Barka da zuwa shafin littafan hausa novels, inda muka kawo muku karshen wahala hausa novel. Zaku iya karantawa dakuma sauke wannan littafin izuwa wayoyinku.
Karshen Wahala Hausa Novel
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
GODIYA
Godiya ga Allah SWA da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin nawa tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad SAW.
JAN HANKALI
Wannan littafin banyi shi don wani ba ko wata nayi shine don fadakarwanishadantar wa don hka a dauki abu mai amfani a bar mara amfani abin da yake kuskure Allah ya yafe minAllah yabamu ikon aikata dai dai a rayuwar mu ameeen_
ZUWA GA MASOYA NA
_godiya mai yawa a gare ku masoya nanima ina kaunar ku_
BAZAN MANTA DA KE BA
_my cwt Sadeey S Adam saNaz Deeyah da irin kwarin gwiwar da kike bani da soyayyar da kike nuna min don Adalilin son da kike nuna min na kai hka Allah ya bar mu tare_
pg 1
Yanayin unguwar irin unguwar masu hannu da shuni ce gwamna road a garin kdfamily din gdn gaba daya suna xaune a kayataccen falon su hira sosae suke da kagan su kasan happy family ne
Alhaji saeed haruna kenan da matar shi hajia maimuna sai yaran su safah itace babba sai nauwarah da karamin su saleemsu kadai Allah ya basu don sun ma fitar da ran sake haihuwa tun da saleem ya kai 7yrs da haihuwa suna matukar kaunar yayan su sosae ana cikin hira caraf nauwarah tayi magana cikin shagwaba take cewa
_Abba gaskia ina son idan na kammala secondary schl malaysia nake son ka sama min university_
Dariya abban yayi irin ta manya sannan yace
_nauwarah yar gidan Abba kada Ki damu Insha Allah xan cika miki wannan burin ke dai Allah yasa muna raye ki kwantar da hankali ki_
Cikin tsananin murna tace
_Ameeen my abba na_
Har ta bude baki xata sake magana safah ta watsa mata harara kamar idon ta ya fado tace
_tabbb Lallai yarinyar ae yanda nayi karatu a 9ja ke ma hka xakayi ba inda xaki je_
Turo baki tayi cike da shagwaba tace _uhm kaji aunty safah da wani xance kuma bayan ynx agaban Ki abba ya amince min koh abb_
_kwarai da gaske nauwarah ta haske mai kyau hasken idaniya ta da ixinin Allah xaki je ke dai ki dage da karatu kmr yanda na san ki_
Wani tsalle ta buga tana ihun murna yayin da safah ta xumburi baki cike da haushi tace
_dallah malama kin dame mu da ihu idan baki shiru ba ynx na tashi na bubbuge bakin ki_
Murguda mata dan karamin bakin ta tayi cike da tsiwa tace
_kaji mu da aunty safah nan ina ruwan ki da ihu ba Naga dai murna nake_
Axuciye safah ta tashi tayo kanta aikuwa da gudu ta buya a bayan ammin ta tana mata gwalo abba da saleem da ammi dariya kawai suke yi musu hannu tasa xata fisgo ta da sauri ammi ta tare tana cewa
_aa safah yi hakuri ki kyale ta kinsan yarinya ce kuma naga ae murna take_
_amma dai ammi Kina kallo gwalo take yi min_
Da sauri ammi ta juya bayan ta ae kuwa taga nauwarah gwalo take mata cikin fada ammi tace
_bana son hka nauwarah baki ga yayar Ki bace ji nake daxu kika gama bibbige min saleem don ya taba miki phone din ki_
_tohh ammi na dai na yi mata_
Ta fada kamar xata fashe da kuka murmishin mugun ta safah ta saki tare da cewa
_yarinya xaki xo ki same ni ne_
Idon ammi ta faka ta Murguda mata baki yanda take Murguda bakin da ka gani kasan ta riga ta saba da hkan
Ko _10 mints_ baa yi ba na hango nauwarah kusa da safah tana wani marairaice fuska tare da langabe kai alamar tana son wani abu safah tana kallon ta ta gefen ido kamar xata tuntsire da dariya hka take ji dakyar ta iya danne dariyar bata kula ta ba ta Kalli inda saleem yake tace
_saleem dauko min maltina a frige mai saukin sanyi_
Ae Kafin ta rufe bakin ta da gudu nauwarah ta nufi frige ta dauko mata maltina ta Miko mata hararar ta safah tayi tare da cewa
_na ambaci sunan ki ne ae Naga saleem na aika_
Murguda mata baki tayi cikin kuluwa safah tace _au Murguda min baki kike_
Da sauri nauwarah ta dafe bakin ta cikin marairaicewa tace
_hba aunty safah na mance ne Im so sorry baxan kara ba ki karba kisha Kinsan baxan ji dadi ba Idan baki karba ba plsss_
Gaba daya falon aka kyalkyale da dariya ita kuma sai wani lalangabe kai take da yake safah tana masifar son kanwar ta bata son abin da xai bata mata rai yasa ta karba ae kuwa ta rungume ta tana dariya ba wanda bai yi dariya ba a wajen
Tana shan maltina nauwarah cikin Karamar murya tace _Aunty safah yaushe xaki kaimu shopping ne gaskia kayan kwalliya na sun kusa kare wa_
Harara ta xabga mata kafin tace
_baxa ajeba sai ki nemi driver ya kai ki_
_Kaiiii aunty baxa ki kai ni ba don Allah ki taimaka plsss_
Abba ne yace _aunty safah ayi hakuri akai ta mana_
Hannu tasa ta dungure mata gaba daya aka tuntsire da dariya kafin tace _kinci darajar abba yarinya_
Cike da doki da murna tace _xaki kai ni my cwt sister_
_xan kai Ki Insha Allah gobe yar cwt kanwata_
Murmishi tayi har dimple din ta ya lotsa tayi kissing din ta a kumatu tare da fadin
_thank you so much my aunty safah_
Saleem yace _har dani xaa je koh aunty safah_
Harara nauwarah ta xabga mishi tare da cewa _baxaa da kai ba yaro_
Bata rai yayi tare da cunkushe fuska kamar xai fashe da kuka da sauri ammi tace _kada ma kayi kuka dole aje da kai_
Xumbura baki nauwarah tayi tare da tashi ta nufi bedroom
_Aishat A muhd Aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
pg 2
WANE NE ALHAJI SAEED HARUNA
Dan asalin garin kaduna ne a wata unguwa tudun wada anan mahaifan sa suke mahaifin sa Baffah haruna yana da rufin asirin shi dai dai gwargwado da matan sa 2 inna zainab ita ce babba tana da yara 2 saeed da mace safiyya sai inna larai dan ta daya sunan shi salisu da yake Allah bai bashi yawan xuria ba
Baffah haruna yana matukar kokari wajen kyautata wa iyalan shi da bawa yaran shi tarbiyya ta kwarai sai dai kwata kwata baa xaman Lfy a tsakanin matan na shi babu jituwa Ko Kadan
Inna zainab mace ce mai hakuri da kau da kai akan komai yayin da inna larai bata da hakuri ko Kadan saboda tana ganin baffah haruna ya fisan su zainab da yaran ta alhalin yana iyakar kokari wajen kwatan ta adalci a tsakanin matan shi da yayan sa
