Kwarton Manya Hausa Novel Complete

kwarton manya hausa novel

Barka da zuwa wannan shafin namu, inda muka kawo muku cikakken littafin Hausa novel Mai suna: Kwarton Manya Hausa Novel.

Kwarton Manya Hausa Novel

Wani irin hayaƙi ne ya turniƙe ko ina na wannan gida , hayaƙi mai saka ciwon kai ,can cikin wani kitchen na hango wannan hayaƙi na fita ,wanda ko ba’a faɗa maka ba kasan icen ɗanye take amfani dashi ta damuna”. Zainabu abamu ta Ashirin, Zainabu abani ta goma”. Muryar yara kake ji kowa na faɗin Abashi na dai dai kuɗin sa, wacce ko aka kira da Zainabu ba abun da take sai aikin goge zufan dake saukowa tun daga goshin ta zuwa wuya”.

Sama’ila ne ya leƙo da kansa ta windon lange langen kitchen ɗin kamin yace ” Taɓ Allah shi kyauta ,mutane na cin Dauɗa basu sani ba”. Saka luddayin tayi cikin ƙullun kalallaɓan da take soyawa ,kamin ta buɗe murya cike da tsiwa ta hau cewa ” Eh Naji Allah yasa dattin jiki na nake ɓanɓarowa nayi maggi da gishiri na zuba a ciki duka bai dameka ba , bashi ne dai nace a sana’a ta babu ,baxan bayar ba”. Ke Ni kike faɗa mawa wannan maganan??.

Yayi maganan a zafafe dama so yake ta tanka ya buga banza”. Eh na faɗa maka ,ai Ni wlh da kowa xanyi faɗa indai akan kasuwanci na ne”. Tayi maganan tana juya ƙullun kalallaɓan nata da gaba ɗaya garin matafi na ɗari ba sai sauran cefane da tayi”. Sama’ila ne yayi saurin nufan Ƙofan fale falen kitchen ɗin da zumman dukan Zainabu ya buga ya gudu”.

Da Umma Halima sukayi arba,nan take ta ɗaure fuska ta mau tana magana cike da faɗa ” Tattara kabar gidan ,idan baxaka tafi harkar neman ka ba,to kaje dai ko ma ina ne ,na rabaka da Zainabu kaƙi rabuwa da ita dai ko? To bari Malam ya shigo zan sa ayi maku iyaka tsakani”. Cike da cizar yatsa Sama’ila ya juya ,sam bai so zuwan mahaifiyar tasu ba ,yaso ya bigi banza ne kamin ya bar gidan kaman yanda ya ƙudirta.

Zainabu abani kalallaɓa. Wani ɗan yaro yayayye yayi mata maganan yana miƙa mata kuɗin hannun shi ,hannu takai tana amsan kuɗin haɗi da buɗewa a tunanin ta ƴan biyar² ne guda biyu ,sai kuma taga ɗaya”. Taɓ amma wannan Uwar taka taci uwar rainin wayo, banda iskanci nine zata aiko ka da biyar in baka wainar fulawa dashi? To kaci Sa’a yau my temper is Off in maka na turawa, da ba don haka ba ,wallahi yanda ka fito mata kana Annuri da kuka zaka koma mata,don sai na kileka ladon bacin ran da ka sani”.

Fice mun da gani dan ƙaniyar ka”. Tayi maganan tana cilla Naira biyar ɗin a wuta haɗi da cewa ” Baxan bada biyar ɗin ba na ƙona ta ladan ɓacin ran danayi”.

Ganin haka yasa yaron ficewa kitchen ɗin da gudu yana komar mawa Uwar sa da kuka. Saidai ƴan sayan kalallaɓa kowa yana Son mawa Zainabu magana kan abun da tayi bai kamata ba ,amma kuma suna gudun bala’i ,hakan yasa sai dai su bata kuɗi ta sallame su suyi ta kansu. Zainabu kiyi sauri ki gama zan aikeki kasuwar Dole ki Sayo mun Kayan yaji”.

