Barka da zuwa wannan shafin namu na littafan hausa novels inda muka kawo muku littafin rainon soja hausa novel book 2 Hausa Novel Complete by Maman teddy.
Rainon Soja Hausa Novel Book 2
Hidima ce ta makarantar ya taso Nasreena? . Muryar Dattijon mai cike da kamala ya katse Nasreen dake tsaye cike da rashin tarbiyya akan sa . Eh zaka bani kuɗin Yes and No. Kuma Abba kuɗi ne masu yawa Wallahi duka semestern nan babu littafi Mai tsadar shi.
“To to badamuwa , kije Wurin baƙo ya baki kuɗin ,Allah yayi miki Albarka ” . Amin Abba ….ta furta tana Gimtse Dariya tana ficewa daga Falon.
Mtswww Ɗan Rainin hankali, Wallahi Allah ɗaya kenan da ina da gado akan tsohon nan babu yanda za’a yi ba zan kashe shi kowa ya huta ba. Ai kashe shi kawai xanyi mu ƙwashi wannan ƙazamin Dukiyar da tayi masa yawa. Wai dama kuɗi na zama hannun jihili mara ilimin boko ɗan ƙauye irin wannan ?
Babu damuwa ko ba komai Ai Umma na tare dashi , idan ya mutu koda bata da ɗa bare jika dole zata samu wani Abun…Bagidajen banza kaxo duniya a asara babu ɗa bare jika sai tara mata har uku duka kuma babu wacce Allah ya bata ɗa ko ƴa da kai.
Ni wallahi lamarin arziƙin sa da kuɗin sa har mamaki nake yi , mutum ya kusa rami amma sai long plans da yake dashi yau yana kasuwancin kaza ba tare da kin yi wani tunani ba zaki ji ya matsa to the next step tirrrr” . Duka Maganan take yi tana ficewa daga part ɗin tare da nufar ɓangaren Hajiya Falmata wato mahaifiyar nata.
#General Saleh Yelwa’s estate.
Wallahi yau sai nayi ƙasa-ƙasa dake a cikin gidan , Mara kunya Shashashan yarinya , lallai kin manta Wacece Ni , Kin manta …..Mami don Allah kiyi haƙuri. Muryar Aliyu ya katse Mami dake mawa Jidder faɗa. Daddy kuwa Wani irin huci yake saukewa yana zaune don baya son ya motsa daga inda yake ran kowa ne zai ɓaci don General bai iya fushi ba sam . Yana riƙe da Ma’eesha dake ta ɗigar ruwa , Khalil ne ya katse Aliyu da cewa “ Wannan yarinyar Jidder muguwa ce ,bata da imani yanda take baƙa haka zuciyar ta yake baƙi,shi yasa Allah yayo ki baƙa a cikin mu . Daga yau duk ranan da kika ƙara wallahi kema sai kin bar cikin gidan nan ,yanda kika barta a ruwa kema sai kin zauna a ruwa . Don ko ruwan ta ɗauki duk inda rijiya take sai na sakaki na mintoci.
General ne ya Girgiza kai tabbas yasan Halin sojojin nasa zasu aikata abin da yafi wannan , don basu ɗauki hakan ma a babban hukunci ba . A’a duk abun bata kai haka ba , ku barni Ni da kaina zan mata hukunci kuma ko yanzu ai ba ƙyaleta nayi ba . Muryar Mami ya katse su…..wanke irin zafi zuciyar Jidder keyi ji take tamkar tayi kukan kura ta shaƙe Ma’eesha ta kashe ta sai suyi mata hukunci da zasu yi.
