Wayyo Nonona Hausa Novel

Hausa Novel

Barka da zuwa shafin littafan hausa novels, inda muka kawo muku littafin wayyo nonona hausa novel.

Wayyo Nonona Hausa Novel

Kallon Manyan idanun ta yayi yana an yin asa da kansa tare da kallon wayar idanun Amrah yana cewa Mene kika ce Cike da Sanyi don jikin ta ya ida mutuwa Ganin yanda tayi sharkaf a ruwan nan yau tasan Da tsumammun kaya zata Wuni har ta kwana hakan yasa ta yin lawaam takaicin Nurain ne yanzu take ji don idan da bata biyo sa ba Da hakan bai faru da ita ba a ganin ta Cikin Nuna ka dameni tace Nurry Dariya yayi mai fidda Sauti fararen hakoran sa na bayyana tare da Siririn Hushiryar sa A dakyau Suna mai dai Ya are maganan yana kallon ta tare da mata Murmushi Cike da Rashin Sanin makaman zancen nasa ta juyar da kan ta gyefe tana kallon Ababan Hawan dake Wucewa gefi don bata ara bi ta kansa ba bare tasan Mene yake yi Ruwan ne ya an fara aukewa wannan yasa Amrah murmushi tana leko da kanta ta Wajen Lange Rufin mai tsiren A hankali ta ago da idanun ta sama tana kallon yanda ruwan ke saukowa ta saman Falefalen Shagon wannan yasa ta cike da murmushi takai Hannun ta tana tarawa ruwan na zuba a tsakiyar taffan hannun ta Tsayawa yayi yana kallon ta tare da murmushi kamin Nurain shima yakai hannun sa yana Daura Hannun ta a saman taffan hannun shi yana tarawa a tare da nashi Waigowa tayi tana kallon sa a wannan karon dariya tayi masa tana cewa Nurry Ruwan ya kusa arewa muyi sauri muyi sauri fa kar ruwan ya dawo Amrah ce tayi maganan cikin Sauri tana janye Hannun ta daga nashi tare da Fitowa daga Rumfar tana nufar inda keken Nurain yake Bayan ta ya biyo yana Tahowa tare da Hawa yana dorata bisa cike da nishai suke tafiyar don a yanzu ruwan ya dauke sai dai an yayyafi Fuskokin su kawai zaka kallah ka tabbatar da suna jin dain kasancewar su a hakan

Tafiya ce ta mintuna Goma sha biyar ya kasu zuwa ga layin su Lokaci daya Faraar nata ya auke Kirjin ta taji yana buga mata da arfi tuno da Baba Zuwai da tayi Nurry Sauke ki anan Bakin sa yakai zuwa Saitin kunnen ta yana cewa Ina ne Gidan ku anan da zan sauke ki Nidai Aa ka sauke Ni idan ba Haka ba Zulai ta ganni a keken ka zata faa ma Baba Zuwai ne Kallon Gyefen sa yayi yana kallon Gidan Mahaifin sa kamin yace Ni kin ga gidan mu Amrah Kema muje ki nuna mun gidan ku Aa Nidai Ka sauke Ni anan zan maka kwatance daga nan Tsayawa da keken nasa yayi yana kai bakin sa dai dai Kunnen ta sauka to Cikin Sauri Amrah ta dure tana kallon sa tare da kama ugun ta tana cewa Nai na kwatanta maka Nurry Tana fain haka ta Zura da gudu tana barin sa anan tsaye Keee Kee Amrah Ina ma ta sauke shi lungun da zai kaita Gidan su tayi Saurin bi tana Dariya a ganin ta Wayo tayi masa Murmushi Nurain yayi yana fain Zan kama ki ai

