Connect with us

Amrah Macijiya Hausa Novel

Hausa Novels

Amrah Macijiya Hausa Novel

Amrah Macijiya Hausa Novel: A wannan shafin munkawo muku amrah macijiya, amrah macijiya complete, amrah macijiya ce,amrah macijiya 25, amrah macijiya hausa novel complete, amrah macijiya page 25, amrah macijiya 10, amrah macijiya page 20, amrah macijiya hausa novel, http amrah macijiya, amrah macijiya page 3, Amrah macijiya da sauransu.

Amrah Macijiya Hausa Novel

Title Amrah Macijiya Hausa Novel
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 498kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author  
Tags amrah macijiya,amrah macijiya complete,amrah macijiya ce,amrah macijiya 25,amrah macijiya hausa novelcomplete,amrah macijiya page 25,amrah macijiya 10,amrah macijiya page 20,amrah macijiya hausa novel,http amrah macijiya,amrah macijiya page 3,Amrah macijiya
Published date 18 – 09 – 2022

Amrah Macijiya Hausa Novel

Download Now

Amrah macijiya 2

Labarin mutuwar malam Abu ya riski kowa dake kauyen, hankalinsu ya matukar tashi dasu kaji cewa macijine ya kashe shi.

A fadar mai gari kuwa kowa ya taru ana jiran iliya mai macixai yaxo, yana isowa a kace ya bude macixai nai a duba bakin su aiko aka duba amman sarar batayi kama da bakin macixanba, haka aka taro akayiwa malam abu wanka da sallah aka kaishi makwancinsa.

Washe gari amrah tana daki tana bacci gwaggo ta shigo ta tayarda ita tana cewa”yar jikalle tashi Dan Allah na aikeki gidansu harira ki karbomin daudawa gurin innah”toh gwaggo ta tashi ta fito bayi ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta dauki mayafinta Green tasaka ta nufi gidansu harira.

Tana xuwa ta tararda harira na wanke_wanke gaisawa sukayi sannan ta nufi inda innah suka gaisa sannan tagaya mata abunda gwaggo ta aiko ta karba, bata tayi sannan ta fito xata wuce harira tace “amrah bayan la’asar xanxo mutafi rafi, toh kawai tace tafice daga gidan.

A hanyarta ta komawa gida taga wasu samari su biyu suna mgn kuma akan mutuwar malam Abu ne, dan tsayawa tayi Dan taji me suke fada, dayanne yace” hmmmmm ni wlh wannan abun yafara bani tsoro ace anrasa gane wane macijine ke wannan kisan har yau.

Dayanne yadafa kafadarsa yana cewa “nima dai abun yafara bani tsoro, amma ai gobe ne maigari yace maccido maciji xaixo da kuma magani, kowa dake kauyen nan xa’a bashi yasha, duk Wanda a maciji toh yanashan wannan maganin xai fara rikidewa, kuma na rantse muddin wannan macijin ya kasance acikinmu toh wlh saina kashe shi har lahira wlh, gaban amrah ne yafadi saikuma naga tana wani shu’umin murmushi Wanda daka gani kasan bana alkhairi bane.

Gida ta karasa tana xuwa tabawa gwaggo daudawarta ta shige daki, da kallo gwaggo tabita sbd taga yanxu duk ta canxa kamar ba amrah taba, ynx mugun halin shiga daki tabijiro dashi, girgixa kai kawai gwaggo tayi ta tashi tashiga bayi, tana fitowa ta dauro alwallah ta nufo dakin, ta tayarda sallah, tashi amrah tayi.

Bakar Inuwa Hausa Novel Complete

Amrah macijiya Page 3

Hannunta tasa a cikin rafin ta ibo ruwa ta watsamata, a firgice ta farka tana ja da baya tana girgixa kanta hawaye na sauka akan fuskar ta cikin rabewar murya tafara mgn”da.. dan Allah am.. rah kiyimin rai kar..

ki kasheni, murmushi tayi sannan tace “hmmmmm harira kenan da inada niyar kasheki da tun ranar da kika fara ganin idanuwana da a ranar xan kasheki amman kuma baxan iyaba sbd yadda na daukeki kamar yar uwata tajini shiyasa baxan iya kasheki ba” ajiyar xuciya harira ta sauke sannan tace “kenan duk kashe kashen da akeyi a kauyen nan kece, kuma ke kika kashe malam abu?

