Abban Sojoji Chapter 45 Book 2

Hausa novel by zamgist.com.ng

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin abban sojoji chapter 45 book 2 wanda hafsat bature ta rubuta takuma wallafah.

Abban Sojoji Chapter 45 Book 2

Abban Sojoji Chapter 45 Book 2 Hausa Novel Complete
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 430kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author Hafsat Bature
File format Txt
Published date 16 – 04– 2023

 

Kadan Daga Cikin Abban Sojoji Chapter 45 Book 2

ABBAN SOJOJi

_mallakin_

_Hafsat Bature_ Boss Lady

Page 45 to 46

_wlh am so eager so see Babban yaya too_

_Subhanah, Walhamdulillah,allahu Akhbar_

“Yeah but we are not sure, ba tabbacin cewa gobe zasu dawo, muna zuba ido dai,’ kanal yusif ne ya bashi amsa,

Jinjina kai captain najeeb yayi tare da cewa “aiko bazan kwana ba, yau zan koma lagos, ba dani ba

dariya su kayi hajiya azeema tace “ashe muna da manyan baƙi, lion da tiger zasu dawo kenan, wannan karan bansan da wata rigima zai zo ba, Allah kaɗai yasan jinin da za’a zubar,’

Hankalisu twins ba ƙaramin tashi yayi ba dama suna zaune matse da juna, sunyi zuru zuru, zuciyoyi na bugawa,

Basu kaɗai ba hada fawan da su jabeer da irfan da sauran atakure suke jin kansu, a wurinsu zuwan Babban yayansu ba alheri bane, bawai don basu son shi ba, sai don tsoran abunda zai faru zuwansa,

“ae na jima ina bama ishaq shawara akan ya tunzura Abba, ya aurar dasu, wlh indai su kaji mace atare dasu zasu samu weakness ajikinsu su daina jin kansu tamkar dodonni,’ sakin baki su kayi jin abunda aunty babba tace,

Azeema tace “da alama bakisan wanene RAFAYET ba, ai rafayet zuciyarsa tamkar dutse take ! ban ta6a ganin mutumin da mace sam bata gabansa ba irinsa, sam bai da shauqi akan mata, ke shi fa hasalima yadda yake kallon jinsin sa namiji haka yake kallon mace,’ 

ta ƙarasa maganar tana kurbar lemun hannunta, general ishaq yace “kwara ki faɗa mata da kanki may be she will understand it now, i had been explaining to her about rafayet but taƙi fahimta,’ ya ƙare maganar yana kallonta,

Murmshi azeema tayi tare da gyara zama tace “Anzo inda nafi auki, anzo dai dai wurin ba mai sauka, rafayet da kike gani ba mutun bane ……..
dariya ce ta kubce mata su kansu dariyar suke ba don komai ba sai don maganarta takarshe da tace rafayet ba mutun bane,

dakyar ta saita dariyar ta ci gaba da cewa, ” Ai dashi da mahaifiyarsa halinsu kusan ɗaya ne, kaifi ɗaya ne wasu irin bauɗaɗɗun mutanene, koda yake in mukayi la’akayi da cewa mahaifiyarsa baturiya ce, sannan kuma ba musulma ba, yanayin rayuwarmu da tasu ba ɗaya bace, amma gasky munsha Wahalar fatima fiye da tunanin mai tunani, ta azabtar damu saboda muna kwakwar ƴa’ƴanta, har yau fa ita bata yarda cewa Allah ɗaya bane, taƙi karbar musulunci, kuma bata yarda cewa ƴa’ƴanta sun musulunta ba, in har zasu taka suje wurinta to fa basu ba yin sallah ko karatun qur’ani sai dai in ba dasaninta ba, dakyar fa aka samu rafayet ya musulunta har yakai shekara 20 aduniya ba shi ba musulmi bane,

ta tsagaita da maganar tana sauke ajiyar zuciya, gaba ɗaya sauraronta sukeyi, musamman Aunty babba da Amani su da basu son komai ba game da su rafayrt ba,

Su twins kuwa da fawan jikinsu yayi sanyi domin ana magana ne akan mahaifiyarsu,

Aunty babba tace “nikam inaso nason wacece fatiman nan, ya akai abba ya aure ta ba tare data karbi addinin musulunci ba, Kuma har akayi gangancin barin ya’yanta suyi koyi da addininta ina nufin rafayet da ki kace yakai 20 yrs batare da yakarbi addinin musulunci ba, sannan ina fatiman take a yanzu, don ni ban ta6a ganin ta ba,’

Anzo dai dai wurin, ina fata kowa zai kasa kunnansa ya saurara muda akayi agaban mu, acewar aunty azeema

……. ………….Bismillah……… ………….

