Dijama Complete Hausa Novel

Barka Da Zuwa Shafin Litattafan Hausa Novels Inda Zaku Karanta Dijama Complete Hausa Novel, Dijama Yar Fulani Hausa Novel.

Dijama Complete Hausa Novel

DIJAMA ƳAR FULANI

Dijama!! Dijama!!!

Dejamar dake can tayi nisa wajen wasan ta da shanayen dasuka fito kiwo…wanda suke kan shan ruwan wani rafi…..

“Kaman daga sama tajiyo muryan umman nata,wanda take can ‘dan nesa dasu acikin wannan dajin…don itama tana tare da nata garken shanayen suna kiwo tare…

Jiyo muryan umman da tayi” yasata cikin sauri ta bata amsa da inworah ummah…
Wato tana mufin tana xuwa…

Cikin sauri tafara ka’da shanayen nasu xuwa inda umman nata take,don lokaci ne ta ruwa.

Hadari ya ha’du sosai,inda garin yakoma ba’kin ‘kirin.iska sai ka’dawa yake…
Magana ta hauyi ma shanayen ta harshen fulatanci…inda kaman suna fahimtan abun da tace” suka kama kamo hanya,ha’di da biyo bayanta….

Gurun wata ‘yar dattijuwan mata naga ta nufah,wanda take sanye cikin sa’ken ta na fulani…

Da isanta,nan matan cikin sauri tace”deejamar maxa muka’da shanayen nan mukoma ruga.
Don hadari ya taso sosai…
“Tohhh umma….!!!
” Deejah tace hadi da cigaba da ka’do shanayen.inda suka dauka hanyan rugansu….

_______________________

RUGAR HAR’DO

A haka su deejamah da umman ta suka karako xuwa cikin rugarsu,wanda akafi saninta da rugar har’do… Inda ummah tasha surutun deejamah har tagaji,don sam bata gajiya da xuba,kamar tsohon ridio…tun umma na bata amsa har takoma cemata”ehmmm…..a’a

Ahaka har suka iso rugan su,inda naga sun nufah
Bukkan su,wanda naga bukkunan fulanin a kewaye da na junan su…kowanne bukkan nasu xa kagani can kasa,don duka a gajirce suke,wanda sukansu inxasu shiga sai sun du’ka sannan suke shigan shi.

Da isansu umma ta ka’da shanayen xuwa rumfan su…
Inda dijamar ta nufi ‘bukkan su,don tagama gajiya,hutu kawai take bu’kata a yanxu…

Bayan ummah tagama kafe shanayen a rumfan su ne,tayo hanyar bukkan su,don har anfara yayyafin ruwa…wanda da’alama ruwan na gab da sauka ne.

Muryan yadiko taji tana cewa” shattu…”kun dawo wurin kiwon ne…!!!
Murmushi umma tayi ha’di da cewa” ehhh yadikko…dawowan mu kenan.

“Yadikko ne tace” dejama ta shige buka kenan…tohh kar dai kuman ta gobe da lumo…
Woto tanan nufin gobe daxuwa kasuwa….
“Tohhh yadiko,ae ko gobe da asuba xamu fita…don mu isah cikin garin da wuri…

KARANANTA WASU DAGA CIKIN LITTAFAN DAMUKA DORA:

Allah yakaimu goben.
Umnah tace’ha’di da ko’karin nufahn bukka.

Nan yadiko tace”Ameen,sannan kuma ki shaidama deejama fitanmu xuwa lumo da wuri da gobe…kar ta6ata mana lokaci da wannan surutun nata…
Murmushi ummah tayi inda tace”yadikko kenan,yau keda kanki kk fa’dan surutun dijahman kuma!!!hmmm ayau kuma???

Jin maganan umma yasa yadikko shigewa bukka tana dariya…

Ummah ma shiga nata bukkan tayi,imda ta cidda dijah…kwance kan tabarman kaba…

Alh.maccido kuwa jin wannan tambayan da ‘yar jaridan tayimae,nan take yasa shi ka’duwa,inda lokaci guda ta tado masa da tsohon famin dake cikin zuciyan sa…
Kasa bata amsa yayi,don dama bae shirya basu amsan kowani tambaya ba,balle kuma wannan tambayan nata…wanda kullum da tunanin iyalin nashi yake kwana da shi yake tashi.

‘Daga mata hannu yayi,alaman baya da lokacin bata amsan ta,inda nan take jami’an tsoron da ke bayan shi,wasu a gaban shi,sukayi saurin rufamai ta hanyar dakatar da ‘yan jaridun…nan take kuwa ‘yan jaridun suka hau…hayanin yansu ta hanyar cewa” don allah ranka ya da’de minti ‘daya mukeso muyi magana da kai…

Wannan ‘yar jaridan ne takuma cewa ” don allah yalla6ai ka bani amsan tambayata…haka dai kowa yake jefo nashi maganan.inda ministern yakasa ce masu komai…wanda nan take excout din shi suka bu’de mai motan da xai shiga.aiko da shigan shi jami’an tsaro da sojoji da ‘yan sanda sukayo bayan shi…sauran mutane kuma suka cigaba da mae kirari ta hanyar cewa” Allah yakara kwana…maccidon mu,maccidon Alkhairy….

Haka suka dinga ihu,dae irin ta matasa,don kafun yabar wurin saida yayi masu Alkhairyn da yasa ba,kuma da suke mai kirari a kan sunan…

Niko sai da nakuma maimaita sunan,ina jin jinawa,kunsan suna linxami….hmm maccidon Alkhairy… Duk wanda ko akasan shi da abu…lallai yayi Alkhairy n ne har yagaji….tohhh Allah yabamu Alkhairy….

