Man of The World Hausa Novel Book 2

Hausa novel by zamgist.com.ng

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin Man of the world Hausa novel BOOK 2.

Tags: man of the world hausa novel book 2,man of the world hausa novels,man of the world hausa novel download,man of the world hausa novel book,man of the world part 2 hausa novel,man of the world namijin duniya hausa novel,man of the world hausa novel,man of the world hausa novel complete,the man of the world hausa novel,man of the world hausa novel wattpad,Man of the world Hausa novel.

Man of the world Hausa novel BOOK 2

Yana ɗaura haɗaɗen rolex a hannunsa kamar kullum ba wanda ya tarar a falo se Meemah datasha uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau abinka da miskilin mutum ya fiske kamar besan da zaman wata halittaba yayi hanyar waje cikin ƙissa ta miƙe haɗe da cewa”Ya Abdallah kaifa nake jira mutafi su Mum duk sun tafi airport ɗin”.

ba tare dayabi takanta ba ya cigaba da tafiyarsa abunsa ganin be kulata ba yasata ta fita cikin sauri tabi bayansa lokacin data fita har security ɗinsa sun buɗemasa sabuwar G-box ɗinsa yana niyyar shiga cikin sauri ta ƙarasa gurinsa tana niyyar shiga  kallo daya jefeta dashi ne yasa ta fasa shiga ya shige abunsa har Sani driver ya tada motar yaji Man of the world cikin husky voice ɗinsa yace”tashiga motar security mutafi”.
“okay Sir”.
nanya fita bejimaba ya dawo ya tada mota suka fara tafiya .

Jingina yayi da jikin kujera ya rasa meke damunsa akanta daya rife idanunsa ita yake gani wani sashi na zuciyarsa se tsunkuninsa yake kan yaje gurin aiki koze ganta wani murmushi ne ya suɓucemasa ya rasa na menene a fili yace “wai meke damuna ne narasa dalilin dayasa dana rife ido ba wadda nike gani se wannan yarinyar anyako ba mayya bace”.

tsaki yayi sakamakon duk yanda yaso kauda tinaninta zuciyarsa  ta hansa har suka isa airport yanata tsaki bemasan sun iso ba sakamakon duniyar tinani daya lula  suna isa cikin nutsuwa Sani driver yace”Sir mun iso”.
firgigit ya dawo daga duniyar tinanin daya shiga yace”ok “.

yafita yazagaya ya buɗemasa a hankali ya zuro haɗaɗɗen takalminsa waje gabaki ɗaya idanun mutanen gurin na kansa kowa so yake yaga wanene ze fito daga motar sake zuro ɗaya ƙafar yayi ya fita baƙaramun ɗaukar hankalin matan dake gurin yayiba yafara cikin takun zaratan maza ko takan Meemah bebiba yana shiga  cikin gurin  ya tadda Rahma rungume jikin Granny tana ganinshi ta saki Granny ta ruga da gudu tayi kansa shima a nashi ɓangaren buɗemasa hannuwa yayi alamar ta taho garesa hakance takasance kuwa tana zuwa ta rungumesa cikin murna ƙara rungumeta yayi tsam a ƙirjinsa yanajin wata irin ƙaunar ƙanwartasa na ƙara shigarsa sun daɗe a haka kafin su saki juna yakama hannunta murmushi Ammi tayi tare da cewa”ja’irar yarinyar badai ni kikaiwa haka ba kan wannan sangamin zakizo ki sameni ina zaune a shararren gurina nima bazan kulaki ba kuma kya koma gurin sangamin kifara kwana badai ɓangarena ba kije can duk abinda ze cinyeki ya cinyeki banda asara tunda dai ba ɗana ya cinye ba”.

dariya gabaki ɗaya gurin sukayi hadda Mommy dake ta faman yaƙe Abbih yace” yau kuma keda ƙawar taki ake jin kanku kuma”.

“eyi aiwai ita me ɗan uwa tana ganinshi ta sakeni tayi gurinsa”.
dariya Rahma tayi tace”tuba nike ƙawata  nike Ammina”.

taƙarasa faɗa tana me kama kunnenta alamun bada haƙuri nan suka ɗunguma suka shiga motocinsu seda zasu shiga mota Rahama ta lura da Meemah nan taita farinciki suka shiga mota ɗaya suka nufi gida.

Tsaye suke a bakin titi suna jiran me napep Inteesar tace”Aunty sekuma yaushe zaki dawo”.
ɗaga kai sama Badi’ah tayi alamun tinani sannan tace”jibi zan taho sekuma Allah yakaimu biki ya tashi”.
“kai Aunty dan Allah kizo da wuri”.
“ki kwantar da hankalinki insha Allahu da wuri zanzo”.
“yauwa Auntyna”.

tunda suka fara magana Jameelah ke sakin wani shu’umin murmushi wanda ita kaɗai tasan ma’anarsa karaf sukayi iso huɗu da Khadijah dake ƙoƙarin tsaida me napep harara suka sakarma juna  kwafa Khadijah tayi nan suka yi sallama da Aunty Badi’ah tashiga napep sukuma suka juya saurin yin gaba Khadijah tayi tabarsu binta sukayi da kallo gabaki ɗayansu suka cigaba da tafiyarsu har suka isa gida.

Suna shiga gida Jameelah taƙara narkewa tayi kalar tausayi alamu batason binsu saboda aga laifin Khadija sosai ran Inteesar yakai ƙololuwar ɓaci ganin yadda Khadijah keta ware Jameelah tana ɗari-ɗari cikin muryar kalar tausayi tace”Aunty Inteesar se anjuma”.
“kitaho mutafi man”.
“a’ah Aunty banason ina hana ƴar uwata sakewa naga Khadijah kamar batajin daɗi”.
“rabu da ita sakarai ce batasan nata ba zanji da ita”.
“dan Allah Aunty karkiyimata komai domin banason ranta yana ɓaci  ata dalilina”.
taƙarasa faɗa tana mai shigewa ɗakinsu sosai tabasu tausayi tana shiga ɗaki taɗan leƙo taga yadda duk ransu yaɓaci dariya tayi tare da cewa”gaskiya Ummah naga plan ɗinnan naki yana tafiya yadda yakamata”.
“nidai abinda nike so dake kiƙara shigewa jikinsu harki samo lambarsa daga nan aiki yaƙare”.
“ai anjumannan zanje insaci numbersa a wayarta zasu gane kurensu dangin matsiyata kawai”.
“yauwa tawan”.
nan sukaita hirarsu ta tsara plan ɗin da zasu mallakeshi.

“Kewai Khadijah wacce irin mahaukaciya ce ya yarinyar nan tana binmu sauda ƙafa amma ke kina nunamata rashin ƙauna ƙiri-ƙiri Ummih wallahi bakiga yadda yarinyar tabamu tausayi ba saboda yarinyar ta natsu taita nunawa Khadija soyayya amma tayita wulaƙantata”.
“wallah Ummih ba tuban Allah da Annabi tayi ba ɗazu ina kallonta tana harar Aunty  yazanyi in nike inso wanda kullum ƙoƙarinsa yaga bayana nikuma ina ƙara shigemasa kamar wadda batasan ciwon kanta ba “.
yin kanta Inteesar tayi a harzuƙe zata doketa saurin ɓoyewa bayan Ummih  tayi tana huci tace”ni kike faɗama  bansan ciwon kaina ba Khadijah saboda kin rainani to wallahi senayi maganinki matsawar baki fita daka harkata ba mara mutunci kawai”.
“wallahi bazan fita daga harkarki ba Aunty ina na fita daga harkarki wazan kula”.
dakatar dasu Ummih tayi ta hanyar ɗaga musu hannu tace”ke Khadijah banason rashin kunya meye dan ƴar uwarku tabiku ai duk arziƙine wallahi idan baki dena wannan halin naki ba watarana sena karyaki sakarai kawai kuma naƙara ganinkinmata wani abu zakiga yadda zanmiki wallahi”.
nan Ummih tayita yimusu faɗa ana cikin haka wayar Inteesar tayi ƙara dubawa tayi taga sunan Pure one na yawo akan screen ɗin wayar murmushi tayi tare da ɗagawa tayi tare da cewa” salamu Alaikum ina yini”.
daga ɗaya ɓangaren ko amsa gaisuwarta beyiba kamar wani mejin haushinta yace”!!!!!!!!!!!!!