Axahirin gaskia yafi kaunar zainab da yaran ta saboda sun fi mishi biyayya musamman saeed yana matukar kaunar shi yaro ne mai hankali da nutsuwa bai dauki duniya da xafi ba shi yasa uban yake son shi sa6anin salisu da ya dauko halayar mahaifiyar shi akwai shi da mugun hassada da kyashin wani yayi abu shi bai yi ba baffah haruna yayi fadan yayi nasihar duk a banxa don hka kawai ya kyale shi yana mishi adduar Allah ya shirya shi
Bayan saeed ya kammala schl ya samu aiki a wani company albarkar iyaye da adduar su tare da yanda yake taimakon mutane yake gani saboda ganin yanda Allah yake buda mishi harkokin sa yana samu sosae ganin hka yasa kishi da hassada a xuciyar salisu saboda ganin saeed ya fishi samu ba shi kadai ba har inna larai
Shi kuwa bawan Allah saeed ba ruwan shi sau tari sai ya dauki kudi ko yayi musu dinki tare ya bashi don yana kaunar dan uwan shi duk da hka salisu bai fasa nuna mishi bakin cikin yafi shi samu don salisu kullum a tunanin shi yafi dan uwan shi samu amma Allah bai bashi nasarar hkan ba
Safiyya kuwa dakyar baffah haruna ya barta ta gama secondary schl ya aurar da ita dan kasuwa lokaci daya Allah ya hada soyayyar su don hka da akayi bincike aka ga yana da Kyan hali ba adau lkc ba akayi auren aka kaita unguwar malali lfy suke xaune da mijin ta
Ahka lokaci yake tafiya har saeed ya hadu da maimuna irin kyakkyawan nan ce don gaskia akwai ta da kyau ba karya yar ogan shi ce Allah ya hada soyayyar su da yake ogan nashi yana son saeed sosae jinin su ya hadu don hka baa samu matsala a koina ba akayi auren
Amarya maimuna ta tare a gidan saeed suna rayuwar su cikin kwanciyar hnkl hkan yasa salisu bakin ciki sosae ta yanda akayi ya auri wannan kyakkyawar kamar balarabiya tun ganin shi na farko yaji yana masifar son ta kamar me anan ya kuduri wani mugun nufi a xuciyar shi
BAYAN WASU SHEKARU
Abubuwa da yawa sun faru a wadannan Shekaru Alhaji saeed ya samu karuwar haihuwa mata 2safah ce ta farko sai nauwarah da batafi 3yrs ba sai tsohon cikin da take dashi haihuwa yau ko gobe
Ana cikin hka salisu yaxo gdn yayan shi cike da bacin rai yana shiga falon ya hada ido da maimuna tana xaune a falon tasha kwalliya kai ba kace ta haifi safah da nauwarah ba ae tuni yaji duk bacin ran da ya shigo dashi ya yaye washe hakora ya shiga yi cikin dariya yace
_uwar gida ran gida maman safah da nauwarah kina Lfy_
Shiru tayi kamar baxa ta amsa ba saboda kwata kwata jinin su bai hadu da salisu ba ta tsane shi saboda yanda yake yiwa Baffah haruna da mijin ta saeed rashin kunya a dakile ta amsa da
_lfy qlau nake_
Bai damu da yanda take bata fuska ba ya samu wuri ya xauna cikin murmishi kamar mai tallan maclean yace
_dftn wannan siririn mijin naki ya nan Don wurin shi naxo_
A fusace tace _Wannan wanne irin rashin mutunci ne salisu kaxo har gida na a gaba na kana ciwa mijina mutunci tohh wlh baxan yarda ba idan ka kara xan dau mataki akan ka_
Ranshi idan yayi dubu ya baci amma da yake dan duniya ne ya kakalo murmishin dole yace _okay ayi min afuwa baxan kara ba matar babban yaya dan yi min magana dashi don Allah_
Sai da ta saki tsaki kafin ta mike ta nufi stairs shi kuma ya bita da kallon yana hadyar yawu tare da lashe leben shi yana tunanin abubuwa da yawa a ran shi
Bata da deba yaji tahowar su don yana jin dariyar su kasa kasa alamar magana mai dadi suke fada wa junan su wani abu yaji ya tokare shi a makwogaron shi ya fada tunani sai da yayan shi ya dafa mishi Kafada sannan ya dawo hayyacin shi ya saki wani huci mai zafi kafin ya fara magana ba alamar ma xai gaida yayan nashi yace
_daman yarinyar da xan aura ce na samu sai old man yace bai yarda ba to nasan yafi jin maganar ka shine nake son kayi mishi magana don gaskia baxan iya hakuri da ita ba idan yaki yarda xan gudu a neme ni a rasa sunan yarinyar binta lawan shana_
Yana gama maganar ya kade rigar shi ya fice daga falon ya bar saeed kamar an dasashi a wajen cike da tunanin abin da salisu yake kokarin janyo musu
_Aishat A muhd Aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
pg 3
Dafa mishi kafadar akayi da sauri ya juyo sai yayi arba da kyakkyawar fuskar matar shi tana yi mishi Murmishi amma ganin tarin damuwa a fuskar gwarxon mijin ta nan da nan fuskar ta ta rine xuwa tarin damuwa cikin muryar kwantar da hankali tace
_ya kai mijina menene dalilin shigar ka damuwa_
Kamo hannun ta yayi ya xaunar da ita kan kujera shima ya xauna yana fuskantar ta sai da ya sauke numfashi Kafin yace
_ba wanine ya sani shiga damuwa ba illa salisu da yake kokarin janyo wa kanshi abin da yafi karfin shi_
_me yake kokarin janyo_
_wai aure yake son yi baffah bai amince da yarinyar ba shine yaxo wae baffah yafi jin magana ta nayi mishi mgn idan ba hka ba xaa neme shi a rasa_
Shiru tayi na dan lokacin kalilan tukunna ta sauke ajiyar xuciya tace
_idan yaki yarda ya hakura da yarinyar toh ku kyale shi ya aure ta sai mu taya shi da addua kada ya gudu kasan xai aikata hakan_
Shiru yayi na yan Mintuna Kafin yace
_xamu yi mgn da baffah ngde da shawarar da kika bani idan Allah ya Kaddara wannan auren Shikenan fatan mu Allah ya xa6a mishi abin da yafi alkhairi amma salisu sai a hankali ya fiye rigima wlh Kinsan wacce yarinya ce kuwa_
Girgixa kai tayi alamar aa _toh yar gdn lawan Shana ce_
Zaro ido tayi Kafin ta gida kai tace _Allah ya kyauta amma sam bai yi dace da mace ta gari ba_
_Ameeen dai amma shi ae idon shi ya rufe bae ga hkan ba_
WANE LAWAN SHANA
Alhaji lawan Shana shine cikakken sunan shi don anfi sanin shi da lawan Shana sunan shana ya samo asali daga lokacin samartakar shi saboda tantirin dan duniya ne mai son ya shana a duniya yana dan rufin asiri ba laifi akwai masifar son yaga ya tara dukiya matan shi 4 da tarin yara har 13 gaba daya tarbiyyar su sae a hankali