‘Bangaren ummahn dijah kuwa da shiganta bukka,ta cidda dijah,kwance akan tabarman kaba…inda tuni ta jingine sandan ta,ta fulani a gyafe…

Xama ummah tayi ha’di dacewa” miyatti allah dijahma…yau kinga mun dawo ruga,ruwan sama bae bugemu ba.

‘Dagowa dijahma tayi daga kwancen da take,nan ta kara matsawa kusa da umman nata,sannan tace”ehhh ummah,yau allah ya taimakemu…

“Ummah ne tace” dijamah bari na dama maki fura da nono kisha,don nasan kina jin yunwa yanxu ko!!!

“Dijahma ne tayi saurin cewa” ehhh ummah, kaman kinsan yunwa ko nakeji…

Dariya ummah tayi inda nan tace”taya baxan san abun da dijamah na takeso ba!!!

“Dariya dijamah tayi,inda nan takuma cewa” ummah nonon da aka dafah yaune….

Ehhh dijah na…bari na dama maki yanzu…

Batare da dijamah takuma cewa”komai ba,ta cigaba da kalllon ummah,wanda take aikin dama mata furan.

Bayan ummah tagama dama mata ne,tamika mata ha’di da cewa” toh gashi dijaman umman ta.maxa kisahnye.

“Tohh umma miyatti…
Kafin ummah ta bata amsa nan takuma cewa” ummah yaushe ne xaki dafamun marori…!!!

Wato tana nufin shinkafah…
“Murmushi ummah shattu tayi” inda cikin sanyin muryanta irin na fulani tace”gobe xan dafa maki marori,kinsan gobe da fita lumo…don haka acan sai na siyo maki…inmun dawo ruga mu dafah ko!!!

Umma ta ‘karke maganan cikin kafe dijamah da ido.

Nan cike da farin ciki da ‘doki dijamah tace”umma da gaske gobe da lumo???
“Murmushi umma tayi” ha’di da cewa” ehhh gobe da yawo ko!!!

Nan dijahma takuma dariya ha’di da cewa”lahhh umma ae baxani yawo ba,xan tsaya na saida maki da nono…kinga masamu sha’de da yawa koh!!!

Dariya ummah tayi ha’di da cewa”ehhhmmm dijamah kenan,kicemun dai kina farin ciki xaku ha’du da binttu acan…

Bawae xamu samu shade ba(wato ku’di)
Nan dijamah ta hau dariya,ganin ummah ta gano dalilin farin cikin da takeyi….

Haka ta amshi furar ha’di dafara sha,tana kuma xuba mawa umma surutu….

 

Dijama hausa novel page 2

002

Kashegari da subahi ummah ta shirya dijamah,don su fito lumo da wuri…
Inda dijamah ansha dige dige na fulani…fuskan nan yasha jan jambaki da ba’kim kwallli…
Haka suka kama hanyar lumo dake cikin garin Adamawa….
Ummah na gaba,yayin da yadikko da dijamah ke tafe suna xuban da suka saba,don yadikko biye mawa dijamah take intana surutun ta,don umma wata xuvin har dariya ma yadikkon ke bata,intana biyemawa dijamah n.

A haka suka isah,kasuwa.inda da isan su wannan kasuwa,kowa ya hau dijamah… Dijamah
..!!!
Don gaba ‘daya mutanen kasuwan ba wanda baisan dijamah ba.
Yayin da kowa ke kaunarta musamman yanda take surutun ta dakowa,koda bata sanka ba…infact dijamah irin wa’inan yaran ne masu shiga ran mutane…kowa nasu ne..

Tun da ta isah ta bar wurin umman nata.inda tuni sun game da bintutu…wanda nan take suka nitse cikin firansu da suka saba.da tsokanan mutane fa’da.

A haka kafin ‘karfe uku,tuni kwaryoyin nonon da suka fito dashi ya ‘kare…don haka ummah ta fara niman dijahma don su ‘dau hanyan komawa rugansu.
Dijamah….!!! Dijamah….
Nan ummah tahau kiran sunan dijamah, wanda dijamah dajiyo kiran umman nata, yasa tayi saurin amsawa,ha’di da nufota…don tasan rugansu xasu koma yanxu.

Kaman daga sama umma taji wata murya ta kira sunan ta da” Hajiya Aisha…
Cikin sauri umma tajuyo ha’di da kare ma mekiran sunan nata kallo…
Tabbas baxata manta da uwani ba,a rayuwanta…
Cikin sauri uwani ta nufota…ha’di da share kwallan idonta..
A hankali umma tace” uwani kece,ashe kinan na.
“Uwani ce cikin tausayama ummah tace” ehh nice,dama kina nan hajiya ta!!!kinsan halin da ko…..
Saurin ‘daga mata hannu umma tayi” sakamakon xuwan dijamah…
Shiru uwani tayi,inda nan ta maida kallonta ga dijamah,wanda ke raba ido kaman mae laifi…
Kama tagani sosai da mahaifin dijamahn.
Inda cikin murya can kasa tace”wannan yarinyan kine…itace khadijan dana sani!!!
Goge hawaye umma tayi,inda cike da dauriya tayi murmushi wanda tafi kuka ciwo….
Nan tace”ehhh itace dijamah…
Nan take uwani ta rungume dijamah, cike da farin ciki,inda a xuciyanta take kisima abubuwa da dama.

Horn da moton bayan su,ya hauyima uwani ne,yasata cikin sauri tasaki dijamah, ha’di da cema ummah”hajiya…a wani ruga kuke anan?
Umma ne ta tsaya kame² don sam bata son,wani yasan inda take,ita da ‘diyar ta ta…
Kaman daga sama taji dijamah na cewa” A RUGAR HAR’DO muke…..
Gaban umma ne ya fa’di,inda lokaci ‘daya tahau tunanin abun da xatayi akan lamarin.

Nan uwani tayi saurin cewa”insha’allah my deejah xan kawo maku xiyara,nida Abban ki….

