Tayi min kankanta COMPLETE hausa novel

Barka da zuwa wannan shafin namu na littafan Hausa novels inda muka kawo muku littafin Tayi min kankanta COMPLETE hausa novel.

Zahra surbajo ta rubuta kuma ta wallafah wannan littafin

Tayi min kankanta COMPLETE hausa novel

Tayi min kankanta Complete Hausa Novel
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 430kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author ZAHRA Surbajo
File format Txt
Published date 19 – 03 – 2023

 

Wasu Na Karatun: Kuskuren Baya Hausa Novel Complete

Kadan daga cikin Littafin Tayi min kankanta COMPLETE hausa novel

Page 1

Zahra’u ya kamata ki fito haka fa kizo ku wuce,tun ɗazu su hanne ke tsaye suna jiranki,bana son sakarcin banza fa”cewar wata dattijuya dake zaune kan kujerar zaman tsakar gida tana ɗaure nono a ledar siga.

Daga can cikin bukkar dake kusa da dattijuwar wacce aka kira da Zahra’u tace “Inna do Allah Do Annabijjo,ki barni in sa jambakina cikin kwanciyar hankali,ke bakisan in bakayi kwalliya ba ko kallonka ba’a yi?”

“aykin kawai,yo tun bara kike sa jambakin amma har yanzu ba mashinshini,se asarar kuɗin siya miki da nike yi”cewar inna daga wajen da take zaune.

Fitowa tayi daga cikin bukkar tana gyara ɗamarar da ta ɗaura a ƙugunta,ko ina a fuskarta kwallliyace irin ta fulani.

Laɓɓanta shafe cikin jan janbaki,yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyar ba.

“kede Inna kinada matsala,bakin ki be taɓa faɗin alkha’iri,se sharri,ni ɗoramin mu tafi”ta ƙarasa maganar cikin turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

Gammo ta ɗora sannan ta ɗora mata kwaryar nonon akanta,ta miƙa mata ledar viva da aka sa ludaya da ƙorai aciki,ta juya gun su Hanne dake tsaye zaman jiranta tayi murmushi kumatunta suka lotsa,siririyar hushiryarta ta bayyana atsakanin fararen haƙoranta masu kyan tsari,tace “na ɓata muku lokaci kuyi haƙuri,mu tafi kar mu sake ɓata wani lokacin”

Murmushi sukai mata,sannan suka rankaya suka fice bayan sunyiwa inna sallama.

Tafe suke suna hirar su ta yau da kullum,ɗaya daga cikinsu Me suna haule tace”wai duk ƙawancen nan namu muna aure inba riga ɗaya muke ba se ya ragu ko?”

Dariya Zahra’u tayi sannan tace,”Allah ya kyauta,ni aradu ko birnin sin naje aure bazan dena ƙawance daku ba,bare ma dukanmu muna ruga ɗaya ba inda zamu”

Hanne ce ta amshe zancen da cewa”ni Auran ma tsoro yake ban,kunga de Ma’u kamar abun arxiƙi Rabi’u ya Aureta amma ku dubi wulaƙancin da yake mata yanzu.

“shiyasa na shiga makaranta dan bazan yarda namiji yamin wulaƙanci ba,”cewar Zahra’u tana murmushi.

Da wannan hirar tasu suka ƙarasa fitowa daga cikin dajin falgore inda rugarsu take,suka miƙo tsawon titin zuwa inda barikin sojojin dake cikin dajin yake,sabida ankawo sababbin sojojin da ake ba training gurin acike yake da mutane kamar kasuwa,dan motocima in sun zo gurin da ƙyar suke wucewa sabida yawan sojojin.

Basu jima da zuwa ba kowa kayanta ya ƙare sabida ƙarancin abincin gurin,a hannu a hannu ake siyan duk wani abun ci na gurin.

gurin me saida burodi suka ƙarasa kowa ta sayi guda ɗaya sannan suka juya cike da farincikin sun sayi burodin da zasu ci yau agurin alibidin sunan Zina,wata ƙawarsu data haihu.