Acikin su akwai wata binta Tana da kyau ba laifi sai dai maimuna tafi ta kyau nesa ba kusa ba gaba daya ta kwashe halin baban ta _100 percent_ shi yasa yake masifar son ta a yayan shi komai xata iya aikata wa don ta samu kudi a kaduna polytechnic take karatu duk da bata bashi mahimmanci irin yan dumama benci neita ta fara cewa tana son salisu don da alama xata huta a gdn shi baya aurar da yaran shi talaka sai mai kudi idan talaka ne mai yaci balle ya bawa yar shi kaji shi sai kace shi ba talakan bane ya mance Allah ne mai axurta bawan shi
An kai ruwa rana kafin baffah ya amince don salisu akwai shi da kafe ya da hka akayi auren duk yan uwan shi basa so daga shi sai babar shi inna larai
Bayan 2weeks da bikin salisu maimuna ta haihu yaro yaci suna saleem
MUN DAWO LABARI
A kayattaccen bedroom din su na hango nauwarah ta kure volume din tv tana jin wakar da deepika tayi a film din rasleela ram Leela kamar wadda tayi practice din rawar hka take yi ta iya rawar sosae kamar itace deepika din lol
Gaba daya ta cikawa safah kunne da kunne da kara gashi karatu take saboda gobe tana da test a schl gaba daya tabi ta dame ta a fusace tace
_wannan kuma sabon wani wulakancin ne nauwarah ina karatu kin samu kin kure volume_
Sae da ta Murguda mata baki Kafin tace _hba aunty safah don Allah ki kyale ni nayi nishadi man Kinsan ina balain son wakar nan_
_ki tafi falo mana kiji_
Zaro ido tayi tana cewa _tabbb kina so ammi ta doke ni tana falo fah a xaune_
Tsaki safah ta ja kafin ta tashi afusace tayi kan nauwarah da gudu tayi hanyar fita daga dakin sai taga ashe kidan ta kashe ta juyo Tana kallon nauwarah tayi wuki wuki da ido hararar ta tayi kafin ta juya ta xauna tana cewa
_sai tsabar tsokana amma tsoro fal ciki_
Ta dauki buk din ta tana dubawa ganin hka yasa nauwarah ta lalla6a tana Xumbura baki taje ta jona socket din da safah ta kashe iya kuluwa safah ta kulu ta tashi da sauri tayi kan nauwarah ae kuwa ta kwasa da gudu sai falo ita ma safah ta bita da gudu sai ganin su ammi tayi kamar wadanda aka cillo da sauri ta mike Tana cewa
_lfy safah me yafaru_
nauwarah tana ihun _Wayyo Mumy Ki taimaka min aunty safah xata Duke ne_
Duk tabi ta cikawa ammi kunne da ihu gashi ta rukunku ne ta cikin fusata tace
_ammi wannan mara kunyar yarinyar ce ina karatu ta ishe ni da jin waka duk ta hanani karatu_
Ammi tace _baki da kunya nauwarah koh safah kike yiwa hka ba yayar ki ce ba ki bata hakuri kuma kada Ki sake na gaya miki_
Cikin murya kamar xata fashe da kuka tace _Im so sorry my aunty safah na dai na amma kada Ki doke ni plss_
Kwafa tayi sannan ta bar wajen nauwarah ta fito daga bayan ammi tana sakin ajiyar xuciya can kuma ta kyalkyale da dariya tace _ohhh thank god to save me_
Harara ammi ta watsa mata sum sum ta shige tana dariya
_Aishat A muhd Aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
pg 5
Tun da abban ta ya bar dakin take xaune cike da tsoro da tashin hankali akan abin da ya sanar da ita me yasa abban ta ya yanke hukuncin sanar da ita bai sanar da ammi da safah ba ae ita tayi kankanta da asanar da mata da wannan rikitaccen labarin mai kama da film Ko mafarki ADALILIN SON matar shi da dukiyar shi ake neman ranshi to suwaye wadannan marasa imanin tunanin da take da kuka su suka hassada mata matsanancin ciwon kai idon ta duk sunyi jawur dasu sai radadi suke yi mata kamar an xuba barkono
Dakyar ta iya mike wa tsaye ta bude wardrobe din ta ajiyar jakar tayi sannan ta nufi toilet alwala ta daura bayan ta fito ta shimfida abin sallah ta fara nafilfilo batasan adadin nawa tayi ba sai da taji jiri ya fara daukar ta sannan ta xauna ta janyo al quran ta fara karatu cikin muryar ta mai dan karan dadi tana hka har asuba tayi tana idar da sallah bacci yayi awon gaba da ita akan abin sallahr
Wajen 10 na safe Abba ya fito cikin shirin tafiya yasha manyan kaya farare sol dasu da yake ranar jumaa ne ya xauna akan dinning table ammi tana hada mishi breakfast ya xuba mata ido ko kiftawa ba yayi har ta gama hada mishi ta juyo don tayi mishi magana ta ga ya xuba mata ido yana kallon ta Murmishi ta saki wanda ya dada fito mata da Kyan ta kafadar shi ta dafa sannan tace
_Abban safah irin wannan kallon hka Lfy_
Ajiyar xuciya ya saki tare da riko hannun ta yace _bakomai gani nayi yau Kinyi min kyau sosae_ dariya ya bata ta kyalkyale da dariya don wannan kalmar kullum sai ya fada mata dariyar da take ta bashi shima dariya don hka yayi murmishi kawai kafin tace
_nima kayi min kyau wlh fiye da koyaushe amman kayi sauri ka gama don nafi son ka dawo da wuri saboda bana son dare yayi muku a hanya_
_an gama ranki ya dade_
A hankali ya fara cin abincin yana ci yana kallon ta tun tana jin dadin hka har ta fara jin tsoro anya wannan kallon nashi na lfy ne kafin ta samu tayi magana safah da nauwarah sun karaso wajen suka gaida iyayen nasu cikin girmama wa gaba daya nauwarah jikin ta a sanyaye yake ko gayun da ake yau babu shi ta samu waje ta xauna tare da xabga tagumi ammi ta xuba mata ido kafin tace
_lfy qlau kike nauwarah duk Kinyi wani iri gashi Kinxo kin xabga tagumi_
Kafin tayi magana caraf safah tace _wlh umma na tambaye tun daxu tace ba komai koh tsokana ta yau bata yi ba_
Har ta bude baki xatayi magana suka hada ido da Abba yayi mata alamar kada ki fada musu don hka tayi murmishi yake tace
_ammi ba komai na tashi da ciwon kai ne_
_Allah ya sauwake kiyi maxa ki karya sai kisha paracetamol_
Kadan ta iya cin abinci ta ture ta xauna har abba ya gama suka mike tsaye don raka shi har wajen motar da xai tafi a ciki suka rakashi duk sai da ya rungume su sannan ya shiga mota driven shi har ya kunna mota sun kusa fita daga get ya bashi umarni ya dawo baya ammi suka tsaya kallon shi cike da mamakin shi sai da ya dada fitowa ya rungume su ya dunga kallon su gaba daya sun tsorata da hkan nauwarah kuwa tuni ta fara kuka ganin hka yasa ya koma mota drive yaja mota yana ta kallon su har suka fice daga gidan gaba daya mai gadi ya mayar da kofa ya rufe da gudu nauwarah ta shige falo tana kuka sosae ammi da safah sai saleem suka nufi falon gaba daya jikin su a sanyaye dakyar suka lallashi nauwarah tayi shiru safah ta vata magani bata dade da sha ba bacci yayi awon gaba da ita