Komawa yayi yana nufa Gidan su tare da tsallaka karamar Titin Gate Man ne ya kalli Nurain yana cewa Nurain ka dawo ruwa ya duke ka Wani irin kallo Nurain yayi masa yana kauda kai tare da kokarin shiga cikin gidan da keken sa Bude baki Mai Gadin yayi zai kara masa magana cike da jaraba Nurain yace Da ruwan ya buge Ni Magani zaka mun ne kome ne Ibeg just open the door Jikin Mai Gadin a sanyaye ya bude masa ofan gate din Nurain na shigewa daga ciki Mama Nanny ce take tsaye a baranda tun saukar Ruwan take jirar tahowar Nurain don yau tasan babu lafiya Ganin sa da tayi yasa ta Saurin tahowa a wannan yayyafin tana nufosa tare da kama shi tana Rungume shi jikin ta Wani iliya mai Bama ma flowers ruwa yana amsan keken nasa Ayya Sorry My Nurain gaskiya Ruwa n nan bai yauta mana ba Taho muje a sauya uniform din Ba tare da ya tanka mata ba yabi bayan ta suna shigewa daga ciki

angaren Amrah kuwa a zaure ta lae tana tsoron shiga cikin gidan tun daga Zauren take jin Hayagagan Baba Zuwai tana cewa To gidan Uban ta ta tsaya ko Uwan ta har karfe Uku Da kusan Rabi yau zanci Uban yarinyar nan Wallahi zata dawo ta same Ni Jikin Amrah ne ya hau Rawa daga tsayen da take idanun ta na fara Ambaliyar Ruwan Hawaye mai tattare da maraici da tsoro ga tashin hankali Kaman daga sama ne ta jiyo Muryar Zulai wacce bata san ta fito ba tana cewa Laa Baba Zuwai ga Shegiyar nan ta maale a zaure bata son ta shigo ne don kar ta kai Miki Tallahn yayi kwantai Lahaila kunji bain hali irin na yarinyar nan aiko yau sai naci Uban ki Baba Zuwai tayi maganan tana leko Zauren tare da kamo Amrah tana jawo ta zuwa cikin Tsakar gidan Kuka Amrah ta fara tana fain Don Allah Baba Zuwai kiyi Hauri wallahi Zani Tallahn Ruwan sama ne ya sa na fake a hanya Wani irin kallo Baba Zuwai ta watsa mata tana daga hannun ta tare da fara Wanke Fuskar Amrah da Mari jikake tasss har sau hudu Jummai ne ta mio mata Bulalan Inji tare da Cewa Aa kar ki Wahalar da hannun ki ga Bulalan da zai shiga jikin ta Amsan Bulalan Baba Zuwai tayi tana Wani irin dukan Amrah tamkar wacce take bugun baligar mace nan ko yarinya ce yar shekaru 7 Tun Amrah na kuka har sai da bakin ta ya mutu Sannan Baba Zuwai ta rabu da ita don tafi mintuna talatin tana dukan ta kaf cikin Gidan nan babu wanda ya fito Kwatar ta Numfasawa Baba Zuwai tayi tana cewa Dan uban ki kuma ki auki Tallahn Gyaan gashi can na ari Biyar da hamsin ne Naira daya ya ata sai naci Uban ki Wallahi A hankali Amrah ke jan jikin ta fuskar ta duk ya kumbura na tsaban Mari hannayen Ta duk sunyi shatin bulala suna zubda jini Jan jikin ta tayi tana aukar Farantin gyaan tare da aurawa a saman kan ta Idanun ta na ganin duhuwa Ga yunwa ga duka da tasha na mutuwa Nufar Hanyar kofar gidan tayi tana tangai kaman zata kife