Karo suka ci da wani matashi sanye da wandon sojoji,hannunsa riƙe da bindiga,se riga tshits army green da hular sojoji,ba laifi kyakkyawane,raɓewa sukayi zasu wuce ta gefenshi yayi sauri yasha gabansu yace yana murmushi,

“don Allah kuyi haƙuri mu baƙi ne anan,kuma abinci mukeso mu ci,isowar mu kenan daga Abuja,amma mun rasa”

Harara Zahra’u ta galla masa sannan tace”amma dan baƙin hali ay kuna gani muka kawo tallan nono, in yunwar kukeji me ya hanaki siya?”

Murmushi yayi dan ya fahimci yarinyar akwai tsiwa,cikin taushin murya yace”Bamu lura bane ƙanwata,ayi haƙuri”

“to yanzu me kukeso muyi muku,tunda mude ba abinci bane bare ku cinyemu”cewar Zahra’u batare da tsoron komai ba,dan ita ba ƙaramin abu bane ke firgitata.

“in anan kuke don Allah ku taimaka mana, kuɗin cefane zamu baku ku dafo mana abincin ku kawo mana nida abokina,”

Shuru sukayi sannan hanne tace”gaskiya rigarmu da nisa nide bazan iya zuwa gida in dawo ba”

“yo inba wahalalle ba waye zeje gida yadawo nan”cewar haule.

“don Allah ku taimaka abokina yanada lalurar gyambom ciki be jure yunwa don Allah ku taimaka ku yi mana kamin yafara jin yunwa wallahi zamu biyaku ladan yi”cewar matashin kamar zeyi kuka.

Zahrau tsintar kanta tayi da tausayawa abokin nasa,sabida itama tana da lalurar gyambom cikin tasan azabar ziwon,dan haka tsintar kanta tayi da cewa

“kawo kuɗin,zan dafo muku,sede muna da nisa zaku iya jira?”

Da sauri matashin ya gyaɗa mata kai,sabida tun ɗazu yake neman wanda ze dafo musun amma be samu ba,ga abokin nashi shegen taurim kai shiba jure yunwa ba amma ko ze mutu baze ci abincin siyarwa ba,shiyasa duk yabi ya damu.

Hannu yasa a aljihu ya ɗebo kuɗin dashi kanshi besan adadinsu ba yabata,juya kuɗin take a hannunta tana mamaki,amma batace komai ba ta ɗauka da yawa suke so, dan haka ce mishi tayi”zan kawo ma insha Allahu ka tsaya a bakin titi de inda zan ganka da wuri”

Godiya yay mata sosai sannan yace”mu haɗu kawai anan,zefi sauƙi,sunana Capt Jameel Ahmad zan jiraki anan”

Bata ce komai ba suka juya suka wuce ita da ƙawayen nata,wanda gaba ɗaya haushinta sukeji,cikin fushi hanne tace.

“nufinki de bazaki gidan sunan ba ko?shiyasa kika amshi girkin gardawan da baki sani ba”

Batare da damuwar komai ba aranta tace”dan bakusan ciwon ulcer bane da kuma kun tausaya kun musu,nide zan musu sabida Allah”.tana kaiwa nan tai gaba ta ƙyalesu a baya.

Tayi min kankanta 2

Gudu-gudu sauri-sauri Zahra’u ke tafiya zuwa gida,dan azahar ta kusa,

Tana shiga gida bukkar innarta ta shiga da sallamarta.

“wai har kun siyar?”cewar inna bayan ta amsa sallamarta,

Murmushi Zahra’u tayi sannan tace”wallahi inna mun siyar,yanzu ma wasu sojoji ne,suka roƙeni in dafo musu abinci,yunwa sukeji gashi suna da me ulcer acikinsu,shine na dawo in musu”daga haka ta kwashe komai ta faɗa mata,gami da bata kuɗin.

