Muhimmancin goruba ga rayuwar ɗan Adam

Goriba na cikin ‘ya’yan itatuwa dangin kwakwa da ake samu a ƙasashen Afirka musamman Masar da Sudan da Kenya da sauran ƙasashen Larabawa.
 
Ga wanda ya san bishiyar goruba, ya san ba ta da kauri da kuma rassa marasa kaushi, kowanne yana ɗauke da koren ganye mai ƙarfi kuma ƙarami mai ɗan faɗi.
 
‘Ya’yanta kuwa suna da ɗan girma kamar na lemon zaƙi masu launin ruwan ƙasa da kuma ƙarfi sosai, wanda ke da zaƙi idan ana ci – har ma a yi santi wasu lokutan.
 
A ƙasar Hausa, goriba na ɗaya daga cikin abubuwan da mata masu ciki suka yi fice da cinta da kuma yara.
Al’ummar Masar da suka gabata shekaru aru-aru na kallon bishiyar goriba a matsayin wani abu mai tsarki kuma dalilin da ya sa ake yawan samunta a ƙaburburan sarakunansu kenan wato Fir’aunoninsu.
 
Sai dai akasarin masu amfani da wannan ɗan itaciya ba su san amfaninsa ba a jikinsu da kuma sauran ayyukan da ake gudanarwa da shi.

Amfanin goriba a rayuwar ɗan Adam

Binciken masana da dama ya nuna cewa goriba na ƙunshe da sinadaran flavonoids da phenols, waɗanda ke ɗauke da kariya daga ƙwayoyin cuta.

Shayin goriba abu ne shahararre a Masar da Sudan da Najeriya da ma wasu ƙasashen, kuma an yi ittifaƙi cewa tana da amfani sosai ga masu ciwon suga.

Al’ummar Masar na yawan amfani da goriba wurin maganin cutar hawan jini.

Tsawon shekaru, al’umma a yankin Turkana na ƙasar Kenya amfani da wani maganin gargajiya da aka samar daga busassun ganyen goriba domin samun kariya daga wasu ƙwayoyin cuta.

Kazalika, wasu kan samar da ruwan lemo na goriba.

Wani bincike da Adaya ya gudanar a shekarar 1977 ya nuna cewa akan yi amfani da saiwar goriba wurin kula da rauni a jikin mutum musamman cizo ko harbin wasu ƙwaruka.

Har wa yau, ana amfani da saiwar goriba wurin haɗa ƙwayar maganin hypolipidemic wadda ke taimakawa wajen jinyar cutar hawan jini.

Haka nan, akan yi amfani da ita wurin hana zubar jini ga mata bayan haihuwa.

Yayin shan shayin goruba a Kano

Wani sabon yayi da ya bulla a jihar Kanon Najeriya shi ne yadda Mazauna birnin da dama suka koma shan shayin goruba maimakon irin na sauran ganyen shayi da aka saba da su.

Karbuwar da shayin yake yi ne ma ya sa matasa da yawa fara sana’ar sayar da shi.

Masana lafiya dai na nuna cewa shayin na goruba na da alfanu ga lafiyar dan adam amma kuma ba kowa da kowa ba.

Wakilinmu na Kanon Khalifa Shehu Dokaji ya ziyarci teburin wani mai shayin na goruba, wato Yusuf Muhammad da aka fi sani da Abba 10.

Ya ce ya zabi sana’ar sayar da shayin goruba ne saboda hana zaman banza da kuma fadar da mutane ke yi cewa tana maganin wasu cututtuka a jikin dan adam.

Wakilinmu ya tarar da matasa da dama a teburin mais hayin da suka ce suna sha ne don kara lafiya.

Ba wai iya maza ne kawai ke shan shayin na goruba ba, su ma mata ba a bar su a baya, sakamakon yadda suke tururuwar sayen garin ta a wasu daga cikin manyan shaguna a birnin.

A yanzu dai a mafi yawan gefen titunan birnin Kano, teburan sayar da shayin goruba na ci gaba da karuwa, wanda matasa da magidanta ne ke tururuwar sayansa.

Masu lura da al’amuran yau da kullum na kallon hakan a matakin kau da zaman banza a tsakanin matasan jihar.