Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin Abban sojoji Page 100 wanda hafsat Bature ta rubuta takuma wallafa.
Abban Sojoji Page 100
ABBAN SOJOJI The Father Of Soldiers
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ_ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ
ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ
Mallakin
HAFSAT BATURE MOH’D
BossLady
Final Page In Part 1
Abban Sojoji page 100
“Kwarai kuwa, yanzu dae ki tattara akwatinan nan ki kai su bedroom ɗinki, Ni bari naje wurinsu naga ya suka kwana, Allah yasa suna raye dae”
ta faɗi tana dariya itama Hafsat ɗin dariyar take yi,
tayi mamakin ganin ƙopan store ɗin abuɗe turowa tayi ta shiga samun su tayi a tsaitsaye sai faman zagaye zagaye suke yi sun jigata sosai,.
Suna ganinta gabansu ya faɗi rass saboda tsoran matar suke ji sam sun gaza magana sai zare ido kawai,
murmushi Aunty Babba tasaki tare da cewa “Ashe kuna raye, gsky kuna da taurin rai,’
Jahad ce tayi ƙoƙarin gaishe ta bata amsa ba sai cewa tayi “ku biyo ni”
Sannan ta juya ta fice suka bi bayanta aransu suna Allah Allah gudun karta yi masu wani abun,
A wani bedroom ta tsaya ta turo door ɗin sannan tashiga, suma suka bi ta ciki, ɗumemiyar katifa ce a ɗakin sai wardrobe ta bango, da ƴar drawer,
“Kada kuyi tunanin a ɗakin nan zan barku, tsohon store ɗin can shine wurin baccinku in dare yayi, na kawo ku nan ne domin kuyi wanka ku samu kuyi sallah, sannan zan baku abinci duk rana plate ɗaya, amma ku sani zaku Aikatu sosai, don Gwamnati bata aikin banza,’
aunty babba ce ke kora masu bayanin nan ba mutunci a fuskarta, a daga tsayen da suke, Kallon juna su kayi jiki asanyaye koba komai sun samu sauƙi atlease,
Jin sunyi shiru yasa ta daka masu tsawa da cewa “Baku ji ina magana bane, kun wani tsayamin kamar ƙerarrun gumaka,’.
Murya na rawa suka haɗa baki wurin cewa “Zamuyi komai kke so insha Allah,”
ta6e baki tayi tana kallonsu tace “kada kuyi tunanin sauƙi kuka samu a wurina, sam ba haka bane don yanzu uƙubar tafara,”
Jahad tace “Laifin me muka yi maki ?.
dariya aunty Babba tayi tare da kallonta ita da tayi magana tace “bakuyi mun laifin komai ba, kawai kun shiga tsakani na da abun Hari na ne shiyasanya,’ tana faɗin hakan ta fuce daga ɗakin,
Shiru su kayi suna kallon juna bakomai ya tayar masu da hankali ba face abunda Aunty babba tace wato kada suyi tunanin sun samu sauƙi yanzu uƙubar tafara, me hakan ke nufi !?!?
ajiyar zuciya Suka saki atare wuce wa Jahad tayi toilet domin ita damuwarta Sallah, Hosana kuwa saman katifar tahau ta zauna idonta cike tab da kwalla luhu luhu Yunwa take ji Over,
Wuce wa kitchen Aunty babba tayi lokacin har hafsat ta koma bedroom ɗinta ta kwashe kaf kayan da aka suyo masu hosana da Jahad ta shige dasu (uwar Son banza)
Sai faman yamutsa fuska take kamar uban wani ya matsa mata ta haɗa musu abinci,..
Duddubawa tayi Cikin kitchen ɗin tana jin bazata Iya girkawa yaran Abinci da hannunta ba, Akwai sauran breakfast ɗinsu na safe da suka rage duk yayi sanyi abincin,
Tsayawa tayi tana tunani aranta kawai ta daure Just for today ta dafa musu ko Indomie ce,
Nan da nan ta kunna gas ta aza pot ta zuba ruwa ciki, shaf shaf ta haɗa kayan haɗi aciki ta zuba musu Indomie ɗin aciki,
Bayan ta kammala dafuwa, ta ɗauko plate mai ɗan faɗi ta baza musu Ita aciki da zafi zafinta sai ƙamshi take yi,
A tray ta ajiye musu ita sannan ta haɗa musu da sauran kayan breakfast ɗinda suka rage na safe, tare da drinks,.
Sai gata tafito ɗauke da tray ɗin ta wuce dashi ɗakin lokacin da ta shiga Jahad har ta fito Tayo wanka tare da Alwala ta maida kayan jikinta, tana a tsaye tana tunanin me zata sa tayi sallah,
Sai gata tashigo ba sallama ajiye musu tayi a ƙasa batare da tace komai ba sannan ta fuce,
Jikin hosana har kerma yakeyi ganin abinci jiki na rawa tasa hannu ta janyo tray ɗin, saboda zumuɗi ta buɗe plate ɗin dake ɗauke da taliyar, a gaggauce ta tsoma hannunta sam bata lura da hayaƙin dake fita ba saboda a makance take da yunwa nan take hannunta yayi jawur, zare hannun tayi tana kuka,
Hankali tashe jahad ta ƙaraso tana faɗin “Hosana meke damunki ne baki ga taliyar tana huci ba ne?