Sosai inna ta tausaya musu sannan tace”Allah miki albarka Batulu na, daɗina dake akwai tausayi, maza zo kije ki cefano abinda yadace ayi sauri ayi musu”

Daga haka miƙewa sukayi suka fito tsakar gida,inna ta bata kuɗin cefanen ta tafi.

Kamin la’asar sun kammala komai,abinci lafiyayye bame cewa daga rugar aka girkoshi,domin,harda,cincin,dublan,duka masu jimawa basu lalace ba kasancewar can cikin garin falgoren Zahra’u tazo cefanen,shiyasa tasamu komai.kasancewarta ƴar makarantar gaba da primary,kuma ɓangaren sciece yasa ta iya komai,sabida food and nutrition da ake koya musu.

Ga kaji da zabbi da suka soya musu rabi da mangyaɗa,rabi kuma da manja sabida me ulcer shima yasamu yaci,suyar sosai tayi kyau.a ledoji ta juye sannan ta zuba abincin a kular abincin baffanta,

A babbar roba ta zuba komai sannan tayi gammo ta ɗauka,inna ta bata canjin dubu biyar daya rage tace ta mayar musu,amsa tayi sannan ta juya ta nufi barikin.

Kusan mintuna arbain ta kwashe tana tafiya kamin ta iso bakin titin,sannan ta ƙarasa gurin da sojojin ke tare.

Inda sukayi dashi zasu haɗu nan ta ƙarasa,ga mamakinta yana tsaye agurin yana jiranta,yana hangota ya taho da sauri ya tarbeta yana murmushi.

Kama mata kayan yayi ta sauke,sannan tace”kuyi haƙuri wallahi gidanmu da nisa ne shiyasa”

Murmushi yayi yace”Ko kaɗan baki buƙatar bamu haƙuri,mune yakamata muyi hakan,mungode sosai,Allah saka miki da alkhairi,”

Canjin ta miƙo masa tace “ga canjin ku inna tace in dawo dashi,kuma tace tanawa abokin naka me ulcer ya jiki dafatan Allah ya bashi lafiya”

Sosai wani jin daɗi ya bayyana a fuskarshi,aranshi ya yaba da tarbiyyarta,cikin murmushi yace”ki maidawa inna kuɗin kice mungode”

Fafur taƙi amsar kuɗin,duk yadda jameel yayi da ita ƙin amsa tayi dole ya maida kuɗin aljihunsa,

“gobe in munzo talla zan tafi da kwanukan”tace sanda take ƙoƙarin tsallaka titi domin ta koma gida.

Sallama sukayi ta tafi,jameel yabi bayanta da kallo yana yaba natsuwarta da hankalinta.

Duƙawa yayi ya ɗauki,robar abincin ya nufi tantin da suka haɗa na tempol sabida ruwa da rana,kamin ay musu izinin shiga cikin barikin.

Zaune yake daga ƙarshen tantin,yana latsa wayarshi,hannunshi ɗaya,riƙe da bindigarsa,

Farine sosai yana da ɗan faɗin fuska kyakkyawa ajin farko,sede ko kaɗan ba fara’a fuskarsa.

Sanda jameel ya shigo tantin,a yatsine ya ɗago kyawawan idanuwansa ya kalleshi sannan ya amsa sallamarsa.

Robar abincin ya ajiye akusa da shi sannan ya shiga ciro kayan dake ciki,

Buɗe ledar soyayyun kajin yayi,sosai yayi mamakin ganin harda wanda aka soya da manja.

Ƙamshin abincin ne,yasa ya ɗago kansa da sauri yana bin ledar da kallo,da sauri ya matso kusa da jameel,yana faɗin”kunyi waya da mummy ne?”ya tambaya cikin zaƙuwa.

 

“me ka gani”jameel ya tambaya.

“itace kawai take soyamin kaza da manja sabida ulcer ta,shiyasa nayi zargin kunyi wayane”

“ko kaɗan,wannan wasu nasamu suka dafo mana,daga cikin garin nan,ka matso kaci abinci kasan tunda mukazo baka ci abinci ba tun ɗazu hankalina be kwanta ba sabida baka ci abinci ba”

Tausayin jameel ɗinne yakamashi ganin yadda yadamu dashi fiye da kansa,yasan duk ƙoƙarinnan yayine domin shi.