Cike da Tsananin ɓacin rai ta kai hannun ta tana dukan Table ɗin dake a gaban ta tana fashewa da kuka tare da miƙewa tsaye. Kallon ma’eesha tayi tana cewa “ To me zai hana ku kashe Ni saboda Ita! Ku kashe Ni ba bar duniya saboda tsintacciyar da ba’a san Asalin ta ba! Ɗifffff………….wurin duka suka ɗauke wuta da jin kalaman Jidder. Cigaba tayi da cewa“keeee Ma’eesha Bara kiji Mami Daddy Duka basu ne iyayen ki ba ,basu ne suka haife ki tsintar ki Yah Aliyu Yayi ya kawoki cikin gidan nan tun kina jaririya shine ya raine ki na tsawon shekaru kana Mami ta amshe ki ta…….Tas-tas-tssss-taasssss ,saukar marin da Khalil ke yi ma kuncinta ya yi sanadin dakatar da ita daga maganganun da take yi . Mari ne ya wanke ta dasu a lokaci ɗaya sunfi huɗu . Mahaukaciya kaiiiii Jidderrrrrr…….Yayi magana yana ƙara idanun shi sun kaɗa sunyi jaa a lokaci guda ya rasa wani irin Abu zai ma jidder .
Da Sauri Aliyu ya kai hannun sa yana dakatar dashi tare da taro shi yana furta “ Wannan duka ba abun ɗaga hankali ba ne? Take it easy please ” . Kuka mami ta fashe dashi mai tsuma zuciya da Sauri tana nufar inda janar yake da Ma’eesha hannun ta takai tana rungume Ma’eesha wacce ta tsaya duka tana bin su da kallo , ƙwaƙwalwarta na wani irin juyawa ta bakin ta na don furta kalma ko da ɗaya ce amma kuma ta kasa ” . Taho baby na … Mami ta furta tana ƙara manna Ma’eesha daga jikin ta wanda sai a yanzu hawaye suka fara bin kuncinta. Kuka suke yi sosai ita da Mami yayin da Muryar Khalil ya katse su mai cike da Amo, kar ki kirani yayan ki inadai baki kira Ma’eesha ƙanwarki ba , wannan shine final say daga gare Ni . Kar ki ƙara nuna kin Sanni indai kin cire Ma’eesha daga cikin Ahalin mu. No…..” Jidder tayi maganan tana Cigaba da kukan ta don marin da Khalil yayi mata sai da ta zube a ƙasa don azaba. Akan ta yau ka dukeni abun da baka taɓa ba , Wallahi tsanarta na ƙaraji kuma dole ba zata zauna cikin gidan matsayin ƴa ba sai dai ƴar Aiki . Baki isa ba! Zan saka a karairaya ki jidder sai dai daga baya mahaifiyar ki tayi jinya! Muryar General Saleh Yelwa ya katse su cikin tsananin bayyanar ɓacin Ransa. Har wani gumi ke tsatstsafo masa ya rasa da wani ido zai kalli Ma’eesha wacce a yanzu babu sauran Alayen da ɓoye-ɓoye da zasu yi mata ”.
Mami da Gaske ne ke ba Mamana Bace, Haka Daddy Uncle Haidar shima……. Saurin saka hannu Mami tayi tana rufe mata baki kana tace “A’aaaa ….mami da gaske ne just say the truth a shirye nake da ko wacce irin ƙaddara , ko da na rasaki na rasa Daddy duka I will take it as my life destination Mami…Zubewa Mami tayi a ƙasa kalaman Ta suke tsinkar mata da zuciya wani irin kuka mami keyi mai tada hankali ji take ina ma zata mutu duka ta huta don bata da baki da idon da zata kalli Ma’eesha ta sanar mata da gaskiyar Al’amarin. Matsawa Jikin ta Ma’eesha tayi tana sa hannu tare da goge mata hawayen kana tace “ Mami kukan da kike yi ya nuna mun gaskiyar Kalaman jidder, Wasu irin ƙwallah ne suka biyo kuncinta kana tace “ Amma Yah Khalil shi Yaya na ne ko mami?….A’a shi ba yayan ki bane!
Muryar Ali ya katse wanda yayi Maganan kan sa tsaye . Duka saurin kallon sa suka yi , kamin ya cigaba da cewa “ Dukan mu ba familyn ki bane,maganan da jidderh ta faɗa duka gaskiya ne”.
“Haidar…..!
