Sakon so Episode 2 Hausa Novel by M Shakur
Sakon So Episode 2️: Tunda yashigo cikin estate dinsu yahango wani magidancin mutum tsaye agaban wani dankareren gida da sojoji guda uku ke tsaye wajen taredashi, kana ganin mutumin kasan zasuyi age mate saidai shi mutumin yafishi tsufa sosai dan ga furfura ko’ina akan fuskanshi,
dan ijiyan zuciya yasauke sannan yakarasa gaban gidan batare daya kashe motan ba yasaukar da glass din motan kasa hakan yasa sojojin wajen suka sassaramai Sir!
Gyadamusu kai yayi a natse batare daya amsasu ba sannan yasauke idanuwanshi kan mutumin daya taho wajen motan dasauri fuskanshi babu alamun rahama akai baiyi wata wataba babu gaisuwa ko sannu cikeda masifa yace
Alhaji Imrana nagaya maka karabun mini da d’ana kaki I agree cewa lokacin nan nagudu na barsu Kaika sashi a makaranta da sauransu yanzu I am back yarona don’t want anything to do with me, imagine ni mahaifin Arif ina masallacin nan amman ko kallo ban isheshi ba sabida kai sai rawan jiki yake yana binka kaman yaga sarki,
karabun mini da dana allow me to be his father” tunda yake maganan kallonshi yake saida batare da yanayi kokuma wani abu na fuskanshi ya chanza ba yagama tsaf sannan yace “nabarka lafiya Baban Arif” tareda maida glass din motan sama aka bude mishi gate yawuce yashiga cikin katafaren gidanshi yabar mutumin awaje yana nuna kanshi yace “ni zaka gwadama miskilanci”?
Duk maganganun dayake sojojin kallonshi suke so suke suje su bubbugeshi amman kallon da Oga kadai yamusu is kallon kar wanda ya kula bakona cikinku yagama duk abinda zaiyi yatafi.
Wajen jerin motocin dasunkai kusan 12 acikin gidan yayi karasawa yayi da motan yana tafiya very slow yay parking sannan yakashe motan yakai kusan 5min zaune a motan kaman bayaso yafito sannan yabude kofan ahankali yafito sannan yamaida kofan yarufe yajuya yafara tafiya yana dumfaran cikin gidan ma’aikatan cikin gidan dake aikace aikacen su na gaidashi da kai kawai yake amsa musu yakarasa gaban babban durmemen flat daya rak dake cikin gidan dakeda girman gaske yabude kofan ahankali yashiga wasu yan kananun yarana su biyar da dukansu bazasu wuce shekaru 3, 4, 5 hakaba suna tsalle tsalle suna ganinshi duk kowa ya natsu duk suka zauna akasa atare cikeda gwaranci irin na yara sukace
“Abee Assalamu Alaykum” maida kofan yayi sanan yajuyo yabi yaran da kallo dayar karaman murmushi daya bayyana akan fuskanshi a natse yace
“wa’alaykumus salam Children” sannan yashigo cikin katafaren falon dawani katon family picture frame ke bangon dake dauke dawata tsohuwa da akalla zatakai 70yrs sai shi yana tsaye agefenta daga yanayin yanda fuskanshi yake ahade zaka gane ko kadan bayason hoton sai wasu manyan mata dasuma sun manyanta masu kama dashi su uku,
saikuma wasu maza su biyu dakana gani zakasan kanninsu ne saikuma yara dayawa a frame din, zama yayi kan kujeran sannan yabi yaran da kallo daduk suke kallonshi sai yanzu yama tuna baitaho musu da komi ba this is so not like him saurin dayake yasa yamanta,
wannan karan dan murmushi kadan yayi sannan yamike musu hannu yace “kuzo nan” kaman jira suke dawani kalan gudu suka taho murmushi yayi anatse yace “zan dauki kowa one after the other okay” gyadamai kai duka sukayi babban cikinsu dake 5 yafara dauka yace “Muhammad” yaron ya kyalkyace da dariya sannan yadauki na biyun yace “Faisal” yadauki macen yace “Nana” sanan ya ijiyeta yadauki dayan macen yace “Miemie” sannan yadauki karaman dake 2yrs yace
“Anees…….” Shiru yayi sabida zafi dayaji ajikin yarinyar hakan yasa yakai hannunshi dasauri yataba goshinta jin dumi yasa yakalli Muhammad yace “call Aneesarh Mom” dasauri yaron yajuya yay kitchen, ko 1sec Muhammad baiyi da shiga kitchen ba wata Yar Babban mace tana kamadashi tafito da apron ajikinta dasaurinta tace “Yaya Imran kadawo” kafin yay magana wata yarinya Yar budurwa fara da akalla zatai 21yrs tafito daga kitchen din da gudunta tana wani kalan mugun murna dudda akwai Aneesarh ajikinshi saida tazo ta gefenshi tawani kalan rungumeshi tace “Abee Assalamu Alaykum” dan murmushi kadan yamata tareda daga kanshi yakalli fuskanta yace “wa’alaikumus salam Kausar, ina dan kwalinki”? Yay maganan yana kallon kanta dababu dan kwali tayi tsifa rabi tabar rabi, dan zaro idanu tayi sannan tajuya da gudu tai sama binta yayi da kallo sannan yadawo da hankalinshi kan kanwarshi yace “why is Aneesarh body hot”?