*MAN OF THE WORLD*
Sighn and update by Real eeshow

_Dan Allah sisters mukasance masu riƙe amanar juna dan Allah idan kinsan baki biyaba karki karantamun idan kuma kinbiya dan Allah karki fitarmun.

Man of the world hausa novel book 2

3️7️ 3️8️

        “ki fito muna jiranki a ƙofar gidanku”.
ya gimtse wayarsa ba tare dayaji tabakinta beyiba shiru tayi tashi ga duniyar tinanj taji muryar Ummih tace”lafiya kike tinani mamana”.
ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙaƙalo murmushin yaƙe tace”bakomai Ummih ba tinani nake ba”.
“kidena saka abubuwa a ranki dukkan tsanani yana tare da sauƙi kuma haƙuri baya taɓa faɗuwa ƙasa banza komai kikaga yafaru da bawa to da sanin Allah kimiƙawa me duka komai dake damunki insha Allah bazaku tama wofanta ba kedai a kullum ina muku nasiha daku riƙe gaskiyarku da amsar ƙaddararku hannu bibiyu”.
“insha Allah Ummih na”.
Ummih zatayi magana kenan Khadijah tace”Ummih wai Abbah har yanzu  beyimiki zancen kayan ɗakin Aunty bane naga har yau ba’ah saimata ko tsinke ba gaskiya Abbah baya kyautawa da bikin Jameelah akeyi da yanzu yashiga ya fita yayimata”.
“kewai wacce irin me kunnen ƙashi ce ne da bakyajin magana ne iyi meye naki akan kayan ɗakin ko dole se anyi kayan ɗaki ake aure”.
ɗage labulen ɗakin Abbah yayi har yana huci yace”yayi munafuka to yaudai Allah yakamaki wato idan nafita tara ƴaƴanki kike kina ƙona namana to banyafe ba suɗin da kike kaiwa ƙarata me suka isa suyimun bakuma zanyi ko zare ba inkinyi zuciya kiyimata naga abinda yazama dole”.

Miƙewa Imteesar tayi tana gyara zaman hijab ɗinta  dakamata tsawa Abbah yayi haɗe da cewa”kee kuma ina zaki”.
jiki na rawa tace”shine yazo yana  waje”.
washe baki Abbah yayi yace”toh toh shine kuma kika tsaya san iyawa kika shanyashi”.
“ba shanyashi nayi ba Abbah yanzu  ya kirani”.
“toh sarkin tsari kota ina aka ɓullomiki sekinsan yadda zaki kare kanki”.
muryar Uwar Gwarama sukaji tace”kaima dai Malam aikasan an tsotsa a mama yaza’ayi barewa tayi gudu ɗiyarta tayi rarrafe ai halin uwarta halinta har son nuna ita ta Allah ce fir’auna a zuciya duk ita ta biyo”
“saura kuma inya baki kuɗi ki ɓoye kiga yadda zanyi dake”.
“gwara dai ka gayamata domin tana iya maƙalewa ta kawowa uwarta”.
jiki a sanyaye ta fice sukaci ka haɗu da Jameelah na fitowa daka ɗakinsu tana ganin Inteesar ta wani wage baki tace”Aunty dama yanzu nake shirin zuwa gurinki”.
“Allah ko “.
“eyi wallahi inason intura whatsapp ne nawa yayi expired”.
“aiko fita zanyi Sis sede  nabaki wayar idan kingama turawa ki ajemun”.
wani farin cikine ya mamaye zuciyar Jameelah a zuciyarta tace”yau zan samu cikar burina daka yau keda Zaid har abada shegiya tsinanniya sarkin rashin wayo”.
a fili kuma murmushi tayi tace”Yah Zaid ɗinne yazo ne Aunty naga irin wannan wankan haka ai wannan sekisa ya kifa Aunty”.
miƙamata wayar tayi haɗe da  yin  murmushi tace”kudai bakwa rabo da shiririta  ingoni sena dawo”.
taƙarasa zancenta tana ciremata password ta miƙamata ansa tayi tare da sakin wani shu’umin murmushi tace”adawo lafiya Auntyna maganin kukana”.
murmushi kawai tayi ta wuce abinta tanajin wata irin ƙaunar ƙanwarta na shigarta.

Tana fita ta hangeshi  tsaye shida  babban amininsa  Muhseen sun haɗe cikin ƙananun kaya sunyi matuƙar amsar jikinsu sunyi sharr dasu cikin nutsuwa take tafiya kamar wadda take tausayin ƙasa   tsaki Zaid yayi  ya shige cikin motarsa  cikin masifa yace”baza  ka taho mutafi koko haifarmu tayi da seta gama isarta zata fito kamar wata uwarmu nina ƙiji jinin baƙin wulaƙanci ko wani abun mukazo nema gurinta da zata rainamana hankali sannan tabamu”.
“anya ko Zaid hankalinka ɗaya Inteenka cefa”.
a zafafe yace” koma wacece  da Allah Malam ka taho mutafi inbazaka shigoba ni zan wuce”.
“to Invitation ɗinda zamu batafa”.
“nafasa ko dolene satayi gayyar  kashigo mutafi”.
ganin Muhseen bashi da niyyar shiga ne yasa yiwa motar key ya tafi a guje tare da bulamusu uwar ƙura  mamakine yakama Muhseen a zuciyarsa yace “anya ba wani abun Inteesar tayiwa Zaid ba kuwa domin naga kwana biyunnan koson inyimasa maganarta bayayi wanda da har so yake ayimasa zancenta gaskiya da abinda yake faruwa bara inji tabakinta koma meke akwai zanji”.
jiki a sanyaye taƙaraso gurin  nunawa tayi kamar bataji duk abinda ke faruwa ba a tsakaninsu ba cikin girmamawa tace”ina yini Yah Muhseen”.
sakarmata murmushi yayi haɗe da cewa”amarya  bakya laifi kokin kashe ɗan masu gida lafiya ƙlau”.
murmushin yaƙe kawai tayimasa haɗe da cewa”hmm haka dai kace Yah Muhseen amma ni ai bankai ba”.
“harma kin wuce domin ninasan halin kayana  mekika yiwa abokinane naga  yaƙi tsayawa”.
“hmm wallahi ba abinda nayimasa “.
“tino dai domin hakanan baze riƙa jin haushinki ba daliliba”.
shiru tayi secan tace”wallahi nidai a iya sanina ba abinda nayimasa”.
“ok zan tambayeshi inji dama zuwa mukayi mu tambayeki events nawa zaki sekuma iv ɗin ɗaurin aure da zamu baki  yaƙi tsayawa “.
baƙaramun sanyi jikinta yayiba sakamakon jin abubuwan dataji Zaid na faɗa akanta ta girgiza kai haɗe da cewa”ba abinda zanyi Yah Muhseen “.
waro ido Muhseen yayi hakan dayayi seda yabawa Inteesar dariya yakama baki yace”haba ƙanwata baki isa ba  kinko san yadda muka daɗe muna jiran wannan ranar ta bikin Zaid kuwa da zakice haka “.
“a’ah wannan dole mutumina yariƙa jin haushinki walkahi ace biki kamar na Zaid ba’ayi komai ba sekace bikin bazawara to bazeyiwu ba dole ki faɗi abunda za’ayi inke bazakiyi ba mu zamu haɗa dakanmu”.
“toh nidai Yah Muhseen walimah kawai zanyi sauran kuma nabarmaka komai a hannunka duk abinda kace haka za’ai”.
“ok yanzu kika yi magana  zan tsara komai insha Allahu”.
“tom “.
“yauwa gobe zan dawo tunda kinga jibi  za’ah fara biki gobe zamuzo mu kawomuku kuɗin ƙunshi koma dai meke akwai zamuyi waya ina  Tweeny ɗin taki”.
murmushi tayi tace”tana gida inkirata ne”.
“a’ah kibarta nakirata a waya muji schedule ɗin ita data tsara”.
“toh “.
nan yayimata sallama yana mamakin canzawar aminin nasa lokaci ɗaya shiga gida tayi shikuma  ya wuce.

