Kyawuna Jarabta ta Hausa Novel

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin kyawuna jarabta ta hausa novel complete.

Kyawuna Jarabta ta

Tudun Yola, Kano! Baban Anguwace kuma sabuwa dan babu mutane haka sosai a anguwan, saidai irinsu uncompleted building da ake kan ginawa dakuma sababbin gidaje da ba’a dade da tarewa cikiba.

Baban gidane dayasha fenti milk color, kana ganin ginin gidan kaga ginin irin family house dinan, tsakar gidan mai bala’in fadi, ga katuwar bishiyan mangwaro a tsakar gidan datai y’ay’a sosai dudda basu nunaba, flat biyune agidan wani babban dankareren flat saikuma wani karamin flat mai kamada boys quarters agefenshi, gidan kana ganinshi kasan bawani gidan mai bala’in kudi bane gidan rufin asiri ne dai namai karfi daidai, motoci biyune parke atsakar gidan wata bus mai kyan gaske milk color saikuma mota sienna ash da mai gadi ke wankewa ga dukkan alamu motar maigida ne sabida yanda ya kuke yana wanketa yanabin wakan sangaya dake tashi a karamin radio daya ijiye kan plastic chair.

Bude kofar karamin flat din dake kusada babban flat din akayi, wani Matashi ne baki dogo baida jiki sosai yana sanye da jallabiya brown hannunshi rikeda makullin mota yafito, takalmi yasaka sanan yasauko daga matattakalan bakin kofarsu yadumfaro babban flat din, da sallama yabude kofa ya shiga ciki. Babban falo dakeda girman gaske, wani Babban Magidanci ne zaune akan kujera akalla zaiyi 60years kokuma 59, kana ganinshi kaga mai gidan, bakine yanada jiki, hannunshi rikeda jarida dayake budewa yana karantawa.

gefenshi kuma wata Mata ce mai kiba Hajiya Balaraba akalla zatai 40yrs tasaka wani hadadden lace tana kurban shayi a cup, saiga yara dasuke zazzaune akasan carpet suna breakfast kowanne nashan tea da bread da soyayyan egg dinshi, Mata uku ne a tsakar falon da maza biyu wanda duk kasansu daya, Amal that is 14, sai Asiya 13yrs, sai Aneela dakenan 11, Mazan kuma Muhammad dakenan 11 sai Mudasir wanda shine autan gidan 6yrs, gabaki dayan yaran kana ganinsu kaga mahaifinsu tundaga bakin fatar da jikin dan dukansu tuluka tuluka dasu very fat gwanin ban sha’awa kana ganinsu kasan sunacin lafiyayyen abinci, dukansu suna sanyeda uniform din makaranta da alamu hadda zasu danyau sunday.

Kitchen aka bude, wata black beauty Matace dan itama ba yarinya bace akalla zatai 38yrs tafito tana sanyeda doguwan rigan atampa mai kyau da akama stonework tana rikeda tray dawasu hadaddun kwanuka ke kai, hada ido tayi da wanda ya shigo dakin dukbasu luradashi ba yasa tace “this children zasusa kayi latti for your program Ya Hamad” kiran sunan shi datayi yasa duka yaran dakowama na falo yadagokai ya kallai, atare duka yaran suka gaidashi “Ya Hamad good morning” batare daya amsasu ba yakarasa shiga falon har gaban Abba yakarasa sanan yazauna agefenshi yace “ina kwana Abba” sanan yakalli matar dake gefenshi yace “Ina kwana Mum” daidai lokacin dayan matar taja coffee table zuwa gaban mijin nasu ta dauramai tray akai tace “your food is ready Daddy Hamad” jaridan ya linke tareda mikamata, karba tayi dayan matan tadauke kai Abba kuma yatura hannu a aljihun sanan yaciro wasu kudi yamikama Hamad yace “inka kaisu kabiya musu kudin makaranta” sanan yajuya yakalli matar dake gefenshi yace “me yaran nan sukeyi asama har yanzu basusan zasu makaranta bane”? dasauri tace “kumafa su tuntuni sukai break, Nanaa, Hawwa” daga chan sama aka amsa, wasu yan mata manya masu jiki guda biyune suka sauko daga stairs, yaran zaka dauka yan biyu ne dan suna kama, irin kama na jini dinnan, Nana itace Babba 26yrs take tana final year a BUK tana karanta Mass Com, sai Hawwa 24yrs tana 300level tana karanta international relation itama a Ado Bayero, Hawwa na kama da Hamad sosai, dukansu suna sanyeda lemon green hijabi na haddan, dukansu ransu abace yake dan sun tsani zuwa hadda suna uni amman suna wani zuwa hadda shikuma Babansu yanuna babu wacce ta isa tabar hadda cikinsu kodako PHD sukeyi, tashi duka yaran sukayi sukama iyayensu bye suka fice, sanan Ya Hamad din yatashi yace “bari nakaisu Abba” gyadamai kai kawai yayi dan haka Babansu yake baifiye son magana ba, sanan yawuce yafice.