Asalin family ɗinmu Hausa fulani ne, mahaifin.mu bahaushe ne haifaffen garin zariya, mahaifiyarmu kuwa bafullata ce yar jihar damaturu, Haɗuwarsu tafarko a barikin sojoji na kaduna state Allah ya haɗa jininsu har takai su gayin aure 

Mu uku ne a wurin iyayenmu banban cikinmu Shine hussain wato (Abban sojoji) tagwaye ne su Allah yayiwa hassan ɗin rasuwa tun kafin su mallaki hankalinsu, Akwai tazarar shekaru a tsakanin mu sosai dashi, shi ne nafarko sai kuma ni azeema daga ni kuma sai ƙanin mu gaba ɗaya, wanda shine autanmu mun girme shi sosai, wato ABUSUFYAN wanda ynx yake zaune a Ƙasar turkey,’

tun yana 20years a duniya, wan mahaifiyarmu ya bashi auren ƴarsa maryam, yarinyace mai ilmin addini sosai ga hankali da natsuwa, maca ce mai saukin kai, bata ɗauki duniya da zafi ba,

Itace matarsa ta farko, sun sha sosai kamar laila da majnun, domin mu kanmu shaida ne akan hakan, duk in yana gari tashiga tarairayarsa kenan, idan aka turasa aiki kuwa nesa ba ƙaramain shiga damuwa take yi ba, duk tabi ta susu ce,

Abban mutunne mai son ƴa’ƴa koda yake bashi kaɗai ba, mu dukkan mu haka muke da son ƴa’ƴa zumuncin family ɗinmu yana da ƙarfi sosai, bama wasa da sada zumunci,

Cikin ikon Allah maryam ta samu ciki, kowa ya hau murna musamman ammin mu grandma ɗinmu, dayake maryam mutuniyarta ce tana sonta sosai kasancewarta yar yayanta modibbo,

Haihuwa tafarko maryam ta haifo kyakkyawan ɗanta, santalelen yaro yaci sunansa Ishaq (wato general ishaq) daga shi kuma sai Abbas wanda ynx yake rike da mukamin colonel general, daga Abbas sai brigadier general Abuhaisam gashi nan zaune kuna ganinsa, daga shi kuma sai major genaral Osman dukansu tazarar 2 years ne a tsakaninsu su duka, daga shine maryam ta ɗan huta,

Bayan nan ne tafiya ta kama su Abba izuwa ƙasar america, an tura su zuwa halartar wani special training na sojoji da za’a gudanar, da courses na dabarun aiki,

Hankalin maryam ba ƙaramin tashi yayi ba, jin za’a tura mijinta ƙasar turai, tsoranta kada wata tagansa ta liƙe masa Acan, saboda yana da farin jini sosai, 

Aiko hakance ta faru domin kuwa da zuwan su Abba u.s wata zankaɗeɗiyar budurwa kyakkyawar gaske ta ƙella ido tagansa taji cewa duk duniya bawan da take so sai shi,

baturiyar ƙasar amurika sunanta Alexandra ita ƴa’ce ga commender in chief na armed forces, 
Mace mai tsananin ji da kanta, ita a tsarin rayuwarta, Namiji baya gabanta, idan akayi mata maganar aure sai tace, ita jin kanta take yi tamkar namiji don haka ba abunda zaisa ta yin aure don tafi ƙarfin ta zauna a ƙarƙashin wani, idan akayi mata maganar ɗa kuwa, sai tace ita karenta tony ya ishe ta, wani jibgegen kare ne Wanda ta raine shi tun yana jinjiri har ya fara tsufa,

Abba shine namiji na Farko daya karya wannan kudurin nata, At first sight taji duk duniya ba wanda yai mata sai shi~

Kuma gadan gadan taji tana son aurenshi, Iyayenta sun so su dakatar da ita, amma dayake su in yaro ya wuce 18yrs yana da ƴanci ba wanda ya isa ya takamasa burki, har shari’a zai iya yi da iyayensa insun takura masa,