Cike da matsanan cin farin ciki dijamah tace”lahhh dama nima da baba!!!…irin na bintoto…?

Tausayim dijamah ne yakama uwani,inda nan take ta ‘daga mata kai alaman ehhh,sannan tacigaba da cewa”kwanan
nan xakiga Abbanki…

Don da xaran yado kasan nan xaiji wannan kyakykyawan albishir,wanda ni kaina nasan bani kadai xan samu Alkhairy daga gareshi ba,har mada sauran mutane…wanda basu mason da xancen yana da iyali ba…..
“Cike da wauta da yarinta dijahma tace”tohhh Adda sai kinxoh…
Nan uwani ta kuma sakin murmushi, don lokaci guda taji matsanan cin kaunar dijamahn a ranta…
” maida kallon ta tayi,akan ummah wanda take tsaye tana binsu da ido,don bata ta6a jin nadaman surutu irin na dijamah ba,da haushi kamar ta yau…
“Uwani ce tace” tohhh xan wuce ni,kuma in Allah ya yarda xan xo inga inda kuke a kwanan.
Murmushi ummah tayi,wanda ita kadai tasan manufahn hakan…inda a sanyaye tace”tohhh uwani Allah ya kawoki lfy…
Nan uwani ta amshe da amin…
Uwani bata bar wurin ba,sai da tayi ma dijamah kyautan kudi…don gaba ‘daya rayuwan tasu ta tausaya masu matu’ka…
Nan ko dijamah ke ta murna,ha’di da yi mata godiya…
A hanyan su ta dawo wa,sam umma bata da karsashi,duk inta kalla dijaman ta,sai ta goge hawayen idon ta,wanda duk basu lura da hakan…
Yayin da dijamah ke can tana xuba ma yadikko bayanin wannan mata da taba shede…
A haka suna tafe suna fira,wanda kafin magriba sun iso cikin rugansu….
Nan kowa tayi cikin bukkanta,inda bintoto,take kara shaidama dijamah,anijima tafito,wasan dare a dandali…

Da shigansu bukka,bayan umma ta ajiye kwaryan su ne,ta fito ha’di da nufahn wurin da suke dafah…
Anan ta samu karyayi,ha’di da kara,ta kunna wuta,don ta girkama dijamah marori…(shinkafa)

Bata dauki wani dogon lokaci ba…ta kammala,inda nan tanufi bukkan da shi…

Bayan ta gama xuba mawa dijamah ne,tayo kiranta ha’di da bata,a cikin wata ‘yar a kushi….

Cike da murna dijamah ke cin abuncin…ha’di dayo mawa umma sunbatun da’di….

Umma dai banda murmushi ba’abun da take mata,don tunanin da takeyi akan uwani yafi damunta sosai,banda tunanin mafita babu abun da takeyi a yanxu…
“Dijahma da ta fahimci kaman da damuwa a tare da umman nata ne tace” umma na tunanin mai kikeyi ne,tun ‘daxu!!!
“Saurin kallonta ummah tayi,inda cike da mamakin fahimtan tana cikin damuwan da dijamah tayi tace” hmmm dijamah na,maxa ki kammala cin abun cinki…inaso xamuyi wata magana…

“Murmushi dijamah tayi” inda Cikin ‘dokin wata magana ce xasu yi da umman nata tace” umma tohhh,ai ma na ‘koshi,wace magana ne xaki fadamun….!!!

Ruko hannun dijamah ummah tayi,inda a hankali kuma cike da sanyin murya da taushi…tace” dijah na yau xamu bar wannan rugan…

Cikin sauri dijamah tace” ummah ina xamuje…maeyasa xamu bar wannan rugan!!!
Ko xaki kaini wajen abban na ne…?
Kwallah ne yafara xubo mawa umma shattu,inda tafa cewa” a’a dijamah bawurin Abban ki xamu ba.
A salima saboda shine xamu bar wannan rugan har’do a daren yau,wanda batare da kowa yasani ba…
Rigima dijamah tafara samawa umma,inda take cewa” umma mai yasa bakyason naga Abbana!!!mai yasa xamu rabu da su yadikko…mubar rugan mu…
Umma ni naji banason ganin Abbana,amma karmu bar su bintoto da yadikko,aradu banason tafiya na barsu….

Kuka dijamah tasa,inda umma ta jawota jikin ta,tana share mata hawaye,ha’di da cewa” dieejah yau xan baki labarina da na mahaifin ki,wanda in kinxa6a mucigaba da xama,a wannan rugan shikenan sai mu xauna…

Dajin haka nan take dijamah ta mike da kwancen da take a jikin umma,nan cikin sauri da ‘dokin son jin labarin umman nata tace” yeeehhh umma na,yau xaki gayamum iyayen ki kenan,dakuma labarin Abbana.!!?

A hankali umma ta ‘daga mata kai,wanda a zuciyanta take cewa yaro yarone…Allah sarki ita gata tana nan tana ‘dokin ganin mahaifinta da dangin sa,hmmm kosu suna ‘yan ina oho…don wanda ya’ki ka,baxai ta6a sonka ba…

Nisawa umma tayi ha’di da gyara xama,sannan tafara da cewa” kaman yanda kika sani….
Sunan Aishatu… Wanda nasamu sunan shattu daga cikin rugar har’do…..

________________________

Kuma ni ba bafullatana bace,kaman yanda kika sani,ko ince kika sanni acikin fulani….
A salina buxuwar agadas ne ce,’yar asalin garin maliy……

Mu hudu allah yaba iyayena,inda nake da yayyu maxa guda biyu,saikuma yayata mace wanda take da suna munawwarah.

Saikuma yayyuna maxa akwai,sama’ila saikum tanimu,wanda nice ‘yar autan su mai suna Aishatu…

Na kasan ce ‘yar gata,kuma ‘yar lele a wajen mahaifina.kasancewar nice auta…sosai nake samun kulawa…duda ba karfi ne dashi ba.