Kaman Maman zatai kuka tace “wlh babu yanda banyi da itaba takishan maganin Ya Imran” kallon fuskan Aneesarh yayi dake kan jikinshi daketa kallon fuskanshi sannan yakalleta yace “kawomin maganin” dasauri tai sama tana murmushi sosai bata taba ganin mutumin da yara ke bala’in so kuma suke tsoro kaman Ya Imran ba dazaran yashigo kowa zai natsu sannan kowa yayta murna suna kallonshi saukowa tayi da ibuprofen na yara a hannunta tazo har gabanshi ta tsaya ta bude maganin ta debamai a marfi 5ml tabashi tace
Allah sa tasha ni karma ta amayo makashi Ya Imran tabata maka jiki” karba yayi sannan yakalli Aneesarh dake kallonshi yadan mata murmushi ahankali yace “haaaaaammmm” yabude bakinshi kadan hakan yasa dasauri yarinyar tabude bakinta tace “haaaaa” samata maganin yayi abaki ahankali with so much care and love kaman yana handling Yar kwai dasauri yarinyar ta shanye murmushi yamata yace “good job Aneesarh” yay maganan tareda sakata ajikinshi tai lamo yana caressing nata sannan yadago kanshi yakalli mahaifiyarta dake kallonsu tana murmushi sosai yace “su Hajiya basu dawo daga gidan bikin ba”?
Gyadamai kai tayi tace “eh amman yanzun nan mukai waya suna hanya, harda Anty Binta itama dazu ta iso da mijinta” gyadamata kai yayi batare dayace komiba hakan yasa tace “nakawo maka tea ko coffee Yaya” girgiza mata kai yayi yace “no anjima” gyadamai kai tayi sannan tajuya tawuce kitchen dan karasa girkin daidai nan itama Kausar ta sauko tana sanye da hula tana kallon mahaifin nata tace “Abee nasaka” kallonta yayi sannan ya Gyadamata kai tawuce kitchen tana murna Maman Aneesarh dake sauke tukunya daga kan wuta tace “mehaka”?
Dariya tayi takaraso kusada ita tace “murna nake Abee yadawo kinga zai tayani karasa tsifan” hararanta Maman Aneesarh tayi tace “ke wai bakisan kin girma bako Kausar kullum Babanki zai fita yaje aiki yadawo inhar yashigo gidan nan saikin sakashi yamiki naki aikin bakiji abinda Hajiya tagaya miki bako kina wahalar mata da dand’a” turobaki tayi ashagwabe tace “nikuma ai Babanane” yanda tayi abinma dariya yabama Maman Aneesarh tace “Allah ya shiryeki ina Abdallah baitashi daga lectures din bane”? Dasauri Kausar tace “4-6 yakedashi aini bazan iya Medicine ba ko kadan wlh wahalallen course” ahaka suka cigaba da hiransu suna girkin gwanin ban sha’awa.
Yana rikeda Aneesarh a hannunshi yana caressing nata ahaka bacci yay awon gaba da ita, haka yake inhar zai dauki yara su dan jima awajenshi duk rigiman yaro saiyayi bacci, tashi yayi yana rungume da ita a kirjinshi har gaban kitchen din yaje batare daya shiga cikiba yace “Kausar” dasauri Kausar dake kwashe shinkafa a flask tace “Na’am Abee” tasaki spoon din tajuya tafice daga kitchen din dagudu ganin Abee agaban kitchen din rungume da Aneesarh datai bacci yasa tace “Abee gani” ahankali yace “jeki kawo zani ki goyata” gyadamai kai tayi dasauri tace “to” tabi tagefenshi tai bene tafara hawa dagudu anatse yace “what did Abee said about running”? Daina gudun tayi dasauri tai piki piki da ido tace “no running” tana tafiya tai sama bata jimaba tadauko zani tazo har gaban kitchen din ta duka gabanshi tace “Abee samin ita” ahankali yazare ta daga kirjinshi sannan yasamata ita abaya ahankali tareda karban zanin yadaura mata akai itakuma tamike tana gyara zanin tace “Abee goyon yayi”? Ahankali yana kallonsu yace “eh” sannan yajuya yayi stairs yawuce sama itakuma Kausar tawuce tashiga kitchen din suka cigaba da aiki.
