Tarihin Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku cikakken tarihin abba kabir yusuf wanda akafi sani da Abba gida-gida.

A ranar litinin 20 ga watan Maris Na 2023 hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana Abba gida gida a matsayin Wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.

Tarihin Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)

An haifi abba kabir yusuf a ranar 5 ga watan January, 1963 a karamar hukumar Gaya dake jihar Kano.

Abba kabir yusuf dan siyasa ne kuma shine sabon zababben gwamnan kano. Abba gida gida wanda surukine ga Rabi’u musa kwankwasa.

Abba gida gida yana da mata biyu da ‘ya’ya da dama.

ILIMI

An haifi Abba ne a karamar hukumar Gaya dake jihar Kano a Najeriya.

Ya yi makarantar firamare ta Sumaila, daga nan kuma ya yi makarantar sakandiren gwamnati a Lautai, karamar hukumar Gumel (jihar Jigawa), inda ya kammala karatunsa na digiri na farko a shekarar 1980.

Daga nan sai ya samu gurbin karatu a Federal Polytechnic, Mubi, inda ya samu takardar shaidar kammala karatunsa a fannin civil engineering a shekarar 1985.

Ya yi karatun digirinsa na biyu a jami’ar Bayero ta Kano a fannin harkokin kasuwanci.

SIYASA

Abba gida gida ya taba zama kwamishinan ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri Na (jihar Kano).

Abba ya tsaya takarar gwamna a zaben 2019 da aka gudanar a shekarar ta 2019, Inda gwamnan jihar Kano mai ci a lokacin (Abdullahi Umar Ganduje) ya doke shi.

Abba kabiri ya kai kara a kotu yana mai cewa shine zababben gwamna, bayan da kotun ta yi watsi da karar.

SHEKARU

Abba gida gida yanada shekaru 60 a duniya. An haifeshi 5 ga watan janairun 1963.

Karanta:ÂSakamakon Zaben Gwamnan Kano 2023