Duk inda baba na xai tafi tare dani yake xuwa…
Don haka gaba daya garin mu ba wanda bai sanni ba…don shiyasa innaga yanda kike mu’amalanki da mutane,dakuma yanda kowa ke nuna maki so,sai intuno da kaina a baya…don yanda kk ganki,kowa naki ne,tohhh haka nima nake a yarinta ta…

Banyi ilimin boko ba,amma inada na mahammadiyya,duda kasancewan mu buzayen agadas bamu damu da ilimin zamani ba,munfi damuwa da ilimin mahamdiyya…saikuma kasuwan cin mu…

Don haka tun ina yarinya nake sana’ar sai da abunci..inda nake kaima mawa ba’ki,wanda sukaxo daga kasashen kusa damu…kaman nijeriya da sauransu…

Muna son muga ‘yan najiriya sun xoh ‘kasan mu,don ganin su muke kaman wasu hallittu na daban…saboda sha’awa…inda a haka nake sana’ata kuma kowa yasanni da yanayin dabi’ata da kowa,inda anan na ha’du da mahaifinki,wanda asalin sa daga nijeriya yake,kuma cikakken attajiri ne ko alokacin,inda ya mallaki abubuwa da dama,don bakankanin arxiki yake dashi ba…

Kuma cikakken ‘dan jarida ne…wanda shine dalilin dayasa yaxo garin agadas…don harkan jaridan sa ne yakawo shi…
Wanda yake da suna……
Umma ne tacigaba da cewa” bakowa ne mahaifin ki ba,illah jounalist Muhammad maccido…kuma ‘dan asalin garin gombe ne….
A sanadiyan aikin sa ta jarida ne,allah ya ha’damu da shi,mutum mai yawan kyauta,tausayin talakawa kullum tsakanin shi da talakawa sai dai son barka…
Sanadin xuwan sa garinmu shine,yana son sanin wasu daga cikin al’adinmu na buxaye…

Don haka koda yasamu wasu daga cikin ‘yan uwan mu na maliy,sai suka ce akawosa wurina.

Acewansu nice mae si
Surutu,kuma xan fa’da mai har abun da bai tambayeni ba…don ni kaina nasan alokacin nan,ni ‘yar fa’di ba’a tambaye ki bane…

Haka aka taho da maccido inda nake sayarda Abuncina…a dandali.

A ranan shi kanshi sai da yagaji da surutu na ko da ake fa’da mashi…don ban barshi ya tafi ba,sai da na sayar da abunci na tasss tukunnah.

Don shima nasan inna dawo xan kara ‘dora ta la’asar ne…

Tun daga wannan rana kullum mahaifin ki,wanda mukai mai lakani da suna maccido sae yazo wurina a dandali…inda nikuma nayi ta koromai jawabin rayuwan mu ta buxaye…dakuma yanda ba ‘dauki karatun boko da wani mahimmanci ba…sosae Yakejinn da’din yanda nake bashi labarin mu…inda nikuma bawai saboda wani abu bane nake fa’da mashi,illah saboda ganin ana haskoni a cikin television…a haka sha’kuwa ta fara shiga tsakanina da muhammad maccido…

Inda daga baya soyayya ta shiga tsakanin mu da shi…
Sosai muke son juna,inda ni dai kawai son shi nake.amma nasan ba aurena muhammad xaiyi ba,duda irin son dayake nunamun…
Ammma sam ban kawo wai muhammad maccido da gaske yakeyi xai aureni ba…dakuma
Saboda nasan halin ‘yan nijeria,insunxo kasarmu haka xakaga suyita cewa”suna san yara,amma duk yaudara ce.
Don daxaran sun tafi ‘kasar su,shikenan sun manta da sun ta6a son wata buxuwa…tohhh da wannan yasa ban samawa raina auren muhammad maccido ba…musamman shima,wanda ko a ‘kasan nasu ansan da xaman sa.

Ana gobe xai koma ‘kasan su nijeriya ne,duk nadamu don nasan shikenan rabuwan mu taxo tsakanina da shi,amma damamaki sai naji yana cewa”inya koma gida,nan da sati xai turo iyayen sa akan maganan auren mu…

Hmm wannan rana nayi matu’kar farin ciki,wanda rabon da inyi irinta ni kaina na manta…

A haka mukai sallama da shi,inda da nadawo gida ne abun duniya ya dameni,don nasan da wuya su baba na su amince…

Musamman dana tuna da yaya ta,munawwarba yanda ta auri wani sojah a najeriya… wanda turosu akayi nan kasan mu,amma tun da akayi mata auren nan da shi,bamajin ko labarin ta…
Kuma ba bawai mara hali ta aura ba,don Lokacin da tayi aure da mukaje ‘yan kauye muka xama…amma tun da tayi aure so daya ta ta6a xuwa garinmu,wanda alokacin dana ganta ni kaina ban gane taba saboda yanda ta chanja,ta dawo kaman baturiya abin ka da farar fata…daka ganta kasan bata cikin wahala…amma halinta bana ‘dafan iyaye ba ne sam.
Tun da taxo sau dayan nan bata ‘,kara dawowa ba har wannan lokaci,wanda koda ta haifi ‘dan ta na farko,sai dai mukaji labari,don bata fada ma kowa ba…
Rayuwanta yakoma irin ta turawa xiryan,don tsakanin ta da kowa sai dai ido…idon ma baya ganin ta.

Kuma munawwarah tun asalin ta bata damu da karatun mahammadiya ba,amma na boko kuwa itace sahun gaba,dun haka da tasamu gidan miji ta cigaba da karatun ta,duda ban mae takaranta ba.