Zaune yake akan haɗaɗiyar kujera system nakan cinyarsa yana operating ɗinta tashigo ɗakin ko ba’ah faɗaba yasan ba wanda ze shigo masa kai tsaye se Sweetheart ɗinsa da gudu taƙaraso inda yike tare da yin hugging ɗinsa ta baya tace”I miss you Ya Abdallah”.
sauke system ɗin dake kan cinyarsa yayi tare da cewa”miss you too dear ina zaki kika sha wannan wankan haka kamar wadda zata gasar kyau”.
yaƙarasa faɗa yana jan kumatunta kyalkyalewa tayi da dariya tare da cewa”shan ice cream zaka kaimu sannam inaso inyo shopping ɗin wasu  abubuwa”.
murmushin daya ƙara yimasa kyau yayi hakan yasa Meemah dake tsaye tana kallonsu ƙara narkewa a duniyar ƙaunarshi yace”menene wasu abubuwa kiyi list kibada su Abubakar su siyomiki man Sweetheart kinga kingaji da yawa ki huta”.
cikin shagwaɓa tace”Allah Allah ni bangaji ba ka shirya ka kaimu yaushe rabona da ƙasar please Bro”.
jamata kumatu yayi tare da cewa”toh shagwaɓatuna bara na shirya muje kizauna a falo  kijirani”.
yaƙarasa zancensa tare da kallon bakin ƙofa Meemah yagani tsaye ta shagala da kallonsa ɗaure fuska yayi kamar be taɓa dariya ba tsallen murna Rahma tayi tare  da cewa”seka fito Bro dan Allah fito da wuri domin so nike mu  zagaye garin Abuja”.
“toh “.
nanta  miƙe cikin farinciki suna haɗa ido da Meemah yajefeta da wani kallo tafice ba tare data shiryaba.

Cikin  wata dakakkiyar  gizna  yafito  brown se ɗaukar ido take baƙaramun amsar jikinsa shadda tayi ba abinka da cikakken namiji me jini a jika daɗan sassarfa  yake sakkowa daga  stair zaune yasamu su Mummy suna hira Rahma naganin sakkowarsa ta miƙe zumbur tare da cewa”tashi mutafi Sis ga Yayah nan”.
mumrmushi Mummy tayi tare da cewa”toh ƴar gidan Yayah se tafiya ko to adawo lfy”.
“Allah yasa Mum”.
cewar Meemah murmushin gefan baki yayi tare da cewa”Mum semun dawo”.
“toh adawo lfy kardai ayi dare”.
“insha Allah “.
yafaɗa yana tafiya nansuka tafi.

Tsaye suke a gurin jeweleries suna dudubawa juyamusu baya yayi yana waya yana katse wayar ya juya yana bin  jeweleries ɗin gurin da ido sexy eyes ɗinsa ne ya sauka kan!!!!!!!

*Wannan littafin na kuɗine inbaki biyaba dan Allah karki karantamun inkuma kinbiya dan Allah karki fitarmun mu riƙe amanar juna Sighn and udate by Real eeshow MAN OF THE WORLD*

Votes and comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger  kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki  ta wannan number 08108362334.*_

 Man of the world hausa novel book 2

3️⃣9️⃣➡️4️⃣0️⃣

         Wasu diamond necklace se ɗaukar ido suke guda biyu iri ɗaya baƙarmun kyau suka yimasa ba hakan yasashi kai hannu ya ɗakkosu jin muryar Rahmah yayi tace”wow Yayah ya akai idanunka ya hangomaka wannan haɗaɗen necklace ɗin ba tare damu mungashi ba”.
“baku da ido “.
“hhh kaji Yayah bani dan Allah”.
satar kallon Meemah yayi ta gefan ido yaga yadda ta tsaresu  da ido tanata zabga smiling murmushin gefan baki yayi tare da cewa”gashi”.
ansa tayi tare da cewa”wannan ta hannunka fa “.
yana lumshe sexy eyes ɗinsa kyakyawar fuskarta  yagani lokacin daya kamata tana ma hotonsa kiss sake tinowa yayi da lallausan lips ɗinta daya yiwa kiss batare daya sani ba murmushi ya suɓucemasa bazato  yana duniyar tinani yaji karaɗin muryar Rahama tace”gaskiyane Yayah niko zanso inga Auntyntinnan tawa me sa’ah haka  datayi wuff da zuciyar ɗan uwana lokaci ɗaya haka naga  ka mutu akanta haka amma ko wacece me sa’ah ce zanso ganinta dan nasan ɗan uwana bazeyi zaɓen tumun dare ba nifa harna ƙagu danaga photonta dannasan ba baya bace Yayah meye sunanta “.
murmushin dabe shirya yinsa bane ya suɓucemasa  ya shafa yalwataccen sajensa tare da satar kallon Meemah daketa faman doka murmushi a tinaninta  ita yake nufi murmushin gefan baki yayi haɗe da cewa”ina ruwanki zata bayyana nanda lokaci ƙalilan kedai kullum ki wanke ido domin nasan kema zaki yaba da ita 100%”.

Wani farin cikine ya lulluɓe zuciyar Meemah a zuciyarta tace”ashe dama shima yana sona yaketa jamun aji yana nunamun kamar bayasona nifa dama nasan yana sona domin duk wani namiji me lafiya ya ga irin shigar da nikeyi dole hankalinsa ya tashi aiko yanzu zan fara nunamaka zallar ƙauna ashe dama bason wannan kucakar yarinyar yakeba kenan dole inzo inzage gurin nunamaka zallar ƙaunar da nike maka”.
jitayi Rahama ta taɓata tare da cewa”yadai Sis tunɗazu naketa magana kinyi shiru koke bakyason kiga matar da  Yah Abdallah ya mutu akanta ne”.
“inaso inganta man Sis”.
riƙe ɗaya sarƙar yayi a hannunsa ba tara daya saka cikin kayan siyayyarba suka nufi gurin biyan kuɗi suka biya suka nufi hanyar oasis.

Ɗaure yafito da towel a ƙugunsa hannunsa kuma ƙaramin towel yana sharce gashin kansa ta mirrior ya ga abokinnasa kama haɓa yayi alamun mamaki yace”mutumin shine zaka ƙaraso koka taɓani”.
harara Muhseen ya maka masa tare da cewa”yanzu ai seka koma tunda nima bakason ganina”.
“nina isa ince banason ganinka”.
“harma kayi yawa tunda ka iya tozartani a idon duniya muje gurin yarinyar nan domin bata invitation shine sekace wanda ze bar gari kashiga zazzaga ruwan masifa ta inda kake shiga batanan kake fita ba kafin ta ƙaraso kabar gurin aini a tinani ko wani abun tayimaka bekamata koni na sani ba seka hukuntata iya kaida ita shine so na haƙiƙa  bakazo kana tozartata a gaban kowa ba idan ni kayi a gabana  ai wani be kamata kayi a gabansa ba domin su magauta haka suke so yarinyar nan ko mara haƙuri ce bekamata kayimata haka ballema ita bameson fitina bace dan Allah abokina abinda nakeso dakai koda wani abun tayimaka kariƙa bari daga kai se ita seka nunamata abinda tayi ba daidai bane seta gyara ba tare da wanima yaji abinda kuke cikiba”.
zama Zaid yayi kan kujerar gaban dressing mirrior tare da cewa”zancen gaskiya ba abinda  yarinyar nan tayimun abokina kawai lokaci ɗaya naji na tsaneta koson ganinta banayi kai datake matsowa bakaji wani shegen wari na fita daka jikinta ba kamar jaɓa zahirin gaskiya kuma banajin zan iya rayuwa da ita domin se yanzu nagane ba ajina bace Jameelah ce daidai da class ɗina”.

