Yadda Ake Wankan Janaba Daga Bakin Sheikh Jafar

Karanta cikakken bayanin yadda ake wankan wato yadda ake wankan maniyyi janaba daga bakin sheikh Jafar Mahmud Adam.

Muna fatan Allah yakai Rahama acikin kabarin malam jafar bisa kokari dakuma gwagwarmaya dayayi wajan yada da’awar musulunci.

Kafin mushiga cikin bayani akan yadda ake wankan janaba, bari mufara dayin bayani akan menene janaba dakuma abubuwan dakesa ayi wankan janaba.

Menene Wankan Janaba?

Wankan janaba wanka ne na wajibi ga duk musulmin da ya kai shekarun balaga. Wankan ya zama hanya ce ta tsarkake jiki daga ƙazanta.

Abubuwan Dake sa Wankan Janaba

Anayin wankan janaba ne idan daya daga cikin wadannan abubuwan suka faru:

1. Fitar Maniyyi

Fitar maniyyi a farke koh acikin bacci yanasa ayi wankan janaba, Aduk lokacin da namiji koh mace suka fitar da maniyyi ta hanyar mafarki ko saduwa toh wankan janaba ya wajaba.

2. Saduwa

Wankan janaba yana wajaba akan duk wanda yayi saduwa da mace kokuma mace tayi saduwa da namiji. Inma tahanyar halal akayi saduwar kokuma tahanyar haram, toh wankan janaba yazama wajibi, koda kuwa maniyyi bai fitoba.

3. Jinin Haila koh Jinin Biki

Wankan janaba yana wajaba akan macen dake haila kokuma Jinin biki.

Yadda Ake Wankan Janaba

Sheikh jafar mahmud adam yayi bayani dalla dalla akan yadda ake wankan janaba awurin wani tafsir dayayi a maiduguri a shekara ta 2006.

Malam yayi bayanin cewa wankan janaba yana da siffofi guda biyu:

  • Siffatu Kamal – Siffa ta kamaala.
  • Siffatul ijza – Siffa wadda ta wadatar.

Yadda Ake Wankan Janaba a Siffa ta Kamala:

Idan kazo zakayi koh zakiyi wankan janaba, zaka ajiye ruwa a gabanka, bayan ka ajiye ruwa agabanka toh farkon abin da za ka fara yi shi ne:

1. Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gabanka.

Adai dai lokacin da zaka wanke gabanka, toh a lokacin za ka kulla niyya ta wankan Janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne. Idan ka wanke gabanka ma’ana kayi tsarki kenan.

2. Daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kakeyi a alwala ta sallah, toh hakan zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu, wanda wannan za ka kyale shi ba za kayi shi ba.

3. Bayan nan sai ka tsoma hannayenka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba, sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi ke kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, saboda gashin dan adam yakan bude musammam gashin sa na ka a lokacin fitar maniyyi, idan ka zuba ruwa a haka, yakan iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban.

4. Bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko ina a kanka.

5. Idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikinka da shi, kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu, kuma ka tabbatar ruwa ya taba ko ina.

6. To idan ka yi wannan, se ka kammala, abu na karshe, shine ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka ta hagu, wanda shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro tun gabanin wankan.

Wannan shine bayanin siffa ta kamala a wankan janaba.

Idan wankan Janaba ne haka za ka yi, in na Haila ne haka zakiyi, in ma wanka ne na Biki ne haka mace za ta yi.

Idan wankan Jumu’a ne ma haka za a yi, wankan Idi ma haka za ka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA.

Yadda Ake Wankan Janaba a Siffa data wadatar (Siffatul Ijzah).

Idan mutum zai yi wankan janaba akan siffa ta ‘Al ijza’ wadda ta wadatar ba sai ka yi alawa a cikin ta ba.

Kana zuwa ka yi niyyar yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko’ina, in ma wani kududdufi ne ko rami ko “swimming pool” sai ka yi tsalle ka fada a ciki, dama ka kulla niyyar ka kafin ka Shiga.

Daga ka fito abin da zakayi shi ne abubuwa guda biyu:

1. kurkurar baki da kuma

2. Shaka ruwa a hanci da fyacewa.

Shi kenan, kuma irin wannan wankan janaba din ya halatta ka yi sallah dashi.

Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka. Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fi ka kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika cikar kamala, kuma ya fika lada kasancewar ba a yi alwala ba ciki ba.

Muna rokon Allahu Yajikan malam jafar yakuma Kai Rahama a kabarinsa Dana iyayen mu baki daya.

Zaku iya ajiye tambayoyinku a comment section dake kasa, sannan kuyi sharing zuwa wasu groups domin yan’uwa su karu.

Allah yasa mudace, Ameen.

Karanta:ÂMalama Juwairiyya Maganin Sanyi