Wannan dalilin yasani kasa mawa su guggo magana…
A haka har lokacin da muhammad maccido yafa’damun xai turo iyayen sa yayi,wanda aranan da yace”bai karya alkawari ba…yako turo iyayen sa.dattijon arxiki.

Don sam basununa kyama a garemu ba…
Sunan baba na baisan da maganan ba ne,amma sam bai nuna masu bai sani ba.. Kuma haka ya kar6esu cikin mutuncin mu na ‘yan maliy…

Koda yaji maganan su,da abun dake tafe dasu,bakaramun farin ciki baba yayi ba.
Sai dai da suka nimi a tsaida magana ne yace”masu yanaso sunyi hakuri yaji ta bakin yarinyan tukkunnah…

Batare da damuwa ba,sukayi ma baba na sallama,akan cewa xasu dawo bayan mako guda.

Inda bayan tafiyan su ne,baba yasameni akan nasan da maganan muhammad maccido???

Ba tare da wani abu ba nace” masa ehhh…tunda baba yaji haka yasan na amince da muhammad maccido kenan.

Don haka guggo da baba sukasamun albarka sosai,kuma nayi matukar mamaki akan amincewan nasu…don ban kawo ba.

A kwana a tashi satin da’aka tsayar ta dawowan iyayen muhammad maccido yayi,kuma a wannan rana suka dawo…wanda ba’a 6ata lokaci ba suka tsayar da auren mu bayan watanni biyu masu xuwa…

Tun daga wannan rana soyayyar maccido yasamu wuri ya’kara xama a cikin xuciyata…wanda haka muka ‘kara sabawa da kuma son juna fiye dana baya…

Guggo har mamakin da yanda kullum maccido yake xuwa hanyar kasarmu take,inda haka yakuma kwantar mata da hankali sosai…xullumin da takeyi akan auran namu ya ragu.

Don ayanzu tasan maccido ba’karamun kauna ta yakeyi ba…gakuma yanda yanda ya ‘dauki guggo da baba…abun sai dai sam barka…

A kwana a tashi ba wuya gai rai,kuma mai nisan kwana…don auren mu yanxu tini ya matso… Don yanzu auren mu saura kwana uku kenan
..

Guggo tana ta zuba ido ko xataga xuwan munawwarah,amma shiru babu itah babu labarinta…wanda a haka har ranan ‘daurin auren mu yaxo….ranan da baxan ta6a manta shi a rayuwata ba…a wannan rana ne,dubban mutane kuma manya tsakanin nijeriya da agadas suka shaida daurin aurena da maccido… Inda kowa kagani a wurin fatan Alkhairy yake….

Bayan kuma ‘daurin aure ne,dangin maccido suka xo akan yanxu a lokacin xasu wuce dani xuwa nijeriya…

Nayi kuka sosai da naga a ranan shikenan na rabu da baba na da guggo… Inda guggo ke tamin nasihohi masu ratsa zuciya…
A haka muka biyo jirgi har cikin garin gombe,inda da saukanmu garin dangina suka ce baxa’a wuce dani gidana ba sai anfara kaini wajen surukata,wato mahaifiyan muhammad maccido… Kuma itace kaka a wurun ki…

 

____________________________

Koda muka isa gidan su muhammad ba’karamun mamakin gidan mukayi ba…don a wannan lokaci in akacemana gidan shugaban ‘kasane tabbas ba xamu musaba…dan gidane nagani kuma na fa’da,girman sa kuwa nayi maki yanda xaki gane tafi rugar har’do baki ‘daya….

Gaba ‘dayan mu muka xama ‘yan ‘kauye,kauyen ma irin wanda suka fito daga daji,badaga cikin mutane ba…

A haka wasu ma’aikatan gidan suka yimana iso har cikin tankasheshen falon hajiya babba…inda anxuba kayan alatu kaman ba’asan ku’din suba,don dukiyan da’aka xuba a falon bakin bama xai iyah fa’da ba.don masalta maku sai yasa na 6ata shafuffuka ban gama ba…

Wasu daga cikin dangin nasa kuwa ban da ya mutsi babu abun da suke bin mu dashi,yanda kasan basuga mutane ba.wasu ko daga cikin su nan take suka kar6emu hannu bibiyo…inda sukayi mana sannu da isowa.kuma anan take suka umarci ma’aikatan hajiyan,wato masu hidimtamata akan suka wo mana kayan motsa baki…

Sannan wata dattijuwa ta shiga don tasanar da hajiya babba isowar mu gareta…

Haka ma’aikatan ko suka dinga kawo mana kayan ciye² wanda sai da suka cika gabanmu tam sannan suka fara kawo mana gaisuwa cike da girmamawa.

Cikin wannan ma’akatan gidan kuwa harda uwani…wanda muka ha’du da itah a lumo…

Toh kunsan abunka ga ‘yan maliey babu dukiya ammma kuma akwai girman kai,dajan ajin kansu.don haka babu wanda ta kalla abun da aka kawo mana…
Haka su ummah shattu suka dunga xama,amma hajiya babba bata da alaman fitowa…don su basu san wainan da ake toyawa ba,don hajiya babba nacan ana fama daitah akan tafito wajenmu,amma sam ta’ki futowa,acewanta ita sam baxata ha’da xuri’a da bugaje ba.

Ganin haka yasa wannan dattijuwan fitowa daga 6arayin hajiya,inda take shaida mana cewa”hajiya babba batajin da’di,kuma kuma ta samu bacci ne…nan ta karke maganan dacewa”amma nan da gobe dakanmu xamu xo mukawota wurin hajiyan…

Godiya su innata sukayi,inda haka muka mi’ke ha’di da nufowa gidana…

Sosai muka yaba da tsarin gidan,dakuma girman sa,don ba’karamun mamaki mukayi daganin irin wannan gida ba.
Ni kaina ban kawo cewa”maccido nada wannan mahaukacin dukiya ba…

Tun daga wannan rana,muke xaune cikin lafiya nida mahaifinki…sosai yake nuna mun so da kulawa,inda ya samun ma’akata masu yawan da xasu ringa’ka mun hidima…
A cikin su kuwa harda uwani,wanda ya daukota daga gidan hajiya babba.