Kaman ance tadaga kanta sama taga gittawan mutum dasauri an bude kofa anshige daki batare da an bari sun hada ido da Mami ba.

Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya dudda bataga fuskanba but ko amafarki aka tadata tasan waye.

Duk suna zaune afalon harya gamacin dumamen tuwon yadauki ruwa yasha, Dan gyaran murya matan dake zaune kusada shi tayi Mum tace “Alhaji nace bari namaka tuni, kaga duka duka bikin Nana bayan Babban salla da sati uku ne, gashi lokaci nata matsowa yanzu baifi wata daya bikin ba, nasan dama kariga kabada kudin kayan daki, cha kayi daman wanan satin zakaban kudin kayan kitchen, kaga idan kabani nida Zainab saimu shiga kasuwa yau muyo siyayyan koya kika gani Zainab”?

Mum tama Mami dake zaune tana sauraransu magana, gyadamata kai tayi sanan tace “eh hakane Abban Hamad” ruwa yadauka a cup yakara kaiwa baki yasha sanan ya ijiye cup din, hannu yasa a aljihu yaciro bandir din yan dubu daya guda biyu yabata yace “kinemi wata kijeda ita kasuwa, Zainab bazata iya zuwa ba itakeda girki, kuma yau lahadi ina gida” yana fadin haka yatashi yawuce sama duk suka bishi da kallo, saida taga yashiga dakinshi sanan tabata rai tace “Alhaji Alhaji bantaba ganin kafaffen mutum irin shiba wlh” tashi tayi batare data kalli Mami ba tai stairs tabude bangaren ta tashige dan saman bangare biyune nata dana Zainab saikuma dakunan yaransu guda uku, na maza kanana dana mata kanana saikuma na yan matan suma dakinsu daban.

Kyawuna Jarabta ta Complete

Novel Title Kyawuna Jarabta ta Hausa Novel
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 530kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author M shakur
File format PDF
Published date 09 – 03– 2023

 

Download Novel

Also Read: Uwa Uwace Hausa Novel By Batul Mamman

TAGS:kyawuna jarabta ta complete, kyawuna jarabta ta 64, kyawuna jarabta ta part 2, kyawuna jarabta ta 80,kyawuna jarabta ta 33, kyawuna jarabta ta episode 50, kyawuna jarabta ta 90, kyawuna jarabta ta 55, kyawuna jarabta ta episode 34, kyawuna jarabta ta 35, kyawuna jarabta ta the end,kyawuna jarabta ta book 2, kyawuna jarabta ta by m shakur, kyawuna jarabta ta book 3, kyawuna jarabta ta complete hausa novels, kyawuna jarabta ta chapter 1, kyawuna jarabta ta complete document, kyawuna jarabta ta littafi na daya, kyawuna jarabta ta end, kyawuna jarabta ta episode 46, kyawuna jarabta ta facebook,kyawuna jarabta ta hausa novel, kyawuna jarabta ta hausa novel page 1, kyawuna jarabta ta hausa novel page 50, kyawuna jarabta ta last page, littafin kyawuna jarabta ta, kyawuna jarabta ta hausa novel by m shakur, kyawuna jarabta ta novel