Tarihin garzali miko, Wakoki da Kadara

Nasan cewa kunzo wannan shafin ne don neman ƙarin sani game da tarihin Garzali Miko ko? Idan amsarku itace eh to kun zo wurin da ya dace.

A wannan shafin zaku karanta cikakken tarihin garzali miko jarumin Kannywood, matar sa, dakuma kadara.

Tarihin Garzali Miko

Garzali Miko Shahararren mawaki ne a Najeriya daga masana’antar kannywood, ya yi fice a fagen wasan kwaikwayo da waka.

An haife shi a (Satumba 1993) kuma ya girma a jihar Kano inda ya halarci makarantar firamare ta musamman ta Gyadi Gyadi.

Daganan Ya wuce Horizon Day Secondary School duk a kano inda ya kammala karatunsa da sakamako mai ban mamaki.

Bayan kammala karatunsa na farko, jarumin ya wuce jami’a kuma ya kammala karatunsa na digiri.

Garzali ya fara sana’ar wasan kwaikwayo tun yana karami, tun yana karamin mai shirya fina-finai zuwa fitattun jaruman masana’antar Kannywood.

A wata hira da aka yi da shi, Garzali ya ce kasancewarsa jarumin mafarki ne ya tabbata domin tun yana karami yake son hakan.

Ya shiga kannywood ne bayan ya fito a wani fim mai suna “Gamu nan dai” wadannan fina-finan sun kara haskaka shi da taimakon Ali nuhu da sanusi Oscar. Ya fito a fina-finan kannywood kusan 20.

tarihin garzali miko

Wakokin Garzali Miko

Mawakin ya saki wakokin hausa sama da 30 tun shigowarsa masana’antar. Wasu daga cikin wakokinsa sun hada da….

  • Shagalin Biki
  • Yakamata
  • Ki Gane
  • Soyayyar Ki Ta Kamani
  • Soyayya Ruman Zuma
  • So Halita Ne
  • Ruwam Zuma
  • Mizanin So
  • Soyayya Ce
  • Aure
  • Kece da dai sauransu.

Karanta: Tarihin Azima Gidan Badamasi

Matar Garzali Miko

A halin yanzu Garzali Miko yana auren kyakkyawar matarsa ​​Habiba . An daura auren ne a ranar 20 ga watan Agusta 2021 a jihar Kaduna.

Jaruman Kannywood da dama kamar su Ali Nuhu, Adam A Zango, Ahmed Lawan, Umar M Shareef da sauran su duk sun halarta bikin na garzali.

Matar garzali miko
Garzali miko DA matarsa Habiba

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*