Gidan Uncle 72

Barkanki da zuwa shafin mu na hausa novels inda muka kawo muku littafin Gidan Uncle 72 by Fauziyyah Tasi’u Umar.

Gidan Uncle 72

Tag: GIDAN UNCLE PAGE 72

Yana fadin haka ya nufi qofa da sauri ya fice daga dakin ko hanun da D.S yake miqa masa bai kulaba wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata ya kamata ya zaunar da ita yace “to ya isa haka kinsan banason kuka ko?” qoqarin tsayar da kukan ta farayi daqyar ta tsayar da kukan yayi murmushi ya miqe yace “zanje gda ke sai yaushe?” Qasa tayi da kanta tace “jibi” kallonta yayi da sauri yace “aa gobe dai” batayi masa musu ba ya juya ya fice bayan sun gaisa da mutanen dake dakin sai Ikcn ta samu damar gaisawa da kowa ta miqe da qyar ta shiga dakin Hajiya ta kwanta tana tunanin Uncle dinta zuciyarta na fada Mata ta tashi tabishi taje taga halin da yake ciki amma saita dake kawai tayi kwanciyarta.

Har dare ya fara ta fita ta koma parlourn Aunty Zarah ce kawai saboda Aunty Jameelah tun uku ta tafi sai Hajiya Kaka da maqota dayake aikin abincin sadakar duk kwangila suka bayar suna zaune har sha daya sannan kowa yaje ya kwanta itama kwanciyar tayi amma zuciyarta taqi hutawa koda D.S ya kirata ma daqyar ta daga tace masa bacci takeji sukayi sallama ta aje wayar tanata karanta wasiqar jaki ranar daga ita har Hameed babu wanda ya rintsa shi gani yake Umaimah taci amanarsa data yarda wani ya kwanta da ita harma yayi mata ciki wannan ciki ya tsone masa ido da yasan mugun ganin da zaiyi kenan da bai dawo 9ja ba yanda yakejin ciwon abinda ya gani a jikin Umaimah bayajin ciwon mutuwar yaran nasa haka saboda yasan su Ikcnsu ne yayi amma ita ta manta da halaccin da yayi mata taje ta bawa wani kanta yanzu abinda yakeji a jikinta shima Sulaiman abinda yakeji kenan?

Wani kishi ya taso masa daqyar ya rinqa danne zuciyarsa da qarfin addu’a.
Washe gari akayi sadakar bakwai basu hadu da Hameed ba harta gama zamanta a gdan D.S yazo daukarta ta hado shirginta ta fito yana yana riqe da hanunta yana zuba mata zance tana dariya Hameed din ya shigo a motarsa sabuwa dal yayi parking duk da batasan shi bane amma saida gabanta ya fadi ta kalli motar sosai jikinta yana bata na cikin motar ita yake kallo.

LaIlai kuwa itadin ya zubawa ido yanajin wani abu yana tasowa qirjinsa zuciyarsa tana tafasa yanda suketa dariyarsu da Sulaiman din yana jamata karan hanci har kuma dan jaraba irin tasa ya kasa daina kallonsu yana qara tsinewa Salma data zama sanadin rabashi da farin cikinsa qiri2 Umaimansa tafı qarfinsa yanason yaga ya cireta a ransa amma ya kasa hukunci ya yankewa zuciyarsa na barin qasar gaba daya dama ya samu aiki a World Bank of America da yace bazashi ba amma yanzu dole ya hada komatsansa ya tafi can qila ya samu sauqin rashinta saboda yasani Umaimah batada ta biyu a gurinsa har yau idan ya kwanta tunanota yakeyi da irin sadaukarwarta ga farin cikinsa.

 

Buruka da yawa daya dauka akan rayuwarsa da bloody dinsa yanaji yana gani sunbi ruwa wai yau bloody dinsa ce da cikin wani a jikinta har tana ganinsa tana razana to meye ma ya razanata dashi? Tambaya ce da bashi da amsarta tashin motarsu ne ya dawo dashi hayyacinsa ya buga kansa a sitiyarin motar tare da dukan qirjinsa yana kiran “ya rabbih” yana hawaye masu zafi yace “Allah Kaine ka halicci zuciyata da son baiwar nan taka Allah kasani bani na dorawa kaina ba kaine ka jarrabeni Allah ka ciremin ita a raina Allah meyasa kullum ina roqonka kamar baka amsawa Allah banaso ka kamani dason matar wani kafi kowa sanin banida qarfin raba zuciyata da ita a jinina take yawo” bude qofar motar da akayi ne yasashi dagowa da idanunsa da har sun dafe saboda kunan zucci ya zubasu akan Yusuf yayi murmushi don yasan kukan me yake Hameed bashi da damuwar data wucce Umaimah a rayuwarsa gashi Umaimah tayi masa nisa.

