Gyaran Nono A Sati Daya

Muna yima mai karatu barka da isowa wannan shafin namu inda muka tanadar muku da ingantaccen bayani akan Gyaran Nono A Sati Daya.

Da farko inason mata musan cewa wajibine ga remu mata mu sani cewa shifa Nono wata babbar kadarace da Allah madaukakin sarki yayi mana wadda take banban tamu da maza, kuma ya sanya sha’awar maza aciki.

Don haka yazama dole mu Kiyaye wannan ni’imar, sannan kuma mutashi tsaye gurin gyaran nono, wannan ya zama dole ga kowace mace (budurwa, bazawara ko matar aure).

So tari zakiga wata dazarar tayi aure an samu haihuwa 1 zuwa 2 sai kiga ta koma tamkar silifas.

Ki sani cewa zaki iyagyara nononki acikin sati daya ko kuma kasa da haka kuma yadawo tsayayye kamar budurwa.

Idan kin kasance cikin masu dan karamin nonuwa ko wadda nononta ya zube to babu makawa kinzo wajanda za’a share miki hawayenki domin kema kishigo cikin jerin “yan mata.

Batare da bata lokaci ba zamu tsunduma acikin bayani akan Gyaran nono a sati daya.

Gyaran Nono A Sati Daya

Acikin wannan shafin, mun kawo maku hanyoyi 5 da zaku dawo da martabar nonuwanku wato Gyaran nono a sati daya, zaki iya zaban hanya mafi maslaha a wajanki kuma kiyi kamar yadda aka bayyana.

1. Hanya Ta Daya

A nemi kankana

Abarba

Gwanda.

Ayanka kanana a zuba aruwan zafi idan kankanar tayi laushi sai a shanye.

Idan kuma shayarwa kikeyi, saiki saka man hulba cokali biyu sannan asaka zuma cokali daya.

Idan nonon ya zube ne, sai a dafa hulba da yansun, idan ya dafu sai atace, asha, sannan a kwaba hulbar da kwan salwa arika shafawa.

2. Hanya Ta 2

Shima wanna wani hadine da akeyi don gyaran nono, kuma yanada muhimmanci sosai , yanda akeyi shine za’a Samu kindirmo, tumatur, lemun tsami, garin kubewa, dakuma garin sallaja.

Sai a hadasu guri daya, a kwabasu sai ki rika shafe nonuwan dashi, bayan kimanin 1hr ko minti 30 sai ki wanke sannan kuma ki shafe nonon da man ridi.

3. hanya ta 3

Za samu Farar shinkafa, Garin Alkama, Garin habbatus sauda, Garin Ayaba (Plantain), Gyada mai malfa (mai zabo), da Aya Madarar gari, sannan zuma.

Za’a bare bayan plantain sai a yanka shi, a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai a hada aya da gyadar a markada a tace ruwan.

Bayan nan, sai a dora kan wuta a zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hade a guri daya, sai kuma ki zuba garin madara da zuma, ki dama ya yi kauri sosai, sai ki rika sha safe da yamma.

Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, idan kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, kirika sakawa.

Idan Kikayi haka na tsawon sati 2, da yardar ALLAH ni’imarki zata dawo fiye da yadda kike a baya.

Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin da aka ambata to kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau 2 a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan.

4. Hanya ta 4

Idan nonuwanki kanana ne kuma kina so suyi manya kamar yadda kikeso, kina iya yin wannan hadi domin samun lafiyar nononki.

Zaki nemi cukwul, garin alkama, aya, nonon saniya, madara da garin hulba.

Cukwul wanda yawansa zai Kai guda uku sai ki samu garin alkama gwangwanin 1, sannan aya itama gwangwani 1, sai ki daka su, zasu zama gari ki tankade ki samu nonon saniya.

Idan bakyashan nonon saniya, sai ki samu madara ki zuba wannan garin kamar cokali uku ki dama kina sha kullum Sau daya, sannan ki lura lokacin da zakiyi wanka ki tafasa ruwa da garin hulba a ciki ki bari yayi sanyi sai ki wanke nonon da shi sannan kiyi wankan.

5. Hanya Ta Karshe

Wanna wani hadine da akeyi don gyaran nono a sati daya, musamman ga budurwa, sannan shi wanna hadi kowace mace indai tana da bukata zata iya amfani dashi saboda tasirinsa.

Yanda akeyin wannan hadi shine:

A samu garin waken soya, garin alkama, garin zogale, garin bawon lemun Zaki

Karanta:ÂHotunan Yadda ake Kwanciya da Mace

Anan muka kawo karshen wannan bayani akan gyaran nono a sati daya. Idan kina da tambaya kokuma wata shawara, to seki ajiye comment a kasa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*