Maganin Girman Nono Na Shafawa

Barka da zuwa shafin mu na gyaranjijki, inda ayau muka kawo muku maganin girman nono na shafawa wanda zai sakasu girma kuma su mike tsaye kaman budurwa.

Maganin Girman Nono Na Shafawa

Idan baku mantaba munyi muku alkawarin zamu kawo muku bayani akan yadda zaku magance zubewar nono masamman awajen mata waenda suke kasada shekaru 39.

Saboda mahimmancin gyaran jiki awajen mata masamman ma gyaran nono, munkawo muku bayanai akan yanayin gyaran nono, aciki mun ambaci cewa gyaran nono yakasu kashi uku:

1- Nafarko shine karin girman nono.

2 – Nabiyu shine rage girman nono

3 – Na’uku shine mikar da nono.

Munyi bayani akan nafarko yau kuma zamuyi bayani akan na ukun wanda shine yadda za’a magance matsalar zubewar nono awaje mata masu karancin she karu, har yanzu sai abimu bashin nabiyun zuwa wani lokaci akusa.

Hakikanin gaskiya kowace mace tanaso taga tanada tsayayyen nono tsawon rayuwanta amma kash.. Saide hakan ba maiyuwa bane, sabida zubewar nono adabi’ance yana faruwa tareda tafiyan shekaru.

kamar yadda aka sani duk lokacinda mace takai shekaru arba’in to gaskiya babu abinda zaihana nononta zubewa, saide matsalan ana iya samun dayawa mata wanda basukai wannan shekarunba kuma nononsu yazube.

Maganin Girman Nono Na Shafawa

Abubuwanda yake janyo zubewar nono kamar

sannan yana daga cikin abubuwanda yake janyo zubewar nono kamar:

1 – shayarwa.

2 – Daukan ciki.

3 – Yankewar jinin haila gabadaya.

4 – Ramewa cikin dan kankanin lokaci.

5 – Kiba.

6 – Wasu cututtuka kamar cancer dasauransu.

Maganin mikar da nono

Atakaice zamu fadi hanyoyi guda uku na mikarda nono batareda shan wahala ko kashe kudiba, nafarko:

1- Asamu kankara ashafa ajikin nonuwan duka biyu, ake shafawa ahankali har tashafa ako’ina har natsawon kamar minti biyu, za’a maimaita hakan na tsawon wasu kwanaki, kankara yanada tasiri sosai wajen matse nono da hanashi zubewa, amma kada yawuce minti uku tana shafawa daga bisani sai tasamu bra dedenta tasaka.

2- Nabiyu kuwa shine man zaitun, dayawa yan’uwa mata suna tareda man zaitun amma suna neman maganin zubewar nono, to wallahi kinbar magani mai mahimmanci sosai, anaso ki milke nononki daman zaitun kullum safe dayamma kishafa da hankali sannan atake kisaka bra wanda yadace dake. Za’a maimaita haka nawasu kwanaki, kuma za’a iya amfani da zaitu Lawz ko jojoba oil amadadin man zaitun.

3- Na’uku za’a iya hada neem oil tareda garin ruman cokali daya agarwaya wannan hadin sai adaura akan garwashi yadanyi zafi kadan sai asauke abarshi yahuce, daga bisani sai ake shafawa nonon sau biyu ayini zuwa wasu kwanaki kadan kuma wannan hadin yanada tasiri sosai.

Za’a iya amfanida kowanne daga cikin waennan hanya guda uku kuma kowanne yanada tasiri insha Allah.

KARANTA:ÂMalama Juwairiyya Maganin Sanyi