Malama Juwairiyya Maganin Sanyi

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku malama juwairiyya maganin sanyi wanda zaku anfana matuka.

Malama Juwairiyya Maganin Sanyi

Ga bayanin akan malama juwairiyya maganin sanyi: Yanda za a Magance kowane irin ciwon sanyi tayin amfani da Garin Tafarnuwa da Nono ko Madarar Ruwa.

Ga masu fama da ciwon sanyi kowanne iri ne insha Allah in suka bi wannan hanya zasu samu sauki, ko masu yawan tari da mura da ciwon gabobi da rikewar baya da kwankwaso da kaikayin jiki dadai sauran illolin da sanyi ke haifar wa.

Abubuwan da za a nema sune kamar haka:

1. Garin Tafarnuwa

2.Nono/madara ta ruwa)

Yadda za a hada Maganin shine:

Za a samu garin Tafarnuwa mai kyau sai a debi chokali daya a zuba a nono rabin kofi a juya asha da safe haka ma za ayi da yamma, wato sau biyu a rana.

Insha Allah indai an samu garin mai kyau akai kamar na sati 2 za aga Nasara sosai cikin Yaddar Allah.

Wasu Na Karatun:ÂLallen Gargajiya Photos, Jan Lalle Style & Bakin Lalle Style 2023

Maganin Infection

Waɗannan itatuwan amfani da su yana warkar da zubar ruwan infection da ma kashe infection ɗin baki ɗaya, infection cuta ne wanda a ke saurin ɗauka da kuma saurin rabuwa da shi in mutum ya san itatuwan da suke da properties da su ke kashe infection, kuma ya cire ƙiwiya ya rungume su.

In ki ka yi haka infection sai dai ki ji labarinsa a maƙota, Sadeeya tana son ki gyara, tana son ki zama gangariya, sai kin kashe infection za ki rabu da buɗewa, sai kin kashe infection mijin ki zai samu abun da ya kamata a ce yana samu daga gare ki my sister.

Duk abun da na faÉ—i ana samu a kasuwa ki nema ki fita a jirgin ban sani ba a ina zan samu.

1. Shan yoghurt wanda ba yi da sugar a cikinsa mai dauke da Lactic acid a ingredient É—in sa, ki sha kuma in za ki kwanta ki É—iba ki sanya a cikin al’aurarki ki kwana da shi yana kashe infection ta ciki da waje da tsayar da zubar ruwa.

2. Hulba yana mutuƙar kashe infection da hana zuban ruwa, shan sa a ruwan zafi da zuma, ko ɗiban garin a ha HBɗiye da ruwa ko yoghurt yana mutuƙar kashe infection. Haka a jiƙa da ruwa na minti talatin ko a dafa a rinka tsarki ko zama da shi sau biyu a rana yana kashe infection na gaske.

3. Tafarnuwa shugaba kuma É—aya daga cikin manya manyan maganin infection, in kina kayan infection kuma baki amfani da tafarnuwa za ki ci wuyan gaske.

Ki rinƙa haɗiyan tafarnuwa ko da kwaya ɗaya ne idan kin tashi da safe, ko ki rinƙa haɗiya tare da yoghurt ɗin da na yi bayani a farko.

Idan wurin ya ishe ki da ƙaiƙayi da ɗashewa ki ɗan daka ki yi mixing da coconut oil ko zaitun ki shafa idan abun da ki ke ji ya tafi ki dakatar.

Za ki iya shan Man tafarnuwa da shafa shi a ƙasan ki domin kashe infection, ki rinƙa yin zallan miyansa da ɗan tarugu kina ci a abinci in ba za ki iya amfani da ɗanye ba.

4. Apple Cider Vinegar wato ruwan khal yana kashe infection da tightening gaban mace, a dafa ruwa a surka a zuba kamar cokali biyu babba a zauna a ciki na minti 10, ko a rinƙa kama ruwa sau biyu ko uku a rana, sannan a rinƙa shan sa a ruwan zafi ko lipton.

5. Ganyen raihan wato basil yana tsayar da zuban ruwa da ma kashe infection, idan babu ɗanyen sai garin a kwaɓa da zuma ko madara ana shan babban cokali sau biyu a rana infection zai tafi.

6. Ganyen gwaiba maganin infection ne, ki dafa shi ki na sha sau uku a rana zai tsayar da zuban ruwa ya kuma kashe infection.

7. Ganyen rumman yana warkar da infection da tsayar da zuban ruwa mai wari da ƙarni, in an samu fruit din a sha, in ba a samu ba a nemi ganyen a sha da ruwa ko madara kullum da safe kafin breakfast.

8. Cin ayaba biyu kullum da safe zai taimaka wajen tsayar da ruwan infection, za ki iya niƙa shi tare da zuma cokali biyu ki sha zai yi har da maganin mata.

9. Neem wato dalbejiya maganin infection ne na haƙiƙa, ki yi garin sa ki sha tea spoon safe da yamma a cikin madara, ko kuma ki daka danyen sa ki dafa da ruwa na minti goma in ya huce ki rinƙa kama ruwa da shi safe da yamma har sai kin daina jin ƙaiƙayi kuma zuban ruwan ya tsaya.