Tsaye yake a Karshen layin da alamar jiran wani abun yake ganin wata mota ta shige yasa shi sakin wani murmishin mugunta tana shigewa ya dauko wayar shi a aljihu ya kira wata number bata dade tana ringing ba aka dauka cikin wata katuwar murya yace
_Oga an cika aiki nan dan lokaci xakuji kyakkyawan labari_
Daga daya bangaren aka kwashe da wata mahaukaciyar dariya dakyar ya tsagaita da dariyar Kafin yace
_aikin ka kyau mu hadu anjima da yamma a guest house dina mu Karasa biyan ka_
Daga hka ya kashe wayar cikin farinciki ya tsayar da keken napep ya shiga suka tafi
_Aishat A muhd Aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
pg 6
Cikin nutsuwa da iya tuki driver yake jan motar sautin karatun alquran cikin suratul baqara yana tashi a cikin mota sunyi nisa da tafiya sun shigo irin jeje nan da ba mutane sai Shigewar ababan hawa wata babbar mota ce ta taho da gudun balai kan motar tayi gadan gadan kansu
Duk cikin motar ba wanda ya ankara da motar sai da taxo daf dasu Innalillahi wainna ilaihir rajiun abin da suka fada lokaci daya driven yayi kokarin kaucewa amma ina tuni motar tayi ciki dasu gangara wa ta dunga yi Kafin ta daki wata bishiya ta tsaya cak shi kuma mai babbar mota tuni ya arce da gudun tsiya ya bace bac
A hankali wata mota kirar jeep black colour ta fito daga duhun bishiyo duk abin da ya faru akan idon su lokaci daya suka kyalkyale da dariyar mugunta sannan motar ta juya ta nufi cikin garin kaduna
Motoci masu shige wa sune suka kawo dauki aka kirawo police bayan sun xo da motar ambulance dakyar aka xaro su daga cikin motar ba wanda yake motsi da gaggawa aka shige dasu babban asibitin kd likitoci suka Dukufa akan su
After 2 hours later
Bayan wadannan lokacin likitocin dake kan kula da su fito wa sukayi daga dakin cike rashin kuxari a tare dasu don gaba daya basa sa ran rayuwar su sai wani ikon ubangijipolice din suka koma wajen da akayi accident din suka kara bincike awajen nan suka ga wayar shi da card din shi sosai sun shi don ba boyayye ne ba
Kwance take a kan kafar ammi gaba daya wata matsanancin faduwar gaba take ji tana jin ammi da safah da saleem suna hira amma bakin ta yayi dauyi kiran wayar ammi da akayi dai dai lokacin taji wata faduwar gaba wadda tafi ta baya Murmishi ammi tayi kafin ta daga wayar ta Kalli nauwara tace
_toh ga abban naki ya kirawo nasan ynx sun isa kanon Mybe suna haramar taho wa_
Nauwara Bata ce komai ba ammi ta daga wayar da sallama wata irin mikewa tayi a xaburi ta dafe kirji Tana fadin _Innalillahi wainna ilaihir rajiun yanxu suna wanne asibitin_
Nan aka fada mata tun lokacin da ta mike tsaye su safah nauwara da saleem suma suka mike tsaye suna cewa _ammi lfy me ya samu abba_
Ina ammi ba bakin magana da gudu ta shige daki ta xundumo hijabi tayi hanyar waje suma suka bita da gudu driven ammi da mai gadi suna ganin su da hka Sun san ba lfy tambayar ta suke amma ta kasa magana mota ta shige suma su safah suka bita drive ya shiga motar dakyar ta iya furta sunan asibitin da xai kai su nan drive yaja mota da gudu don da ganin iyalan mai gidan nashi ya san ba lfy mai gadi ya bisu da adduar fatan alkhairi
Cikin 30 mint suka isa asibitin police suka tarar a wajen suka yi musu bayanin komai gaba daya suka rushe da wani kuka mai ban tausayi sun bawa mutanen wajen tausayi wasu har da dan hawayen su nima da nake daukar rahoto da kawata saNaz mai min rakiya muka ja gefe guda muna share hawaye
Driven ammi ne yaje ya sanar da baffah da inna habiba yana kuka yana sanar da su don Alhaji saeed haruna mutum ne managarci mai taimako baya kyamar talaka tuni inna habiba an fara share hawaye sun isa asibitin a lokacin da safiyya kanwar Alhaji saeed suka isa abin da yayi matukar daure min kai har na dakata da kukan da nake ganin Alhaji salisu da matar shi hajia binta sun fito a mota daya da safiyya suna kuka
Kukan da yanke mai suna da kukan munafurci ashe shine ya je ya taho da safiyya ya biya ta gida don dauko su baffah ya tarar sun taho yanda hankalin shi ya tashi sai ka dauka basa hannun shi nan na bashi number 1 na masanin tuggu da iya yaudara
Daf da sallahr laasar Alhaji saeed haruna da driven shi malam inuwa suka amsa kiran ubangiji Allah Akbar rayuwa kenan ya tafi ya barsu da duniyar suyi abin da xasu yi wataran suma xasu xama kamar hka don Allah swa yana cewa acikin suratul al imraan kullu nafsin xaikatul maut Wato kowanne mai rai xai dan dani dacin mutuwa yau gare ka gobe ga wanin ka jebi a kan ka don hka ina kira a gare mu da mu kyautata rayuwar mu Wajen aikata abu mai kyau don mutuwar nan ba sallama take yi ba _Allah yasa mu dace duniya da lahira Ameeen thumma Ameeen_
Shi kanshi babban likitan dakyar ya iya yi musu bayani don sai da ya fara da yi musu nasiha Kafin ya sanar su ae Kafin su ankara ammi nauwara da inna habiba sunyi baya a sume
_ni kai na tsananin tausayin su yasa ban san lokacin da wayar tawa ta subuce ba don hka fans Kuyi hakuri sai na dawo hayyaci na xan cigaba da daukar muku rahoto shin Wacce irin KARSHEN WAHALA wadannan familyn xasu shiga_
_Aishat A muhd Aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
pg 7
Gaba daya waje ya rudai da kuka hankali sun tashi safah da saleem sun gigice iya gigicewa ga mutuwar abba sannan ga ammi da nauwara a sume kuka kawai suke yi
Nan likitoci suka basu taimakon gaggawa bayan sun farfado aka basu gawar Alhaji saeed da driven suka nufo gida don a sada su da gidan su na gaskia
Cikin lokaci kalilan mutuwar Alhaji saeed haruna ta kewaye garin kaduna ae kuwa nan da nan mutane suka dunga taho wa domin halarta janaixa suna alhinin mutuwar bawan Allah kenan mutumin da yake xaune da kowa lfy bashi da abokin hamayya
Bayan an kammala hada su aka umarci makusantar shi dasu xo ko da wanda xai mishi kallon Karshe ko aaddua dama an nemo iyalan malam inuwa drive don hka kowa yaje inda gawar dan uwan shi suke masu karatun alquran da Adduoi nayi masu kuka Nayi don nauwara bakin ta yayi mata nauyi ta kasa bude shi har gwanda ammi da safah sun kokar ta yi mishi addua sai mahaifin shi baffah haruna managarcin tsoho kenan yayi jarumatar sosae don mutuwar dan shi ta buge shi sosai shine yayi kokarin yi mishi karatun alquran