A gigice Muhseen ya ɗago jin furucin abokinsa murya na rawa yace”anyako Zaid kana cikin hankalinka kuwa Jameelah fa ƙanwar Inteesar wanne irin mummunan abu kake ƙoƙarin aikatawa haka”.
duƙawa  Zaid yayi  a gaban Muhseen kamar wanda zeyi kuka yace”niko nasan menake cewa Muhseen zancen gaskiya bazan kwari zuciyata ba na tilastata kan abunda bataso ba dan Allah ina roƙonka daka tayani neman mafita domin idan na rasa Jameelah wallahi zan iya samun babbar matsala Inteesar kuma dan Allah kazo muje nabata haƙuri domin gaskiya yanzu bana ra’ayinta……”.
cikin tsananin ɓacin rai Muhseen ya bugamasa tsawa tare da dakatar dashi da hannu yace”nagaji da jin wa’innan miyagun kalaman naka marasa daɗi kuma bari kaji infaɗamaka karka indai seda sa hannuna zaka samu Jameelah wallahi bazaka taɓa samunta kuma daka ranar daka aikata wannan mummunan aikin da kake ƙoƙarinyi karka ƙara nuna kasanni domin ni bazan iya rayuwa da mutum butulu irinka ba mayaudari wanda besan abinda kemasa ciwoba mezaki da ragowar maza yarinyar daba abinda tasani sebin maza”.
a zafafe Zaid yaci kwalar Muhseen yana huci idanunsa sun rine se uban huci yake yace”kai waye da zaka riƙa faɗan munanan kalamai akan farincikina to bari kaji infaɗamaka abinda bakasani ba kan Jameelah a shirye nake dana ɓata da uban kowa dan haka iname gargaɗinka da indai kanaso mushirya dakai kaso abinda nake so “.
fizge jikinsa yayi daga riƙon da Zaid yayimasa cikin ɓacin rai Muhseen yace”ni ba kowa bane face abokinka meson ganin cigabanka amma tunda kace zaka iya ɓatawa da uban kowa kasani daka yau bani bakai kowa ya kama gabansa ko a hanya kaganni karka ƙara nuna kasanni ka manta dani a babin tarihin rayuwarka banza butulu kawai”.
a harzuƙe Zaid yace”seme ninamafi son haka sarkin takura kawai kai kaje ka aureta man shine zan tabbatar dakai ba butulu bane ɗan sa ido kawai rayuwarka ko tawa”.
nan Muhseen yafice rai ɓace tsaki Zaid yayi yacigaba da shafarshi yana gama saka kaya wayarsa dake kan gado tashiga ringing zama yayi a gefan kan gadon tare da jawo wayar hakan yayi daidai da katsewar kiran buɗe wayar yayi yashiga cal log dan duba waye mekiran wani kiran yaƙara shigowa baƙuwar number ya gani har ze jefar da wayar yafasa ya ɗaga tare da karata a kunnensa daga ɗaya ɓangaren Jameelah naji anɗaga tasaki doguwar ajiyar zuciya tare da cewa”Yah Zaid ina yini”.
jin muryarta ne yasashi lumshe idonsa haɗe da buɗe lokaci ɗaya yace”lafiya ƙlau dawa nake magana”.
yaƙarasa faɗi tare dason ƙara tabbatarwa dakansa ba gizon data saba yimasa bane murmushi Jameelah tayi me sauti wanda yaƙara narkar dashi a duniyar ƙaunarta taƙara narkar da murya tace”au Yayana baka ganeni bane ƙanwarka ce Jameelah”.
“a’aahhh kice Malama ce”.
“eh Yayah nice ya gida dasu Ummah”.
“lafiya ƙlau ƙanwata ya dalibanki”.
“Alhamdulillah ai se anjuma zasu zo Yayah”.
“ok masha Allah Malama Jameelah yaushe nima za’ah fara koyamun karatun nima”.
dammm ƙirjinta ya buga sakamakon jin ze ƙureta dakyar ta aro jarumta tace”haba Yayah aiku manyanmu ne kune masu koyamana mukuma mu koyawa na ƙasa damu”.
“a’aaah ƙanwata kice dai bazaki koyamunba dai”.
“zan koyamaka man amma ba yanzu ba dama kira nayi naji ya lafiyar Yayana”.
“aiko naji daɗi ƙanwata idan da kina free baki da wa’inda zaki koyawa karatu anjuma danazo kin rakani unguwa”.
“kaji Yayah meze hanani rakaka aiko sunzo nabasu haƙuri na tafi raka babban Yayana inmun dawo na koyamusu kazo kawai na rakaka baka da wata matsala”.
“nagode ƙanwata da kulawarki gareni idan kin shirya kiyimun flashing senazo na ɗaukeki mutafi”.
“bakomai Yayah ka taho yanzu mutafi a shirye nike nanda 8pm ma dawo”.
“toh gani nan zuwa”.
“yauwa”.
nanya kashe tare da ɗaura wayar a ƙirjinsa ya rungume yanajin ƙaunarta naƙara nunkuwa miƙawa yayi yaje bakin mirrior yaƙara turare a jikinsa tare da saka hula matching ɗin kayansa ta ɗauki wayarsa da car key ɗinsa ya nufi down stairs.

A falo yasamu Mum ɗinsa da Yasmeen zaune suna hira cikin girmamawa yaƙarasa inda suke ya langwaɓar da kansa tare da cew”Mum sannu da hutawa”.
“yauwa Son ina zuwa haka naga kasha uwar kwalliya kamar wanda zashi gasar kyau kodai gurin ɗiyae tawa zaka”.
sosa ƙeya yayi alamun kunya tare da cewa “eh Mum can zani”.
“ok idan kaje kace ina gaisheta”.
“zataji”.
Yasmeen da kanta ke cinyar Mum ce tace”Yayah wai wanne event Aunty zatayine naga guri na ƙurewa har yau bamu sani ba”.
dammm ƙirjinsa ya buga yawun bakinsa ya ƙafe lokaci ɗaya a zuciyarsa yace”bazan sanar daku gaskiyar al’amari ba domin nasan halin Mum zata iya yimun wani abun”.
yana cikin zancen zuci yaji muryar Mum tace”kayi shiru saboda tanaso tashiga cikinsu ne ayo komai da ita”.
wata dabara ce tafaɗomasa yasaki murmushi yace”Mum nima na tambayeta mezatayi tace wai ita batason ayi bidi’ah a bikinta batason komai wai idan akayi bidi’ah a biki befiye albarka ba na rasa yadda zanyi da ita dana dameta da maganarma harda yimun kuka nikuma banason abinda zeriƙa ɓatamata rai shiyasa na haƙura nima”.

Murmushi Mum tayi a zuciyarta tana ƙara godewa Allah daya bata kamilar suruka a fili kuma tace”aiko daughter bata isaba dole ayi ko kamune duk salahancinta kuwa ina za’ayi biki sulungudi kamar na mutuwa”.
“wlh kuwa Mum kinji Auntynnan tawani kwafsa mana data bari ansha shagali aida ba haka ba nifa harta ɓatamun rai “.
murmushi Mum tayi tace”da gaskiyarta gaskiya yarinyar nan tanada hankali shiyasa nake ƙara godewa Allah dayayimun kyautarta a matsayin suruka samun irinta a wannan zamanin se an tons kariƙa dakyau Zaid domin yarinyar bata da laifi insha Allahu zan kula da ita tamkar Yasmeen ka gaisheta kace nace dole ayi kamu”.
“zataji Mum sena dawo”.
“toh seka dawo Allah ya tsare”.
“Ameen “.
nanya fita yabar Mum da Yasmeen sunata yabon Inteesar.

Direct unguwar su Inteesar ya nufa ya tsaya daka ɗan nesa da gidansu yayi parking yayi hakan yayi daidai da fitowar Hauwah zata shiga gidansu Inteesar daga nesa ta hangi kamar motar Zaid mamakine yakamata ganin ya tsaya nesa da gida shiga gida tayi cikin sauri Jameelah dake raɓe a zaure tana ganin wucewar Hauwah cikin sauru ta fice ta nufi inda yayi parking tashiga yaja suka ɗauki hanyar oasis.

