Sakon Barka da Juma’a & Barka da Juma’a Messages

Barka da zuwa wannan shafin namu mai albarka inda muka kawo muku sakon barka da juma’a, barka da juma’a messages, gaisuwar juma’a dadai sauransu.

Falalar Ranar Juma’ah

Ranar Juma’a rana ce mai falala da girma, wannan ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yake girmamata, yake kuma ware ta da Karin wasu Ibadoji na daban, ga kadan daga abubuwan da ranar Juma’a ta kebanta da su:

1. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya kasance yana karanta Suratus Sajada da Suratul Insan a duk asubar ranar Juma’a, kamar yadda Imamu Muslim ya rawaito.

Shaikhul Islam Ibni Taimiyya yana cewa “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yana karanta wadannan Surori ne saboda sun kunshi abin da ya faru, da ma abin da zai faru a wannan ranar, kuma Surorin suna dauke da bayanin halittar (Annabi) Adam, da ambaton makoma (lahira) da (bayanin) abin da zai faru ga bayi (a lahira), duk wannan zai faru ne a ranar Juma’a……..” (Duba “Zadul Ma’ad” (1/364).

2. Mustahabbi ne a yawaita salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) a daren wannan rana, da yininta, saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) “ku yawaita yi min salati ranar Juma’a da darenta” (Baihaki ne ya rawaito shi).

Imam Ibnil Kayyim yana cewa “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) shi ne shugaban halitta, ranar Juma’a kuwa ita ce shugabannin ranaku, don haka yin salati ga Manzon Allah (Sallallahu Aliahi Wa Sallam) a wannan ranar yana da fifiko akan sauran ranaku…….” (Zadul Ma’ad) (1/364).

3. Yin sallar Juma’a da halartata yana daya daga cikin maya-mayan taruka na Musulunci, don haka ma duk wanda ya ki halartar Juma’a da gangan to Allah zai rufe masa zuciya, alheri ba zai rika shigarta ba.

4. Yin wanka acikinta.

5. sanya turare, an karbo Hadisi daga Abu Sa’id ya ce “Wankan Juma’a wajibi ne akan duk wani baligi, sannan ya yi aswaki, ya sanya turare in ya samu” Bukhari ne ya rawaito shi Hadisi na (880).

6. Mustahabbi ne yin aswki a wannan ranar, kamar yadda ya gabata a Hadisi.

7. Zuwa Masllaci da wuri.

8. Shagalta da sallahr nafila da Zikiri, kamar karatun Alkur’ani har zuwa fitowar liman.

9. Wajibi ne a saurari Huduba, da yin shiru ya yin da ake yinta.

10. Karanta Suratul Khahfi a wannan rana, saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) “Duk wanda ya karanta Suratul Khahfi a ranar Juma’a, wani haske zai daga daga karkashin kafarsa har zuwa kololuwar sama, zai zamar masa haske ranar alkiyama, kuma za a gafarta masa abin da yake tsakanin Jumu’o’in guda biyu”.

Hakim da Baihaki ne suka rawaito shi (Shiekh Albani ya ingantaa wanan Hadisi a cikin :Irwa’ul Galil” (3/93).

11. Ana so a karanta Suratul Juma’a da Suratul Munafikun, ko kuma Suratul A’ala da Gashiya ya yin Sallar Juma’a.

12. Rana ce ta idi ga Musulmi, wanda yake maimaituwa duk sati.

13. Mustahabbi ne a sanya kaya kyawawa, saboda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Ssllam) yace

“Duk wanda ya yi wanka ranar Juma’a ya sa turare-in ya samu-sannan ya saka kyawawan tufafina, ya fita cikin nutsuwa, har ya isa Masallaci, ya yi nafila gwargwadon abin da yaga dama, bai cutar da kowa ba, sannan ya yi shiru har liman ya fito ya yi Sallah, to hakan ya zama masa kaffarar abin da ke tsakanin Jma’a biyu” Imamu Ahmad ne ya rawaito wannan Hadisi.

14. Mustahabbi ne a gyara Masallaci asa masa turare. Umar Dan Khaddab (R.A.) ya yi umarni a lokacinsa a rika sawa Masallacin Madina turare a duk ranar Juma’a bayan rana ta raba.

15. Baya halatta ayi tafiya a ranar Juma’a, kafin ayi Sallar Juma’a in dai lokacinta ya shiga. Amma idan lokacin bai yi ba, to malamai sun yi sabani akan hakan. Sai dai zance mafi rinjaye ba laifi a tafi Duba “Almugni” na Ibnu Kudama (3/248). Da “Zadul Ma’ad” (1/370).

16. Ranace da ake son yawaita yin Ibada a cikinta, kamar yawaita Salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), Zikiri, nafilfilu, karatun Alkur’ani da sauransu.