Eh nice kuma duk wanda kikaga na kashe toh yashiga gonata neh, kuma ni bana yafiya kuma bana mantuwa, kuma wannan abun daya faru inason yaxama sirri a tsakanin mu sbd koh gwaggo batasan cewa ni MACIJIYA ce bah”inshaa Allah ba Wanda xaiji toh amma wa’ennan da kika kashe yaza muyi dasu?

Anan xamu barsu, ido harira tafitar waje tana cewa “anan kuma amrah? Eh tashi mutafi, xata sake mgn amrah ta daka mata tsawa tare da tsareta da green eyes dinta, ai nan danan harira tahadi ye abunda tayi niyar fada, cikin kauyen suka nufa, AMRAH tashige gidansu itama harira tayi gida.

Washe gari da misalin karfe 4:00 mutane sunfara taruwa a fadar mai gari kuwa jiran maccido mai macixai yake ya kara so dansu wannan masifar tayi yawa.
AMRAH koh tuni ta fice daga gida lokacin gwaggo na bayi batama San da fitarta bah.

Farkon shigowa gari tanufa ta haye saman bushiya tana jiran isowar maccido mai macixai, aiko can ta hangoshi saman rakumin sa da wata katuwar leda da gani dai kasan magunguna neh a cikin ta.

Murmushin mugunta tayi sannan ta diro daga kan bishiyar ta tsaya bakin hanya, tun daga nesa ya hangeta, sanye take da kaya green har mayafin kanta green neh, yana isowa ya sauko daga kan rakumin sa, yanufi inda take yana cewa”ke yarinya me kikeyi anan gurin maimakon ace kina fadar mai gari”.

Mayafin kanta ta yaye ai maccido nayin toxali.

Karanta: Silar Fyade Hausa Novel Complete

Amrah macijiya 25

 

Bayan jalal yayi parking, sai kuma su kaji ansake bude get, motar Sadeeq ce ta shigo, sai motar driver, tsayawa suka yi shida daddy,

Bayan su Sadeeq sun fito hakama su gwaggo, daddy yace “aa hajiya(ammi) meke faruwa naganku haka,

Murmushi ammi tayi sannan tace, alhaji mu shiga daga ciki sbd mgnr bata waje bace,

Bayan sun shiga baffa da gwaggo harda harira sai faman raba ido sukeyi, dan suga ta inda amrah xata bullo,

A hankali ammi tace” alhaji nace koh amrah tananan, sbd maganar da xanyi ta shafeta,

Ta shafeta kuma ammi, jalal ya tambaya fuskarsa dauke da mamaki,

Ai ynx xakaji komai, kirata kawai,

Tashi yayi ya nufi dakin amrah, da mommy yaci karo, koh kallonta beyiba ya nufi dakin amrah,

Daddy koh tashi yayi ya nufi dakinsa, yana cewa hajiya ku bani minti 2 pls,

Mommy kam ganin daddy ya hauro saman yasata bin bayansa da sauri, tana shiga ta rufe kofar da key,

Juyowa yayi ya kalleta ransa a bace, yace keee jahila bakida hankaline xaki shigomin daki bbu sallama,

Da sauri tace “Muhammad yau ni kake kira jahila lalle nayi sake, toh wlh baka isaba,kai har ka isa ina fada kana fada, wlh….

Wani wawan mari daddy yakai mata, wani irin ihu tayi tace” wayyo Allah na asiri ya karye,

Nan ta shiga tonawa kanta asiri duk wani mumunan abu data aikata saida ta fada,

Ai daddy kam jawota yayi ya kaita wani dakin da bbu komai aciki ya rufeta, sannan ya dawo falo,

Daidai wnn time dinne amrah da jalal suka sauko, gabanta sai faduwa yake,

Suna karasowa falon idonta ya sauka kan gwaggo ai da sauri ta isa gurin ta ta rungumeta, tana kuka, can idonta ya sauka kan harira, da sauri suka rungume juna,

