Hatsabibin Boka Complete Hausa Novel

Barka da zuwa wannan shafin namu inda zamu kawo muku cikakken littafin hatsabibin boka complete hausa novel

Hatsabibin Boka Complete Hausa Novel

HATSABIBIN BOKA

Page 1-2
By
Gentle Lady

Hatsabibin Boka Complete Hausa Novel

Dasunan Allah mai rahma maijinkai”” dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki maikowa mai komai ina kara godiya ga Allah subhanahu wata ala “” Wanda yabani ikon fara wannan labarin Allah yasa jama a zasu amfana da fadakar wardake cikinsa

Hakika komai kaga yasamu bawa mukaddarine daga Allah Amman kuma akwai sanadi wannan labarin kirkirarren labarine nayishi domin tsokaci dawadansu abubuwa dasuke faruwa acikin al umma””

Wacce wannan labarin yaxo daidai darayuwarta saita tuba tadaina domin ganin makomar Wanda yake kwatankwacin irin halintaa Allah yasa mudace Ameen

Wannan labarin narubutashine ra ayin kaina danhaka Wanda yaji zai iyah karantawa banhanashiba saidai kuma akiyaye karwani ya sarrafamun shitawata hanyaa idan kunne yaji gangar jiki tatsirah

BISMILLAH

***********************
Gabadaya unguwar cinkushe take da manyan motoci sai kaikawo sukeyi alamu sun nuna wani mihimnin buki akeyi na wani kasurgumin maikudii Dan la akari da yawan motocin dasuketa karakaina hakazalika masu tsadar gaske kaima kasan ba bikin”” fukara”u bane

Bakin kofar gidan tacika makill da maroka dakuma masu kidaa”” ahakan nasamu tattakawa zuwa kofar gidan duk da dakyar nasamu nakai wajen asheni banga jama a ba dankuwa cikin gidan tamkar anabikin nadin sarautane””

Sai rarraba ido nakeyi domin samun hanyar shiga wannan katafaren gidan ginane namusamman maihawa hudu anyimasa fentiii da farin fentiii maishegen kyau da shekiii wannan gidan kusan yafi kowanne gida kyau dakuma tsari gabadaya ya haskaka unguwar anayiwa gidan nan lakabida farin gidaa!!

Tofa Allah yasa abunda yakecikinsafarine

Kutsa kaina nayi Cikin gidan kofar shigama abar adubace””nagama zagayena nikam banga alamar  matar gidan ba”” dankuwa irin wannan gidan yakamata ace matar gidan ta banbantaa dayanbukiii ajikinta kadai za agane””

Nayi zugum inabinsu dakallo nace tomezaihana insaurari firarsu watakil nagane matar  gidan  aciki wannna shawarar nayarda da itah nafarabi lungu dasako ina saurare abun takaici abun bakinciki duk inda nawulga zancensu kusan dayane kishiyaaa!!!!

Waimenene illar kishiyane??? Kumata kunada abun mamaki idan mijinku ya aureku yace zaikara aure kuyita fitinaa toyakenan idankuma keza a aura??? Itakuma matarsa taceme??? Yakamata zuwa yanxu mata sugane Susan kalar kishinda zasuyi kuyi koyi da matan Manzon Allah (S A W) suma sunada kishi saidai nasu sunayinsane abisa tsari kowacce tanarigengen wajen kyautata masa domin tasamu matsayi fiye Dana dayar

Amman wasufa saboda tsabar bala.i da masifa daga ranarda yasoma maganar kara aure tofa ya ballowa kansa likii zatadaina wanka tabar dafamasa abincii wata hatta gadonta baxata barshi yakwantaba dazaran yace yimun kaza tace bazanyiba kajecen wajen amaryarka taimaka tabar yayanta acikin wahala waifa a irintata wautar waita naso tazubawa mijin haushine shikuwa dayafita iyawa saiyabuge iskanta yayima dadai duniya kamarma baisan da zamantaba sai idan tayi masifar  tagababuci kuma biki yanata karatowa sai afara yangyare gyare waidaga bayakenan sadaka da bajawara bayan kinzubarda girmanki kimarki darajarki

