Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku kalaman soyayya masu nishadantarwa wadanda zaku turawa masoyanku domin faranta musu rai dakuma Karin dankon soyayya.
Wadannan kalaman soyayya masu nishadantarwa suna da matukar tasiri ga rayuwar masoya, tura irin wadannan salon izuwa masoyi kokuma masoyiyarka zai kara muku farinciki dakuma karfin son junanku.
Ina fatan mai karatu ya shirya tsab domin yanzun nan zan fara antayo muku da wadannan kalaman soyayya din masu nishadantarwa.
Ko kunsan me kuwa? A ranar dana turawa masoyiyata wadannan kalaman, ranar harda wainan fulawa tayomin. Abun yabani mamaki nace baby na, yau kuma harda hidima haka, sai tace kaidai bari honey wlh kalaman naka ne nayau duk naji sun sa naji sonka yakaru a zuciyata.
Anma dai bari nayi Shiru a haka kar nacika ku da surutu.
Kalaman Soyayya Masu Nishadantarwa
1. A duk lokacin da nake tare dake nakanji natsuwa ta game mani jiki, hakan nasani manta duk wata damuwa dake tattare dani. Inason ki kasance kusa dani a kowane lokaci.
2. Kece kike sani tashi bacci da murmushi a kowace safiya, kece fitilar dake haskan min duniyar nan masoyiyata.
3. Nakanji natsuwa ta game mini jiki a duk lokacin dakake rungume dani masoyina. Ina matukar alfahari da irin soyayyar dakake nunamin. Ina Sonka!
4. Babu adadin kalmomin dazasu iya bayyanar da irin son danake Maka, kai ba masoyi kadai bane a gurina, kaidin rayuwatane. I love you!
5. Dariyar ka itace jindadina, murmushin ka kuma shine farincikina. Ina alfahari dakai masoyina.
6. Haduwa ta dake nagane cewa shi so, bawai jinsa ake kadaiba, shi so zabine shiyasa nake zabenki a matsayin masoyiyata a kowane lokaci na rayuwata.
7. Soyayyarki itace babbar kyautar dana samu a duniyarnan, nayi matukar sa’a da samun masoyiya kamarki a kusa dani, nayi miki alkawarin takatsan-tsan da wannan soyayyar tamu a kowane lokaci.
8. Tazara takan iya sa muzama nesa da juna, anma hakan bazai iya sauya irin soyayyar danake miki ba. Kina zuciyata a koda yaushe.
Kuci gaba da karantawa anan:Â Kalaman Soyayya 2023 Masu Dadi