To Umma na kusa baifi na soya ta ɗari ba yanxu ƙullun ya ƙare,tayi ƙare maganan tana karkata kwanon ƙullun da baifi kudayi ɗaya da rabi ba,nikam nace bala’i wannan wani irin riba Zainabu kebi haka?. Zainabu wai inji maman mu tace ” Kiyi haƙuri ki bashi kallaɓan ta biyar ɗin yaye akayi masa”. Cike da masifa Zainabu ta juyo tana kallon yarinyar da ƙanin nata da ta cilla biyar ɗin sa a wuta ,kana tace ” baxan bayar ba ,ita tana bada bashin kayan sana’ar tane? Ni sai ta nemi cin mun mutumci a nawa ? To na cilla kuɗin huta ,ƙarikon yaye Allah yasa yau ya fito daga ciki duniya”.

Ki fice mun ke dashi kamin na tashi…tayi maganan tana rintse ido na masifa wanda da sauri yarinyar ta tasa ɗan ƙanin ta suka fice. A haka Zainabu tayi ta sai da kallaɓan ta gata da jama’a ,amma ba haƙuri kamin ta gama tayi faɗa babu iyaka. Tana gama kallaɓan ko wanka bata tsaya yi ba ,bare wanke fuska ta zura hijab ɗin ta iya gwiwa ,yaji dauɗan duniya baƙiƙirin. Umma karo kuɗin?”.

Wayyo Gindina Hausa Novel

Umma ne ta kalle ta sama da ƙasa ,kamin tace ” Zainabu Bazaki ɗan wanke koda ƙafa ba a haka zaki tafi??. Ɗan gyara zaman hijab ɗin ta tayi kamin tace ” Eh Umma a haka xan tafi , wa’anan mutanen Lagos ɗin ƴan iskan mutane ne,ko wanka nayi naci ado nasa gyale da atampha na fita sunana matan Aure a wurin su…baxasu taɓa kira na da budurwa ba indai ba shigar banza nayi ba ,nasa wando 3 quater ,idan kuma shi kikeso nasaka shikenan sai yanxu inna fita na tsaya a ƴan gonjo na siya da ribar da nasamu ta kalallaɓa”.

A’a ina ,maza kinji amsa ta fi ki Sayo mun Kayan yaji komai da komai ta ɗari da hamsin…to Umma sai na dawo “. A dawo lafiya”. Ficewa Zainabu tayi daga gidan tana nufan kasuwar Dole, alhmdullh a wannan karon batayi faɗa da tasi’u mai kayan yaji ba ,ta ɗauki hanyar dawowa gida ,wanda duk nesan gidan su da kasuwar a ƙasa take zuwa ta dawo a ƙasa ,ɗan kuɗin da aka bata na moto ta riƙe tace ” zata jah jarin wani abun ,haka take Zainabu yarinya ce mai zafin nema,tayi wannan sana’a tayi wancenn kuma duka du basu taru sun zama guda ba, yarinya ce fitinanniya ta gaske gata bata da tsoro a ko ina ta shiga ,indai kayi mata sai ta maka ,ƙarya ne a wuni batayi faɗa har da su damme ba ,wanda ita har gadara take da cewa ” bata faɗa da yarinya ɗaya sai su kai biyu zuwa uku,don idan ɗaya ne to tabbas xata mata lahani ,gomma sukai biyu zuwa uku ,to sai ta casusu.

Gata da farin jinin ƙawaye kowa Zainabu haka matar Aure da yara.amma fa Zainabu bata da mutunci sam….ita idan batayi faɗa ba har ciwo ma take cewa takeyi,faɗa ya zama mata jinin jiki, gata duk ƙawayen ta tsoron ta sukeyi ,saboda tana da ƙarfi kaman Shari’a ,bata taɓa dambe ba ita taci nasara akan wa incan ba. Haka xata kama ƴaƴan mutane ta bigi na banxa ,idan iyayen su sun gidan Umma sun kawo ƙara. Umma Halima tayi ta basu haƙuri tayi faɗa ma Zainabu har ta gaji.

