya mike naji wayeshi farhan din dad malamin mune a sch what kina da hankali kuwa awacce unguwa yake dad dan unguwar nan ne yadan xauna dan wane gidane dad dan gidan rinji ne ya mike wallahi baxai yiyuba yata baxata taba auran talakaba ta fashe da kuka nima wallahi bansan yaya salim farhan ne xabina.
 
Yauce ranar farko dayafara danasanin yima fara duk abinda take so.
Alhaji lamarin yarinyar nan yafa fara ban tsoro ta dena fitowa abinci in ankai yadda aka kai haka ake daukowa ya mike bara naje basameta tana kudundune akan gado ya dagota jikinnan rau xafi subhanallahi baki da lpy sai hawaye da sauri ya fice ya hado mata tea mai xafi yabata nan danan gumi ya rufeta haba fara yakikeson illata kanki tai shiru kiyi hakuri da xabin danai miki nan gaba xaki fuskanceni sai kuka dad dan Allah kabarni da xabina wallahi banasan salim xan iya mutuwa na aureshi aiko saidai ki mutu aure ba fashi ya mike gami dayin tsaki ya fice .
 
Alhaji kasan mai xakai yaron xaka kirawo kabashi kudi kasa shida kansa yace bayayi yaxo yace mata yadena santa kin kin kawo shawara gobe xansa akiraminshi yawwa alhaji dan gaskiya banasan kasaida akuya taxo tana cimana danga ai hakan xanyi Allah dai  yakaimu goben
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Kanwis yakika ganni takalleshi gaskiya ka hadu yaya amman hularce dai bari kaga ta shiga dakin tadauko wata yawwa kaga wannan itace dai dai yakarba yana dariya kai nima sai yanxu naga nafito kanwar tawa ta iya xabi.
 
Yaya naji umma na cewa agaidasu wai ina xaka ne yai dariya aff afuwan nayi mantuwa ban fadamiki ba baban auntinki yake kirana bansan mai xai cemunba tai dariya wadda kana gani yake ce to yaya Allah yasa adace agaida mun da ita yace amin bari naje yana fita ta fada bandaki tasha kukanta ta fito.
 
Zaune yake kasan kafet din kansa akasa yaji shigowar sa ya mike alamar girmamawa saida ya xauna sannan shima yakoma mazauninsa yagaidashi cike da girmamawa kafin yace.
 
Nakirakane dan muyi wata masala Fara ta fadan komai inasan kamin wata alfaema komai kakeso xan baka daga million daya xuwa hamsim yakalleshi baba wacce alfaema kenan yawwa so nake karabu da fara what yabfada baxan iyaba wallahi kudi baxai taba sawa in saida soyayyata ba  to kuwa inbakai tasaukiba inada hanyoyi da dama na rabaku inason daga yau bakai ba yata na fada maka baba dan Allah karka rabamu wallahi inasanta kai ni kake fadima haka maxa fitaemin daga gida da alama talauci baxai barka ba natsiyaci kawai.
 
Yaya lpy kuwa naga kafita cike da farin ciki kadawo duk rai abace yadan kalleta kafin ya share kwallar data kawo masa subhanallahi yaya kuka kuma nan yafada mata abinda ya faru ga mamakinta mai makon taxama mai marin ciki sai tasamu kanta cikin kunxi kayi hakuri yaya ai kasan halinsa da ake fade yasaba cima talakawa murunci kuma in matarka ce dole sai ka aureta kudi kuma insha Allahu sai ka bashi mamaki kudi bashine jin dadi ba kaji yayana yadago yakalleta nasani kanwata nagode da kokarinki na karfafan gwiwa.
 
Kanwata
Na.F.A.Ya’u
Yaya dan Allah ka cire damuwa aranka komai dan hakuri ne yai dariya Fadya kenan abinda ke damuna gidan nasu an hanani xuwa innaje mai gadi ya hanani shiga a sch dinna naje yafi akirga van ganinta kawarta tace an gahanata xuwa se bayan bikinta yanxu sauran sati uku.
 
Tai shiru kafin tace inada dabara lokacin dabaka da lpy ba tareda kakarta taxo ba yace to kasamu kasa taje can gidan kakar naga alamar tanasanta da yawa tasauyama baban ra’ayi ehto kin kawo shawara but yanxufa nace miki banida damar samunta wayoyintama an kwace kabari xanje gidan nasu nagode sosai kanwata Allah yabarmu tare tai dariya baka bukatar godiya yaya ta mike ta fice.
 
Sun gaisa da mum din fara kafin fadya tace momy fara tananan kuwa eh tana dakinta ta nuno mata dakin ta mike tai dakin tana kwance afadonta ta rufe idanta da alamu ba bacci takeba tadan tavata ta bude idon ganinta yasa ta mike xaune kanwarmu kece tai dariya en nice da fara’arta tace lalelale taje ta kawo mata ruwa da lemo tace gambo ta kawo mata abinci bayan tadan xaunane take fada mata abin da yakawota tai shiru kumafa kin kawo shawara suka dan taba hira kafin fadya ta mike bara na wuce har farfajiya ta rakota.
Dad dan Allah inasan xuwa gidan inna kaka ok kibari xan kaiki inyaso inxan dawo naxo na tafi dake to dady.
 
Amarya da yawo aishiyasa nace bara na kawota da kaina yagaida innar yabar gidan ya fita Fara ta fada kan innar tana kuka yanxu inna da ranki xa’amin auran doke kekinsan Farhan nakeso tasa salati yanxu daman yaronnan karya yamun yace ku kuka shirya kanku keda salim din kodaya inna wallahi banasansa kibarni dashi dagashi har faiz din ta ce daukon wayata kiramin faiz din ta kira tana shiga ta mika mata kaxo kaida salim inasan ganinku ta kashe kiramin shi baban naki ta kirashi shima tace yaxo yanxunnan.
 
Cikinku ba wanda akaima auran dole dan haka itama zabinta xa’a bata kuma duk wanda yakibin abinda nace van yafe masa ma salim ne yace haba inna karki mantafa ni jikanki ne wancan vare ne tai dariya ban mantaba shi aure ba ruwansa da alaka kubata abinda takeso faiz ya mike gami da yarfe hannu daman nasani kintsaneni gashi abin har yakai ga kan dana bai jira amsarsuba ya fice yabar gidan shida salim din dady ya daka mata tsawa sai kitashi mu tafiko kaga masur karka takura mata na fada maka.
 
Tunda kin nunan ni ban isa dakeba harkinasan hadani da uwata kisani zan aura miki wanda kikeso ta buga tsalle alhamdulillah dakata ai ban gama anman inasan kisa aranki daga randa kika fita gidannan matsayin matar wannan yaron kisa aranki kin fita kenan karkiyi tunanin ke daya na haifa yadda kika nuna ni ba ubanki bane to wallahi kema ba yata bace dad dan Allah kayi hakuri bana nufin batamaka rai vata rai na nawa ai kin ban mamaki ace duk gatan danai miki ki kasamun alfarma daya danataba naima agurinki.
Kanwata
Na.F.A.Ya’u
Tunda suka shiga motar take kuka tanai masa sannu yayinda hankalinsa baima jikinsa gaba daya ya gama fita daga hayyacinsa suna xuwa akai emergency da su likitocine wajan su hudu akansa sunfi minti goma sha biyar kafin daya daga cikinsu ya fito yana share gumi sukai kansa suna tambayar lpy yai office inda baba yabi bayansa.
Gaskiya yaronku na cikin matsala domin kodarsa duk biyun sun lalace yana bukatae adasa masa wata subhanallahi yanxu doctor yaxamuyi ehto xuwa xakuyi a gwaggwadaku in ansamu mai lpy acira anman sai kun hanxarta dan yanacikin hatsari bara naje nan ya fita su umma sukayo gurin suna tambayar lpy ya fada musu fara da tun fitowarsu fadya tai mata waya yanxu ta fito tai office din doctor ni aciri tawa yace muje sai an gwada.
 