Wannan wacce irin magana ce so kuke ku kashe mun Ma’eesha? , Yarinya ce fa ƙarama? So kuke zuciyar ta ya buga ko kuwa ta tashi tana tunanin wasu ahalin bayan mu? . Mami ke Maganan cikin sarƙewar murya….kallon Aliyu Haidar Ma’eesha tayi kana ta motsa a hankali tana tankawa tare da wuce su ɗaya bayan ɗaya tana nufar Bedroom ɗin ta”. Tsittt kaji wurin yayi sai shashsheƙar Mami da zuciyar ta ke mata wani iri …Kallon su jidder tayi tana haurawa saman up stairs tare da barin su anan itama tana nata kukan ”.
Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un Furucin da General Saleh yayi kenan yana kaiwa da komowa a tsakiyar falon.
Zumbur! Mami ta miƙe tana Saurin bin bayan Ma’eesha . Kowa yaje yayi harkar gaban sa , bai dace ku saka ma ranku damuwa ba. Aliyu ya furta yana maida Gilashin sa tare da ɗaukar Keys yana fucewa daga falon shima. Mene wannan Yaron yake nufi? Khalil ya fara maganan a zuciya, ai shine yafi kamata ya shiga cikin damuwa amma kalli ko a jikin sa . Bayan shi ya ɗaukota shi ya saka Ma’eesha a wannan bakin cikin na yanzu . Girgiza kai Khalil yayi kamin Daddy ya dafa shi yana kiran sunan sa “Khalil”. Na’am Daddy” . Hummmm Numfasawa Daddy yayi kana yace “ Kayi mun Alƙawari zaka kula da Ma’eesha ko bayan ran mu ba zaka bari tayi kukan maraici ba , don Allah ka tsaya mata ka zama uwa uba dangi kar ka bari tayi kukan baƙin ciki. Kaine babba shiyasa na damƙa maka Amanarta…..Daddddyyyy ….ka bar wannan maganan zamu kula da Ma’eesha bai kamata ka shiga wata damuwa don ɗan wannan Abin da ya faru ba . A’a kaine nake so ka kula da ita. Ali har yanzu da ƙuruciya akan sa. Hummmm Jan numfashi Khalil yayi yana saukewa kana yace “ Daddy nayi maka Alƙawari inshallah ”.
**
A gaban mirror din ta taga Ma’eesha na sanye cikin rigar wanka idanun ta sun kumbura sosai alamu ya nuna kuka take yi , da taji motsin ta ne ta share hawayen ….Kallon mami Ma’eesha tayi tana murmushi kamin ta kira sunan ta “Mami”. Tana mai faɗaɗa fara’ar ta tare da ɓoye damuwarta . Ƙwaran idanun ta mami ta kalla tana jin wasu irin ƙwallah na sauko mata….ma’ee… Ma’eesha kiyi Haƙuri ki yafe ma Mami. Saurin riƙo hannun mami Ma’eesha tayi kana tace “ Bana son jin labari na Mami kuma ina so kisa a Ranki na manta da zancen bakyace Mami na ba , Zan cigaba da zama daku duka . Ki bar kuka kinji mami . Gyaɗa mata kai mami tayi tana danne kukan nata a zuciya . Nayi fatan Allah ya bani ke matsayin nice na haife ki na kawo ki duniya, halayyar ki me ƙyau ce tun kina ƙarama kina tsarkakkiyar zuciya . Taho muje Mami kimun wanka sai nayi barci . Murmushi Mami tayi tana cewa “ Ma’eesha na kin fara zama ƴan mata fa? Yau ina kallon ki zaki wanke mun jikin ki Ni nawa inda baiyi ba sai na gyara. Dariya duka suka saka tana kama Ma’eesha tare da nufar Toilet.
Duk Abun da suke yi A idon Jidder dake maƙale a jikin ƙofa talauci ne da bakin ciki ya rufe ta. Juyawa tayi tana fashewa da kuka tare da jin tsananin tsanar Ma’eesha yana ƙara kama zuciyar ta .