Ba musu ya matso yasa hannu ya ɗauki cinyar kazar yasa abakinsa,daɗin daya gauraye bakinsa sosai yatafi dashi,zagewa yayi yaci abincin sosai dan wannan girkin ma yafi na mommynsa daɗi.

Bayan sun gama cin abincin,su cincin da dublan din duk acikin jakun kunansu suka saka,sabida taimakon gaggawa,abincin kuma rufe sauran sukayi,sabida dare.

Se a lokacin suka samu natsuwa,Jameel ne ya dubi abokin nasa yace cike da kulawa”Gaskiya Hammad yarinyar nan ta iya girki,ba me cewa ita ta girka,ji abinci don Allah sekace a birni”

Cikin rashin fahimta,Hammad ya kalleshi,yace”dama yarinyace ta dafo abincin?

“eh yarinya ce dan bata wuce sa’ar su surayya ba,ma’ana bazata wuce 14 to 15 years ba,nono suke siyarwa na roƙeta ta girko mana”

Sosai abun yaba Hammad mamaki dan shi de in ze iya tunowa ba ya jin ko gas surayya ta iya kunnawa bare ayi zancen dafa ruwan zafi,to taya yarinya sa’arta za’ace har tafi mummynsa iya girki,ta ya?

“Dan haka in munyi settling komai zan bita inga gidansu,dan mu dinga zuwa cin abincin can gidansu mudena sata wahalar kawo mana”jameel ya faɗi yana kallon Hammad ɗin.

“ba damuwa “Hammad ya faɗi yana nazarin zancen.

“innarta ma tace aymaka sannu gameda ulcer da take damunka “jameel ya faɗi yana murmushi dan yasan bazasu wanye lafiya ba.

A fusace Hammad ya dubeshi yace”Au kace bara kaje kayi da ciwon dake damuna,amma wallahi ka cuceni kuma ba inda zani wallahi bazan je gidan nasu ba”ya faɗi sanda ya miƙe ya fice daga tantin.

Surbajo for life

TAYI MIN ƘANƘANTA

Zahra Surbajo

don Allah masu cewa asa su agroup ɗinnan kuyi haƙuri ni bana adding,haka kuma bana tura novel private,iyakacina posting a group,kar ki buƙaci ɗaya daga ciki ban miki ba kiji haushi,pls

Tayi min kankanta 3

Har dare Hammad haushin Jameel yake ji,dan shi a duniya ba abinda ya tsana irin a faɗawa stranger yana da ciwon ulcer,aganinshi kallon mayunwaci za’a masa.

Haka suka ci abincin se cika yake yana batsewa.

Koda gari ya waye,basu wahala ba cincin sukai ta ci da dublan.

Wajen azahar Hammad yafara jin yunwa,duk yadda yaso ya daure ya kasa dole ya isa ga Jameel wanda shima tun ɗazu yake kallon hanya yanaso yaga ta ina zata ɓullo.

“ya kamata fa kasamo wasu yaran abasu kuɗin suje su girko mana abinci ni yunwa nakeji”hammad ya faɗi sanda ya isa ga Jameel.

karka damu nasan yarinyar jiya zata dawo,tabani tabbacin hakan,mu ɗan jirata kaɗan”Jameel ya bashi amsa cike da kulawa.

Hammad Juyawa yayi ya nufi cikim tantinsu,Bayan yaba Jameel ɗin wayarshi ya riƙe masa.kamar jira yana barin gurin Zahrau ta ƙaraso gun Jameel ɗauke da kwaryar nononta,ɗaya hannun kuma ledar abincin data dafo musu,shinkafa da wake dafadukan manja taji alayyahu da albasa se ƙamshi take.

Murmushi tayi tace”duk da baku buƙata ba amma na dafo muku wannan,sabida me ulcer nan”ta faɗi tana miƙa masa ledar da kular abincin take.