Samun Inteesar tayi ta fito daga wanka se ƙamshi ketashi sakamakon anfara yimata gyara cikin girmamawa tace”Ummih sannu da hutawa”.
“yauwa Hauwah”.
“Inteesar kunyi waya da Uncle Zaid ne naga motarsa a ɗan nesa da gidannan”.
“a’ah mekika gani “.
“motarsa nagani aɗan nesa da gidannan “.
“ko ɗaya wataƙila gurin Abbah yazo zasuyi wata maganar”.
“ƙila kuwa”.
nan suka cigaba da hirarsu batare da zargin komai ba.

Suna isa Oasis yana gama parking cikin shaukin so yace”ƙanwata bara na buɗemiki saboda banaso kina aikin wahala”.
“kaji Yayah daka barshi ma na buɗe aiki ni nake aikin abincin gidanmu gabaki ɗaya”.
“eh dai kidaibari na buɗemiki”.
“toh”.
nan ya fita ya zaga ya buɗemata suka fito suka nufi cikin gurin ɓangaren Namijin duniya ma baƙaramin siyayya yayiwa su Rahama ba shikuma yasamu seat ya zauna yasa sukayi oder duk abinda sukeso aka kawomusu bayan sun gama cine yabawa Rahama atm card ɗinsa aka ciri kuɗin abubuwan da suka siya yayi gaba suna binsa a baya necklace ɗin dake hannunsa ce ta faɗi ya duƙa da niyyar ɗakkowa kafin yakai ƙasa Zaid ya rigasa!!!!!!!!!

*Kuyi haƙuri Sisters bani da lafiya se yau na samu sauƙi  dan Allah ku sakani a addu’o’inku .*

Votes and Comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger  kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki  ta wannan number 08108362334.*_

Man of the world hausa novel book 2

4️⃣1️⃣➡️4️⃣2️⃣

           Yana ɗagowa da niyyar basa sukayi ido huɗu da Namijin duniya kallon-kallo suka shiga yi yayinda Namijin duniya ke jifansa da kallon tuguma  cikin inda-inda Zaid yace”Ina yini Yah Abdallah”.
“lafiya “.
yana gama faɗin haka ya miƙa hannu ya anshi necklace ɗin hannun Zaid ta gefan ido ya kalli wadda ke gefan Zaid a zuciyarsa yace”kenan yaudarata yakeyi”.
rasa me basa amsa ne yasashi fara tafiya yana mamakin abinda idanunsa suka ganemasa lokaci ɗaya yaji wani abu na tasomasa daga zuciyarsa se huci yakeyi yayinda yakejin haushin kowa direct gurin da yayi parking ɗin motarsa yashiga tare da jingina da jikin seat yanajin zuciyarsa na mugun tafarfasa a zuciyarsa yace”meyasa zeyimata haka seda yarinya ta aminta dashi shine ze zage yariƙa cin amanarta aiko yazama dole na ɗauki babban mataki akansa “.
wata zuciyarce tace”tokai meye naka na damuwa da yarinyar da bata ganin darajarka yaje yayita yaudararta matsalarsu”.
wata zuciyar ce tace”yazama dole ka kula da rayuwarta tunda a ƙarƙashinka take kaje kawai ka faɗamata koda zata gwasaleka shine kawai mafita”.
jin shigowar su Rahama ne yasashi buɗe rinannun idanunsa da yaketa ƙoƙarin ɓoye damuwarsa  yashiga yiwa motar key dafa kafaɗarsa Rahama tayi tare da cewa”Yayah meyasa naga gabaki ɗays mood ɗinka ya canza daka haɗuwa da Yah Zaid lafiya”.
ba tare daya kalleta ba yace”bakomai sweetheart muje nakaiku gida inada wani mahimmin aiki a office “.
“toh mutafi tare man Yayah”.
“a’ah bari na kira Salisu  driver yazo yamaidaku gida”.
“toh”.
nan yayi dialing number Salis yayimasa kwatancen ta hanyar da zasu haɗu yabada su ya nufi office ɗinsa cike da zaƙuwar son yaganta.

Karanta: Jarababben Namiji Complete Pdf

Ɓangaren Muhseen ko yana isa gida ya nufi part ɗin Abbansa zaune ya sameshi yana karanta jaridah Amminsa na haɗamasa tea ƙarasawa yayi cikin falon ya zauna kusa Abbansa yayi ƙasa da kansa kamar me neman wani abu yace”Ammih sannunku da hutawa”.
“yauwa Auta waya taɓamunkaine “.
cewar Abbah yana aje jaridar dake hannunsa yajawo Muhseen jikinsa kwantar da kansa yayi a cinyar Abbansa tare da cewa”ba Zaid bane”.
“me aminin naka yayimaka”.
cewar Amminsa tana miƙawa Abbansa tea turo baki yayi kamar wani ƙaramin yaro yashiga zayyanewa su Amminsa duk abinda yafaru har abinda Zaid yayimasa be rage komai ba seda ya faɗamusu murya a raunane yace”Abbih dan Allah inaso kuyimun wata alfarma”.
“faɗi Auta kota mecece indai munada halin yimaka zamuyimaka”.
sauke numfashi Muhseen yayi tare da cewa”Abbih batama fi ƙarfinku ba dan Allah ku temakeni kuyimun “.
“faɗi munajinka”.
cewar Amminsa dake maida hankalinta garesa ƙasa yayi da kansa yana wasa da ƴan yatsunsa tare da cewa”dan Allah Abbih inaso indai Zaid ya fasa auren Inteesar ku ɗauramun aure da ita a ranar kuma misalin lokacin ɗaurin aurensa da ita  banaso a fasa komai”.
shiru gurin gabaki ɗaya ya ɗauka zuciyar Muhseen se bugawa takeyi da sauri-sauri gani yakeyi dakyar idan iyayensa zasu yadda gyaran muryar da Abbansa yayine yasa jikinsa ƙarayin sanyi a zuciyarsa yanata addu’ah muryar Abbah ce ta katseshi daga dogon tinanin daya shiga yaji yace”indai wannanne Auta ka kwantar da hankalinka indai yadda ka faɗamana zancennan haka yake insha Allah zan nemamaka aurenta”.
cikin farinciki Muhseen ya rungume Abbansa tare da cewa”nagode Abbana maganin kukana ina alfahari da samunka a matsayi mahaifina I love you  Abbah”.
murmushi Ammih tayiwa tilon ɗan nata ganin yadda yaketa farinciki tace”wato ni baka alfahari dani ko”.
saurin sakin Abbah Muhseen yayi tare da rungume Ammih yace”niko nake alfahari da uwata datafi ta kowa a duniya amma Abbah karka faɗawa kowa wannan zancen a gurin ɗaurin aure idan yafasa sena aureta domin banaso duniya tayimuj kallon maci amanar abokinsa”.
“toh Allah ya nunamana”.
“Ameen”.
nsnsuka cigsba da hirarsu daka bisani Muhseen ya nufi part ɗinsa ya kwanta a makeken gadonsa tare da kara wayarsa a kunne tare da cewa”ƙawar amarya se yanzu naga miss call ɗinki”.
“eh dama kira nayi naji ya zancen schedule ɗin biki najiku shiru kuma abu se matsowa yakeyi ko ƙunshi bamuyiba”.
murmushin takaicin abubuwan da abokinsa keyi yayi tare da cewa”turomun da account number ki nasakamuku kuɗin ƙunshi shaf na manta ne muna cikin hidima munata tsara event ne”.
“okay toh bara na turomaka “.
“tom”.
nan sukayi sallama yanamaijin tausayin Inteesar.

Yana shiga Comphanynsa ko parking beyi mekyauba ya buɗe ya fita ko takan masu gaidashi bebiba ya nufi gurin elevator yashiga ya nufi office ɗinsa mutane se gaidashi sukeyi bemasan sunayi ba ya tura ƙofar office ɗinsa da ƙarfi kalloj kujerar Sakatariya yayi yaga ba kowa hakan yasashi cikin sassarfa ya buɗe ƙofar da zata sadashi da office ɗinsa yana buɗewa sansanyan ƙamshin room freshner daya haɗe da sanyin ac  ya bugi hancinsa lumshe sexy eyes ɗinsa yayi yana shaƙar daddaɗan ƙamshin tare dabin ko ina na office ɗin da kallo gani yayi ko ina fes dube-dube yashigayi koze ganta ganin beganta anan bane yasashi nufar toilet direct ya buɗe nanma beganta ba jiki ba kwari yakoma kan ɗaya daka cikin kujerar office ɗin yazauna tare da  tinanin ta inda zefara nemanta  yabata shawara kan karta yarda ta auri Zaid ba mutumin kirki bane ganin bashi da wata mafita yasashi fita ya shiga motarsa nufi unguwar daya taɓa ajeta yana tinanin koze ganta ya daɗe a cikin mota ya dube-dube ko Allah zesa yahanta amma bega kome kama da ita lokaci ɗays yaji kansa na mugun ciwo tsintar kansa yayi da jin haushin kansa na nemanta da dayayi yaja motarsa yanata tsaki ya nufi gida.