Tun wannan rana Ma’eesha Tasan Wacece ita a cikin gidan , haka take daure duk wani wulaƙanci daga Jidder ….sosai take jin dadin rayuwar ta a hakan don tana samun kulawa sosai , a ɓangare ɗaya ne take jin wani iri a duk lokacin da suke tare shine “Haidar , basa maganan minti ɗaya dashi sam….Ga masifar saka aiki duk idan ya dawo bata da Sauran Hutu . Ga shi da sassafe zai tashe ta ya tashi jidder training yana shirin maida ta namiji don wahalar training din nasa har farin ciki take yi idan ya koma. Sau tari a yanzu mamaki take yi wai shine ya tsince ta ,amma sam baya damuwa da ita a ganin ta. Da yake Ma’eesha irin yaran nan ne da ko ka ɓata masu baka fahimta saboda fara’ar su ,wannan yasa a babu mai mahimtar komai daga gareta. Abun da bata sani ba duk wani motsin ta Ali na kalla yasan ta fiye da yanda tasan kan ta. Ko me zata ɓoye shi a sarari yake kallon sa.
Shekaru na tafiya a yanzu Ma’eesha takai shakaru goma sha biyar wanda a matakin karatu take SS 1 .
Saturday (Asabar)
5:50am.
Ƙwance take tana sharan barcin ta , sosai ta nitsa cikin blanket don yau babu school sai takai 9:00am bata tashi ba ,haka Mami ba zata tashe ta ba . Kaman daga sama taji ana motsa ta tare da bubbuga saman gadon ta. Juyi ta sake yi tana miƙa tare da Cigaba da barcin ta tana cuno yar mitsulun bakin ta alaman tsiwa. Ƙurrrrr Ali haidar yayi mata yana bin ta da kallo dukan ta . Mamaki ne yake yi da yanda ta zama ta wani cika tamkar wacce ta haura shekarun ta. Tsayawa yayi yana kafe Ƙirjin ta da yakasa Ɗauke idanun sa da kallo…yaushe wannan Abin ya faru? Rufe idanun sa yayi yana tuno watanni sha shida kenan da barin sa gida , A ɗan wannan lokacin ne ta girma haka? . Bin kyaƙyƙyawar fuskar ta yayi da kallo a hankali ya tsinta kansa da ɗaura taffasan yana shafa kuncinta….Babu abun da yake tunowa a wannan lokacin sai Yarintar ta. Cikin Muryar barci yaji tana cewa “Mami ba zan tashi ba sai 9 . Ki tafi barci xanyi …..Cike da Arrogant voice ɗin sa taji Muryar Dodon nata tamkar daga Sama yana cewa “ Keeee tashi mu tafi morning exercise . Da sauri ta ware idanun ta tana ƙara mutsika su tare da tunanin kodai mafarki take yi . Kallon shi take yi tana ƙara Bin sa da kallo zuciyar ta na tunanin yaushe ya dawo? kana cike da rashin sani tace “wayyo Allah yasa ba gaskiya bane” . Manyan lulun idanun sa ya kafeta dasu , giran sa a haɗe A kuma Miskilance ya furta “ Zaki miƙe ko kuwa……………?”.
Last free page
To anan na kawo mana ƙarshen book 1 free page labari ne mai cike da abubuwa kuma a rikirkice har yanzu ba’a fara komai ba a cikin labarin . Ya al’amuran zasu kasance tsakanin ALI HAIDAR…KHALIL MA’EESHA JIDDERH, NASREEN , ina su Adam ,mu dawo ɓangaren su Areef, sannan mu dawo ɓangaren wannan attajirin da bai san Yes and No ba Shi ɗin waye? Ga su Hajiya Falmata da sauran matan sa . Jaruman suna cikin littafi na biyu inda zamu Cigaba a Paid group ….a yanzu masu buƙatar payment regular group ₦500…Vip group ₦1000 …
Also Read:Kurkukun kaddara Book 2 Hausa Novel Complete