Da Sauri ya amsa yace”mungode sosai wallahi,shima yanzu yagama tambayarki,nace baku zoba tukunna”

Murmushi tayi batace komai ba,Wayar da Hammad ya miƙo masa ya riƙe masa ya ɗaga yasa camera yace”yakamata muyi hoton tarihi ko ƙanwata?”

Zahra’u murmushi tayi batace komai ba ya fara ɗaukarsu hotuna,tana dariya wani tana murmushi,har seda yagaji ya dena ɗaukarsu selfie ɗin.

Kwanikan jiya ya bata,dan dama suna ajiye agefenshi,sannan ya ɗauko kuɗi masu yawa ya bata yace”ki ajiye wannan agurinki ki dinga yo mana girkin,in sun ƙare ki sanar dani zan ƙara miki,sati uku zamuyi anan mu tafi”

Amsar ƙuɗin tayi tana murmushi,ta juya tabar gurin ta ƙarasa inda suke siyar da nonon.

Ɗaukar ledar Jameel yayi ya nufi gun Hammad,da hanzari,dan yasamu yaci abincin.

Ganin jameel da abincin sosai ran Hammad yayi masa daɗi,matsowa yayi kusa dashi yana murmushi duk fushin da yake ya huce,yace”ta zone yarinyar?”

“Kana baro gurin tazo wallahi,yarinyar akwai kirki ga sanin ya kamata,kaga yau tun kan musa tayi tayo mana”

“naga alamar hakan”Hammad yace sanda ya ciko cokali da abincin ya danna abakinsa.

Lumshe ido yayi yana tauna abincin gashide ba nama akasa ba amma daɗin abincin ya wuce inda yake tsammani.

Jameel na janshi da hira ko sauraronsa bayayi ya maida hankali kan abincin seda yaji yacika cikinsa tab sannan ya ajiye cokalin.

Kamar daga sama suka fara jiyo ƙarar harbe harbe da guje gujen mutane ana ihu.

A hankali suka fito daga tantin ga mamakinsu ankashe mutane da dama agurin musamman ƴan talla da suka zo.

Harbin ne yafara yo ɓangarensu,da gudu suka nufi bayan wani dutse,hankali atashe,Jameel a firgice ya kalli hammad yace”ƴar filanin nan data dafo mana abinci tana gurin can,bari inje in taimaka mata kar wani abu yasameta”

Yayi yunƙurin zuwa harbin ya yawaita dole ya tsaya,guri yayi guri domin tankokin yaƙi aka fito dasu daga cikin barikin aka fara ɓarin wuta tsakanin sojoji da Ƴan bindigar da suka kawo hari garin,dan tuni sun shiga cikin rigagen sun ƙona komai sun kashe mutane,shine suka dawo nan bakin titin.

A gigice Jameel yaja hannun Hammad suka ruga da gudu zuwa cikin jejin domin su samu mafaka,sede ƙarar da jameel ɗin ya kwalla ce tasa Hammad tsayawa ya waiwayo yaga me ya samu aminin nasa,

Wayyo Allah harbinsa akayi agadon baya,rungumeshi yayi suka faɗi tare,ya tallafoshi yana ƙarajin kiran sunanshi,”No!!!!!!!! Jameel !!!!!!!! wake up!!!!”!!”yana ihun jijjigashi,Jameel wanda idonsa ke shirin lumshewa a hankali yace”ka kula da ƴarfilanin nan Hammad”yana kaiwa nan yafara salati jini na fitowa ta bakinsa.

A gigice yake jijjigashi amma ina jikinshi ya riga ya saki.

Ihu Hammad yake iya ƙarfinsa yana jijjiga aminin nasa,yana kiran sunanshi,amma shuru,

Harbin da ake yowa ta ɓangarenshine yasa ya miƙe da gudu,Ɗauke da Aminin nasa a kafaɗa ya ƙara nausawa cikin jejin,zuciyarshi na masa zafi.

Karata: Tsintacciya COMPLETE hausa novel pdf

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top