Ganin ana kokarin daukar makara yasa nauwara tafi karfin hali wajen kwararo wa abban ta Adduoi don neman dace wa da rahmar ubanjigi lokacin da aka dauki makarar gaban nauwara ya fadi Shikenan baxa ta kara ganin abban ta ba baxa ta kara jin muryar shi ba har abada ya tafi ya barsu a duniyar nan mai cike da rikici da tashin hankali kuka ta saki da karfin gaske amma da yake muryar ta ta dushashe baa jin sautin kukan sosai
Kamar ance ta daga kan ta ta Kalli mutanen wajen karaf ta tsinci Murmishi akan fuskar Alhaji salisu gaban nauwara ya fadi dum dum cak ta tsaya da kukan ta xuba mishi ido sai da akace ya kama makara tukunna ya takarkare ya fashe da kuka mutane na bashi hakuri
Gaba daya hankalin nauwara ya tashi sosai kuma bata yarda da uncle din ta ba sam kuma tayi wa kanta alkawarin sai tayi binciken dalilin mutuwar abban ta
1 week later
Bayan kwana 7 da rasuwar Alhaji saeed haruna yau aka kammala xaman makoki duk mutane suka watse sai iya yan gida kawai su nauwara duk sun rame sosai abin gwanin ban tausayi musamman nauwara da abu 2 suka hade mata mutuwar abban ta da kuma ta yanda xata fara bincike akan uncle din ta don sanin me yasa shi murmishi a lokacin da ake cikin tashin hankali na mutuwar dan uwan shi yayan shi
Bayan sallahr ishae baffah haruna da matan shi inna habiba da inna larai sai ammi safah nauwarah da saleem sai safiyya kanwar Alhaji saeed da kuma Alhaji salisu kanin shi suna xaune a falon bayan baffah ya bude taro da addua sannan ya fara da yiwa su ammi da nasiha mai ratsa xuciya da suyi hkari hka Allah ya shirya iyakar lokacin da aka dibar wa saeed kenan a duniya muma nan ita muke jira Kafin ya dora da cewa
_yanxu mun gama shiryawa xamu tafi ki kula sosai da ke da yaran ki sai Kinsa ido akan su sosai idan kina neman taimako sai ki neme mu_
Cikin muryar kuka tace _toh baffah Insha Allah xan yi kokari wajen kula da hkan mun gode_
Anan aka rufe taro da adduar Allah ya jikan Alhaji saeed haruna ya kai rahma kabarin sa tare da sauran al umma da suka riga mu gidan gaskia Ameeen su amsa daga hka suka tafi akabar su ammi su kadai kadaicin rashin abba ya dame su sosai dakyar bacci yayi awon gaba da su yayin da nauwara ta dauko jakar da Abba ya bata ta fara bincike a ciki duk takardun dukiyar shi ne kusan gaba daya kuma original din ne sai wani pictures din su da suka dauka gaba daya Mayar dasu cikin jakar tayi kafin ta tsunduma a tunanin yanda xata fara binciken ta
After 2 months later
Wata yarinya ce yar kimanin 16yrs da wasu yan watanni na hango ta a tsaye a jikin wani gida ta raku6e alamar jiran wani abun take tana sanye da jeans blue da tshirt red colour ta sanya wata riga a saman kayan irin ta sanyin nan har kusan gwiwar ta black colour ce sai tayi rolling din kanta da dark blue din veil da yake fara ce sol ya haska ta ta sanya wani glass ya rufe kusan rabin fuskar hannun ta dauke da waya jin alamar bude get yasa ta da da lafewa a jikin ginin wata motace kirar honda accord ce ta fito daga gidan ta harba kan titi da sauri ta fito daga jikin ginin ta nufi titi Tana tsayar da keken napep amma Bata samu ba har motar ta bace wa ganin ta mtssss taja tsaki kamar ta tsinka harshen ta saboda takaice sau 2 kenan take kokarin bin motar amma take bace mata wani murmishi ta saki ganin ta samo hanya mafi sauki don hka ta tsayar da keken napep ta shiga direct gida ta wuce tana sauka a kusa da gidan ta biya shi sannan ta shige gida
_Aishat A muhd aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
pg 8
Da sallama ta shiga falon su ammi na xaune suka amsa mata sai da ta warware mayafin da tayi rolling dashi Kafin ta xauna tana cewa
_washhh ammi na gaji wlh kai saleem samo min wani abun na jika makoshi na_
Da sauri saleem ya tashi ya nufi kitchen yayin da ammi tace _wai ni nauwara ina kike xuwa ne kullum sai kin fita idan kika dawo daga schl na rasa yaushe kika koyi yawo wlh_
Murmishin yake tayi sai da tasha ruwan da saleem ya kawo mata kafin tace _ammi ki yarda da ni wani dan bincike nake yi amma da xarar na gama Shikenan_
Harara safah ta xabga mata kafin tace _wanne bincike kuma sai kace wata lawyer ko police yar rainin wayo kawai ki fada mana inda kike xuwa_ mtsss taja tsaki tare da cewa
_wlh aunty safah kin fiye sa ido da yawa ina ruwan ki naga da ammi nake magana_
Ta Karasa fadi tana Murguda baki safah ta cillo mata pillown hannun ta caraf tasa hannu ta cafe har ta bude baki xatayi magana amma maganar ta makale sakamakon ganin mutumin da ya bace mata da gani daxu ya shigo da sallama kamar wani mutumin kirki bayan shi wata mata ce ammi ce ta amsa musu sallamar ya samu waje ya xauna ya xuba wa ammi ido kamar wani tsohon najadu ko nace tsohon maye nauwara tana kallon shi har tana mamakin wannan wanne irin kallo ne yake yiwa ammin ta hka dam dam gaban ta ya fadi sakamakon maganar da abban ta yayi mata ta fado mata Adalilin son ammin ki da dukiya ta ake neman ranshi nan take ta shiga tunani maganar da yayi ita ta dawo da ita hayyacin ta baki ta saki tana kallon shi yace
_dama yar aiki na samo muku tunda na lura mai yi muku aiki bata nan_
Caraf nauwara tace _ae uncle ba sai ka kawo mana mai aiki ba tun da muna iya aikin mu babu abin da ya gagare mu_
Kallon ta yayi ita ma ta xuba ido ko kiftawa babu a xuciyar shi yace Idan nayi wasa wannan yarinyar sai ta sai ta bani mamaki sosai ina sane da irin binciken da take yi akai na amma Idan tasan wata ae batasan wata ba kuma komai abin ta yafi ta dade wa a duniyar kuma yafi ta sanin tuggu amma da yake dan duniya ne a fili sai ya saki Murmishi yace
_hba nauwara ni da nake so ku huta bana son Kuna wahala ku barta ta dunga taimaka muku_
Har ta bude baki xatayi magana ammi ta riga ta da cewa _Shikenan salisu ae ba damuwa ta dunga taya ni hira idan sun tafi schl mun gode_
Wani dan iskan Murmishi ya saki na jin dadi abin da ammi tace ya wani watsa wa nauwara kallo wanda na kasa banbance wane kalar kallo ne Kafin ya mike tsaye yana cewa
_toh maimuna xan koma sai na sake xagayo wa_