Washe gari suna tashi da sassafe suka shiga aikace-aikacen gida ita da Khadija sunkusa gama wanke -wanke Jameelah ta fito tana miƙa alamun tashinta bacci kenan kama baki tayi cikin iya bariki tace”Aunty meyasa baki tasheni nazo munyi ba kuketa gumurzun aiki ku kaɗai”.
hararta Khadijah tayi a zuciyarta tace”tsinanniya sekace yin aikin dama takeyi “.
murmushi Inteesar tayi cike da soyayyar ƴar uwarta tace”ai aikinma ba yawa harma munkusa gamawa kije ki shirya idan muka gama semu tafi gurin ƙunshi”.
“toh Aunty”.
nanta koma ɗaki tana yiwa Inteesar dariyar tagama da ita a zuciyarta tace”toh a ina tasamu kuɗi bayan Yayah Zaid yacemun ko biyar be bataba “. ƙumƙunai Khadijah tashiga yi harara Inteesar ta watsamata haɗe  cewa”kinga Khadija inbaki fita idonaba wallahi zakiga yadda zanyi dake koke zaki biyamat”.
nan taitayiwa Khadijah faɗa har suka gama wanke -wanken suka shirya gabaki ɗayansu suka tafi gidan ƙunshi.

Ɓangaren Namijin duniya ko kobaccin kirki besamu yayiba Allah,Allah yakeyi gari ya waye ya nufi comphany ɗinsa ana kiran asuba yana fitowa daga masallaci yana komawa bedroom ɗinsa ya faɗa wanke yana fitowa a gaggauce yashiga shafa mai yana gamawa yasaka wasu haɗaɗun ƴan kanti sunyi matuƙar amsar jikinsa ya ɗauki phones ɗinsa ya shiga sauka daga bene cikin hanzari kaciɓus sukayi da Abbih ɗinsa daya dawo daga masallaci kallonsa yayi cike da mamaki yace “ina zaka haka da sanyin safiyar nan “.
cikin girmamawa yace”Abbih ina kwana dama office zani inada wani aiki me mahimmanci ne shiyasa zantafi da wuri”.
“lafiya ƙlau amma dai ka tsaya ko tea ne kaɗansha kafijin kwarin yin aikin”.
“ai da wuri zan dawo  idan na dawo nayi breakfast”.
“ok seka dawo ina fatan dai ka tuna yaune ranar da alƙawarinmu ze cika”.
“eh Abbih idan na dawo zan falamaka”.
yaƙarasa zancensa yana ficewa dankar Abbih ɗinsa yaƙara tayo da wata maganar  murmushi Abbih yayi ya wuce .

Yana fita ta anshi makullin ɗaya daga cikin sababbin motocinsa yashiga yaja ya nufi comphany ɗinsa lokacin daya isa tsirarin mutane ne suka isa ya nufi office ɗinsa yana shiga ya zauna tare  kunna syatem ɗinsa  yashiga duba abubuwa yanayi yana duba lokaci wasa-wasa har 11am ba Inteesar ba alamunta ɓangaren Namijin duniya ko yarasa meke damunsa se tsaki yakeyi yana duba cctv camera koda zega ɓullowarta amma shiru bata bs labarinta har ƙarfe huɗu jiki ba kwari haka ya nufi gida  yanata tinanin meya hanata zuwa!!!!

Votes and Comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger  kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki  ta wannan number 08108362334.*_

Book 2

4️⃣3️⃣➡️4️⃣4️⃣

            Yana isa gida  direct y part ɗinsa ya nufa a ya zube akan haɗaɗen gadonsa ya lumshe sexy eyes ɗinsa ya lula duniyar tinani dakyar ya iya  tashi yashiga toilet yayi wanka yafito yana fitowa ya  shirya cikin ƙanan  kaya marasa nauyi ya nufi hanyar fita domin samawa cikinsa abu mara nauyi a falonaa yayi kaciɓus da Rahama datazo kiransa tana ganinshi tayi saurin juyamasa tana kukan shagwaɓa murmushin daya ƙarasamasa kyau yayi tare da kawota jikinsa cikin tausasa murya yace”sorry Sweetheart nasan nayi laifi na fita da wuri “.
yaƙarasa zancensa yana kama kunnensa alamun bada haƙuri murmushi Rahama tayi tare da yin hugging ɗinsa cikin shagwaɓa tace”indai kanaso in haƙura seka faɗamun sunanta”.
“wakenan”.
“wadda ta zautarmana dakai kaketa zabga smiling jiya wadda ka siyawa necklace”.
murmushin dabe shirya yi bane ya suɓucemasa ya lakacemata hanci tare da cewa”zaki santa amma ba yanzu ba”.
bubbuga ƙafa tashigayi alamun bata yardaba kama hannunta yayi yace”muje yunwa nakeji idan nagama cin abinci zan faɗamiki kinji amma sekin dena kuka”.
“yauwa Bro na Abbih na nemanka a part ɗin Granny”.
damm ƙirjinsa yabayar domin yasan kwanan zancen jiki ba kwari yace”muje”.
“toh”.
nan suka nufi ɓangaren Granny yayinda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri.

Suna isa falon Granny suka tadda Abbih da Granny suna hira cikin girmamawa suka samu guri kan carpet suka zauna ƙasa da kansa yayi cikin girmamawa yace”sannunku da hutawa”.
“yauwa sannu mesunan Manya “.
cewar Granny tana kallon Abdallah kallon Rahama Abbih yayi cikin nuna alamun rashin wasa a fuskarsa yace”ki shiga ɗaki zamuyi magana”.
“toh Abbih”.
nanta miƙe tashige bedroom ɗin Granny shiru ne ya biyo baya naɗan lokaci kafin daga bisani Abbih yayi gyaran murya tare da tattara hankalinsa ga Abdallah dake wasa da zara-zaran ƴan yatsunsa yace”kai muke saurare inafata dai yanzu kasamu daidai da ra’ayinka ko?”.
cikin dakiya tare da basarwa kamar besan me Abbih yake nufi ba yace”bangane ba Abbih”.
murmushi manya Abbih yayi domin yasan halin ɗannasa yace”kasan dai yaune ranar ƙarshe dana ɗibamaka akan ka fito da matar aure shine zaka nuna kamar bakasan inda zancena ya dosa ba to yanzu na tunamaka kasamu ko kuwa haryau bakasamu daidai da ra’ayin naka ba”.
jiɓine yashiga ketomasa dukda sanyin ac dake falon abinka da Namijin duniya seya make ya sosa ƙeya yace”eh to gaskiya har yanzu bansamu  wadda ta kwantamunba amma aɗan ƙaramun lokaci zuwa lokacin dazan samu wadda tayi daidai da ra’ayina”.
“aiko kayi kaɗan yaro kayi ƙarya ka kwana da yunwa jiƙaka kakeso muyi musha yau ni Indo naga abinda ya isheni anyako wannan katon ba aljana ce ta aureshi ba kuwa yaza’ai ace duk irin zuƙa-zuƙan matan dake sonsa yace duk basuyi daidai da ra’ayinshi ya yaro da anyi maganar aure seyace a ƙaramasa lokaci inbaka da lafiya ka faɗamun in nemamaka magani domin so nike naga masu yimun addu’ah gaskiyar Meramu tacemun jifan jikana akayi shiyasa yaƙi aure naƙi yadda aiko kowaye senayi maganinshi ungo kiramun Meramu mutafi Malam na bayan tsauni ya bincikamun domin banga ta zamaba za’ah kassaramun jika”.
taƙarasa faɗa tana miƙawa Abbih waya yakiramata aminiyartata ansar wayar Abbih yayi tare da cewa”Innah ki kwantar da hankalinki ba wanda yayimasa wani abun basekin tafi wani gurinba”.
“yo ina hankalina ze kwanta anjefi jikana bakaga yadda idonsa yakoma kamar gautaba daka yin maganar aure oh ni Indo ka tashi ka miƙani gidan Meramu mutafi gurin wannan mutumin na bayan tsauni”.
“naji Innah amma inda kike ƙoƙarin tafiya ba gurine mekyauba Malami baze zauna a bayan tsauni ba sede boka kuma babu kyau zuwa gurin boka”.
matsar kwalla Innah tashiga yi tana jan majina tana cewa”yanzunan Iro ni kake ciwa zarafi kan zanje samowa ɗanka lafiya shine zakayimun sharri a ina nafaɗamaka gurin boka zani to nabarka da ɗannaka magautan su kasheshi insuna iyawanz zame hannuna akan ɗanka kuma ku barmu sashina tunkafin nima naci zarafinku”.
murmushi Abbih yayi ganin yadda Innah ta haƙiƙance wai ita ala dole an nunamata iyakarta lallashinta Abbih yashiga yi dakyar ta sakko tabarsu su zauna a falonta kallonsa Abbih yayi naɗan lokaci sannan yace”tunda kace har yau bakasamu wadda ta kwantamaka ba to ni dakaina zan lalubomaka”.
damm ƙirjinsa ya buga yayinda yaji yawun bakinsa ya ƙafe lokaci ɗaya kai kawai ya ɗagawa Abbih nan Abbih ya miƙe yayiwa Granny sallama ya tafi .