Shikam jalal duk sun daure masa kai, baffa ne yace “fatima”,

Da sauri ta juyo amma kuma batasan shiba but taga kamar su da gwaggo,

Ammi ce tayi gyaran murta, snn tace, inason duk kubani hankalinku nan, sbd wata muhimmiyar mgn da xanyi,

Shiru suka yi na, nan Ammi ta gaya musu duk labarin da gwaggo ta fada musu,

Da sauri daddy da jalal suka Mike, a tare sukace what!! Amrah macijiya ce, suna nuna ta da hannu,

Ita kam amrah gaba daya jikinta rawa yake jin mahaifinta na raye kuma wai gashi a gabanta,

Da sauri ta tashi ta fada kan jikin baffanta tana sakin wani irin kuka,

Gaba daya dakin shiru akayi, jalal kam sai ynx ya yarda da mafarkin sa akan amrah,

Baffa ne yace “ynx dai abunda xa’ayi mu tashi mutafi *TIGADAM* sbd ayi gaggawar raba BAHUUL da yata,

Daddy yace ai ynx ma we are ready kawai mutafi, da sauri ammi tace” toh ina hajiya Sarah,

Manta da ita hajiya nan dai ya sanar dasu abunda tayi musu, kowa na dakin saida ya tsine mata albarka, inna lubabatu ma tace xata bisu, kuma suka amince,

Mommy kadai aka bari, dan Suhaima ta tafi gidan kawarta, kuma acan xata kwana, kuma sunyiwa mai gadi kashedi kar abari kowa ya shigo,

Ammi ma ta sanarda alhaji ma’aruf mahaifin Sadeeq abunda yake faruwa, kuma ya yarje mata akan taje,

*TIGADAM*

Bayan sun isa, inna tayi farincikin dawowar amrah,

A gidan gwaggo suka sauka gaba dayansu, inna ma gidan ta dawo, sai tabarwa su jalal Nata gidan,

Washe gari, gaba daya garin TIGADAM ya dauka amrah ta dawo, mutanen kauyen da dama sunce idan ta fito sai sun kashe ta,

Mai gari da kansa yaxo gidan gwaggo, kuma sunyi farincikin ganin magaji, shawararda suka yanke itace xa’aje gurin malam, domin asan makarin kafarda BAHUUL daga jikin amrah,

*GIDAN MALAM*
Daddy da jalal da Sadeeq, sai su mai gari, aka tafi,

Wasu abubuwa malam yayiwa amrah nan take ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya, ba jalal ba hatta daddy saida ya tashi xurawa da gudu, sbd ganin girman macijiyar,

Goshin macijiyar malam ya dafa, nan take ta koma mutum, kuma babu wani abu na jikinta dake aiki, sbd malam ya kafarda ita,

Ajiyar xuciya malam ya sauke sannan yace “a gsky magaji yarka tana cikin matsanancin hali, a halin ynx na kafarda BAHUUL sbd inba hakaba xai kashe wani daga cikinmu,

Kuma BAHUUL xai fita jikin amrah amma sai idan tayi aure, mijinta ya sadu da ita wnn hanyar kadaice xaisa BAHUUL ya fita jikinta, kuma koda ya fita ya riga ya mayar da ita macijiya,

Shiru gaba daya dakin yayi, daddy ne ya kalli magaji, sannan yace “magaji ina nemawa JALALUDDEEN auren yarka”,

Da sauri magaji ya dago ya kalli daddy, shima shi yake kallo, jalal baffa ya kalla,

Murmushi jalal yayi yana sadda kansa kasa,

Baffa yace”alhaji anya kowa danka xai iya rayuwa da macijiya,

Magaji, daddy ya kira sunansa sannan yace”ai jahadi ne xaiyi, kuma shima yana sonta, fatana dan Allah shine ka bamu auren fatima, ya karasa fadar haka hade da rike hannun magaji,

Toh na amince Allah ya saka da alkhairi yabar xumunta, gaba daya dakin aka amsa da amin,

Nan take aka daura auren JALALUDDEEN DA FATIMA AMRAH MACIJIYA, akan sadaki naira dubu dari cifff.

Nasan masu karatu zasu so su karanta littafin: Hariji Hausa Novel Complete

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in Hausa Novels

To Top
× Chat Zamgist on WhatsApp