 

Dafashi yayi yace “mutumin ya kamata ka cire bloody dinnan taka aranka ka nemi wata yar baby ks aura ka qarasa rayuwarka da ita” wani kallo ya watsa masa wanda ya tilasta masa rufe bakinsa jikinsa har tsuma yake saboda bala’i yace “waikai anyama kuwa kasan meye so a rayuwarka Yusuf to bari kaji idan baka sani ba ka sani inasonta kuma ina fatan na mutu da soyayyarta wlh nayiwa zuciyata alqawarin bazan sabawa farin cikinta ina sani ba Umaimah tana sona jiya nagano soyayya ta da tausayina har yanzu a cikin idonta Maliha ta fadamin tun jiya take tambayarta Ina Ina me nakeyi har turowa tayi tazo taga Ifyta Umaimah tana kishin ganin nayi tarayyah da wata mace saboda haka bazanyi ba har abada zan hqr na ringa azumi har zuwa Ikcn da Allah zai yankemin ya kawomin mafita amma bata hanyar aure ba na hqr da aure har abada indai bada bloody bane kuma koda banda rabon sake aurenta inason na mutu da soyayyarta saboda itama nasan da tawa zata mutu wlh Yusuf na tsani mutumin nan da yake ganin kansa wai mijinta kayyy! kayyy!! kayyy!!! badai miji ba dan riqon qwarya wai harma ciki yayi mata kuma ma harta kusa haihuwa”

 

Ya mgnr yana dafe kansa yana jan zuciya yace “babu komai qaddara ce da kuma rabo wannan kadai ya isheni ishara” ajiyar zuciya Yusuf yayi cikin tausayin abokin nasa yace “kayita addu’a Allah yana sane dakai zai kawo maka mafita yawwa kaji kuwa cewa matarka tana gdan mahaukata?” Dagowa yayi da sauri yace “wa kenan?” Murmushi yayi yace “matarka data rabaka da kowa kaqiji kaqi gani matarka data rabaka da farin cikinka jiya nake samun Ibrn ta haukace sai tonawa kanta asiri take har tana fadin yanda tayi ta rabaka da Umaimah da bayan ka daketa ka saketa komawar da tayi akan a haukata Umaimah yanda bakai ba wani ma bazaiyi sha’awar rayuwa da ita ba taje ta hado abinta tazo tayi ita kuma Umaimah tayi aure wannan dalilin da kuma addu’a sune suka mayar Mata da abinta kanta” qwafa yayi yace “narasa me muka tsarewa mutane kowa yake nufin mu da sharri Allah shine muka dogara dashi kuma shine abin dogaron bloody” yana mgnr yana dafe qirjinsa yace “bani maganina nasha qirjina ciwo yakeyi”

YA KAMATA KI KARANTA:Matar Makaho Part 11 Hausa Novel

Haka sukayi sallama Yusuf ya tafi kwanaki biyar tsakani ya gama dukkan shirye2nsa ranar daya cika sati da dawowa daga India ya shirya sai birnin
California na qasar amurka inda suka bashi katafaran gdan zama da zundumemiyar mota da matsayin me girma a world Bank.

Sati hudu da rasuwar su Shurafah Umaimah ta haifo yaranta biyu mace da namiji kyawawan gaske farare tas masu kama da ubansu fari irin na fulanin Yola wai zokuga murna gurin D.S anyi yaya shine yayi musu huduba da Zulaiha da Kabir aka mayarwa da Hajiya chibinar ta sannan yasa wa namijin sunan mahaifinsa aikuwa yaran sunga gata amma shi yayi musu inkiya da Nawwas da Nawwarah ranar suna tazo akasha bidiri abu gwanin sha’awa har kuka Umaimah tayi saboda gatan data samu gurin danginta da dangin mijinta goga Hameed ma da Daddy ya tura masa hoton yaran yayi murna sosai yaji qaunarsu har cikin jininsa ya rinqajin dama shi ta haifawa yaran bayan taro ya watse da kwanaki uku suna kwance da Sulaiman aka kirashi a waya ake fada masa anyi musu rasuwa a Adamawa qanin mahaifinsu ya rasu yaji mutuwar sosai don zaune ya tashi ya hada kai da gwiwa daqyar ta lallabashi suka kwanta da asuba ya tashi ya shirya Ikcn har qaninsa Nura yazo daukarsa zasuyi sammako itadai Umaimah hakanan tarinqa jin gabanta na faduwa daqyar ta bari yayi kissing yaran ya rungumeta a jikinsa ya fita har ya fita ya dawo ya kirata ya janyota jikinsa yace “amana nabar miki yarana ki rayu dasu cikin aminci inasonki Umaimatu”.

gidan uncle 72

KARANTA:Gidan Uncle 2 Complete Hausa Novel