Cikin kuka tace “Yunwa nake ji sosai ne”
“Nasani ae,” jahad ta faɗi tare da zama gaban tray ɗin, hannu tasa ta buɗe ƙaramar warmer ɗin dake ajiye cikin tray ɗin,soyayyen dankalin turawa ne da doya da kwai duk ta haɗe masu sunyi mugun sanyi,
Cikin sanyin murya Jahad tace “Ki ci wannan hosana ba zafi duk da yayi sanyi sosai, ruwan kashe gobara ba dole sai da mai kyau ba,”
Hannu suka sa atare suna ci daker suke tura shi cikin baki musamman yam ɗin data sanƙare, sai da suka rinƙa haɗawa da Coke ɗin data kawo masu, bayan sun cinye ne suka koma kan taliyar lokacin ta ɗan gare zafi,sunji daɗinta sosai,
Ba laifi sun ɗan cika cikinsu,
Shiga toilet jahad tayi ta kuskure bakinta sannan tafito ta bude wardrobe ɗin data gani a ɗakin, wasu tsofaffin kayane aciki dama ita Sallaya take nema kuma tasamu,.
ɗaukowa tayi ta shimfiɗa don tayi sallah,
Kamar daga sama ta faɗo musu hannunta ɗauke da kaya, watsa su tayi saman katifar dake ɗakin tana cewa “Gasu nan in kunyi wanka ku sanya,”
sannan ta ɗauki tray ɗin da suka kammala cin abinci dashi ta fuce dashi tana murmushin mugunta ita kaɗai tasan me take ƙissawa aranta,
duba kayan su kayi kala bibbiyu ne dogayen riguna masu kyan gaske, sai jalbaba guda biyu da takalmi silifas shima biyu, shine abunda suka samu,
Jahad tace “ina ji araina yaya Omar ya turo da kuɗi asiya mana kaya shiyasa ta bamu wannan hosana ki tashi kiyi wanka kizo ki canza kayan jikin ki,”
tayi maganar tare da cire rigar jikinta, ta ɗauki wanda Aunty babba ta kawo musu ta zura ajikinta doguwace mai dogon hannu tayi mata kyau sosai launin rigar Pink colour ce, daker hosana tayi wanka itama ta canza kaya daga nan kuma Aunty Babba ta zo tafita dasu domin nuna musu aikinsu
___________Ataƙaitace________________
A kwana a tashi yau wata ɗaya kenan da zamansu Hosana da jahad a gidan general Ishaq haƙiƙa sun fuskanci matsanancin tashin hankai kullum cikin tsoro suke da fargabar me zai je ya dawo, sam Aunty Babba da Hafsat basa raga masu sun mayar dasu Tamkar Jakuna marasa Ƴanci, kullum cikin ƙuntata musu suke, gashi duk wani aiki na gidan duka akansu yake ƙarewa, tun da asussuba Aunty Babba ke tashin su daga bacci tasa su fara aikace aikace, sune wanke wanke, sune shara, sune goge tiles tunda ga ƙasa har saman Bango duk girman gidan nan sai tasa sun goge ko’ina, ga Uban wanki hada na barguna, in sukayi mata kuskure kuwa har bugu take kai musu, ta tsane su kamar mutuwarta, tabbas su hosana da jahad suna cikin masifa kullum cikin kuka suke idan baka samu jiƙaƙƙun hawaye a idonsu ba to zaka samu busassu ne, duk wannan uban wahalar a rana plate ɗaya take basu na abinci su biyu don tsabagen mugunta irin nata, wani lokacin ma sai dae Jahad ta bar ma Hosana saboda tausayi ita kuwa kamar zata mutu da yunwa haka zata jure, dai dai da minti ɗaya basu samu na hutu, in ba ƙarfe sha biyu na dare ba take barinsu su kwanta, kuma acikin wannan tsohon store ɗin nan take garƙamesu sai da asuba ta buɗe su atashi ayi aiki, Wani lokacin idan yunwar dare ta addabesu Dankalin hausar nan dake acikin store ɗin suke ɗauka suna 6arewa suna Ci
Duk dare sai sunci dankalin hausar sannan cikinsu ke ɗan cika,
Duk wannan abun dake faruwa Marshal Omar sam bai sani ba, domin kuwa duk lokacin daya kira waya ya tambaye su sai ta shirga mashi ƙarya, in kuwa yace tabasu yayi magana dasu, sai ta fara Ja musu kunne ta buga musu warning akan karsu kuskura su sanar dashi halin da suke ciki sannan ta basu wayar, kuma agabanta suke yin wayar suna yi suna kallonta tana galla musu harara tana ƙara gargaɗinsu,
lokacin da Omar Ya shirya ziyartarsu ya kira Aunty babba ya sanar da ita zaizo, Jiki na rawa ta gyara su tsaf kamar basu ba hada kwalliya tayi musu, sannan taja musu kunne da barazanar zata kashe in suka kuskura suka tona mata asiri a wurinsa ko kuma suka yi yunƙurin cewa zasu bishi,