Yana ganin fitar Abbih yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya miƙewa yayi tare da zama kan kujera ya lumshe idonsa kamar koda wannan lokaci tinanin  kyakyawar fuskarta yashiga yi wani ɓangarena zuciyarsa se tsukulinsa yakeyi daya kira Ahmad daya turomasa da numberta  yaji ko lafiya batazo ba jin muryar Innah yayi tana cewa”mesunan Manya ka rabu da wancan sakaran uban naka bawani boka wallahi Malami ne gobe da safe zanje gidan Meramu ta rakani in ansomaka kasha abunka ba tare daya sani ba duniya ba gaskiya kai baka damu da mutumba shiya damu dakai kodai baka da lafiya mesunan Manya”.
jin abinda tacene yasa Namijin duniya yin wata dariyar dabe shirya yinta ba jin waiko bashi da lafiya a zuciyarsa yace”Granny dakinsan yadda lafiya tayimun yawa da bikice haka ba domin ina tausayawa yaran mutane domin nikaina nasan nakama ɗiyar mutane nasan bazataji da daɗiba”.
a filikuma ɗagamata kai yayi alamar eh bashi da lafiya riƙe hannunshi tayi tare da cewa”aikoda naji aiko gobe zansa Barirah ta tafi ƙauyensu tasamomin magunguna kafara sha shiyasa kenan naga kamar kana tsoron mata ashe ga inda matsalar take doleko kaji tsoron mata ashe ba kayan aiki aiko ba zance yanzu dai ka kwantar da hankalinka insha Allahu zaka samu lafiya kaima kamar sauran maza”.
dariya Namijin duniya yaƙarayi jin wai shike tsoron mata yace”Granny ya mutum yake gane yafara soyayya”.
washe baki Granny tayi tare da cewa”Mesunan Manya wata ka kamu da sonta ne”.
“a’ah abokina ne yakamu dason wata shine ya tambayeni”.
“ayo aina ɗauka kai ka fara soyayya “.
“a’ah”.
“zakaji kana son ganinta akowanne lokaci baka da buri sena ganinta komai nata ze riƙa burgeka kodako rashin kunya tayimaka bazakaji haushi ba zaka kasance mejin tausayinta akowanne lokaci”.
ƙirjinsa ne yabada damm jin abinda tace a zuciyarsa yace”kenan sonta nike”.
wata zuciyarce tace”Allah ya kyauta inrasa wadda zanso se ƙasƙantacciyar cleaner  tausayinta kawai nakeyi “.
a fili ya furta “no tausayinta nakeji domin ni bani da lokacin ɓatawa”.
kallonsa su Granny sukayi Rahama tace”intayi wari maji”.
hararta yayi tare da miƙewa ya fice yabarsu.

5:00pm
Zaune kowa yake a ɗakin taro kowa yasha kwalliya ta alfarma ba abinda ke tashi a gurin se kiɗa zaune take akan kujerar higher table ita kaɗai tasha make-up harta gaji inba farin sani kayimata ba bazaka ganeta ba domin tayi  kyau sanye take da wata rantsatsiyar gown white me adon stone red se net ɗin da aka rifemata fuska daya kasance red komai na jikinta red ne  shiru-shiru ba ango ba alamarsa se amarya tsu kan step ɗin Hauwah tahau ta nufi gurin Inteesar da idanunta sunfara tara ruwa ta sunkuya daidai kunnenta tace”Besty ki kwantar da hankalinki insha Allahu ba abinda yafaru dashi”.
maida hawayen dake ƙoƙarin fitowa tayi tare da yin murmushin yaƙe tace”Allah yasa Besty kinga irin abinda nake faɗamiki kinƙi yadda kikayo uwar gayya gashi ba lallai yazo ni bikinnan wallahi duk yaficemun daka rai domin jikina duk sanyi yakeyi”.
“dan Allah kiriƙa haƙuri wataƙila wani abun yatsayayi bakiga abokansa duk sunzo ba shima yana hanya”.
“Allah yasa”.
nan Hauwah takoma seat ɗinta na babbar ƙawar amarya.

Dariya Jameelah tayi  ganin Inteesar kaɗai akan kujera tare da kallon ƙawarta Hindatu tace!!!!!!!!

Votes and Comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger  kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki  ta wannan number 08108362334.*_

Book 2

4️⃣5️⃣➡️4️⃣6️⃣

        “Hmmm kalli tsinanniyar se zare kurma-kurman ido take a kujera ita kaɗai kamar kazar da aka tsoma cikin ruwan zafi ai wallahi tunda tace zata jadani tana tare da wahala domin muddum Ummanmu na numfashi bazata taɓa barinsu suyi aure gidan jindaɗi ba sede suganmu muna hutawa suko sede su ƙare dayin aikatau da wanke-wanken gidan mutane da shara domin ni idan na auri Zaid ko kwancen kaya bazan temakesu dashi ba”.
“gaskiyane Mrs Zaid Cheif judge aikinki na kyau  mudai idan abunnan ya tabbatu Allah yasa kar a manta damu domin nasan halinki dakinsamu duniya kike shafawa idanunki toka ki babbake komai”.
“haba ƙawata kisha kuruminki wannan karon zanbaki mamaki domin so nike kema kiyi ramm da zuciyar babban amininsa Muhseen kinga shikenan amincinmu yaƙara ɗinkewa”.
“Allah ƙawata ammafa kinaja sosai amma kina ganin ze kulani kuwa domin gayennan naga alamu kamar yanada girman kaifa”.
“ke da Allah jacan girman kanshin banza munada Umma fa faɗuwar gaba asarar namiji ai ba’ah shiga dawa dan ƙarya kedai kawai ki kwantar da hankalinki zakiga yadda jikinsa ze riƙa tsuma akanki ai ina tinanin duk girman kansa bekai ɗan gogana ba amma dayasha aiki idan yaganni kamar ze lasheni haka yakemun shima zakiga yadda ze koma kai gaskiya nagaji so nike naɗan fita shan ice cream bara na kira Sweetheart yakaimu gurinnan yacika zafi”.
dariya Hindatu tayi tare da tafawa da Jameelah daketa faman yatsuna tace”lallai ƙawata gaskiya kin ƙaro wulaƙanci wato angon da amaryarsa ke jirama keshi zakisa ya kaiki shan ice cream baki da case kina cin duniyarki da tsinke wallahi”.
“sosaima kuwa idan banci lokacina ba yanzu yaushe kikeso naci koko so kike nayi ƙara’ih shekaran jiya da muka fita yasiyamana layin me &u dan yariƙa jina a waya suko wa’incan gaulayen da kikaga sunata faman kiranshi aikin banza sukeyi domin nina sakashi ya kashe wayarsa bazasu taɓa samunsa ba sa ƙaraci nacinsu su haƙura inbada abin namiji mezeyi da ɗiyar marasa asali bayan ga ƴar dangi gaba da baya itakuwa fa waya taɓa sanin dagin wannan me farar ƙafar”.
“gaskiya ne tawajena kici lokacinki”.
“yauwa tawajena”.
nan ta ɗakko wayarta daka jaka murmushi tayi tare da cewa”oh kinga ɗan halak yanzu muke maganarsa sega kiranshi ai bara naɗauka”.
“yadai kamata tawan”.