Angwada saidai itama tatan vatada cikakken lpy duk ta wanda aka gwada bataiba ta fadya ce kawai normal dan haka tata xa’a cira abba yasanya hannu akan takaddun yayinda fadya taja Aisha gefe Aisha inaji araina baxan tashiba duda kuwa doctors sunce ba matsala ki min wata alfarma inajinki samo min biro da takarda tasamo suka xagaya baya taxauna tai rubutu gashi wannan nasanki kinada rukon amana karki sauya ayau kitai maka saikin ga gawata xaki baima yaya farhan bance ki karantaba inna fito lpy xaki bani abata ta rungumeta ki rike alkawari nasani xaki tashi kedai vari taja hannunta suka dawo ta shiga dakin aikin tana daga musu hannu.
Aiki kam komai lpy fan har fadya ta farfado an xagayeta anata mata sannu yayinda shima farhan ya farfado har yana gane jama’a
Yau kwanansu hudu a asibiti har mgn suke tana iya xama tana komai yau daga ita sai ummanta sai yaya farhan dake bacci wayyo umma kirjina jinake kamae xuciyata xata fito ta mike da sauri vari na kira likita ta fice tana kwala masa kira  yaahigo da sauri ganin nunfashinta na sama da kasa yasanya yace nurse ta fito da ita daga dakin wani dakin aka kaita inda umma keta kai kawo agurin abin ya wuce tunanin doctor duk wani tai mako daxai iya yayi ba sauki nan yakira wani doctor dinyana xuwa yadan dubata yace xuciyarta ce ba lpy dan yanxu dakyar take iya aiki hankalinsu umma duk atashe yake doctor ya fito yana goge gumi yayinda suke tambayarsa lpy yadai yadan tsaya sai hakuri Allah yai mata cikawa saidai ba sanadiyar wannan aikin bane xuciyarta ce ta buga ya wuce yavarsu masu kuka nayi masu salati nayi.
Saida aka biya komai kafin su iya daukar gawar.
Farhan da baisan meke faruwaba ya farka baiganta bai kawo komai ransaba dan jiyama ya farka ba gadonta adakin daga bisani nurse suka dawo da ita Aisha tai sallama ta shigo yaya ya jikin ya amsa da sauki ta mika masa takarda gashi inji fadya ta mike tabar dakin dan kukan da yakwace mata.
 
Kanwata
NaF.A.Ya’u
Ya kalli takarda har ya aje gefen gadon komai ya tuna oho ya dauka ya bude dan karantawa.
Assalamu Alaik.
Yahna nasan xakai mamakin ganin wannan takardar daga kanwarka anman ni gurina bata xama bin mamakiba naso ace baki da baki xamuyi ban kwana sedai bansamu wannan damarma.
 
Yahna na rubuta maka wannan takardar ne dan infada maka wani abu da yadade yana cimin rai wanda nakasa samun damar fada maka sai yau.
 
Yahna naso ace lokacin da muke raye tare koda saudaya ne kace kanwata kece irin matar da nake muradin aura sai gashi har nabar duniya burina bai cikaba .yahna inasan kamin wata alfaema komai tsawon lokacin daka dauka baka karanta takardata ba duk sanda ka karanta kadaure ko saudayane kace inasanki Fadya matsayina na fadya ba kanwarka ba.
Kasan wani abu akullum idan kace inasanki nakanso naji karshen shine fadya saidai kash kullum bakinka kance Fara.
Naso barmaka wani abu nawa saidai kash banida komai da ya cancanceka anman xan xamto mai alfaharin wani abu nawa yana jikinka kana rayuwa dashi kadaure karka manta dani akullum ni maisan abinda kake so ce naso ace xanga aurenka da fara saidai kash mutuwa taxama katanga inai muku fatan alkairi a auranku Allah ya baku xurriya ta gari ina tabbatar maka da Fara maisankace baxa samu kamarta ba kadaure ka riketa amana.
Maisanka kanwarka.
Ya fashe da kuka gami fa rungume takardar mai yasa ban fuskanta ba mai yasa nakasa ganowa wayyo kaicona kuka yakara kwace masa muttaka ya shugo kayi hakuri wayema ya fada maka rasuwarnan saidafa baba tace kar afadama anman kayi hakuri duk mai rai sai ya dan dana xafin mutuwa.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Farhan dane ga malan isa wanda ke xaune agarin kano shida matarsa da sauran yan uwansa gidansu irin gidan gandunnan wato babban gida daya hadarda kanne da matansu yayu da matansu da yayensu.
Farhan nada shekaru tara aduniya Allah yaima mahaifiyarsa rasuwa watanninta uku da rasuwa bavansa yakara aure inda ya auro wata axxalimar mata babu irin axabar dabata ganawa farhan abinci sai taga dama xata bashi sauran mutan gidan nakallo basa cewa komai yaron duk yabi ya rame yai baki sabida wahala.
 
Cikin wannan halinne daya daga cikin kannen malan isa wato sule yai aure inda ya yanki bangaren daga bangaren yayan nasu yai nasa bangaren shida amaryarsa.
 
Yadda amaryar sule taga irin axabar da farhan ke ciki tun bata magana saidai tadau abinci tabashi aboye har takai tana sabaki wajen bada hakuri in ana dukansa.
 
Dukanda yau dijan taima farhan yabama mairo tsoro tadaureshi adaki ko abinci ta hana abashi tun yaron na ihuu haryai shuru hakan yasanya maigidanta na dawowa ta fada masa aiko yaje yaxaje matar yayan nasa ya balla dakin yadauko yaron dako motsi bayai sai asibiti.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Koda sukaje asibiti kin karbarsa sukai sesun kawo police dakyar aka amahesu shima dan sunsan wata doctor basu suka baro asibitinba sai dare.
 
Cikin daren da dawowarsu yayan nasa yaxo yaxageshi tas yakwace dansa gami da masa katanga da gidansa da kuma iyalinsa matar na xugashi  kai har ka isa ka hana uwa yin hukunci akan danta xagi kam vabu wanda baishaba shida matarsa ko takan magungunan basu biba balle ayi tunanin bashi.
 
Malan isa yai fushi ya cire hannunsa kan batun m
Dan yayan nasa duda kuwa ya jin ciwo da tausayin yaron  yau kanwar mahaifiyar farhan taxo gidan ganin yadda ake axabtar dayaron yasanya taje tasamu mai unguwa tasanar masa bai kasa aguiwaba yaxo gidan yai musu nasihohi nan baban Farhan ya hau balai da ai nawane yadda ban nuna ma kowa iko kan nasa iyalinba dan haka nima abarni da nawa mai unguwa ya hasala anan take ya bugawa police sukaxo sukai awon gaba dashi saida yakwan ya yini sannan aka sallamoshi kan sharadin xai dauki mataki koda ya dawo gidan yakira sauran kannensa kansu shaida yadda kan farhan aka kulleshi yasallamashi xai maidashi dangin uwassa kamar yadda ya basu kannensa mata biyu.
 
Bayan shigowar malan sule ne yake fadama matarsa mairo yadda sukai tai farat tace malan tunda har yau bamu samu haihuwaba maixaisa kai kace yaba kinsan halin yaya tunda ya auri kulu duk ya butse bai san gaskiya hakane anman ka gwada.
 
Yasameshi da bukatunsa dakyar yasamu yace xanyi tunani.
 
Da asuba bayan sun dawo daga masallaci yaya isa ya tarasu nataraku ne dan kushaida ni nacire farhan daga cikin xuriyata na baima sulemanu koda wasa kar wani abu nasa ya taso ace xa’a nemen haba yaya ina lefin kavashi ya rike inji jibrin kaga jibrin ba shawara na kira kubanba face sheda yaja bakinsa yai shuru.
 
Tun daga wannan lokacin rukon Farhan yadawo hannun babansa sule komai shike masa kafin wani lokaci saiga yaro yai kyau baxaka taba cewa shine wannan farhan dinba da duk yai baki ya rame.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Duda Farhan yabar hannun kulu hakan baisa duk sa’adda hanya ta hadasu sai yaji ajikinsa.
 
Cikin ikon Allah farhan na aji biyu a secondary mairo ta haifi yarta mace murna guri  farhan ai ba’a mgn farhan anyi kanwa ko makarantama dakyar yake iya futa ranar suna yarinya taci sunanta Fadya.
 