17. Yin sadaka a wannan rana daban yake da yin ta a sauran ranakun sati, kamar yin sadaka ne a cikin watan Azumi.

18. Ranace da Allah ya yi wa wannan al’umma kyautar ta kamar yadda Hadisi ya nuna (Duba Za’dul Ma’adi (1/40).

19. Rance da ba a kebance ta da Azumi, sai dai in mutum zai hada ta ranar Alhamis, ko Assabar.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce “ka da dayanku ya yi Azumin ranar Juma’a, sai in ya Azumuci ranar da take gabaninta ko bayanta” (bukhari da Muslim ne suka rawaito).

20. Haramun ne saye ko sayarwa ga wanda ya ji kiran Sallahr Juma’a, lokacin da liman ya hau Mimbari. Idan kuwa an kulla ciniki a wananan lokaci, to malamai sun yi sabaani a kan ingancinsa. Imam Khurdabi da Ibnu kasir sun rinjaya rashin ingancinsa, don haka ya zama lalatacce (Duba Tafsirin Khurdubi (18/96) da Tafsirin Ibnu Kasir (4/392).

Muna Rokon Allah ya bamu ladan dukkan ibadun da zamuyi a cikin wannan rana mai albarka.

Karanta: Kalaman Soyayya 2023 Masu Dadi

Sakon barka da juma’a na masoya

1. Hhmm da kyakkyawan murmushin dake bayyane akan fuskata, wanda ke wanzuwa aduk lokacin da natunada kyakkyawr suffarki, Sallam agareki kyakkyawr zinariya kuma kasai tacciyar sarauniyar kyawawa, kisni cewa akicin wannan b tunkararki da sakon barkar da kyakkyawr safiya. – Sakon Barka da Juma’a

2. Gami da tanbayar kintashi lfy ne kadai ze warware kullin da ke zuciyata domin samar da farincikin ruhina, yake abar kaunata kisani cewa farinciki da walwalar zuciyata ya ta allaka da jin amsar sakona agareki, ata daya bangaren kuma zan farada bayyana asalin yanda nake jinki arainane. – Sakon Barka da Juma’a

3. Hkk naka sance mai kwana da tunaniki nakanso naji saudin mafi dadi akunnuwana wato na muyarki nenan, ina jin kaunarki a ruhina tamkar yadda nakejin sautin bugun zuciyata, zan miko sakona agareki da kyakkyawr manufa, domin bana jin akwai safiyar da bazan ta shi da tunaniki ba, yauma kamar kullum abar kaunata gasakona Inafatan yazo gareki. – Sakon Barka da Juma’a

Barka da juma’a messages

1. Kasancewar Kowane Lokaci Kina Cikin Raina Hakan Shine Zai Sake Kasantar Dani Wajen Kasantuwa Cikin Mika Sakon Gaysuwar Aminci Agareki.

2. Lantarkin Dake Kawo Hasken Wutar Dake Chaja Zuciyata Ya Kasantune Cikin Fitowar Murmushin Dake Fitowa Daga Fuskarki. – barka da juma’a messages

3. Kinzama Jami,ar Sanin Minene Wata Damuwata Hakanne Yasa Baki Bari Na Fuskanci Dukkan Wata Damuwa Domin Kina Yawan Gabatarmin Da Kyakkyawan Murmushinki.

4. Sallama Nake Agareki Yake Abun Son Zuciya Mai Saka Nishadi Acikin Zuci Kwanaki Masu Yawa Inata Dakon Soyayyarki.

5. Kyawun Lafuzza Suna Fita Daga Kyawawan Labbanki Masu Sarrafa Hankalin Idanuwana Alokacinda Nake Kallonki. – barka da juma’a messages

6. Dare Zuwa Rana Dake Nake Cika Baccina Tsananin Tunaninki Yana Yawan Samun Wuri Yana Karuwa Acikin Raina.

7. Kinzama Kyakkyawar Zinariya Mai Kyakyalin Kawata Duniyar Masoya Lallai Samunki Babban Rabone Acikin Rayuwata.

8. Kallon Farko Da Naimiki Alokaci Daya Nake Dakon Soyayyarki Iya Tsawon Shekarun Da Ban Iya Tantancewa Ba.

9. Taya Zan Iya Rayuwa Batare Dake Ba Bayan Kinsan Soyayyarki Tayi Nisan Da Babu Mai Iya Hangowa. – barka da juma’a messages

10. Ruhina Yana Samun Madadine Daga Ruhinki Shiyasa Komai Namu Yake Kasantuwa Alokaci Daya Aduk Sanda Muke Tuna Junanmu. – gaisuwar juma’a

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top