tsananin tsoranta yasa har Omar yazo yini guda ya tafi basu ce masa uffan fa, duk da yatafi da mamakin meyasa yaran Basa Dariya? Musamman mai ta6in hankalin saboda yasanta kullum cikin murmushi take, amma zuwan nan nasa harya tafi ko kallonsa basa son yi ba don komai ba sai don gudun kada hawaye su kufce musu yagani ya tuhumi Aunty babba, ƙarshe abun kansu zai ƙare, Wannan shi ake kira da Rana Zafi Inuwa ƙuna
______________________________________
A 6angaren sehrish kuwa ta shiga halin ha’ula’i, domin kuwa Haroon Ya addabi rayuwarta, ya takura mata over, sam bai mata da sauƙi, ya gama firgitar da ita ya tsoratar da ita da yi mata barazana akan zai tona mata asiri in bata biya masa buƙatarsa ba, kullum cikin kuka take tarasa wa zata kai ma kukanta akan haroon, saboda matsa matan dayake sai ta same shi aɗaki kuma ba yadda ta iya dole taje saboda gudun karya tona mata asiri, in taje kuwa haka zai matse ta abango yana shafa jikinta kamar maraye daker take kwace kanta, in jaraba tayi jaraba har bedroom ɗinta yake biyo ta, saboda wani lokacin tana mantawa bata rufe ɗaki ba, saboda tasan ba mai shigo mata in ba Aunty Azmee ba , kamar daga sama yake faɗo mata wani sa’in sai dai taji mutun ya faɗo mata saman gado ya tsoratar da ita, sehrish tasha kuka fiye da tunanin mai tunani duk da haryanzu haroon bai ida tarwatsa mata rayuwa ba, Allah na taimakonta tana kwace wa daga hannunsa ta faɗa toilet ta datse, tasha kuka iya kuka, taso ta sanarwa aunty azmee amma ranta na bata cewa Aunty azmee ba abunda zata iya saboda ƴar aiki ce ita, haka zalika taso ko Junaid ne ta sanar mishi amma sai take ganin tonawa kanta asiri zatayi ƙarshe ma tayiwa kanta sanadiyar barin gidan gaba ɗaya
a 6angaren sgr Sam bai sake tunanin ya tuhumi mai aikin nasu ba, ba don komai ba sai don wasu dalilai, tun ranar da suka haɗa ido ta sume, ya tabbatarwa kansa cewa koma wacece muguwar matsoraciya ce, Muddin yace zai yi mata tsawa to tabbas zuciyarta zata iya bugawa ta mutu, Saboda irin hakan tasha faruwa dashi, akwai masu laifin da tsawa kawai yake daka musu zuciyarsu ta buga don tsoro, shiyasa ya zubawa lamarin ido zuwa wani lokaci, 👀👀👀👀👀 ~~~~~~~~~~~~~~~~
A 6angaren Junaid kuwa soyayyar sehrish a kullum ƙara ninkuwa take yi, bawan Allah bai da tunani daya wuce na sehrish sometimes ko isasshen bacci bai samu saboda tunanin ta, yaso ace ko chat su nayi don ya ɗebe kewarta sai dai kash a halin da ake ciki ita kanta sehrish batasan inda ta wurga wayarta ba, Saboda tsananin damuwar da take ciki yasa ta manta da wata waya ma, Aunty azmee ta lura da yanayin sehrish domin ko aiki suke wani lokacin tana firgita ita kaɗae, har tambayarta take yi ko akwai wata damuwa, amma sai tace ba komai sai in ta koma ɗaki taita kuka kamar ranta zai fita, duk ta fige ta ram_____
Ataƙaice kenan abubuwan dake faruwa acikin rayuwar waɗan nan bayin Allah, shin me zai faru nan gaba ? kuna ganin Aunty babba zata kyale su hosana ? Mai zai faru in ta sa aka zubar dasu kamar yadda tace? Wane hannu kuma kke tunanin zasu faɗa? Yaya rayuwarsu zata kasance?
Shin me zai faru da sehrish in haroon ya cimma burinsa? Yaya rayuwar junaid zata kasance aranar da ya gane cewa Sehrish babban yayansu take so bashi ba?
Allah ya kaimu monday Lpy zamu shiga part 2, masu mun ya jiki Alhamdulillah
______________________________________
Also Read: Abban sojoji Book 2 Complete
Abban sojoji Page 100 Download
Abban Sojoji Page 100 | Hausa Novel Complete |
Uploaded by | Zamgist.com.ng |
File Size | 405kb |
Hausa Novels WhatsApp Group | Click here |
Telegram Group | Click here |
Tag | Abban Sojoji Page 100 |
Novel Author | Hafsat Bature |
File format | |
Published date | 02 – 04– 2023 |
Karanta: Abban Sojoji Hausa Novel Book 3