Barka da zuwa wannan shafin namu inda zamu kawo muku sakamakon zaben jihar kaduna 2023 wanda aka kammala tattara bayanai.
A ranar asabar aka gudanar da zaben gwamna dakuma ‘yan majalisun jiha a Kaduna
A wannan shafin zamu muku sakamakon zaben jihar kaduna 2023 inda zamu sanar muku waye ya lashe zaben gwamna a jihar ta kaduna.
Sanata Uba Sani (APC) ya lashe zaɓen jihar Kaduna
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC, ta ayyana ɗan takarar APC sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Kaduna 2023.
Bayan share sama da kwana biyu ana jiran sakamakon jihar, a ranar Litinin kuma aka kawo karamar hukuma ta karshe (Kudan), wadda ɗan takarar PDP Isa Ashiru ya fito daga cikinta.
Sanata Uba sani na jam’iyyar APC shine wanda zai gaji gwamnan jihar na yanzu Malam Nasi El Rufa’i da wa’adinsa zai kare a watan Mayu.
Hakan yana nufin jam’iyyar APC mai mulki za ta ci gaba da jan ragamar jihar har zuwa nan da wasu shekaru huɗu dake tafe.
Sakamakon Zaben Jihar Kaduna 2023
Sanata Uba Sani, dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna ne ke kan gaba a sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana a Kaduna.
Daga cikin sakamakon da aka sanar a kananan hukumomi 22 cikin 23 da ke jihar, APC ce ke kan gaba da kuri’u sama da 12,000 a kananan hukumomi 10 da ta doke dan takarar PDP Isah Asharu, duk da cewa ya samu nasara a kananan hukumomi 12.
APC ta yi nasara a Giwa, Ikara, Kauru, Sabon Gari Kubau, Zaria, Kaduna North Kananan Hukumomin Kaduna ta Kudu, Igabi da Birnin Gwari.
PDP ta samu nasara a kananan hukumomi 12 wato; Kaura, Sanga, Kajuru, Jaba, Makarfi, Jama’a, Zangon Kataf, Soba, Chikun, Kagarko, Kachia da Lere.
Sakamakon zaben karamar hukumar Kudan, har yanzu ba a bayyanashi ba, inda anan ne gidan dan takarar PDP.
INEC ta dage tattara sakamakon zabe zuwa karfe 10 na dare.
===================================
Ku kasance da wannan shafin namu inda zamu kawo muku cikakken sakamakon zaben da yanda ya gudana a jihar.
Sakamakon Zaben Shugaban kasa a Jihar Kaduna
Jam’iyyu | Kuri’u |
---|---|
PDP | 554,360 |
APC | 399,293 |
Labour | 284,494 |
NNPP | 92,969 |
Parfesa Mohammad Zayyan Umar wanda yakasance mataimakin shugaban jami’ar tarayya ne dake kebbi ya sanar da sakamakon zaben shugaban Kasa daga kananan hukumomi 23 dake jahar Kaduna.
A lokacin sanarwar ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP ke kan gaba da kuri’u kimanin 554,360, A yayin da APC tazo na biyu da kuri’u 399,293, Inda Jam’iyyar Labour tazo na uku da kuri’u 284,494 saikuma Jam’iyyar NNPP ta zo ta hudu da kuri’u 92,969.
Wakilin manyan Jam’iyyu (Party Agents) guda hudu da su ka fafata a zaben, duk sun amince da sakamakon kuma sun sa hannu.
Kwamishinan ‘yan sandan kaduna Mai suna, CP Yakini Ayoku wanda aka fara tattara sakamakon da shi kuma aka kare zuwa cikin daren ya nuna gamsuwar sa da sakamakon.
Shima Jami’in zaben, Parfesa Mohammad Zayyan Umar wanda shi zai kai sakamakon zaben Abuja yau Talata ya ce tattara sakamakon ya gudana cikin armashi da inganci.
A halin yanzu cibiyar bayyana sakamakon zaben shugaban kasa dake abuja na dakun isowar wannan sakamakon zaben na jihar Kaduna domin sanarda sakamakon a hukumance.
WASU NA KARATUN:
Leave a Reply