Wata irin shakuwa ce tsakanin farhan da fadya komai yasamu kanwata yarinyar ta shaku dashi sosai har takai ko sch xaije tana kuka xasu rabu duk abokansa sun san da xaman fadya yadda yake musu xancenta yadda farhan kesan fadya yasanya umma takara jansa ajiki abinka da mai da akace wawa.
 
Cikin ikon Allah umma ta kuma haihu saidai hakan bai janye shakuwarsu da fadya ba dan rainanta ma kamar hannunsa ya koma har wanka wani xubin shike mata.
 
Lokacin da xata shiga primary shi yatara yasai mata jaka da takalmi daukanta ma yai sukaje ta xabo abinta tun daga lokacinduk rintsi tare suke tafiya sai ya goyata a keke yasauketa sannan ya wuce.
Yanayin yadda fadya ke shiga tafi sauran yan gidan sa ointa domin domin komai farhan yasani na yayi kanwata basai gidan yadauka ba mairo ta mallake yaro yaxama bawanta ita da yayanta.
Xuciya nasan mai kyautata mata yanayin yadda farhan kema fadya yasanya ahankali tafara jin sansa tun tana daukan abin wasa sai wayar gari tai xuciyarta cike taf da kaunarsa sanda ko kanta ba lallai tanaima ba yayinda shi ko kadan hankalinsa bai kai nanba shi yadauketa ne a matsayin kanwa ta uwa daya uba daya.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Awani bangaren Fara diya ce ga Alhaji Hamza wani hamshakin dan kasuwa wanda kusan duk wani wanda ya kwan ya tashi da an ambaci sunansa yasan da xamansa.
Alhaji hamxa haifaffen kanone shine na biyar a family dinsu wanda ya kasance da tun auransa Allah vai bashi haihuwa ba shekararsu ta takwas da aure Allah ya basu da namiji saidai yaron  yana da shekara daya da watanni Allah yai masa rasuwa tun daga lokacin haihuwa ta bude saidai babu wanda ya xauna Fara itace ta hudu wanda itama tunda suka haifeta take laulayi kala kla dan itama din sun fara cire rai da ita.
 
San duniya daga uwar har uban sun dauka sun dorama Fara duk abinda take so shi ne suke mata yarinya ce ba kwaba batasan ta nema ace babu ba kullum akwai tasani gata ko yayan shugaban kasa basa nuna mata ba.
 
Duk wani buri na duniya Alhaji hamxa ya dora kan diyar tasa burinsa tai karatu mai xurfi ya aura mata mai kudi kamarsa yadda baxatai kuka ba.
Alhaji hamxa irin mutananne dabasan talaka kai duk wani talaka na unguwar yasan da xaman rashin mutuncinsa sai Allah ya hadashi da mata irinsa  wadda ke kara xugashi.
Saidai kash sunyi sake saiga diyarsu diyarso daya jal da duk buribsu ya dori kanta ta afka cikin kogin san talaka sunan da sukafi tsana kuma ma talakan dan gidan da duk unguwar babu yasu a talauci.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Dagaske fara ta rasu hakuri xakai summa tafi da ita gida tun daxu nasan yanxu ankaita yafashe da kuka maiyasa ba’atashen naimata kallon karsheba mai yasa baku tashen ankaini da ita ba hakuri xakai haka Allah ya kaddaro ayanxu addu’arka kawai take bukata ba kukaba hakane hawayensa suka karu Allah yajikanki fadya yai miki sakayya da gidan Aljanna yawwa ko kaifa kukan ya isa haka kasan va cikakkiyar lpy ce dakaiba kayi hakuri karka jamakanka illah ka kyaleni nai kukana nikadai nasan rashin da nai ni akama wannan mutuwar eh hakane kowama haka yake fadi anman hakuri shine kasan kukan vaxai dawo da ita va.
Acan gida ana tsefe mata kai inda suke jira a gama a hadata dan kaita makwancinta kakarta  na gefe tai tagumi ta tsurama gawar ido anya kuwa ba motsi naga takeba baba kenan idonkine dai dan naga tun daxu kike fadin ke baki yarda ta mutuba hakuri xamuyi mu mata addu’a Allah ya jikanta uhum ni nasan idona gaskiya yagani anman tunda kunce haka Allah ya jikanta.
 
Dagaske tana motsi wallahi inji umma hadixa dake tsefe mata kan dasauri umma bilki ta mike bari asamo mota tai waje inda masu jiran afito da gawa suke dako ta fada musu daranta asamo mota dasauri wani makocinsu dake daura alwala ya ijiye butar yai gidansa kankace me ya kawo motarsa kofar gidan abaya akasanyata sai ummanta dake ciki abbanta agaban mota sukai asibiti.
Sauran yan uwa suka biyosu a motar haya.
Batare da wani bata lokaciba likitoci suka bayyana akanta dan bata taimakon da take bukata sunyi darajar saita numfashinta.
Likita ya fito abbanta yai gunsa ya ake ciki likita gaskiya tana cikin matsala sosai xuciyarta ce ta kunbura take samun matsala wajan bugawa.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Duda kasantuwar cewar likita ya fada musu halin datake ciki na rayuwa ko mutuwa hakan baisanya su farin ciki da godema Allah ba da yai bata mutuba.
 
Dan Allah da gaske kake ko da wasa wallahi da gaske nake fadya bata mutuba ynx haka tana asibitinnan saidai batasan inda kanta yakeba mekake sanyi xuwa gunta xan mana kace tana asibitinnan eh nace kuma batasan inda kanta yakeba baxasu barka ka gantaba sun hana kowa shiga pls ka koma kaxauna kasan ba lpy ce dakaiba.
Gaskiya abin nata ya wuce tunaninmu aiki xa’a mata aiki doctor eh bakuma anan ba india ya xaro ido india eh hakan yasa nake sanar muku kutanadi at list two million koma da rabi million fa doctor ina kake tunanin xamu samu wannan kudin ya watsa hannu gami da tabe baki taya xan sani kuyi gaggawar kawowa dan komai xai iya faruwa in aka samu jinkiri.
Allah sarki fadya Allah ya jikanki haba malan ya kake da saurin karaya haba mairo inban karayaba to mai xanyi kina kallo duk wasu yan kadarorina nasaida lokacin dashen kodar farhan kinajin yadda mukai da yaya danai mgn cewa yai ai nine ubansa tunda tun yana yaro yasallamamin shi suma sauran kina kallo kowa naima mgn sai yace babu to inaga naje ga maganar million eh hakane amman Allah yana tare damu saikaga ya fito mana da mafita inda bamuyu xatoba kaidai muyi tamata addu’a ya kada kai eh kema kince wani abu.
 
Fara kina xuwa sch kuwa eh mn anya kuwa tai dan murmushi kayi shuru kasan bansan kana yawan mgn baka gama warwareba eh kyace nai shuru mana tunda kina gwangwani yawwa daxu da kikaje dakin kanwarmu ya kikaga jikin nata tai shiru dan tuno yadda ta ganta saida tai mata kwalla bakiji mai naceba tadanyi kamar batajiba maikace nasan kinji anman bari na maimaita yakikaga jikin kanwarmu ah jiki da sauki duda tana bacci harna tawo hakane kitashi ki tafi kar kiyi dare aikasan yau lecture har six munada kona kai mgriba babu abinda mum xata xata pls indai vaso kike nai fishiba ki tashi ki tafi to shikenan kar ai fushivdani Allah ya kara sauki ta mike ta fice.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Wai yanxu da gaske haka munaji muna kallo fara xata auri wannan matsiyacin kedai bari muga lokacin dana bata muga wane xata xaba mu iyayenta ko shi tai dariya Allah ya nuna mana saidai kinsan wani wani abu karta kuma hadani da inna kaka ka kyaleni da ita indai ni na haifeta baxata kuma xuwa kai mgnar nan gun hajiya kakaba.
Tun kwanciyar farhan a asibiti fara tai hijira xuwa makaranta domin inta fito da xummar agida ta tafi sch asibiti take tawowa direct kullum tana gunsa koya ya motsa xata mike tanai masa sannu komai ta samu duk yan kudinta anan yake karewa indai annemi wani abu indai tananan toko ita xata biya bakyashi ko wani shayi sai yayi da gaske take iya tafiya intana xaune tausayinta yakeji sosai burinsa aduniya bai wuce fadya ta warke ba ya nuna mata so ya nuna mata gata irin wanda babu wata diya daxatace ta sameshi danshi sai yanxu yagano shima din yadade yana santa.
Yanxu doctor babu wata mafita dai ta aikinnan ehto akwai magani saidai shima yanada tsada bai kuma cika yiba aiki yafi dan inakai sa’a aka dace shikenan yawwa doctor mai xaisanya abamu maganin mu gwada ko Allah xaisa mudace tunda nasan shi vaxai kai kudin aikinba ok shi ya biyoni office sai a rubuta muku.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Cikin ikon Allah maganin yana aiki tunda doctor dakansa yafada musu gashi kunburin datai harta fara sabewa.
Sukansu sunfara ganin cigaba dan da kawai sunajin doctorne takan bude ido wani sa in harta dan murmusa.
Ai farhan yadda ya takura musu saida adole suka kaishi inda take yana yin yadda yaganta duk tausayinta ya kamashi haushi kansa ya cika masa xuciya dakyar ya tafi dan cewa yai saita farka dakyar suka ce ammata allurar varci yatafi.
 