Hakan yasa suka ƙyale Alexandra ta auri Abba, ba tare da sanin family ɗinsa ba, shi kuma soyayya ta rufe masa ido baya ganin kowa in ba ita ba, dama fa su akwai iya tarairaya ga ɗaukar wanka da jan hankali,

A nan los angels california suke da zama a katafaren gidanta, nata na kanta dayake itama ta tara kuma ta fito daga babban gida, kuma ita ma soja ce tana riƙe da muƙamin major genaral,

Sunsha soyayya kamar romeo da juliet, acan kuwa 9ja sunyi mamakin jimawar abba, ganin sauran da aka tura Us tare dashi duk sun dawo sai shi kaɗai,

Ga maryam da ƙaramin ciki, kullum cikin zullumi take akan mijin nata,

time ɗin daya shirya dawowa 9ja yasha wahala kafin Alexandra ta amince cewa zata biyo shi na wucen gadi,

Aiko lokacin sun ga tashin hankali, ganin abba ya dawo da mata jinsin turawa, ran mahaifiyarmu baƙaramin 6aci yayi ba, saboda ta tsani jinsin turawa, sbd tasancewa basu da kunya fitsararru ne, an tada tarzoma a lokacin, gaba ɗaya danginmu sukayi masa caaa akan alexandra,

Amma abun mamaki mahaifinmu Salahudeen ya amince masa, kuma ya tsawatar da kowa akanta, ya hana kowa ya sa baki akan alexandra, haka yayan mahaifiyarmu modibbo ya tsawatar mata akan taja bakinta tayi shiru, haka kowa ya zubama sarautar Allah ido 👀

A katafaren gidansa dake abuja suke zaune ya ware mata part ɗinta daban, na maryam ma da ya’yanta daban, kowa baya shiga harkar kowa,

Sam maryam bata kishi da alexandra, tafison su samu zaman lafia a tsakaninsu,amma ita alexandra kishin maryam take ji, bakomai yaja hakan ba face sanin cewa su ba’ayi musu kishiya, basa zama da kishiya,

Cikin rashin sani sai ga ciki a jikin alexandra wanda ya tayar mata da hankali saboda tana shan maganin hana ɗaukar ciki don ita bata buƙatar ƴa’ƴa arayuwarta,

taita faman kiciniyar cire cikin hankalin abba ya tashi, faɗa sosai sukayi a lkcn, yasha wahalarta sbd sai da takai ga har zuƙunna mata yake akan guiwarsa yana roƙonta akan karta cire masa ciki yana so,

dakyar ta amince bisa sharaɗin inta haihu, ba ita zata shayar da yaron ba, kuma ba a nigeria zata haifesa ba, tafi so taje can ƙasarsu saboda tafi yarda da likitocinsu, kada a kashe ta tsoran mutuwa gare ta, 

haka ta maida Abba kamar ɗan aikinta da matsayinsa da komai haka zai zauna, yana mata aiki komai takeso shi zatayi, ita dai maryam bata cewa komai binsu kawai take da ido 

Hankalinta kwance saboda haryanzu Abba yana tsananin sonta bai wulaƙanta taba, bai kuma canza mata ba, sa6anin wasu mazan da zaka gani daga inda suka yi sabuwar amarya tofa ita waccen tazama expire product, 

wata rana yana zaune ɗakinsa saiga alexandra ta shigo da ƙaton cikinta, hannunta ɗauke da farar takarda da wani rubutu ajiki wanda aka rubuta da harshen spanish, ta miƙa masa takardar da biro tace yasa hannu,

_Gudun rigima yasa bai tambaye ta takardar mecece ba kawai ya raftaka signature ɗinsa, ajiki tare da miƙa mata , tayi murmushi ta kar6a…

Domin sauke cikakken Littafin sai ku taba bulun rubutun dake kasa.

 

Download Now

 

WASU LITTAFAN DAZAKU SO KU KARANTA

Matar Hariji 61 To 70 Hausa Novel

Abban Sojoji Hausa Novel Book 3

Man of The World Hausa Novel Book 2

Abban Sojoji Page 100 Hausa Novel

Abban Sojoji Chapter 65 Book 2

Alheri Dankone Hausa Novel Complete

Yayana Mijina Complete Pdf Download

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*