Zaki Hausa Novel Complete

Barka da zuwa shafinmu na hausa novel inda muka kawo muku zaki hausa novel complete By Khadeeja Candy.

 

Zaki Hausa Novel Complete

Carar Zakaran dake harabar gidan ne ya katse min dogon bachin da nake. A hankali na matsa fuskata dauke da murmushi domin ko kadan hakan be bata min rai ba, na daga hannuna a sama ina mika tare da kara watsakewa, kamar kullum yau ma bachin ya min dadi, ba dan gurin da nake kwanciyar ba, sai dan farinciki da kwanciyar hankali da natsuwa irin ta masu wadatar zuci data cika min zuciyata nake kwanciya da ita a kowane dare.

 

Kamar wacce akai wa dole haka na bude manyan kuma lussasun idanuwana da suka rine suka sauya kala sakamakon dadewar da nai ina bachin. Akan farinciki na sauke idonuwana wato mahaifiyata wacce ke sanye da wani jan yade kodadden irin na talakawa kuma na gadonmu.

 

“Wainar ki ce take ci tun dazun aka aje miki”

Da yaren buzanci mahaifiyata take muna min kyanwar dake kusada ni tana cin waina.

Murmushi nai na kai hannuna na shafa kyanwar kana na shiga mata magana da yaren buranci.

“Kin cinye min waina ko?”

“Ataa yau ba za ki je baranki ba ne?”

Kanane ya tambaya, hakan yasa ni saurin tashi daga kwancen da nake, na fito daga cikin bunkar ina hamma ba tare dana rufe bakina ba, ba dan kuma ban san babu kyau ba, sai dan rashin kula da watsi da addini irin na mu na…

Da hanzari na nufi wani dan guri da muka killace da kwano domin yin wanka ko kuma ba haya. Ba wanka nai ba domin wanka be dame ni ba duk kuwa da kasancewar na fi kowa tsabta a cikin gidan mu amman a hakan sai na kwana uku ban yi wanka ba.

 

Fitsari kawai nai na fito da sauri na wanke fuskata da fassashiyar butarmu marar murfi, sai da na gama wanke fuskar sannan na nufi gurin da muke girki na dauki gawayin kara na saka a bakina na tauna na saka yatsana na wanke bakin na kuskure sannan na wanke kafafuwana na nufo bukkarmu da sauri tuna ban yi sallah ba yasa na dawo na dauki butar nai alwala na sake kowa bukkar wanda zan iya kiransa da dakinmu.

Zanen dake daure a kirjina na cire na dauki riga da wando na wani shudin yadi mai kamar laile na saka na dauki hijab na saka nai sallah mai kamar asha ruwan tsuntsaye, wato da sauri domin cikin kannanen lokaci na yi na gama. Bakin dankwali na dauka na cire hijab din kaina na saka bakin dankwalin mai kama da karamin gyale na rufe kaina kamar yadda na saba ko kuma na ce muka saba.

Na kai hannu na dauko madubi tare da gawayin dana daka na kwaba tare da man shafi a guri daya, tsayawa nai kallon kaina a madubin ina murmushin daya kara bayyanar da kyauwona har dimple dina suka bayyana, sai faman lumshen manyan idanuwana nake ina budewa. Abu ne da ya ke bayyane, bana bukatar kowa ya kalleni ya fada min cewar ina da kyau, kyau na hali ko na halitta kyau na jiki ko na fuska, ni kaina idan na kalli madubi kyawona tsorata ni yake, idan ba a kirani balaraba ba to ba za a cireni a jinsin india ba indiyawan ma sai an tona, hakika ni kaina na san ina da kyau na wuce misali, kyan dake hana ni shakaf a cikin al’umma, gashin kaina kadai idan na sake ya sauko mutune har mamakin yadda nake da yawan da tsohon gashin dake saukona har mazaunaina suke.

Ba sai na fada ba, duk wanda yasan jajayen buzaye yasan su da kyau da gashi sai dai a cikinsu ni din ma ta dabam ce a bangaren kyau.

Man dake gabana na gawayi na dauka na shafa a fuskata a take farin fuskarta da kyau ya gushe na koma kamar ba ni ba, dogon hancina kawai zaka gani ka iya gane ni shima kuma sai idan ka sanni farin sani sosai.

Sannan na mike tsaye na dauki kwagirin dana saba ratayawa a koguna (kwankwaso) idan zanje yawon bara na daura. Gurin da mahaifiyata take zaune naje ina mata sallama da yaren buzanci.

“Na tafi Nana”

Haka nake kiranta da sunan dana tashi naji mutane na kiranta da shi duk kuwa da kasancewar ba shine aihanin sunanta na gaske ba.

“Allah ya tsare a samo da yawa”

Ta fada min tana dariya ni kuma na kada kai na fice ina murmushin domin bata san gaskiyar abun ba, a duk tsawon kwanakin da nai ina aikin.

Sai da nai nisa da bukkarmu ta yadda babu wanda zai iya hango ni sannan na ra6a ta cikin kangon gidan da muke gaban bukkar mu wanda wani shahararren mai kudi yake ginawa na shiga ta gurin da aka fasa domin yin windows na fada cikin wani gurin da ban san me za ayi da shi ba, daki ko falo, na dauki kayan aikina na bi ta kofar gaba na fice, na saba ba tun yau ba, idan nai nisa da gidan mu da sunan zuwa bara kamar yadda mahaifiyata take saka ni sai na biyo ta window kangon gidan na dauki kayan wankin motana, na bi ta kofar fita na fito, har yau mahaifiyata bata ta6a sanin cewar ina wannan aikin ba, ni kuma ban ta6a ganganci fada mata ba, domin na san zata hana ni idan ta gano ba bara na ke ba, kamar yadda take son nai, ni kuma bana son barar domin tana ci min rai, kamar yadda take kankantar ni ga duk wanda na mikewa hannu na ce ya bani.

Karanta: The Sexy Boss Hausa Novel By Mamam Teddy

 

Download Novel

0 thoughts on “Zaki Hausa Novel Complete”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top