An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a ranar Laraba 28 ga watan Yunin shekarar 1927 wanda ya yi daidai da 2 ga watan Al Muharram shekarar 1346 a garin Nafada jihar Gombe, arewa maso gabashin Najeriya.
Mahifinsa mutumin jihar Bauchi ne, yayin da mahaifiyarsa kuma ‘yar jihar Gombe ce, kuma dukkanninsu Fulani ne.
Yana kuma da ‘ya’ya sama da 80, wadanda a cikinsu wadanda suka haddace Alkur’ani sun kai 73 ko 74.
Malamin ya rayu a gaban mahaifinsa kuma ya haddace Alkur’ani a wurin mahaifinsa, kana ya tura shi ya shiga duniya don ya gyara tare da karo karatunsa.
A hirarsa da BBC a shirin Ku San Malamanku, malamin ya ce ya kuma samu nasarar kara fahimtar haddar Alkura’ani mai girma a wuraren da ya tafi neman karatun.
”Lokacin har na rika ji wasu mahaddata na kirana da Goni ko kuma Gangara, saboda haddace Alkur’ani mai girma,” in ji shi.
Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma ce mahaifinsa ya sake tura shi karo ilimi a garin Bauchi amma kuma neman ilimin bai yi tsawo ba saboda yana cikin karatun sai Allah ya bayyana sha’anin darikar Sheik Ibrahim Khaulak, inda daga nan ne ya shiga ciki ya kuma zama daya daga cikin almajiran Sheik Ibrahim Khaulak din.
Malamin ya kuma kara da cewa; ”Saura kadan in haddace Alkur’ani ina da shekara 13 amma sai muka shagala wajen noma da kiwo, don haka ban karasa haddacewa ba sai da na kai shekara 19 zuwa 20.”
Ya kuma ce babban malaminsa shi ne mahaifinsa, amma kuma ya ce ya soma karatu a hannun Malam Baba Sidi, da Malam Saleh, da Malam Baba Dan Inna.
Kana ya ce ya kuma je garin Zaria wajen su malam Abdulkadir nan ma ya taba karatu, kana ya je garin Kano inda ya sadu da manyan malaman Kano ya kuma yi karatu a wajen Malam Shehu Mai Hula, da Shehu Malam Tijjani, da kuma Shehu Atiku.
Sirrin Malam na haddar Alkur’ani
Gaskiya ne da farko muna da asiri na Alkurani da iyayenmu suka samu a Borno wajen Bare-Bari, da shi muke amfani wajen haddar Alkur’ani.
“Daga bisani lokacin da Sheikh Ibrahim Inyass ya bayyana ya ce ya roki Allah ya ba shi karamar haddar Alkur’ani, sai ya zama shi kenan an huta da nemo maganin karatun Alkur’ani Shehu ya riga ya roki Allah mutane su haddace Alkurani cikin sauki,” in ji shi.
”Za ka samu yaro mai shekara bakwai ya hadadce Alkur’ani, har mai shekara biyar ma ya haddace Alkur’ani,” in ji malamin.
”Na gode wa Allah, babban abin da Allah ya ba ni babu kamar Musulunci da son Annabi Muhammdu (S.A.W), da haddace Alkur’ani, ya kuma kara min da karbar darikar Sheik Tijjani jikan Manzon Allah.”
Malamin ya ce ya tattaba karatuttuka amma wanda yake da shaida a kai shi ne haddar Alkur’ani, da tafsiri wanda ya ce su kan su manyan malaman tafsirin sun tabbatar ya iya.
Dangantakarsa da Sheik Ibrahim Inyass
Sheik Dahiru Usman Bauchi ya kuma shaida wa BBC cewa, baya ga kasancewa almajirin Sheik Ibrahim Inyass, akwai karin dangantaka mai karfi a tsakaninsu.
Ya ce: ”Alhamdulillah baya ga zama almajirin Sheik Ibrahim na kuma zama khadiminsa, kana na zama surukinsa, don na auri ‘ya’yansa har sau biyu, na auri daya bayan ta rasu ya sake bani auren daya.”
Kana malamin ya ce baya ga haka, yana ƙauna tare da mutunta malamai a ko ina suke, musamman malaman Tijjaniyya.
”Babu abin da ke faranta min rai irin na ga Musulunci ya bunkasa, in ga darikar Tijjaniyya ta bunkasa,” in ji malamin.