Sosai muke zaman lafiya da ma’aikatan gidana…don ni macace mai yawan surutu da barkwanci…don haka suke tsananin kaunata…

________________________________

Sati na biyu da aure,maccido yace mun xai kaini na gaida hajiya,kuma acan xan mata wuni,in yadawo wurin aikin sa sai ya dauko ni mudawo gida tare….

Cike da farin ciki na shirya,inda nace mawa uwani ta shirya itama muje tare,don naji da a hannun hajiyan take…

A haka muka shirya duka ha’di da nufan gidan hajiya babba…

A wannan rana ne na fahimci yanda hajiya babba ta dauke ni a zuciyanta,don wannan rana naga wulakancin da ban ta’6a gani ba…

Ciki da fara’a muka shiga falon hajiya babba, inda na sameta xaune kan 2 seater,dayan ‘6angarenta kuma wata mata ce,wayyayyiyar gaske,irin wa’annan matan da sukaci boko har suka gaji,wanda suke neman maza ido rufe…

Ko arzikin amsa sallaman bamusamu ba,inda cikin sayin jiki na duka har kasa na gaishe da hajiya babba…. Amma kallona batayi ba,illah ma cike da tsawa da masifah ta hau cewa”kehhh…..matsa ki bani wuri…kina tunanun xan kar6eki a matsayin suruka!!! Tohh lallai kinyi kuskure….jubiki da allah,gayyar yunwa…tohhh ni nan dakika gani,inkin malleke shi,tohh ni nafi karfin ki makirah….

Nan tanisa ha’di da kallon maccido wanda gaba ‘daya maganan hajiya babba bai masa da’di ba…

Kai kuma saunawa xan fa’da maka baxan yarda wannan busasshiyar taxama suruka ta ba..amma ka kiji…tohh kutashi kubarmun gida…ranan daka amince da auren binta ne xaka iyah shigomun cikin gida….
Ku tashi kufita nace….hajiya babba tace” cike da tsawa…yayin da doc.binta ke gyafe tana sakin murmushi,itah ala dole tayi kamu da uwar miji….

Kallon ta nayi,inda lokaci guda idona ya ciko da kwallah,uwani ko ganin halin dana shiga yasata,saurin girgixamun kai alamun kar nayi kuka akan maganan hajiya babba…
Nan maccido yafara ba hajiya hakuri akan tayi hakuri,kallon shi batayi ba,illah fixgixga batare da tace mashi komae ba…

Bai kuma bin ta kanta hajiya babba ba,yajuyo ha’di da mana sallama sannan ya nufi wurin aikin sa….

A wannan rana nasha wulakanci a wurun hajiya babba, amma sam ban nuna na damu ba,inda rashin nuna damuwata yakara bakanta ran doc.binta…
Haka rayuwa ta cigaba…inda shekarata daya a gudan maccido na haifoki,kuma har alokacin hajiya babba bata daina nuna mun kiyayya ba.amma sam ban duba wannan,tunda maccido yana nuna munso matuka….a wannan shekara kuma sai danaje wurin su baba na,inda kan na haifeki sai da naje sau biyu…wanda har alokacin munawwarah bata xoba…kuma taji labarin nayi aure….a nijeriya kusa dasu….amma bashi yasa ta nemeni ba…

Ba karamun murna Abbanki yayi ba dana haifeki,inda nan take yasa maki suna NANA KHADIJA…wato sunan hajiya babba… Hajiya kuwa bakaramun bakin ciki tayi ba,dajin hauhuwa ta…

Kwanan ki uku a duniya ne,ina xaune a kan gado na,a bedroom…inda nake goye dake abayana….

Kattawan maxa ne suka shigomun bedroom ba ko salllama,fuskan su duka a rufe da wani bakin kyalle….ihun su uwani nakeji,inda nan take na hau salati…amma kafin na farga tuni wani daga cikin su ya shakamun wani powder a fuska…

Wanda tundaga nan ban kuma sanin halin da nake ciki ba,sai farfadowa nayi naga ganni a rugar har’do….
اللهمَّ أَبْلِغْ عنَّا نَبِيَّنا وشَفِيعَنا وحَبِيبَنا أفضلَ الصلاةِ والتسليمِ ، وابعثهُ المقامَ المحمودَ الكريمَ ، وآتهِ الوسيلةَ والفضيلةَ والدرجةَ الرفيعةَ التي وعدتهُ في الموقفِ العظيمِ

جمعة مباركة 🌹🌹🌹

Allah kasa mana abarkan wannan rana,kabamu ikon aikata abu mafi kyawu a rayuwan mu,ka nisan tamu da shirrin mutum,ko shaidan….Ameen ya Rabbil ixxaty…🤲🏻

*_____________________________*

Bu’de idon danayi akan na yadikko ne,wanda take tsaye akaina…tana min firfita ta da wani langa langa abun fifita…gyafe guda kukan dijamah nakejiyowa,inda wasu daga cikin fulanin suke ri’ke da itah…

Ganin na bu’de ido,yasa yadiko cike da farin ciki,ta hau godiya ga allah, ta harshen su ta fulatanci…

Bin su kawai nake da ido,don bana fahimtan abun da take cewa”…

Magana tayi takuma ta harshen fullo…inda cikin hanxari wata mata tayo cikin bukkan,ha’di da isowa gareni har inda nake kwance takawo mun deeja…a hankali kuma cikin hausan ta wanda bai fita tafara cemun”ki bata nono take bu’kata tun jiya,sai yanxu muka samu kika farfa’do….don haka maxa kibata ai ma tayi ha’kuri…

Babu musu na Amshi deeja nafara bata nono,inda a raina nake tunanin ta yadda wa’innan mutanen suka tsiratar dani daga wannan axxaluman mutanen,wanda bansan wanda ya turosu wurina ba.

