Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin bintu diyar bayi ce book 2 complete wanda khadijah sani ta rubuta takuma wallafah.
Bintu diyar bayi ce book 2 complete
Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 8
Sidiya ce…..
Shiryayyan d’aki mai had’e da 6and’aki aka aje su Ladiyo, su Bintu kuwa d’aya daga cikin d’akunan Goggon nan a matsayin ta na uwar gida aka sauke su kan a gama wankan amarya a mik’a ta ga na ta 6angaran.
Su na shiga masaukin na su ba da jimawa ba, wata baiwa ta sake dawowa d’auke da kaya, gaban Bintu wacce ke zaune bisa gado har lokacin ba ta bud’e fuskarta ba baiwa ta zu6e, ta na mai aje kayan gaban ta, ta ce ‘’ an gaida Gimbiya Fatima, wagga kaya tsaraba ne da ga
Goggo nan, ta ce a shedawa Gimbiya Fatima ta sanya su yayinda za ta hito wajan wankan amarya nan ba da jimawa ba’’
‘’Gimbiya Fatima ta amsa, ta na godiya’’
Cewar Gwaggo Munari. Bayan fitar baiwar Gwaggo Munari ta yaye alkyabbar Bintu, sai ga ta ta yi wuri wuri da ido. ‘’Gimbiya yanzun ga ba lokacin tuntuntuni ba ne, kin dai san dalilin da ya sa ki wanga Masarauta da kuma a gurbin wacce ki ka zo, gwara dai ki sake shawara ki nutsu in har ba so ki ke ki rasa ran ki sa’annan ki haddasa yaki da gaba wanda ka iya halaka ta mu Masarauta gaba d’aya’’
Fad’in Gwaggo Munari cikin gazawa da halayyar Bintu dan kuwa idan ba ta yi da gaske ba ko shakka babu asirin su mai
tonuwa ne. A sanyaye Bintu ta ce‘’ina tuba….’’ ‘’ba tuban ki mu ke buk’ata ba!’’
Gwaggo Munari ta katse Bintu, kana ta k’ara da ‘’ Aikin ki mu ke buk’ata Gimbiya!
Wanda za ki fara yanzu ta hanyar zama Gimbiya ba d’iyar bayi ba. Allah ya mi ki zubi irin na jinin mulki, kowa ya gan ki ya san hakan nan Allah ya yo ki, ba ki gada ba amma Allah ya baki su a halittar ki, Dan haka tak’ama da isa shi na ke so daga gare ki, ki saka a ran ki wannan dama ne da Allah ya baki dan jin dad’in rayuwa da kuma taimako ga Masarautar mu, idan asirin mu ya tonu gaba d’aya farin cik’in masarautar mu ne zai koma ga zubar jini, ina fatan kin fahimce ni?’’
Bintu ta gyad’a kai.
Kana Gwaggo Munari ta dafa kafad’ar Bintu ta ce ‘’madallah da d’iya ta gari. Sai ki yi shiri yanzu su Ladiyo za su
zo su had’a mi ki ruwan wanka. Hakuri za ki yi na san kin saba yiwa kan ki komai amma daga yau komai yi mi ki za ake yi, ki jure Bintu wata rana sai alkhairi’’ Bintu ta dad’a jinjina kai. Ana hakan kuwa su ka ji an sake turo
kofa an shigo.
Maimakon Ladiyo da Gwaggo Munari ta ce, Lantana ce baiwar da Yarima Nuhu ya za6a ta musammam domin kular masa da al’amran Bintu ta shigo ta zube gaban su. Gwaggo Munari na mai duban ta tace ‘’Lantana gide ke ce mai shirya ruwan wankan ne? yo to ina
sauran? Kar dai sun tsaya kallan kauye mu ka biya ku fa sai mu makara!’’
Lantana waccen ita dama da ka gan ta ka ga zubin munafunci, dan ko magana ka ke da ita haka za ka ga ta na sinsin da
idanu sam ba ta bari a ga kwayar idanun ta. Ta kada baki ta ce‘’ai ga su nan tafe, sauri na yo dama na shirya ruwan wankankada a makara’’ Jin haka Gwaggo Munari na mai mata nuni da bayan gidan da ke cikin d’akin ta ce ‘’yauwa madalla da ke, maza je ki ga bayan gidan can shirya mata gide’’ Sim sim ta shige bayan gida. Sai da ta fara taran ruwa sannan ta shiga had’a ruwan da turaruka iri iri kamar yanda su ka saba
had’a ruwan wankan Gimbiyoyi. Ko da ta zo kan turaren karshe, sai ta faki idanun Gwaggo Munari ta tabbatar hankalin
ta na kan su Ladiyo da shigowar su ke nan, ta na mu su bayanin yanda ta ke so su kasance wajan taro. Sannan ta jawo
kofar bayi ta rufe.
Gefan zanin ta ta kwance, ta dauko wani
kullin magani, cikin sauri da azanci ta bud’e maganin ta na mai zazzage shi cikin ruwan wankan Bintu. Tuni wani irin bakin hayaki mai wari ya taso daga ruwan yayi sama, ita kan ta Lantana sai da ja baya ta na mai toshe hancin ta cikin tsoran kada fa su Bintu su ji duk da dai Yarima Nuhu ya tabbatar mata babu wanda zai ji warin bayan ita da ta zuba. Sai da ruwan ya dena kumfa da hayaki sannan ta mayar da sauran kullin maganin cikin zanin ta ta kulle, ta fito hankali kwance kamar ba ta aikata komai ba.
Bintu Diyar Bayi Ce Book 2 | Hausa Novel Complete |
Uploaded by | Zamgist.com.ng |
File Size | 863kb |
Hausa Novels WhatsApp Group | Click here |
Telegram Group | Click here |
Novel Price | Free |
Novel Author | Khadijah Sani |
File format | Txt |
Published date | 13 – 04– 2023 |
WASU LITTAFAN DAZAKU SO KU KARANTA
Yar Sadaka Complete Hausa Novel Download
Bintu Diyar Bayi Ce (Book 4 Complete)
Nida Dalibata Hausa Novel Complete
Man of The World Hausa Novel Book 2
Abban Sojoji Page 100 Hausa Novel
Abban Sojoji Chapter 65 Book 2
Leave a Reply