Dan Allah yaya farhan wata alfarma xaka mun inajinki Aisha daman so nake kataimaka kaban takardar dana kawo maka sabida mai inasan naxamto mai cika alkawari kamarya munyi da fadya kan baxan baka takardarba sai ta mutu intaji na baka vaxata kuma yadda daniba ni nai gaggawa daban bari ankaitaba shikenan Aisha xan baki saidai na manta inda na ajiyeta saboda banma karantaba nayi xaton ko kawai rubutunta ne da tasaba bani inxata fita ina bacci sannan dan Allah kataimaka karka taba nuna mata cewar nabaka  pls yaya shikenan naimiki alkawarin ko da wasa baxatasan nasan meta bakiba yawwa yaya na gode.
In tambayeki kekinsan maita rubuta a’a tace ta yadda dani in taimaka kar inkaranta yadda tavan haka na baka gashi nima bansan me ta rubutaba mutuwar da aka fadan tasa banbi takantaba muje na duba miki sai in vaki.
Aisha taji dadi dataga dagaske bai karantaba dan da auka koma dakin ma saida yadanyi lalube ya dauko mata dan haka takarbi abarta da kwarin gwiwar in fadya ta warke ta bukaci abarta xata iya rantse mata yaya farhan baisan maine ta rubuta ba.
Kanwata
Na .F.A.Ya’u
Jinyar fadya kabaki daya farhan ne da fara duk wani abu da baxau iyaba ita takeyi saidai in batanan sauran yan uwa suyi .
Jiki kam yai sauki dan yanxu ma anbasu sallama danshi farhan tuni aka sallameshi .
Umma dan Allah inasan xuwa gidansu Aisha ina ba inda xaki dan Allah yaya wallahi baxakiba yadda bakida lpyar nan haba yaya nafa warke anman sai kadinga cewa banda lpy ni banga alamun waraka atare dakeba adalci daya xan miki inje inkirata to yaya nagode .
Yawwa Aisha so nake inkuma tambayarki karki gaji dani sai nake ganin kamar kin baima yaya takaeda ta haba fadya saunawa kikesan na rantse miki koso kike na hadiyi alqur’ani hankalinki xai kwanta to yi hakuri maida wukar na yarda suka dan taba hira kafin Aisha ta mike bari naje wanke wanke nake yaya ya tasoni ta rakota kofar gida ita kuma ta dawo gida.
Akullum ya xauna bashi da aiki sai tunani yasani tabvas yanasan fara inya barta baimata adalciba to anman yaxai yida kanwarsa wadda yakeda yakinin baida masoyiya kamarta aduniya baijin xai kuma samu kamarta to mai xai hana kahadasu biyu inji zuciyarsa ina ya fada abayyane baxai yiwuba banda burin mata biyu fadya ta shigo rike da kwanon abinci yaya tashi kaci abinci ya dan mike a firgice yaya tunanin mai kake yai wani malalacin murmushi ba tunani nakeba uhum yaya kenan ta fada gami da xaunawa.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Kinajina kinmun shuru sai kace da kurma nake mgn ko suk salon wulakancin ne dan Allah dady kayi hakuri ba cewa nai kiban hakuriba dan hakurinki bashi nake bukataba so nake kiban amsa abvan salim ya daka mata tsawa malama ke muke jira muna da abin yi kina batq mn lokaci.
Inaso ki kara sanin wannan damar itace ta karshe da kikeda ita inkin xabi salim shike nufin kin xabi iyayanki inkin xabi farhan shike nufin rabuwarki damu na har abada tadaga kai takallesu daya bayan daya sai hawaye kinga ba kuka muka kiraki kimana ba kiranki mukai ki fada mana wanda kika xaba dadi ina kukan saba muku daxanyi ne nasani van kyauta muku ba ku yafemun na xabi farhan momi ta mike da hargagi xata daketa ya daga mata hanni batta ta riga ta gama nunan ni bata daukeni uba ta canja uba to wallahi ki sani yadda kika sanyama idonki toka haka xan rufe nawa idon in manta ni na haifeki xan manta inada ya dama can bansaka ran rayuwarki ba da bansameki ba am doing ok so when kin xabi ki rabu damu i will still be happy fiye dama kina nan.
 
Na vaki sati daya shi uban da uwar da kika canja yaxo ya biya sadakinki kibarmin gida bana bukatar komai nasa kamar yadda kaeyasanya rai da xanyi miki wani abu ke kika ga xaki iya inkina da kudin yima kanki sai kiyi ta mike shikenan dady nagode tabar dakin.
 
Alhaji wannan hukuncin dakai shine dai dai tunda ta nuna ita bata haifuba inji baban salim yakalleshi bai ce komai va yabar dakin danshi kadai yasan dacin da ransa ke masa Abban salim yai wata dariya ta mugunta gami da jan dansa subar giddakin.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Tana kwance akan gado tana jiyo motsin momi ta rufe idonta kamar mai vacci tashi muyi mgn nasan ba bacci kikeba tai shuru bakiji mai nace bane ki tashi muyi mgn nace ko badake nake bane ahankula ta mike ta xauna.
 
Wallahi fara kin bani mamaki da har kika iya xabar namiji akan iyayanki so nake kifadan wane irin dadi yake baki da har tafiye miki iyayanki  tai shuru koda yake baxaki fada ba anman ni nasani kun gama lalacewarku a waje shiyasa kika kasa rabuwa dashi wallahi momi ba haka bane to in ba haka bane yane eyhe.
Ta fashe da kuka momi dan Allah kifadan gaskiya ke kika haifeni awwa lallai kin rika wato kokwanton kasantuwarmu iyayanki kike ma wato kin manta irin gatan da muka baki a vaya ko ba haka bane momi ina mamakin yadda kudi ya fiye miki farin cikina alhalin nasan ko wacce uwa na fifita farin cikin danta kan komai bama kudi ba vaxaki ganeba abinda yanzu nake miki shine xai dawwa mar miki da farin cikinki na har abada yanxu sone ke janki dakinyi aure xaki fuskanci mai muke hango miki momi ni aguna kudi ko dukiya bashine farin ciki ba dalla ni yimun shuru naxo in fada miki indai har ni nahaifeki nakuma isa dake kije kisamu babanki kice kin janye aurenki da wannan matsiyacin kinajina ko fuu ta fice tabar dakin.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Fadya an warware dan yanxi harta koma sch kullum ummanta cikin mata nasiha take kan ta dena sanyama ranta damuwa kodan lpyarta yayinda farhan ya ninka kulawarsa akanta ko ya yaga tai shuru ya dinga janta da wasa kenan harsai yaga ta ware.
Tana iya kokarinta wajen cire farhan aranta duda tasan abune mai wuya so daya ne ta kuma riga ta vashi ta yanke shwarar cema muhd ya fito watakil intaga angana mgnr aurenta ta hakura ko yaya ne ta soshi .
 
