Azima Da Aziza macizai ne complete hausa novel

Azima Da Aziza macizai ne complete hausa novel

Advertisements

Azima Da Aziza macizai ne complete hausa novel: azima da aziza,azima da aziza 30,azima da aziza 25,azima da aziza 23,azima da aziza part 3,azima da aziza 50,azima da aziza complete,azima da aziza 1,azima da aziza book 3,azima da aziza 26,azima da aziza hausa novel,Azima da aziza

Azima Da Aziza macizai ne complete hausa novel

PAGE 1 – Subhanallahi! Wannan bala’i ya yi yawa, a ce a kwana uku an kashe mutane goma? Masu kama macizai mutum takwas, wannan wani irin masifa ce ta macizai da ya fara addabar mu haka a gari? abu sai tsamari yake yi, tun ana samun sara kaɗan-kaɗan, ga shi saran macizai din bakinsu da girma! Me yake shirin faruwa ne haka a cikin wannan alƙarya na da mutanen yanki na?” cewar mai garin yankin kauyen kwana dake jihar yola da yake can cikin dajin fulani wanda ya cika da albarkatun korayen shuke-shuke, a wannan sassanin fulani ne suke rayuwa a wannan yanki, kuma su na da yawa dan sun hayayyafa, basu fita cikin gari kuma ba a shigo musu.

Azima Da Aziza macizai ne complete hausa novel

Advertisements

Jama’ar da suke tsaye a wajen ne cike da jimami da fargaba su na alhini, wani dattijon tsoho cikin harshen fullanci ya ce gaskiya muna cikin hatsari a wannan alƙarya, ga shi yanzu an fara samu kisan macizai da yawa, ya kamata mu san abun yi” sai tattaunawa suke yi ta yadda zasu shawo kan wannan babbar matsalar da suke ciki, wata kyakkyawar budurwa ce a tsaye a can gefe fara sol, tana da idanun mage, sanye take da kayan fulani ta naɗa farin mayafi a saman kanta, ta rufe gefen fuskarta da shi, rabin gashinta ya sauko ya rufe mata rabin fuska wanda ya sake hana asalin kyawun nata fitowa sosai a gani,kafarta babu takalmi.

A hankali ta bi mai kama macizai wanda aka kashe da kallo, ranta a b’ace ta juya a hankali tana tafiya dukkan sassan jikinta yana lankwasawa, a yadda take taka kasa da ka ganta kasan bata yi maka kama da cikakkiyar mutum ba, daji ta yanka ta shiga cikin korayen bishiyoyi inda zata samu yar uwarta kawai take hari, can kusa da wani rafi mai sanyi da dadin kallo ruwan fari k’al da shi abun sha’awa taja ta tsaya, bata ankara ba taji saukan wani zureriyar wutsiyar maciji, ko kaɗan hakan bai tsoratata ba, tunda ita ma macijiyar ce, d’aga idonta ta yi saman bishiyar da wutsiyar macijin ya sauko mata, ta kalli yar uwarta wanda dukkanta macijiya ce,a hasale ta ce.

AZIMA!! me yasa kika son kashe mutane kwanan nan ne kam?” macijiyar da aka kira da Azima a hankali ta sulalo daga saman bishiya ta kanannaɗe yar uwarta tana lasarta da harshe, hannu dayar tasa ta ture kanta a macijiyar, sannan ta ce
“Azima tambayarki fa nake yi?” gefe ta koma ya yinda ta saki wani huci ta girgije nan ta zama rabi mutum rabi macijiya, daga ƙugunta abun da ya yi sama mutum ce, daga kugunta abun da ya yi ƙasa macijiya ce. Kuyi download din novel din anan kasa

Azima Da Aziza macizai ne complete hausa novel

AZIMA DA AZIZA MACIZAINE NOVEL Complete
Name Azima da Aziza novel
Author ZG Sidi
Size 242 KB
File Type TXT
uploader ZG hausanovels
ebook compiler Hausa ebooks
Price Free
Source ZG HAUSA NOVELS
Group NIL
Story Created Story
Image Credit Shuraih 99%
date modified 22 DEC 2021
Tags azima da aziza,azima da aziza 30,azima da aziza 25,azima da aziza 23,azima da aziza part 3,azima da aziza 50,azima da aziza complete,azima da aziza 1,azima da aziza book 3,azima da aziza 26,azima da aziza hausa novel,Azima da aziza

 

Next >>>> Zuma Da Madaci Hausa Novel Complete

Advertisements