A hankali komai yake dawomun,inda nan take na hau xubar da hawaye mai dacin gaske…

Yadikko ne ta dafani ha’di da bani baki,akan komai na dauke shi a matsayin kaddara…

Haka na kwana uku a cikin rugar har’do,inda kullum wannan fulanin suke dawainiya dani da kuma kehhh deejamah…

A wannan rana da muka cika kwana uku ne,mai gari wanda yake yayane wurin yadiko,yayo kiran na…

Haka na isah wurin mae gari,inda anan yake shaidamun da yanda suka ha’du da ni,kuma da yanda suka taimakeni a hannun.
Bayan sun bar dani gidan maccido, basu tsaya dani a ko’ina ba,sai a kusa da wannan rugan…

Inda su mai gari na hanyar ta dawo wansu ruga daga cikin gari…nan suka ga wannan mutayen na janye da ni…abunka ga mara gsky,ako’ina sai ya nuna kansa…

Kunsan fulani ba tsoro..cikin tsawa da kuma hausan su wanda bai fita,su kace” waye wannan,mai kuke anan wajenn…

“Cikin muryan ‘yan ta’adda suka maida ma mai gari da magana ta hanyar cewa” kai tsohon najadu bar wurin nan,kasheta xamuyi,inkuma ka6ata mana rai mu ha’da da kai…

Cikin xafin ran sunan da suka kira mai gari yace”tohhh bari kugani,xare sandan su duka sukayi,inda suka nufi wainnan ‘yan ta’addan…
Ganin fulanin sunnufo su,kuma sun san bafillatani ya kasheka ya kashe banxa,musamman irin na daji irin wa’innan,yasa su saurin sakin ummah,inda sukayi wurgi da deejamah,suka kwasa da gudu ha’di da shigewa ta cikin dajin…

Bun bayan su sauran xasuyi,nan mai gari ya taresu,hadi da cewa” su barsu,suyi saurin ceton ran wannan bayin Allah…

Haka ko sukayi,inda da shigowan su,cikin ruga.suka sauka a bukkan yadikko…a haka sai da aka kwana guda sannan umma ta farfado…

Nan mai gari ya nisa, ha’di da tambayan ummah daga inda ta fito…
Shiru ummah tayi,don ita sam batasan ko’ina a nan najeriya ba,ita dai tasan tana najeriya…

Nan ta basu amsa da daga nijeriya take…
Shiru mai gari yayi,kan daga bisani yace” ae nan duka sunan shi najeriya…amma wani gari muke nufi kike?

Ganin umma bata da Amsa yasata cewa” ni ba ‘anan nake ba,ni ‘yar asalin garin agadas ne,aure ne yakawo ni nan.

Nan na xauna ta fara basu labarina komai da komai…

Sosai mai gari da sauran mutane suka tausaya mun,inda nan suka shaidamun suma basu san birni ba,kuma basu gane daga inda nake ba,saboda sunfi rayuwansu a cikin ruga…

Haka mai gari yace”na kara hakuri na xauna tare dasu har Allah ya kawo ranan da xan ha’du da dangina,ko miji na…

Sosai nayi farin cikin xama da su…fulanin kirki.
Kewa daya nayi,shine kyewan baba da guggo,sai kuma halin da maccido yake ciki a yanxu…amma duk inna kalleki sai naji gomma da allah ya barni dake…

A haka nacigabada rayuwa a wannan ruga,inda a haka kika girma a cikin wannan ruga.
Kuma su yadikko su suke maki fulatanci,kinji yanda akayi kk iya yaran fillo,don ni ban iya ba…sai dai na biku da ido,amma yauda gobe xaman tare yasa har na fara fahimtan wasu abun…

Nisawa umma tayi ha’di da kallon dijamah,wanda kuka takeyi sosai,tausayin ummah yagama kamata,cikin sauri ta mi’ke cike da yarinta tafara cewa”ummah ki tashi mugudu,kar su abbana suxo su tafi damu,hajiya ta turo aka shemun ke…

Goge kwallan idonta umma tayi,inda ta kamo hannun dijamah ha’di da cewa” a’ah deeja ba hajiya ce ta turo wa’innan mutane ba,nima bansan waye ba…
Sannan kuma dama ayau xamu bar wannan rugar har’do…

A hankali umma ta mi’ke ha’di da nufahn kasan gadon karan bukkan,inda ta fito ma wa da dijamah kayanta na saken fulani guda uku…
Sai kuma nata kala biyu…
Saida su ka tabbatar da kowa ya shiga cikin bukkan sa,sannan suka fito ha’di da barin rugar har’do…
Tafiya sukeyi suna waiwayon wannan ruga,inda suke tunani ranan da wowansu wannan ruga…

_____________________________

Tafiya suke cikin dare,inda a haka suka isah tasan cikin gari.

Batare da umma tasan inda xata ba,ta kutsa kai cikin wata mota dataji ana cewa”Adamawa…

Shiga sukayi,inda saida dijamah ta ganta a cikin mota,ta hau tambayan umma tana da shede ne…
Nan umma ke shaida mata,tana da kudin da uwani ta basu,dakuma wanda sukayi ciiniki a lumo…

Safiya tayi masu ne,acikin garin Adamawa,inda dijamah cike da farin ciki take bin garin da kallon sha’awa…

Sai da umma tasha fama,sannan drivern ya amshi kudunta,don kudin nasu bai kai ba…

Ware ware ta suka hauyi,inda wasu samari ganin suna ware² yasasu tambayan inda xasu?