Babban sama ne gidan akalla akwai dakuna dakuna sunkai kusan ashirin ko da biyar dan irin babban family house din nan ne, asaman ma wani kebentaccen bangare yawuce da kofanshi ke cikin lungu sannan yabude kofan dakin ahankali yashiga da sallama ko kadan dakin babu wani hayaniya ko tarkace aciki lafiyayyen gadone aciki dake shimfide da white sheet ga white bargo akai an gyarashi tsaf saikuma study da akayi agefe daya da shelf’s na bango dake cike da littatafi sai desktop akan table da kujera saikuma wasu dakuna biyu wanda day bathroom ne daya kuma closet,
bathroom nashi yashiga wanka yayi sannan yafito yashiga closet ta shirya cikin wata faran jallabiya mai haske agoge kar yana wani kalan kamshi yasaka wani farin hula kwankwasa kaji hadisi din nan gemunshi na kyalli fuskanshi na annuri ga tabon salla ijiye wayanshi yayi akan gado sannan tazura wasu flat takalma na gida yafito tun kafin yakai wajen stairs yakejin hayaniyan su muryan Hajiya haryakai stairs yafara sauka yanabin kowa na falon da kallo.
Wata har tsohuwar mata ce kan doguwan kujera tana sanye dawata atampa mai kyau anmata dinkin bubu da zani irin dinki tsofaffi dai kana ganin matan kasan ta kwan biyu aduniya dan akalla zatai 70yrs, saikuma wata mata dake zaune akan lallausan carpet akasa tana sanye da lace na alfarma tana kasa su dibla da alkaki da nakiya a babban tray yaran duk sun zagayeta kowa na Mama bani nawa, ga Maman Aneesar dakuma da Kausar suma kowa na jiran nashi,
ga wasu manyan mata biyu suma kana ganinsu kasan da mai rabon dasu duka yan uwa ne Zainab da Sajida saikuma wasu maza dasuka zazzauna kan kujera suna danne dannen waya kowannensu na sanye da shadda, yanda yake tafiya ko kadan bazakaji karan sahun tafiyanshi ba amman kamshin turarenshi daya fara isowa falon yasa jikake falon yay tsit kowa yadago kanshi yakalli stairs Anty Binta dake kasan su alkakin ne tai wani kalan murmushi tace “Yaya Imran” dan murmushi kadan yayi anatse yace “Fatima ina mijinki”?
Murmushi tamai tace “yaje gidansu anjima zaizo” gayadamata kai yayi yakalli maza biyun dasuke azaune dazu daduk sun tashi tsaye kowa kanshi akasa anatse sukace “Ya Imran ina wuni” gyadamusu kai yayi yace “mutafi masallaci” sannan yajuyo da kanshi yakalli mahaifiyarshi da tunda yafito shi take kallo ahankali yace “Hajiya barka da dawowa” ahankali tace “Imrana aiko su Umman Arif sunce amaka godiya sosai sunyi murna” Anty Binta tace “eh wlh, musamman aka bamu Leda cike dasu cincin da alkaki da nakiya da nama akace mu kawo maka, Sajida ina yake nashi”? Dasauri Sajida tashiga kokarin bude wani jakan hannunta dan yatsine fuska yayi yace “baranci ba” Hajiya tace “batun dazu nagaya muku Imrana bayacin duk ire iren shirmen nan ba saidai su Ibro da Hamza kubama su Ibro wannan kusai kuraba wannan” tai maganan tana nuna kannenshi dasukai gaba sannan tace “wai haryanzu jama’a jikana Abdallah bai dawo daga boko ba”
Anty Binta dake bama yara kasonsu tace “Hajiya nakirashi yana hanya” wucewa yayi yafice abinshi hakan yasa Hajiya itama tamike ahankali tace “kuwuce kowa yaje yay salla” karasa bama yaran nasu tayi itama Kausar ta karbi nata tawuce daki ta ijiyema su Abdallah da Ibro da Hamza nasu.
KARANTA:Sakon so Episode 1 Hausa Novel by M Shakur