_okay ka gaida gida a gaida hjy binta_
_xata ji da kyau kuwa_
Yayi hanyar fita daga falon sai da ya bigi kafar wadda ya kawo a matsayin yar aiki ta dago da kanta karaf suka hada ido ae kuwa ya kashe mata ido daya ita ma ta mayar mishi da martani toh fah ba wanda ya kula da hkan sai nauwara da yake ba karamin xargin shi take ba shi yasa kowanne action din shi akan idon ta da hka ya bar gidan cike da farin ciki wani sashe na xuciyar shi yana tunanin yanda xai aiwatar da mugun nufin shi akan nauwara don ya fahimci yarinyar tana bibiyar shi ya sha ganin ta awajajen da yake yawan Xuwa
140 am
Karfe 140 na dare na hango nauwara ta fito daga bedroom din su tana sanye da wata night gown blue colour cotton ce rigar ba takalmi a kafar ta amman ta sanya wata white din hula akan ta tafiya take sadaf sadaf don iita hankalin ta bai kwanta da ladi mai aiki ba sai taxo dai dai dakin da aka bata ta tsaya sai taji ana magana kasa kasa bata ji mai ake cewa ba jin anyi shiru kuma sai ta dan tsaya can kuma taji motsin bude kofa da sauri tayi baya ta shige cikin labule tukunna ta dan leko da kanta sai taga ladi ta fito sai da ta dan dudduba bata ji wani motsi ba sai ta nufi stairs tana hawa a hankali nauwara ta fito daga bayan labule cike da mamaki take bin bayan ta taga ina xata je mamakin ta ya karu ganin tayi part din abban ta nan ta dunga binta a hankali
Bata tsaya a koina ba sai bedroom din abba ta shiga bincike kain da nain kamar ta bawa wani ajiya har tayi nasarar fito da wani file cike da takaddu sosai mamaki ya dada kama nauwara don exactly irin takardun da abba ya bata ne sai dai wadannan basu kai na hannun ta yawa ba ji tayi kmr ta fito ta nuna mata ta ganta sai kuma tayi tunani idan baka iya kama 6arawo ba shi ya kama ka kuma tana son taga yanda xata yi dasu
Gaban nauwara ne yayi mugun faduwa ganin ta nufo inda take nan jikin ta ya hau rawa don tsab Wannan matar mai kama da kirar samudawan kwaf daya xata yi mata nan ta fara kiran sunan Allah a xuciyar ta tuni ta fara hada uban gumi ganin da gaske inda take nan ta nufa
_Aishat A muhd aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd aunty_
pg 9
Wata sassayan ajiyar xuciya ta saki ganin ta kauce daga inda take ta nufi inda computer abba take har ta dauka sai kuma tayi tunanin amfanin me xatayi tun da ta samu abin da ake so don hka kawai ta juya ta fice daga bedroom din
Nauwarah ta fito daga bayan labule tana share gumin fuskar ta tare da sakin ajiyar xuciya sai da ta xauna ta huta kafin ta mike tsaye har xata fita sai kuma tayi baya tsayawa tayi adai dai inda computer abba take hannu tasa ta dauke ta kafin ta fito daga dakin tana tafiya a hnkl sai taga ladi tana wuya mamaki ya dada Kume nauwara da taji tana cewa
_salisu naga files din da kake bukata Gasu a hannu na gobe da yamma xanyi dubarar fito wa na kawo maka mu hadu a guest house din ka_
Tana gama fadin hka ta kashe wayar sannan ta shige dakin ta ta rufe ita ma nauwara bedroom din su ta shige ta jona computer a charge Kafin ta shiga toilet alwala ta daura bayan ta fito ta shimfida abin sallah ta fara nafilfilo akan Allah ya kare su daga sharrin Alhj salisu
Gaba daya yinin ranar ba inda nauwara taje tana xaune tana kula da shige da ficen ladi mai aiki har xuwa 5 na yamma sai gata ta fito daga dakin ta durkusa wa tayi agaban ammi kafin tace
_hajia don Allah ina son ki barni naje na debo sauran kaya na a gidan Alhj salisu ynx xan dawo_
Shiru ammi tayi kafin tace _ban da abinki ladi ba sai mu baki wasu kayan da xakiyi amfani dasu ba idan yaso ko drive na aika ya karbo miki_
Gaban ta ne ya fadi ta kuma rasa mai xata ce ta fara kame kame na rashin gaskia gashi nauwara ta xuba ido ta rasa me xata ce can kuma tayi wani tunani cikin marairaicewa tace
_hajia da anbar ni naje akwai abu masu mahimmanci acikin kaya na kada sauran yan aikin su dauke min a taimaka ynx xan dawo_
_Shikenan sai kiyi sauri ki dawo Kafin mangariba_
Ammi ta fada tana mika mata kudin transport tasa hannu ta karba cikin murmishi tace _ngde hajia kuma in Allah ya yarda ynx xan dawo_
Sai da ta koma dakin ta Sannan ta fito ta tafi xumbur nauwarah ta mike tsaye ta nufi bedroom din su wayar ta ta dauko daga jikin charge da sauri ta fito tana cewa _ammi ina xuwa don Allah ynx xan dawo_
Kafin ammi tayi magana ta fice daga falon cikin sauri ammi ta bita da kallo Kafin ta girgixa kai tace Allah ya shirya ki nauwara Ko ina xaki kike wannan saurin hka
Tana fita ta hango ta nesa da ita ta hau keken napep da sauri ita ma ta shiga wani tace
_don Allah yi sauri kabi bayan wannan_
Ta fada tana nuna mishi toh yace ya tayar dashi suka tafi yana bin bayan keken napep din da ya dauki ladi har suka Karaso guest house din ta sauka sai da ta biya shi sannan ta shige ciki
Nauwara kuwa tun daga nesa Kadan tace ya sauke ta ce _don Allah malam ko xaka jira ni na fito ba dade wa xanyi ba xan biya ka har xaman da kayi_
_toh ba damuwa xan jira ki_
Mai keken napep ya bata amsa juya wa tayi ta fara tafiya a hankali har ta karaso gidan abin da ya bata mamaki ganin kofar a dan bude a hnkl ta tura Kadan ta dan leka sai taga ba kowa tukunna ta shiga ciki da addua a bakin ta sai da tayi yar tafiya Kadan tukunna ta isa bayan gidan ta window ta fara leke sai taga falo ne hadadde ladi na xaune akan kujera ita kadai bayan yan mintuna sai taga an bude kofar falon an shigo batayi mamakin ganin su ba Alhj salisu da Alhj lawan shana sai yar shi kuma matar Alhj salisu Wato hjy binta bata jin abin da suke fada amman ta ga ladi ta basu files din da ta dauko sai da ya dudduba Kafin ya dago kai cikin bacin rai yace da karfi har nauwara tana jiyo wa
_wadannan ae ba original din takardun bane me yasa baki duba sosai ba to ina computer tun da nasan duk wasu abu masu mahimmanci suna ciki_
Cikin muryar yan duniya tace _yo ae ni baka ce na dauko da computer ba don wlh har naje xan dauka na tuna bakace na dauko ba_
Mtssss suka ja wani tsaki a lokaci daya kafin tace _yau da dare sai na dauko amma kai xaka xo ka karba gaskia ni wlh wannan yarinyar nauwara ita take ban tsoro ta fiye sa ido da yawa ga shegiyar tambaya_