KARANTA: Littattafan Hausa Novel Complete Guda 500

Hee heey Madam for ur babies”. Nan Zainabu taji Muryar wani inyamuri yana katseta da cewa ” For your babbie ,yana ɗaaga mata gonjon bby suit na yara”. Wani irin fusata Zainabu tayi a zuciyar ta tana cewa ” Wa’annnan inyamuran kullum iskanci ƙaruwa yake yi”. Bama baby ba a’a yanxu babbie take dasu. Kai kalle Ni da kyau Dan Uwar ka kaga nayi kama ma da wacce take da Aure har da yara??. Shegu ƴan iskan mutane kawai ,wato sai na fitar da tsaraici ne sannan nake budurwa a wurin ku ko? Wanda sukayi sabo da ganin tsaraicin mata,shiyasa shekaru ƙalilan ido ya makance”.

Inyamuri ne ya kalle yaya kallon ta kusa dashi haɗi da ware ware yana cewa ” what is she saying?. Eiyee kana nufin ma baka san me nake cewa ba?”. Kamin ya ƙara mawa Zainabu magana ne nan yaga ta ɗaga hannu tassss tana wanke fuskar sa da mari”. What of now? Nace yanxu fa kaji me nake cewa ko sai na ƙara wanke fuskar ka da wani marin?. Cikin tsoro da rawar jiki inyamurin yace Sorry my friend sorry pls.

Yanxu kayi magana tayi maganan tana wuce shi da mutanen da suka fara taruwa tana tafe tana cigaba da zage zagen ta”. A wurin ba inyamurin kaɗai ba ne ya tsorata da Zainabu kusan duka inyamuran sun kasa mata mgn ,basu taɓa ganin yarinya wacce ashekaru ba zata haura sha takwas 18 ba ƴar bala’i kaman Zainabu ba…wannan yasa su kasa yi mata haɗin kan da suka saba ,suci mawa bahaushe mutunci. Haka suna kallon ta ta ɓace ,sauran ko hausawa sai dariya sukeyi ,suna jin daɗin abun da Zainabu tayi…………

 

Ƙwarto ƙwarto manya naji wurin ya ɗauka ,waigawa nayi don ganin waye ake kira da wannan suna haka?? Amma sai dai nakasa fahimta a cikin su huɗun waye ke da wannan suna,kasantuwar dukkanin su Kaki ne jikin su ta Sojoji. Ɗayan su na gani wanda shi gaba ɗaya su hankalin su ke akan shi….idon shi a lumshe suke bai buɗe su duka ba, hannun sa riƙe yake da Sigari yana busawa haɗi da fitar da hayaƙin ta baki da hanci irin na tatattun ƴan duniya…a sojojin ma shi ɗin Zakka ne cikin su a tachewa”.

Irin jijjiga jijjagan mazan nan ne ,don sun wuce akira da ingarma,ga tsawo ga ƙiba…. Fari ne tass wanda yafi kama mun da ba cikakken bahaushe ba ruwa biyu. Wata ƙil ɗaya ciki daga iyayen sa ba ɗan Africa bane ba duba da yanayin zubin sa..ƙara sa sigari yayi yana zuƙar ta da ƙarfi yana furxarwa cike da tacewa t ƴan duniya,wanda anan ne na kuma ƙare masa kallo ,hulan kansa na gani yasha ban ban dana Sojojin dana saba gani.

 

Domin kuwa tasa jah ne,wanda yasani jah baya ina naɗo maku rahoton baya baya kasantuwar fahimtar wani soja ne a gaba na… Soja ne militry Army wanda idan sojoji suka ga ɗayan su gudu sukeyi ,su ba’a yar je masu faɗa da soja ɗaya ba ,sai idan sun kai goma zuwa sha biyar ,saboda idan suka ce zasu ba Soja horo ko duka zasu kashe shi zuwa ɗaya”. Wannan yada su Bama ka ganin irin su masu jan hula , a ko’ina suna killace sai wani irin babban ɓaraka ko yaƙi ya tashi a ƙasa ake fito da irin su kaman goma,to duk girman runduna sai sun gama da ita”. Habab naji an kira sunan shi”……………..

Wasu Na karatun: Sakon Barka da Juma’a and Barka da Juma’a Messages

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*