Batare da wani tunani ba,umma tace”ruga…!!!

Shiru sukayi inda suka ce,wani ruga kenan mama?
Rugar ya windo….ko rugar surbajo….
Nan umma tace”Rugar surbajo….
Nan suka sa su umma a abun hawa,ha’di da biyan masu kudin,wanda badon kowa suka biya ba,sai don dijahmah….

Gaba daya dijamah tagaji,ga wani irin mahaukacin yunwa da takeji,tun tana daurewa har takasa,inda a haka suka isa wannan ruga,…bayan sun sauka daga abun hawane,suka fara takowa daga ‘kasa,don isah cikin wannan ruga,wanda tafi rugar har’do wayewa…

Nishi dijamah ta hauyi sama² inda umma cike da ru’du tafara ware² n ruwa…amma sam babu ruwa a wurin,wulkawn mutum ma babu bare,ruwan.

Tun dijamah na fitar da numfashi,har ta kasa,inda lokaci daya numfashin ta ya ‘dauke…kuka umma tasa ha’di da kiran sunan dijamah…amma sam babu alaman numfashi a tare da itah…

Dai² wasu tsofaffin fulani,wanda da’alama mata ne da mijinta,sukaxo wucewa….
Cikin axama matan tayo inda umma ke a durkushe,nan ta hau tambayan ta daga innah take???

Kasa magana ummah tayi,illah cewa da umma take” don allah ku taimakamun kar dijamah ta mutu,’ya ta ce….
Duka ta harshen fulatanci suke maganan.

Wannan tsohon ne yayi saurin ci6an dijamah ha’di da nufah cikin ruga da itah,wanda da isan su suka nufi cikin bukka ha’di da kwantar da dijamah…

*_____________________________*

*Cikin garin…..*
*GARIN ADAMAWA*

Wani tan’kasheshen gida ne na ganj,wanda girmansa yasa turawa ke kiranshi da estate house…

Gida bakaramun gida ba,wanda girman sa.ma,baxai fasaltu ba…
Sojoji kuwa xasu kai kimanin fiye da 50 xuwa sama,ko wannan su na kewaye da wannan gida…wanda da ‘alama tsaron gidan sukeyi…licrout da sauran securities,wanda ba sojoji ne ka’dai ke tsaron gidan ba….

Jiniyan jami’an tsarone najiyo daga bayana,wanda yasani saurin jirgawa daga bakin tan’kamemen gate ‘din danayi nisa wajen kallo…

Wasu motoci ne ke biye dana GEN.SUFYAN TABAWA…
Inda motocin sun kaifi 15 ke bin yanshi,wasu a gaba wasu kuma a baya…

Bayan anware tankamemen gate ‘din ne,nayi saurin shugewa…daga ciki…

Hmm gidane wanda daga waje ashe banga komai ba….arxiki nadaga ciki….

Bude mawa hajiyan nashi mota akafarayi,inda sauran securities suka bude ma sauran side dun…

Cike da ixxa da jida issa da dukiya ta fito,tana ciko wuya…wanda kayan dake jikinta kadai ya isah yasa katafi duniyan tunani….jikin nan kuwa ta ko’inah yasha zinarai….

Niko nace”JUSTICE MADINA KENAN..

Uwar gida kuma amarya a wurin General sufyan tabawa….

Fitowa yayi cikin shigarshi ta alfarma,inda ya juyaga ‘yar tasa wanda saukan su kenan daga ‘kasan,nan yace mata”welcm back to nijeria my kid…!!!ya kika ga new house ‘din mu na nan?

“Ya tsina fuska yarinyan tayi,inda cike da mulki tace” ba laifi dad,amma kayimun laifi guda ‘daya…

“Kallon ta justice madina tayi,hadi da cewa” okay my baby mai yafaru,mai kuma ya6ata ran baby na…ta fa’di tana sakin mata ‘kayataccen murmushi…wanda bamai ganin sa,sai ‘yan ‘ya’yan nata…

Cikin basarwa a kuma wula’kance” ‘yan nata tace” dad yace mun kid…bayan ni ba kid bane yanxu,ko mom baiga na’kara girma bane…?

Don haka yabani ha’kuri.
Nan ta karke maganan ha’di da turo ‘yar mitsilan bakin ta.

Cikin rayuwansu ta ‘yan cin da suka saba,dad yayi dariya ha’di da shafa kan ‘yar tasa,sannan yace” eyyah sowie my dear meenash…baxan karaba…

Justice ne tayi”murmushi, inda meenash tayi wani barander da xai sada tada sitting room…batare da tace” ma dad komai ba…

Bin bayanta sukayi,inda ma’aikatan gidan ke auki ‘kame masa,yayin da wasun su ke kaimasu gaisuwa…

Basu ta kansu ba sukayi cikin falon tasu,wanda tagaji da kayan alatu da more rayuwa…

Ganin babu meenash,afalon yasa justice haurawa saman stairs,don tasan can tayi,yayin da a zuciyanta take cewa”ohhh meenash ‘yar daru kenan…har yanxu fushi take,ala dole batason nijeria…

Kaman ko tasani zaune ta samu meenash a kan wani super cushine,inda ‘yan aikin part ‘din ke xube a gabanta suna kwasan gaisuwa da mata barka da dawo wa.

Kallon su batayi ba,inda take cike take batsewa…

“Justice ne tayi saurin nufo inda take,ha’di da xama gyafenta,ta jawota ha’di da xaunar da itah a jikinta.

A hankali kuma dai² kunnen ta,ta hau yima magana.inda batare danaji abun da tace ba sai dai maganan meenash naji tana cewa” No mom bana son nan ‘kasan,kawai mukoma Abroad plz….

Kuma innan kasan nada da’di mai yasa ya Aliyu bai dawo ba….????