A kufule Alhj salisu yace _ina Ae xancen gama ya gama don bama xaki samu wannan computer ba amman nasan ta yarda xan bullo abun ae ba ke kadai wannan shegiyar yarinyar take yiwa hka ba ko ni hka take min kuma na kusan kawo Karshen alamarin_
Nan yayi musu magana a hankali gaba daya suka kyalkyale da dariyar da ta firgita nauwara jiki na rawa ta dauke su pictures a wayar ta da gudu ta fice daga gidan ta fada cikin keken napep din tana mayar da numfashi Kafin tayi mishi magana su tafi ta da machine din yayi suka tafi
Alhj salisu ya dawo da kallon shi daga jikin window da nauwara ta makale ashe yana kula da ita shi yace ma mai gadin ya bar Wajen gate saboda yasan xata xo sosai yarinyar take bashi mamaki yanda take da jarumta hka da ace namiji ne ae da tuni asirin su ya tono kai dole ne ma ya dau mataki akan yarinyar nan tun Kafin ta bashi mamaki bai sanar dasu ba da hka suka watse gaba dayan su
_Aishat A muhd aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd Aunty_
pg 10
A dai2 bakin gate mai keke napep ya sauke nauwara ta fito bayan ta biyashi kudin shi bata tsaya karbar canji ba ta wuce cikin gidan don gaba daya a rude take batasan mai uncle din su ya radawa masu a kunne ba don tasan abin arxiki bane sai da taxo dai2 shiga falo ta dan dai daita nutsuwar ta da sallama ta shiga ammi da safah suka amsa mata kafin ta xauna safah tace
a yawo sai ynx kikayi raayin dawo wa
Hararar ta nauwara tayi hade da murgua mata baki kafin tace ohhh aunty safah wllh kin cika sa ido ina ruwan ki dani ne
Ammi ce tayi mata dakuwa tace gidan ku nauwarasafah kike cewa tana sa ido to idan bata sa miki ido ba wane xai sa miki ni wllh yawon nan naki ya isheni
Cike da shagwaa tace hba ammina Allah aunty safahr ce sai a hankali kuma fitar da nake tana da dalili
Kafin wani ya kara magana a cikin su ladi ta shigo falon da sallama ammi da safah sune suka amsa mata but nauwara harara ta watsa mata hannun ta dauke da katuwar ghana must go kaya ne aciki amman ko rabin jakar basu kai ba cikin ladabin munafurci tace
hajia na dawo
okay sannu da dawo wa dafatan baa taa miki komai aciki baammi ta tambaye ta murmishi ta saki sannan tace
ae naci saa hajia don basu taa komai ba hankalin su bai kai wajen ba
Daga hka ta mike ta nufi bedroom din da aka bata nauwara ta bita da harara har da jan tsaki jin tsakin da taja yasa ammi da safah kallon ta
Lfyn ki kuwa nauwara kike tsaki ke daya
ammi ta tambayi nauwara yatsina fuska tayi kafin tace ni wllh ammi wannan er aikin da uncle ya kawo mana ita ban yarda da ita ba ni tsoro ma take bani
Harara ammi ta xabga mata kafin tace bana son irin hka nauwara Hka kawai ki tsani mutum ba daliliidan ma tsoro take baki duk lokacin da kika ganta kiyi addua kawai amman kada ki sake ki nuna mata na gaya miki
Zumura baki tayi kafin ta tashi tsaye tayi gaba tana dan kunkuni safah tace Allah ya shirya ki wllh
Cikin tsiwa ta juyo tace idan da gaske kike toh Ameeen
Har ta bude baki xatayi magana ammi ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu shiru tayi cike da takaicin abin da nauwara tayi mata
BAYAN KWANA BIYU
Nauwara bata kara fita ba acikin kwana 2 nan tana gida a xaune da tunanin yanda xata illo da Wannan alamarin don tana tsoron kada su nemi hallaka su wasu hawaye masu xafi suka sauka kan fuskar don ta tuno da abban ta takai wajen 5mint tana kuka Kafin ta mike ta shiga toilet alwala ta daura bayan ta fito ta shimfida abin sallah ta fara nafilfilo tare da adduar Allah ya shiga tsakanin su da su Alhj salisu
Kamar yau ranar monday da misalin karfe 130 na rana Alhj salisu ya xo gidan su nauwara a falon kasa ya samu waje ya xauna bai fi 3mint da xama ba ladi mai aiki ta fito daga kitchen suna hada ido dashi suka saki wani murmishi a tare kafin yace mata
Yawwa ladi yi min magana da hajiar ki turo min ita don ina son a yau ayi ta takare wllh
Harara ta watsa mishi kafin tace nima ae na gaji da xaman bauta wlh gwara ayi ta a watse na samu kaso na sannan na tafi inda nafi wayo _daman ladi karuwa ce yaje ya dauko ta don tayi mishi wani aikin da farko bata yarda ba sai da taji magudan kudin da xasu bata yasa ta amince da hkan_
shegiyar karuwa ae kuwa anjima Kadan xaki tafi sai ki dora inda kika tsaya
Mtssss taja tsaki ta shige xuwa stairs don ta kirawo ammi da sallama ta shiga ammi ta amsa mata sallamar ta juyo don taji lfy wow masha Allah Kaee na yarda da salisu da nace sai ya aure ta Gasky akwai kyau sosai ita kanta ta burge ta balle namiji dakyar ta sai ta kanta cikin ladabin munafurci tace
Hajia daman Alhj salisu ne yaxo yake son magana dake
okaykice mishi ina xuwa Ki kai mishi ruwa da drinks
angama hajia
Nan ta fito xuwa down stairs kitchen taje ta kawo mishi abin da ammi ta ce ta bashi ajiye mishi tayi akan table Kafin ta tsiyaya mishi lemon ta bashi cike da wani iyayi cikin murmishi tace
amman don Allah anjima na dan xagayo guest house ka dan rage min xafi kaga yau wajen 1wk ba harka
Ae tuni ta tsumashi da salon ta yace kada ki damu ki xo nima na dan huta da
Kafin ya Karasa fadi an turo kofar falon an shigo a raxane suka juya gaba dayan su cikin tsananin tsoro
Toh masu karatu sai ku canka na baku gari lol
_Aishat A muhd aunty_
KARSHEN WAHALA
NA
_Aishat A muhd aunty_
Wannan pg din ki ne my sadeey saNaz thanks for the love and support Allah ya bar xumunci ameeen
pg 11
A raxane suka juya don ganin mai shigowa a lokaci daya suka saki ajiyar xuciya ta kwanciyar hankali ganin safah ce ta shigo tuni Alhj salisu ya wayance yana cewa
maxa ki dauke drinks din nan ya isheni hka
Da sauri ladi ta dauka ta shige kitchen safah tace
uncle ina yini
Lfy qlau yata ya skul dafatan ana bada himma a karatu
Alhj salisu ya tambayi safah kamar wani na gari nan kuwa xuciyar shi cike da tarin tsanar ta Allah ya taimake shi ba shegiyar dayar bace nauwara yake nufi da itace sai ta dago wani abun cike da murmishi safah tace
skul lfy qlau uncle sosai ma ina mai da hankali
toh yayi kyau hakan