Zaune yake a saman ayataccen Bed in shi afafun shi na akan jikin Mama Nanny wacce take ta matsa masa afan a hankali tana basa labarai masu dai tamkar yanda mahaifiyar sa ke masa Kallon Nurain nayi Da yake sanye cikin Kananun kaya Rigar jikin sa Tshirt Blue sai Wandon jikin sa Farin jeans mai an yalwa bai takura shi ba Sunan Labari Mama Nanny ke basa Amma sam baya ta kan ta idanun sa na akan laptop in sa dayake playing Game Saurin Kallon Nanny yayi yana kiran sunan ta da Halima arfe nawa yanzu aga idanun ta tayi tana kallon Agogon dake maale a bangon Bedroom din nasa kana tace arfe Huu da rabi Ohhhh God Saurin Miewa yayi yana Zura Room silipers din sa tare da cewa Ina zuwa Ficewa yayi daga Dakin yana nufar Wajen Farfajiyar gidaninda ya hango mai Gadi can zaune a Kujeran sa Nufar inda yake yayi yayin da mai gadin yayi Saurin muskutawa yana Miewa tsaye tare da cewa Barka da fitowa Nurain Bude mun kofa ina kujeran nan naka Kasa mun a waje zan zauna yau Cike da dan gajeren mamakin yau Shine zai zauna a waje Yaron rainon turawa sam baya son hayaniya kullum yana daki yau shine zai zauna a waje Murmushi yayi yana cewa Ohk sir Yanda suke basa Girma ka rantse babba ne nan kuwa yaro ne wanda a wannan lokacin baifi Shekaru 16 ba Jiki na Rawa Gate man ya aje masa Robber chair tare da ja gyefe Nurain na zama Mintinan sa baifi Uku da zama ba ya hango Ta dauke da farantin gyaa a bisa tsakiyar kan ta Idanun ta na kallon asa Jan jikin ta kawai take yi dagani kasan da Akwai Abin dake damunta Idanun sa ya kafe a kanta na yan Daiu har ta zo ta gaban sa zata Wuce bata Gan shi ba don gaban ta kawai take kallo Motsa Laansa yayi yana kiran Sunan ta yanda zata ji shi Amrah
A hankali ta ago da idanun ta tana sauke su bisa Fuskar sa wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyar ta nan take ta Wangale masa baki tana dariya tare da Cewa Kaine

LONDON
JENNYLYN_MARCADO INTERNATIONAL SCHOOL
SS 2 class Hayaniyar aliban gaba aya kake ji tun daga Upstairs din har asan ajijuwan Gaba daya yaran Class din basu wuce 12 ba mata da mazan su Malaman nasu da yawa sun shigo akan suyi shiru Amma kuma sam hakan ya gagara don su a ganin yanzu seniors ne daga Wannan Term Din zasu shiga SS3 tsiiitt naji Ajin yayi kaman ruwa ya cinye su Wannan yasa Ni saurin juyawa ina maida idanuna kan kofar shigowa ajin Wani cute Handsome boy na gani Sanye cikin kayan Sport wear na Makarantar Fari ne Tassss dogo suman kanshi yayi Askin su ta zamani gaba an tara gashi baya an kankara Gyefen Kunnen sa Dan kunni manne na gani Yayin da Fuskar sa ke cikin tabarau irin manyan nan amma fari ne Ko baa Faa maka ba an Wani Attajirin ne sannan kuma an gayu mara ji na arshe Mamaki ne ya kamani ganin Yanda Kaf student din suka tashi daga Seat din su suna furta Good morning Zaid Takowa yayi yana shigowa kaman wani malamin su yana fain Morning Friends mu zauna ko Yayi maganan Fuskar sa dauke da Faraa wanda da gani kasan ba maabocin yin Faraar bane a yau yana cikin Wani farin cikin ne da dole sai ya bayyana Zama yayi a cikin Gang din Abokan nan sa su biyar yayin da daya daga cikin su ke tambayar sa Zaid Wannan Faraar fa meke faruwa ne Kallon Abokin nasa Zaid yayi yana cewa Abokina Nurain zai Dawo America da zama a bakin Momyn sa naji nan da 2 mount zai taho America

To Kai ai anan London kake shi kuma America zaije Meye Amfanin Farin cikin Murmushi Zaid yayi yana cewa Transferring komai nawa zan yi na koma America dama Daddy na acan yake Mom ne ke nan Yana dawowa zan koma can muyi SS3 a can the same school zamuyi dama primary tare muka yi Secondary ne yace shifa Nigeria yake so kaga yanzu haka the next 2 mount yana America

Wayyo Nonona Hausa Novel Download

Novel Title Wayyo nonona hausa novel
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 410kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Written by Zamgist Writers
Tags wayyo nonona hausa novel, Wayyo nonona dadi, Wayyo yaya nonona complete, Wayyo yaya kayi hakuri zafi, Wayyo Nonona uncle
Published date 25 – 08– 2023

 

Karanta: Karshen Wahala Hausa Novel Complete

DOWNLOAD NOVEL

Littafin: Man of The World Hausa Novel Book 2

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*