Gavaki daya gidan an sauyama fara danko gaisuwarta basa amsawa ba ruwansu da mai take ciki lpyrta ko rashin lpyrta taci abinci ko bataciva saidai taurarriyar xuciyarta kasa bata shawarar sauya ra’ayi tanajin xata iya jure komai akan farhan indai xata aureshi.
 
Yau da wuri ta shirya dan vata dabwayar farhan dan ta sanar dashi yadda sukai da dadin nata koda taje gidan sun gaisa da umma cikin sakin fuska dan sun saba sosai ta nuna mata dakinsa suna ciki suna hira shida fadya ta shiga suka gaisa kafin fadya ta mike dan varin dakin ina xaki ki xauna mana ba wani abu bane inji fara ta koma ta xauna nan ta fada masa komai yai shuru baice komai ba ta tsaya tana kallonsa dan tagano hakikanin halinda naganar tasanyashi wato farin ciki ko bakin ciki saidai ta kasa fuskanta shurun yai yawa fadya tace yaya baka ce komaiba ya mike ina xuwa yabar dakin
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Ina zuwa fadya ta mike tabi bayan farhan haba yaya yaxataxo maka da mgn irin wannan anman ka kasa nuna mata farin cikinka saima katashi kabarta yadan juyo to mai kikesan nanata kinasan inbata goyon baya ne wajen sabama iyayanta to anman yaya da wanne xataji da abinda ake mt agida ko taxo ka nuna ko in kula akalla kamata nasiha dan ta fuskanceka hakane kuma kince wani abu muje.
Shikenan ta goge hawayenta bayan gama sauraron dogon bayanin farhan din Allah yai daman nidin ba matarka bace nagode ta fice tana kuka jiyai baxai iya hakura yabarta ta tafi ahakaba da sauri ya bi bayanta tanaji yana kwala mata kira saima sauri data kara saida yadan kara sauri kan ya sha gabanta ruwanda ke hannunsa ya mika mata pls kitaimaka ki wanke fuskarki yakarbi robar bayan ta wanke ya karbi robar ya mika mata hankici ta goge fuskar suna tafe yana kara bata baki kafin suje kofar gidansu harya yasamu ta gamsu saida ta shiga gida sannan ya juya sai asannan wani zazzafan hawaye ya zubo masa dan sanin ya gama rasa Fara.
 
Zaune suke suna kallo tazo asalube ta zauna arakube can gefe babu wanda ya daga ido cikinsu ya kalleta balle su nuna alamar sun san da ita a hankula tace dad gurinka naxo to ingurina kikaxo baki iya mgn daman abba so nake infada maka nafasa auran Farhan inasan auran  duk wanda kuka ban to inkin fasa auran farhan saimai ta daga ido a tsorace dad dan inasan yimuku biyayya biyayya ai lokacin yagama ficeki kin riga kin bata wayanki tun afarko.
Kanwata
Na. F.A.Ya’u
Ya tabe baki aimun riga mungama mgn kin san Allah baxan janye mgn ta ba ni baxan kara karan banin zaba miki mijiba kinriga da kin nunan iyakata dan Allah dad kayi hakuri karki ban hakuri inma yaron ne yace baiyasanki to kiyi gaggawar kawo wani kafin juma’a inba hakaba xakibarmin gida nafasa miki ummanta dake gefe tace Amman alhaji ya daga mata hannu karkice dani kala ya mike yabar gun itama dagudu ta tashi tai daki tana kuka yadda dad yai fishi tasan baxai sauya batunsaba.
 
Fadya kenan to yanxu mai kuma kikesan na miki tai murmushi dan kanwa taxo gun yayarta wani abune tai dariya to muje ciki suna shiga Fara ta fada jikin fadya tana kuka adan tsorace tadagota yayarmu lpy fadya nashiga uku kowa ya tsaneni mai ya faru nan ta fada mata duk yadda sukai da dad dinta to ke wane hukunci kika yanke ehto na yanke baxan kawo kowaba in dady ya yanke korata xantafi ta xaro ido to ina xaki bansaniba gaskiya daman kakalece kawai nakeda itama din bansan meyasaba takanas taxo taci mutubcina wai inasan raba mata kan yaya kinga banda nadafa shikenan xan tayaki addu’a insha Allahu Allah xau kawo miki mafita bari naje har kofar gida ta rakata taxo fita ta riko hannunta pls fadya kimin alkawarin baxaki fadawa farhanba me yasa sabida banso yadauka nidin nakasa bin umarninsa nakasa ma iyayena biyayya tai murmushi karkiji komai yayarmu kisa aranki baxaiji ba tai dariya nagode kanwis.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Duk yadda sukai da fara ta fadama ummanta ummanta ta tausaya mata koda babansu yadawo ta fada masa yace shikenan xamuje Allah ma yataimaka sadaki suke bukata kawai kinga sauran sai asai katifa da dan sauran kayan kitchen to gurin xama ai ba matsala bane ita fadya tunda itama sauran kadan tabar gidan sai ta dawo dakin kannenta inyaso dakinta tunda yafi nasa girma sai ya xame musu nasu dakin nasa sai sunaida kitchen tai dari gaskiya hakan yai Allah yasa abokiyar arxikinsa ce yace ameen.
 
Ta daga ido taga tara dai dai tasaukar da ajiyar xuciya watakil dad ya hakura tunda gashi har tara baixo yace tabar masa gida ba.
 
Turo kofar dataji yasanya gabanta faduwa mikewa tai alamar bashi waje ya xauna ba xama naxoba maxa ki tashi ki hada kayanki kaya dad eh ba dogon mgn naxo yi dakeba tana kuka tana hada kayanta haka tagama shi yajawo ta agaban mum dinta ya tsaya inxakice mata wani abu ta fashe da kuka tai ciki da gudu ta juya kamar tavi mum dintata saidai kash ba dama.
Saida sukaxo bakin falon ya kamo hannunta ya danga mata kudi ga sadakinkinan amman dad yadora hannunsa kan bakinta karki cemun komao daman burin kowanne uba yarsa ta girma ya aurae da ita nima nawa ya cika saidai karki manta yau shi xai xame miki rana ta karshe da xaki taka kafarki a gidana.
Kanwata
Na F.A.Ya’u.
Akofar falon taga umman fadya da wasu mata biyu su suka tafi da ita tanaji tana kallo saida sukaxo kofar gida ta daga ido danma gidansu kallon krshe kuka ya kuma kwace mata.
Tun xuwan Fara gidan mutan gidan sukabi sunka addabeta duk wata tsana yimata suke habaici ba irin wanda batasha inka dauke fadya ummanta sai Farhan agunsu kawai take samun farin ciki.
Inka sameta a babban gidan to ruwa xata diba shima bata tsayawa wajen cikawa shiyasa sau tari saidai fadya ko kannenta su devo mata inba haka ba da hawaye xata bar gurin.
 
Wata sabuwa duk wani mai xuwa gurin fadya farhan ya koreshi tsirfa kala kala haka yake fito mata da ita kan samari abin har mamaki yake vata abinda ma baimata dava yanxu yi yake na takura ita kanta fara abin yadan fara bata wani tunani na daban.
 
Ni wallahi duk hankaliba ba’a kwance yakeba wai yaronnan ya rasa wayakeso sai yarinyarnan me matar tasa ba kedai bari nima abinda ke dagan hankali kenan har yaushe yai auren gashi babansu yace yaji yagani gaskiya maza sai abarsu dayasan ita yakeso yaje yai auren maganganun da fara take jiyo umma da yayarta nayi kenan rasa mai xatai tayi kuka ko dariya kowanne yaki xuwa sai wani kululun takaici da yaxo mata wuya ta tsaya na takaici.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Ba laifinsa bane laifina da tun farko na kasa ma iyayena biyayya na xabeshi tun farko mai yasa na kasa gano tsantsar soyayyar da yakema kanwarsa har na dage saina aureshi takasa kuka sai takaici kawai da haushin kanta dana farhan da ya cikata yama rasa waxai auro mata sai wadda ta gama sanin sirrinta wayyo kaicona farhan ka cuceni.
 