Haka nan in akwai ƙuraje sosai ki jajjaga ki zuba coconut oil ko zaitun in babu ki ɗebi zallan sa ki shafa a dukkanin wurin da kuraje suka feso na minti 30 sai ki wanke. Ki siyo oil ɗin ki rinƙa shafawa a gabanki in da ki ke jin ciwo da ƙaiƙayi, haka nan za ki iya shan tea spoon na man safe da yamma.

10. Turmeric wato kurkum yana kashe infection, ki rinƙa cin sa a abinci ko ki samu madara ki dan dafa kadan ki zuba tea spoon na shi ki sha rabin kofi safe da yamma zai mutu, zai hana wannan zuban ruwan mai wari.

11. Aswakin mata ko Aswakin zaki yana kashe infection da tsayar da discharge, ki dafa shi har sai ruwan ya canza kala ki sha rabin kofi safe da yamma, ko rinka shan tea spoon na garin safe da yamma da madara.

12. Man kwakwa mai kyau pure one yana kashe infection da hana duk wani matsala a ƙasan ki, ki rinka samun auduga kina goge wurin da shi safe da yamma kuma ki ɗan sa a ciki zai kashe infection ya rage zuban ruwa.

13. Malmoh maganin infection ne, yana wanko duk wani ruwan da infection ke fitarwa a jiki, yana kuma gyara vaginan mace, ki dafa shi ki sha kuma ki rinƙa kama ruwa ko zama a ciki.

14. Green tea yana kashe infection na haƙiƙa da cutuka masu yawa, ki siyo green tea ki rinka shansa ko da zafi ko da sanyi duk ba damuwa, ka da ki saka sugar sai zuma.

15. Tazargade maganin infection ne na haƙiƙa, yana kashe infection, tsayar da zuban ruwa da duk wani matsalar da suka shafi ƙasan ki, ki tafasa kina sha safe da yamma har sai ciwon ya tafi.

16. Aloe vera maganin infection ne sosai, domin kashe infection da tsayar da discharge a cire abun cikin a É—an jajjaga a zuba ruwa ana shan kofi É—aya da safe da yamma, kuma a rinka inserting gel din a cikin al’aura zai kashe kuraje, hana Ć™aiĆ™ayi, É—ashewa da budewa.

17. Babunaj da hulba suna kashe infection a dafa kaÉ—an a zuba zuma a sha zai kashe infection.

18. Bagaruwan mata yana kashe infection a dafa shi tare da tafarnuwa da kanunfari a zauna ciki ko a kama ruwa zai kashe shi ya gyara ƙamshin wurin.

19. Alum yana kashe infection, a dafa ɗan ɓangale ana kama ruwa da shi yana rage buɗewa da kashe ƙuraje, ƙaiƙayi da ɗashewa.

20. Lalle yana kashe infection sosai, rage budewa da wari. A dafa shi tare da kanunfari a zuba musk, tafarnuwa, da bagaruwan mata ana zama a ciki ko tsarki.

21. A samo ganyen magarya a dafa da lalle a na zama ko tsarki infection zai mutu ko ya ragu.

22. Shammar fennel kenan yana kashe infection in ana shan tea sa ko a daka a sha da madara.

Sai koyon tsafta, gyara, da canza way of life ɗinki, in zaki shekara amfani da maganin infection muddin baki daina abubuwan da suke ƙaro bacterian ba za ki rabu da su ba. Allah Ya sa mu dace.

Ban san adadin magungunan infection waɗanda ki ke da su a cikin gidan ki ba, bana son ki da kashe kuɗi mace ta gari, bana son ki da wari, ƙarni da zuma ruwa, ki shigo jirgina mu haɗu mu kashe infection ya tafi ya bar jikin mata baki ďaya.

Karanta: ÂMaganin Girman Nono Na Shafawa

Maganin Sanyin Mara Mai Tsanani (Infection ) Da Wankin Mara.

Ka daure ka tura zuwa sauran yan uwa domin su amfana baki daya.

Wannan magani yana da matukar muhimmanci ga maza ko mata domin yana magance matsaloli da dama a cikin jikin dam adam zuwa marar sa.

Kadan daga cikin aikin sa.

1. Magance sanyin mata
2. Magance matsalar ciwoara
3. Magance matsalar zafin fitsari ko wahalar yin sa.
4. Yana wanke mahaifa ma mace.
5. Yana wanke mara
6. Yana karawa mata niima.
7. Yana kara karfin Namiji.

Abinda zaa nema kuwa shine

1. Citta danya
2. Kurkum
3. Lemon tsami
4. Kaninfari

Kowanne zaa same shi a kasuwa basa da wahalar samu guda daya ne wasu ke basu wahala wajen nema wato(kurkum) gashi nan photon sa zaku ganshi kamar citta amma shi yalo ne,kuma ana samun a wajen masu saita citta.

Zaa samu citta mai yatsu guda 1 babba,kurkuma guda 2 lemon tsami 1 kaninfari chokali 1 ruwa kofi 4,sai a hada a tafasa sosai idan ya wuce a rika shan karamin kofi safe daya yamma.

Ragowar zuwa washe gari a karasa shan sa,idan ya kare a sake hada wani,zaa sha na tsawon sati biyu.

Allah yasa a dace.

Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.