Ɗagawa tayi tare da yin ƙasa da murya tace”hello Dear yakake”.
“lafiya ba lafiya ba tunda banji lafiyar sarauniyar birnin zuciyata ba tunɗazu naketa kiranki kinyi bakiyi picking ba lafiya”.
murmushin daya ƙara narkar dashi a duniyar soyayyarta tayimasa tare da cewa”tuba nake My King ina gurin shagalin aurenku ne”.
“kingaki ko zaki farako kinsandai na faɗamiki banaso kina haɗani da wannan me warin jaɓar shine kike ƙara lanƙayamun itako ko sokike na fara miki kuka to “.
wani daɗine yaƙara kamata zuciyarta tace”sorry My nadena karkamun kuka wasa nake maka idan ba wani abun kakeyi ba inason muje shan ice cream inba damuwa”.
“kinji sweetheart ai koda aikin da nikeyi na bari nakaiki kisha kina ina nazo na ɗaukeki mutafi”.
jinjina Hindatu tayimata alamun aikinta na kyau kashemata ido ɗaya Jameelah tayi tare da cewa”Sweetheart ina gurin kamu “.
“ok gani nan zuwa amma sede ki fito waje domin banason aganni  a zata gurin abun nazo”.
“tom shikenan inka iso ka kirani sena fito mu wuce”.
“toh gani nan zuwa”.
yaƙarasa zancensa jikinsa na tsuma kashewa tayi tare da cewa “bara inje inɗan nuna alhinin rashin zuwan ango dankar a zargeni”.
“aiko dai”.
nanta miƙe ta nufi step tashiga nuna alhininta .

Zaune yake a falonsa ya zubawa tv ido kamar wanda yake gane abinda akeyi ba abinda kemasa yawo se kalaman Granny na tambayar daya yimata  hannunsa ɗauke da glass cup yana shan coffee turo ƙofar da akayine yasashi dawowa daga duniyar tinanin daya lula kallo ɗaya yayiwa aminan nasa  tare da amsamusu sallama yacigaba da shan coffeensa hankali kwance zama sukayi akan kujerar dake facing ɗin tashi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya murmushi Ahmad yayi tare da yaɓa Adam dake gefansa suka saki murmushi taɓe baki Abdallah yayi tare da cewa”kwagama munafuncinki a gidanma mutum be tsiraba se anbi mutum da gulma”.
dariya Adam yayi tare da cewa”ai gwara mu munafunafunci mukeyi da wanda yakeson abu yana hana zuciyarsa abunfa yariƙa basarwa waishi ala dole bayason raini fa”.
“mekake nufi”.
dariya Ahmad yayi tare da cewa”abinda kunnenka yajiyemaka saura kwana biyar afara tafiya gurin seminer nan kaikuma kaƙi motsawa  wallahi mudai tafiyarmu zamuyi tunda muba gwauraye bane  irin wataƙil baka da rabo idan mundawo maɗan sanmaka riba”.
“bangane saura kwana biyar ba har abun yazo”.
“eyi badai munbaka shawara kaƙi ɗauka ba da yanzu seka tafi da ita  inmundawo ka saketa kaga riba biyu ga sauro ga revenge ga ribar seminer”.
shiru yayi secan yace”to yanzu meye abunyi kasanfa banason rasa wannan seminer “.
“bara nakira Hauwah naji yadda za’ayi tabamu number Aishatun”.
“ok “.
dialing number Hauwah yayi tare dasata a hansfree yadda kowa zeji  bugu ɗaya ta ɗauka tare da komawa gefe saboda hayaniyar kiɗa tace”salamu Alaikum Sir”.
“wa’alaiki salam”.
“ina yini?”.
“lafiya ƙlau  Hauwah dama number Inteesar mukeso inba damuwa”.
shiru gabaki ɗaya sukayi danjin mezatace daga ɗaya ɓangaren Hauwah tace”Sir yanzu haka muna gurin kamun Inteesar gobe ake ɗauramata aure”.

Lokaci ɗaya hankalinshi yayi mugun tashi ya rasa mekemasa daɗi amma dake namijin duniya ne seya dake kamar beji komai ba har suka gama wayar bayan sungama Ahmad yace”tokaji irin abinda muke gujemaka tunfarko da yanzu ba wannan zancen akeyi ba yanzu sede a nemi wata”.
ɓangaren Man of the world ko kasa magana yayi sakamakon wani kullutun abu dayazo ya tsayamasa a maƙoshi lokaci ɗaya sexy eyes ɗinsa suka rine zuwa ja yayinda jijiyoyin kansa suka tashi sukayi ruɗu-ruɗu ba abinda ke ketowa a jikinsa se zufa yayinda kansa ke mugun saramasa ganin zasu ɗago jirginsa ne yasashi lumshe idanunsa ganin halin daya shiga ne yasa  Adam zungurar Ahmad ya raɗamasa”mutuminmu fa ya auka ba tare daya sani ba”.
“hhh aini tun kwanakin baya na lura yanzu dai yakamata muyi wani abu akan aurennan nata”.
“hakane kam”.
nan suka miƙe suka yimasa sallama kai kawai ya ɗaga musu sakamakon wani ciwon kan dake barazanar tarwatsamasa kai ba abinda ke kai komo a ciki zuciyarsa se kalmar Hauwah na cewa”gobe za’ah ɗaura mata aure “.
a zuciyarsa yace”ashe zata iya aure batare data sanarmun ba”.
wata zuciyarce tace”to waikai meye naka naseta sanarmaka “.
rasa me bashi amsa ne yasashi miƙewa yana haɗa hanya kamar wani ɗan maye ya nufi bedroom ɗinsa ya zube kan tanƙamemen gadonsa  wani zazzaɓine me zafi ya rifeshi har kyarma yakeyi  dakyar ya miƙe ya kashe ac ɗin dake aiki ya kashe hasken ɗakin ya kwanta yanata rawar sanyi.

Ɓangaren Inteesar ko har ƙarfe tara ba ango ba alamunsa sunyi kiran number Zaid har sun gaji amma amsar ɗayace switch off ƴan uwansa se mamakin rashin zuwansa sukeyi har aka tashi taro bezoba komai dayakamata ango yayi Muhseen ne yayi a makwafinsa har aka tashi taron yayinda ran Ummin Zaid yayi mugun ɓaci akan abunda ya aikata haka kowa ya tashi yayinda jikin Inteesar yaƙara yin mugun sanyi akan aure.

Washe gari da safe yana tashi ya nufi ɓangaren Abbansa zaune ya samesa akan sallaya yana lazumi gefansa ya zauna tare da jiran ya idar yana gamawa ya shafa tare da yin murmushi yace”Abbah na lafiya kamar da magana a bakinka”.
murmushi Zaid yayi tare da sosa keya alamun kunya yace”eh Abbah”.
“ok faɗi damuwarka Abbanah kanka tsaye”.
ƙasa dakai Zaid yayi tare da cewa!!!!!!!!

Karanta: Inayah Hausa Novel Complete

Man of the world hausa novel book 2 Complete Download

Novel Title Man of the world hausa novel book 2
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 491kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author Oum Hairan
File format Txt
Published date 05 – 04– 2023

 

Also Read : Abban Sojoji Page 100 Hausa Novel

 

Download Novel

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*