Umma wai ina yayarmu tana daki na leka tacw batajin dadi kinsan mai ciki sai a hankali bari na leka ta shi tana xaune ta rabka tagumi subhanallahi yayarmu lafiya wani haushi ya kara cikata bansaniba dalla malama barmin daki yayarmu konai miki wani abune wai bakiji nace kifitar min daga daki bane sun sun ta fice tabar dakin aiko tana fita wani kuka yaximata tako fashe da kuka.
Yaya wai maikaima yayata ne yai dariya maikikagani na shiga naga tana cikin damuwa ban mata komaiba bari naje nagani lpy muka rabu.
Subhanallahi ya fada ganinta tanata sharar kuka fara lpy ya fada yana dagata tako tureshi kasane mugu axxalumi me nai miki haka me ne mekamun lallaima ta fadi aranta wannan mutumin ya raina mata hankali kafita ni kaban waje na tsaneka kasakeni towo mai yakawo maganae saki kasakeni kaje ka auri yar uwarka ta gano inda ta dosa kishine yai murmushi lallaima wannan ya rauna mata hankali dariyama ta bashi to wayace miki da saki atsakaninmu ai aurenmu mutu karaba inkinga kinbaeni saidai inna mutu wallahi baka isaba saika sakeni ka cuceni karabani da kowa nawa yai shuru ni na taba cemun muki ki rabu da wani naki akaina ko na taba cemiki baxan miki kishiya ba eyye lallai to wallahi gidanmu xan tafi to aisaikije in xasu karbeki kin manta yadda kukai dole nan xaki dawo ta fada gadon tana kuka lallai tai kuskuren rike namiji garkuwa tun ba’aje ko inaba ma yanai mata gori fuuu ya fice yabar dakin.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Saida ya fita yadan xauna sannan hankalinsa ya bashi tabvas bai kyauta mataba abinda yai mata ya fara dawo masa kukanta na ratsa kwanyarsa.
 
Ahankula ya shiga dakin har yanxu kukan take tausayinta yakara kamashi inda take yaje yadagota haba tawan kukan ya isa haka atakaice adaren suka shirya yai tai mata dadin baki da alkawarirrika kala kala har yasamu ta aminta da batun auran ida yavama kudin hado lefe komai biyu yace ta siyo.
 
Ita da fadya yawanci ke fita wani sa inma fadyar ke xaba dan xatonta kayan hai huwa take hadawa tunda cikinta wata bakwai.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Angama komai dai dai yau fara na xaune farhan ya shigo rike da ibi lpy naga kamar kana cikin damuwa kedai bari na rasa yadda xanyi  inma fadya mganar auran haryaufa batasan da batunba baba yace dole sena fada mt da kaina tai dariya kabarmin komai ta karbi ibi din ta mike ina xuwa tai dakin da fadyar take tana xaune tana chat ta kwace wayar gami da mika mata  ibi din mene karanta afirgice ta mike baxai yuwuba wai wace fadyar ke mana da sauri xai waje ta rukota gami da zaunarta haba fadya maine haka bansanki da waytaba.
 
Wallahi baxai yiwuba ni na taba cemuku inasan farhan ne ni wallahi baxan aureshuba ai wannan tauye hakkine    ke ba wanda kike so aka vakiba nima muhd nakeso haba kekuwa amaryarmu kikalli tsukeken mijina kice baki sansa ai fade kike to shi so anfada miki kyaune ni wallahi baxai yuwuba ina ganin mutunciki ki yi kokari mudore ayadda muke.
Dakuka tasamu ummanta haba umma anmin adalci kenan basai atambayi ra’ayina ba jafin xartarwa abbanta dake uwar daka ya leko sannu isasshiya dake kedin baxawarace ko duk yadda fadya xatai kan mgnar auren tasha ruwa tayi kowa yaki saurararta ala dole ta hakura..
 
Andaura aure inda fadya itama xata xauna cikin gidan sabon gurin da’aka yanka mata saidai tace ita gaskiya baxata xauna asabon gurinba tabarma yayarta kotadan samu saukin rashin mutuncin mutan gidan duda ba wai xata bar gidan bane tadai yu nesa da kadan dasu seta fito xata gansu haka kuwa akai.
 
Duk inda xaman lpy yakai sunayi ita da yayarta fara watansu uku da aure fara ta haifo diyarta mace taci sunan umman farhan marigayiya.
Kanwata
Na F.A.Ya’u.
Fadya ankammala karatu dan yanxu aikima take xamansu lpy fara bata taba nuna kyashi wajen aikin gida ba koda yakasance kuwa girkin fadyarne indai tana aiki haka take xagewa tai abinta.
Hakan yasanya itama fadya ko kadan bata kyashin kashe kudinta kan fara da yayanta dan ita har yanxu haihuwar shuru sunje asibiti ance ba wata matsala bace likacine baiba fadya ta toshe kunnenta ga duk wani abu da ake fadi agidan nasu kan fara tamata asiri bama ta nuna tasan da batun.
Albashinta na farko uku ta rabshi tai musu sayayya da daya daya ta aje daya kuma ta rarrabama yan uwa kusan rabin siyayyar ta fara da yaranta ce itakanta tasan fadya nasanta da xuciya daya take santa.
Cikin shekara fadya ta tara isasshen kudi tasai dan jaramin fili kan kace maine ta fara gini.
Kwanci tashi va wuya gida ya kannalu tsaf komai ta xuba dan jiyama sukaje ita da yayarta suka gani aiko fara sai yabon gidan take .
Umma so nake na baima fara gidan nan da na gina nasan kona baima yaya baxai karbaba inaso takoma can dan wallahi na gaji da abinda ake mata agidannan dako kin kyauta to kin fada mata a’a inaso inji mai xakice to Allah yasa albarka ta ce amin umma bari naje nasameta.
Tana xaune malan karami na sukuwa abayanta tace dan rikici kana nan kana damun ummankako yai dariya gami da xuwa ya fada jikinta ina takwarar tawa ta fice daxu baban ya daukesu ita da hajiya karama suka fice.
 
Daman wajenki naxo towo Allah yasa lpy tai dariya lpy kalau ta mika mata mukullai me xan dasu karbi mana ta karba gidan da mukaje jiya ne so nake nanda sati xaki koma hhh xadai mu koma ah aikinganshi gidan mace daya aiko ba’ayi haka ba saidai ke ki koma aiko wallahi baxan koma va towo haba kanwis maye na saurin rantsuwa to kin fadama yaya a’a umma xata fada masa godiya kam sai tashi tai tabar dakin dan tayi tayi tai shuru taki.
Shima farhan dakyar ya amince da batun komawar saida umma tai tabashi baki ya amince.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Cikin ikon Allah auransu yanada shekara biyar fara nada yaya hudu maryam wato hajiya karama malan karami sai sagira wato fadya sai dan karamin mai sunan babanta suke kiransa da Abi yayin da fadya keda shekara hudu cif da aure haryau ba bayani.
 
Cikin ikon Allah ance mahakurci mawadaci itama fadya saigata da nata cikin duk wani mai san fadya ya tayata murna.
Yaya na’am kanwis daman wata shawarace inajinki mai xaisa tunda aikin gwamnati yaki ka koma kasuwa yai dariya kumafa kinkawo shawara ban taba tunanin hakaba tosaidai kinga albashina bazai isa jariba tundabkina kallon yadda muke kaiwa dakyar yake kaimu wata to mai xai hana inbaka ina baxai yuwuba haba yaya wai dan Allah yaushe xaka yadda mun xama daya saidai ai dawajewa kiban bashi to shikenan na amince yai dariya to nagode Allah yasa da alkairi.
 
Cikin fadya ya tsufa sosai haihuwa koyau ko gobe yayin da kasuwancin farhan kullun sai bunkasa yake fiye da tunani dan harya biya fadya kudinta danma saida sukaso rigima dan cewatai baxata karba ba yasai filinsa a jan bilo haryafara gini danma yadan tsaya savida haihuwarnan.
 