Daga hka safah ta shige ta nufi stairs shi kuwa ya bita da harara kamar idanun shi sa fado kasa shi ae kishi yake dasu kamar yanda yake kishi da uban su wani kamshin turaren mai sanyin kamshi ya shaka a hancin shi da sauri ya dago kanshi tuni ya shiga wani hali ya kiime ganin yanda tayi mishi kyau kamar bata haifi su safah ba dakyar ya iya saita kanshi suka gaisa kafin su yi shiru na wani dan lokaci can Alhj salisu ya fara da cewa
daman abin da yasa kika ga naxo nasan xakiyi mamakin hkan toh ba wani abunne ba illa ina son ki amince min na aure ki
Dummm gaban ammi ya fadi a matukar tashin hankali ta dago kai ta kalle shi tace sake mai2 ta abin da kace don banji sosai ba
Murmishi ya saki tare da gyara xaman shi tukunna ya sake mai2 ta mata maganar wani kallo ta watsa mishi cike da tsantsar tsanar don sai da gaban shi ya fadi ganin yanda ya karanto tsantsar tsanar shi a fuskar ta amman hka ya dake cike da tsawa ammi tace
daman abin da ya kawo ka kenan toh maxa tattara tsumman jikin ka ka barmin gida Allah ya sauwake min na aure ka ai ko maxa sun kare a duniya baxan aure ka ko da ina da raayin auren balle ba kara auren xanyi ba
hba maimuna kalle ki fah yarinya sharaf dake Kice baxa ki sake aure baae kawai ki cire matacce a xuciyar ki gani yaro sabon jini na aure ki don nasan baxa Ki iya jure rashin namiji a kusa dake ba dole ki nema don hka
Kafin ya Karasa fadi ammi ta cike da takaice ta cilla mishi wayar hannun ta a goshin shi ji kake kum da sauri ya dafe wajen cike da radadi nan da nan idon shi ya kada yayi jawur sai huci yake kamar wanda ya hadiyi kunama cikin masifa ammi ta cigaba da cewa
kuma daga rana ita yau kada ka kara shigo min gida tunda kai baka da mutunci dan akuya kawai kuma ina sane da dukiyar su nauwara da kake ci kamar na ka wllh salisu kaji tsoron Allah don kayan marayu kake ci kuma aure ne naga ya maka bazan yi ba koda xanyi baxan aure ka ba mtssss
Ammi ta Karasa fadi tana jan tsaki don ba karamin haushi ya bata ba da xata iya hada hannun ta da fuskar shi ae da marin shi xata yi mara imani kawai shi kuwa Alhj salisu iya kuluwa ya kulu tayi mishi cin mutunci da tunda ya fito daga cikin babar shi baa taa yi mishi don hka ya mike tsaye a fusace yace
ko kin ki Ko kinso sai na aure ki wllh sai na cika buri na akan ki naga wanda ya isa ya hana don adalilin sonna saNaz dana ke miki xan iya aikata komai don hka ki xuba ido ki ganikuma dukiya ce anci ki fadawa duniya naga uban da ya isa ya hana
Yana gama fadin hka ya fice fuuuu a fusace kamar ya tashi sama ammi ta xube akan kujera tana kuka tare da ambato sunan Allah a bakin ta Allah yayi musu tsari da sharrin salisu
Shi kuwa yana fita daga falon a farfajiyar gidan ya hadu da nauwara tana fito wa daga mota harara ta bishi da ita shima hararar ya watsa mata a xuciyar shi yana cewa xaku ci uban ku yau don gaba daya sai na huce takaicin da uwar ku ta kunsa min a xuciya ta da matukar gudu ya fice daga gidan
Nauwara ta tae baki kafin ta shige kwata kwata ammi bata nuna wa su safah wani abun ba ko da nauwara ta tambaye ta mai yaxo yi gidan ammi cewa tayi ina ruwan ki tunda ba wajen ki yaxo ba daga hka nauwara ta ja bakin ta tayi shiru amma can kasan xuciyar ta bata yarda ba da abin da ammi tace ba saboda yanayin ammin tasu ya jan xa
Bedroom ta shiga ta bude wardrobe din ta ajiyar jakar da abban ta ya bata ta dauko tare da bude wa tana gyarawa har da dauko pictures din su wanda suka dauka gaba daya tana gani tare da goge hawayen da ya xubo mata a fuskar ta gyara jakar tayi tare da dauko er Karamar laptop din abba ta sanya a ciki kwanciya tayi akan bed tare da rungume jakar a jikin ta don kamshin turaren abba take yi Har ynx da hka bacci ya dauke ta
1245 pm
Karfe 1245 na dare gari koina yayi shiru baka jin motsi mutane sosai saboda lokacin sanyi ne kowa ya shige gidan shi abin da ban mamaki ganin wani haske nayi a gidan su nauwara ya tashi da na sake matsawa sai naga ashe gidan ne ya kama da wuta gaba dayan shi kuma a lokaci guda duk kuwa da girman gidan yanda wutar ta tashi lokaci guda da wuya wani ya tsira da ranshi sai dai wani ikon Allah
Aishat A muhd aunty
KARSHEN WAHALA
Na
Aishat A muhd Aunty
pg 12
Cikin kankanin lokaci mutane suka taro a wajen duk da sanyin da ake xabga wa a daren Hka en unguwar suka firfito cike da tashin hankali Kafin a samu a kirawo en kashe gobara gashi ba ta yanda xaa samu a shiga saboda wutar ta kama koina na gidan balle a taimaka musu
Ba au wani dogon lokaci ba en kashe gobara suka shigo unguwar nan da nan suka fara aikin su wajen kashe wutar ana cikin hka suka ji ana cewa help me please somebody help me
Jin Hka yasa suka fara neman hanyar shiga dakyar suka iya samun hanya aka shiga ta Wajen da suka ji ana neman taimako ai kuwa sunyi nasarar fito da mutum 2 mace da namiji wani ikon Allah basu kone sosai ba sai hayakin da suka shakane ya sumar dasu nan da nan aka nufi hospital dasu
Da gaggawa aka kare su nan likitoci suka Dukufa akan su don ceto rayuwar su bayan sun gama duba su numfashin su ya dawo normal suka yi musu allurar bacci don tsabar rudewa tasa su suma
Acan kuma dakyar sukayi nasarar kashe wutar amma baa dauki komai a gidan ba sai yara 2 da aka dauko sosai makwabtan su nauwara hankalin su ya tashi don sun san maimuna ammi da safah sun mutu tun da iya nauwara da saleem aka samu gashi ba mai number wani acikin en uwan su nauwara balle aneme su don hka suka hakura xuwa gobe da safe a neme su
920am
Misalin karfe 920 na safe nauwara ta tashi a firgice ta duba ta ganta a gadon asibiti nan kuma tayi shiru kwakwalwar ta ta fara tuno mata da abin da ya faru a daren jiya
Karshen Wahala Hausa Novel PDF download
Novel Title | Karshen wahala hausa novel |
Uploaded by | Zamgist.com.ng |
File Size | 500kb |
Hausa Novels WhatsApp Group | Click here |
Telegram Group | Click here |
Novel Price | Free |
Written by | Aisha A. Muhammad |
Tags | Karshen wahala hausa novel |
Published date | 20– 08– 2023 |
Karanta:ÂAuren Sirri Hausa Novel
DOWNLOAD NOVEL
Littafin:ÂThe Sexy Boss Hausa Novel By MamamTeddy