Fara ba yadda bataiba kan fadya ta dawo suxauna dan su kula da ita tace ita ina tafisan xama gata ga ummanta haka suka hakura suka kyaleta.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Ciwon datakeji ya fuce tunaninta duda cikin darene haka ta tashi hajiya karama dake yaran suk suna guda anma barmata hajiya karama ta tashi dudu yarinyar ba wayo gareta sosaiba ta bata fitila maxa jeki ki kiramin umma da sauri ta fice dan vata da tsoro taje tana buga dakin waye nice anti ce tace na kiraki afirgice suka bude kofar tana ina tana daki takira kanwar fadyar maxa kuje ku kwanta keda hajiya karama tai dakin fadyar yanayin datake ciki ya wuce tunanin umma dole adaren suka wuce asibiti adaren su farhan suka xo asibitin.
Sai gefin asiba tasauka tasa wuya sosai dan harjini aka kara mata yaranta biyu haka ta haifosu lafiyayyu mace da na miji kowa kagani fakinsa wai.
 
Fara ce xaune gefen gadon tana rike da baby macen ke hotonki kawai kika dire tai dariya haka aketa cewa wallahi kamarku ta baci.
 
Umma daman inasan infada miki dan Allah in antashi sakama yarannan suna namijin asa masa sunan baba sulaiman wato baban farhan na gaskiya umma tai dariya ke ko kunya bakyaji yayan farine fa tai dariya umma kenan dan miko min su ban daukesuba datsu cikina na ciwo bakyajin kunya atso aganki dasu a hannu fara ta mike haba umma yanxufa andene wannan abin ta miko mata su umma ta mike badaniba axoganni agabana ake wannan rashin kunyar sukai dariya vaki daya fadya ta dago facen tana shafa kanta tabvas kamarmu daya ta mikawa fara duk subiyun tace rikesu naga ta rike nabar mikisi kirikesu har amana tai dariya kanwarmu kenan Allah sun dace dake da kika rike kamar naki tai dariya ai kayanki nawane dan haka yayanki nawa ko bakice kin banva tai dariya bacci nakeji vari nadan huta kafin cikina yakuma murdawa.
 
Baccin da bata farka ba kenan dan har wajen magariba in anxi dubiya saidai aga yara mai jego na bacci saida nurse mai xagajen yanma taxo taga anya kuwa tana da rai taje takira doctor aiko ba irin duban da basuyi mata va anman ina babu Allah ya karbi abarsa fara kam tai kuka kuka mai isarta duk wani da yasan fadya saida yai kuka musanman in aka kalli danyun jariran da ta bari dake anan take aiki a asibitin sukansu saida sukai kuka dan sun saba mace ce da kullum take maida komai ba komai ba komai akai mata.
 
Farhan kasa saka hannu yai gurin sakata akabari dakyar aka samu yasata xaman dirshan yai agun kabarin yana kuka dakyar da nasiha suka samu yataso yabar gun bayqn bakwai fara ta debi jariran suka dawo gida dan ita xata shayar dasu tunda daman awatannan xata yaye danta kawai saita barma umma svashi.
 
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Mutuwar nan ta daki fara sosai dan takasa sakinta musanman inta kalli yaran tausayinsu sai ya cikata.
 
Ummi ce ta shigo da gudi da gwalan gwalantunta na yara momi kinga karami ko ta cafeta yana kokarin dukanta haba yaya kaifa babba ne mai taima ba itace ta cinye nata cake din ta hada da nawaba yi hakuri kaga kai vabvabe kaida xaka dinga siyo mata inka girma ni  tabdi ya fice itama ta diro tabi bayansa da dan gudunta tai dariya yaro kenan yanxu kuma seta gansu tare.
 
Farhan yagama gidansa inda gidannan iya haduwa gidan ya hadu duk yadda yai dasu umma atare tare dasu suka ki dan haka nasu bangaren haka ya gyare musu shi inkana bangarensu baxaka taba tunanin awanna gidan kasar kake ba.
 
Dakyar da nasiha farhan ya ke ma babansa abubuwa duk kuwa abunda yake masa vaya gani dan matarsa kullun cikin xugashi rake kan wai yana fifitashi akan wani haka kawaima sai yaxo yaita bala’i wai sun mallake masa da sudai vasa ce nasa uffan dan sanin halinsa duda kuwa duk abinda farhan yai musu shi yake masa anman baya gani.
 
Koda ya tashi kai abban maka tare da baban nasa da daya kanin baban ya hada anman sai cewa yai wannan cun fuskane danmai baxai fara biya masa shi dayaba dan nuna musu shidinne ya haifeshi shidai vai ce masa komai ba sai hakuri da yai ta vashi.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Dakyar farhan yasha kan fara da nasiha kala kala kan ta daure taje ta nemi gafarar iyayanta dan haka yau ta shirya tsaf itada yan biyunta sai karami kayansu iri daya dan sauran yaran suna can vabban gida gun umma tace itama abarmata su dan kannen fadya sunyi aure namijin kuma yana makaranta.
 
Kai tsaye gidansu ta wuce komai na gidan ya sauya mata bakamar yadda ta barshi ba kamar ansake gyarashi ganinta a mota tsaf maigadi ya bude mata ta shiga matar ta karbetacikin fara’a da sakin fuska suka gaisa ina matar gidan ai nice ta xaro ido ke kuma eh mun sayi gidan ne sheka biyu da ta wuce ok ko xan iya sanin inda masu gidan suka koma ehto ban saniba gaskiya saidai ki tambayi mai gadi ok to xan tambayeshi na gode ta mike tavar falon.
 
A farfajiya ta suka hadu take tambayarsa eh yanxu suna dorayi ko xaka min kwatance nan yai mata kwatance ako vata koma gida ba ta wuce can.
 
Bata sha wuyava ta gano gidan dan lokon bamai wuya bane gidanma bata sha wuyaba tagano gidan da sallama ta shiga umnanta ba wanke wanke ta amsa da gami da saurin dagowa kamar miryar fara nice momi taxaro ido gami da bankawa daki fara dagaske kece ko mafarki nake nice umna but dad dinki yace kin mutu sai hawaye mutuwa umma wallahi van mutuba  ki fito miyi mgn nan ta fito jiki na bari mum ki nutsu kitamaka ki tsaya ki saurareni ta xauna kwanaki kimanin shekaru biyu da xamu taso  babanki ya gano komai yaje dan neman afuwarki ya tadda a gidan naku anyi mutuwa akace matar farhan ta rasu tare aka kai gawar dashi yaxo ya fadan tai shuru mum vani na rasuba kanwata nan sukai ra hirar yaushe gamo.
 
Dad ne ya shigo fara na bayi tana alwala maman fara ta fito rike da karami towo ina kika samu yaro tai dariya jikanka ne jikana kuma ya kamo hannun yaron ya sunanka sunana Hamza anman karami ake cemin a kace takwara bane yai dariya kaima karami ake cema eh amman kai vabbane kai wannan yaro da wayo kake ummi ce ta fito tana kuka ina mominta dan ita vata cuka sabiba irin yarannan ne nasu nacun uwa ah ashe yaran da yawa ya kamota tako kara tsanyara kuka fara ta futo da sauri ta dauketa to yar rigima takwantar da kai a girjinta tana saukarda ajiyar xuciya dad ya xaro idi wanake gani kamar fara nice dad yakalli mum tai masa murmushi jeka masallaci kadawo sai kaji komai.
 
Koda ya dawo ta fada masa yadda sukai yace ikon Allah rabon tun alokacin baxamu gana bane tace dad mai yadawo dakunan naje can kunsaida sai hawaye kuskurena ne bakomai ba haba dad mai yajawo kuka kayi hakuri in mgnta ko xuwana ya bata maka rai ko kusa basu suka batanba sai tuna abinda dan uwana yamin.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Tun bayan mukai mgnar auranki kika bujire tun lokacin naji tsanarki haka kawai banasan ganinki na rasa mai yasa sai bayan da akai auren yaya yaxo duk wata harkata ya shiga tsimdim dafarko komai normal dan nama manta dake yayinda a hankula inna kaka tafara canja min ko naje gunta bata shiga sabgata gai suwata ma tadena amsawa na rasa mai nai mata ahankula komai nawa ta dena karba saima ta hada kayanta ta koma gidan yaya.
 
Ban fiskanci komaiba saida aka gama cuta ta domin ina gida akaxo wai ansaida gidan nace kamar ya aka ban takarda naga sa hannun yaya naje nasameshi sai na taddashi a kujerata a gun aiki wai ai daman yai alkawari kuma alkawarinsa ya cika domin tun muna yara anfi sona agida komai ni shi kuma abin na masa ciwo angirma na fishi arxiki gashi har yanxu ummanmu tafison yata kan nasa shiyasa yaci burin sai ya rabani da komai dan inji bakin cikin da yakeji aduk sanda aka fifitani shiyasa yafara da rabani da diyata uwata da dukiyata aranar nai kuka nai kuka kamar mai haka yasa akamun korar kare yace jibima innaxo ansaida kamfanin itako inna kaka badamar ganinta dan yace kar abarni na shigar masa gida tsanata yasa aka sanya a xuciyarta ki yafemin komai ba lefina vane lefin asirine duda kuwa asirima na tadda hali tasa kuka dad nice xan nemi gafararka ni nakasa maka biyayya watakil danayi yaya salim ya aureni da duk hakan bata faruba.
Sai tara tabar gidan tabar musu karami dan yan biyu basa yadda da kowa sai ita sai vabansu in yan wulakancin suka motsa ko shi basa kulashi suna manne daita.
 
Kanwata
NaF.A.Ya’u
Washe gari fara ta aiko da mota dan su mum dinta suxo suga gidanta aiko tunda aka shawo lokon suke gwala la idanu dan kam duk lokon babu karamin gida basuga gidan da yai dai dai da farhanba ga mamakinsu gidan da yafi kowanne aka nufa dasu basu kara tsindima cikin mamakiba saida sukaga fara tsaye tana jiransu.
 
Dadi kasa shuru yai saida ya tambaya anya kuwa nanne fara tai dariya nanne mana das shima yajira baku isoba yace bara yaje ya dauko yara dan kugansu acan babban gida.
 
Basu dade da xamaba ya iso aikon farhanne saidai duk ya sauya kana kallonsa xakasan kudi sun xauna yakara kyau yai yar giba dai dai shi nan yagaidasu cike da ladabi dad yai tabashi hakuri yace aishi bai taba rike shiba.
 
Koda suka dawo gida cike da alkairi iri iri dad yace lallai ikon Allah sai kallo mum tace aini naga haka mutum ba’a bakin komai yakeba kedai bari naga ishara yanxu mukuma akiramu mai tace ai nikam batun yauba nadaukarma kaina alkawarin dena cin xarafin talaka yai dariya to muma cin ina kudin aimuma daya muke arxiki daga Allah kigadai yaronnan lokacin da nake cin mutuncinsa waxai ce xaiyi koda keke ne nasa segashi koda ace inada kudin vaxan kama kafa dashiba kinajifa har gwala gwalai yake da shagonsu a saudia da Dubai haka naji sudai haka sukai da danasaninsu kala kala.
 
Duk wani nauyi na su dad farhan keyi dan yanxu ya saimusu gida anan rijiyar xaki daman wanda suke ciki na dorayi na haya ne abubuwa sun fara komawa dai dai dan kasuwancinsa ma farhan ya sanya masa hannu ya kara masa jari ya fara far fadowa abu daya ya dameshi shine inna kanasu.
 
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Shawarar da Fara ta kawo suka bi duk juma’a ana dafa abinci abaima almajirai sauka kuwa asati sai ai sau uku ko hudu addu’a ba kama hannun yaro kan Allah ya karya abinda akaima inna na farraku ita da dad.
 
Akace wanda ya kama addu’a baya danasani domin kuwa inna kaka yau ta tubure fada ita sai ankaita gurin danta yaya yanaji yana gani yadauketa har gidan kanin nasa dan yasan inda yake aiko anan ya sauketa ko gidan bai shigaba yajuya dan sunyi da matarsa akan yana kaita yaxo su koma gurin boka dan wani abin ita ke dorashi akai duda shima da bakar xuciyarsa.
Akan hanyarsu ta xuwa sikai hatsari nan take matar ta mace asibiti aka kira wayar hamxa bai bata lokaciba ya xo ganin halin da yayan nasa ke ciki ne ya daga masa hankali shi yai masa komai kafin yaje ya tawo da inna kaka da mum saida yaga komai normal yadauki gawar umma amarya sai gidan acan aka hadata aka kaita inka dauke yayanta ba wanda ya damu dan murnama suke sun rabu da masifa musanman ma sauran kishiyoyinta abinda kawai ya damesu kawai lpyar mai gidan.
 
Inna kaka na gefe yana kuka ya ruko hannunta inna ki taimaka kisa kanina ya yafemin itama tana kuka mune sanadi da tun farko muka dasa maka tsanar sa ta nuna banbanci mu muka kasa danne xuciyarmu.
Nikam tun farko ban rikeka ba lefina nadauka nagode kanina farama haka ya nemi gafarar ta tace ita tuni ta yafe masa.
Jinyarsa gaba daya inna kaka ce tai kulawa ta musanman take bashi duda tasan abune daxai gogeba tun farko sunyi kuskure na nuna ban vanci tsakanin  yayan nasu.
Kanwata
Na F.A.Ya’u
Jiki kam yai sauki ansallami shi ya koma gida kullum inya xauna bashi da aiki sai rokar kanin nasa afuwa.
Kinsan me sai ka fada kasu wanci na na Malay nakesan xuwa sabida wasu abu buwa da suka taso kuma akalla xanyi watanni yakike gani tai dariya sai innemo maka yar yarinya ka aura katafi da abarka kwasha amarci yai dariya kinfiye xaulaya da gaske fa nake to ya xamuyi da yaranmu daman hutu suke suna babban gida karami yana gunsu dad se mu tafi da yan biyu sune daman dai matsala tai dariya to Allah ya nuna mn.
Duk wani shirinsu sun kammala angama komai fara taje duk tai sallama da yan uwa abinda ya vata  mamaki shine dataje babban gida kowa sai nan nan ake da ita kamar ba itaba ce wadda suka dauki karan tsana suka dorama va abinda vata saniba shine duk abinda farhan ke musu yakance injita.
 
Baban yara na’am inajinki yako batun masallacinnan eh an gama inaso kafin mu tafi afara sallah yawwa na gode ranar da xa’a su tafi ta tace masa nasadaukar da masallacin ga kanwarmu yai dariya Allah yasa da alkairi danshi baisan iya abinda  yai sadaukarwa ga kanwarsa mai sansa ba duda kasantuwar yayansu yara ne anman sun dorasu kan insunyi sallah ko kiran sallah suka jiyo su musu addu’a suyima umma fadya abin har ya xame musu jiki dai dai da yan biyu sun iya.
 
Harfilin jirgi aka raka su anata daga musu hannu tana rike da ummi yayinda farhan han ke rike da abi saida sukaga dagawar jirgin sannan suka watse.
 
Nima anan nake cewa Allah yakaisu lpy yabar so da kauna dan banda kudin binsu balle inkawo muku rayuwarsu a Malaysia.
 
Alhamdulillah Allah abin godiya da ya bani ikon kammala wannan littafi fatana ya amfanar.
 
Wani abu da nake san agane.
 
Banyi dan cin mutunciba ko bata sunan wani sai dan nishadan tarwa fadakarwa.
 
Wani abu game da labarin da nake san a fuskanta.
 
Mutum baya xama mutum har sai ya girmama mutum dan uwansa duk yadda kakejin kafi wannan mutumin bakasan irin baiwarsa ba bakasan yadda xata kaya maka ba akarshen rayuwarka.
Biyayya ga iyaye dolene komai sukai maka indai harkana san cigaban farin cikinka kamar yadda fara bata samu farin ciki mai dorewaba saida iyayanta suka yafe mata.
 
Gareku iyaye nuna ban banci tsakanin yayanku kan jawo musu kin juna da tabarbarewar xumunci ko kafisan daya daure kabar abin aranka treat them equal.
 
Manta alkairi ga wanda akaima bai xamto halin dana gariba kamar yadda fara ta kasa mantawa da karamci mutuncin fadya ga rayuwarta.
Godiya
Godiya ga duk wani ko wata da yabada lokacinsa wajen  karanta wannan littafi fatan duk wani kuskure da’aka gani xa’amin afuwa dan adam axijine.

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

0 Comments

  1. Pingback: Da Ciwo a Zuciyata Complete Hausa Novel - HAUSA NOVELS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Uncategorized

To Top
× Chat Zamgist on WhatsApp