Bari nabaku wani sirri wlh idan mijinki zaiyi aure kika kwantarda hankalinki zakici arziki komai kikeso zaiyimaki domin yataushi zuciyarki kuma zai rika tambayarki menene kikeso haka zalika komai zaiyiwa amaryar zairika neman sha wararki”” sabanin idan kikasoma fitina zaiyibanza dake duk wuyartadai kece akasa bazaki hanashi auren ba

Saikiyi ba1 ba 2. Darajarki dayake gani kinbata bazaisake yarda dakeba kuma koda amaryar tashigo gidan akatada fitina kodakuwa kece mai gaskiya bazai yardaba zaice aiyaga take takenki tunkamin yayi aure kiketa fitina tosaidai kiyi abunda zakiyi matadai matar sace matsayinku daya awajesa uwargida kinga mutuncinki yaragu

Idan kikacigaba da fitina karshenta yasakeki yazauna da amaryarsa wagari yawaya???? Hakan yana faruwa sosai acikin al.umma

Iyayena mata iyayen gobe mukula mukiyaye kishii ba haukabane!!!

Nafara biyar lungu dasako cen saman hawa na uku nayi katari da matar gidan “” sosai nafirgita daganinta sam bazaka taba cewa matar gidan bace”” irin matan nan ne wadan da mazajensu suke dakudi amman idan kagansu bazaka siyesu kwandalaba duk kayanda suke siyamasu basa sakawa idan kagansu mai aikinsuma tafisu daraja amman fa idan zasuje gidan bukii kokuwa zasuje unguwa zakadauka basason taka kasa saboda tsabar tsafta””

Abokananta dasuke gefenta dayar tace wai lubabatu mezaihana kitashi kiyi wanka gidan nanfa yanbiki sunfara cikashi kosokike araina class nakii
Wacce take gefenta nadama tace hajiya larai kibarta hakan mana”” dame zataji dakishiyarda akai mata kokuma da kwachakwaimar kwalliya?? Kinsan Allah danice kotaron biki bazanyiba

Wata tace habadai hajiya larai aiyanzu andaina wannan yayin idan za akawomaka kishiya kahana kanka jindadin rayuwa yanxu kissa akeyi kikwantarda kai tamkar mumina ni wlh mijina yayi aure saina gasawa amaryar gyada ahannunta

Suka kwashe da dariya haryanzu uwargidan uwar iko batayi  maganaba”””
Larai tace hajiya sadiya  kenan ashe wacce tsautsayi yasaka tashigo gonarki zatafi gwammacewa kwana akabarintaa” suka sake shekewa da dariya”” amman banda itah””

Haba kukuwa banda abinku ai kishiya abokiyar  zamace menene abunkishin??? Abunda akasaba bakifa badainawa za ayiba nisam banajin kodar akan auren nan
Hajia lubabatu ce mai wannan maganar””

Hajia larai tarike haba lallai hajiya kodayake wannan bashine nafarkoba bakyada jinkomai nikam wlh bazan sakewa mijina fuskaba dahar zaiyi sha awar karawani auren”” tirkashi ranarkuwa dahakan tafaru wlh sai yayi zaton aturu aka kwantoni dan zankoma masa  mahaukaciyar karfi dayajii

Wannan karon harda hajiya lubabatu wajen dariya wata matashiyar budurwace tabude kofarda sallama””” sukabita dakallo babu  wanda ya amsa tafara kallon mutanen dasuke cikin dakin daga bisani tadauke kanta kamar taga kashi
Hajiya lubabatu ce ta daka mata tsawa ke wacce irin shashashar yarinyace labila???? Zakishigo wamutane daki haka bakiganin bakine dani??? Baki tatabe nagansu mana mom kuma ainayi sallama “” takai karshen maganar tanasake wurgamasu mugun kallo ta murguda bakiii
Kinyi sallama gidanwa mu kuramene dabamujiba”” ta kwabe fuska to tayazakuji bayan kuna tazuba shegen surutu wanda bazai kareku  dakomai ba””
Ido lubabatu tazaro sukam su hajia larai inda sabo yaci acesun saba dahalin  labeela”” tace labila waiyaushe kikazama tsagera nifa mahaifiyarkice kinamun magana tarashin da a

Tasake mere baki”” tacee  malamai niku gyara zanduba jakata “” tayi maganar tana rike kunkumi afusace hajia lubabatu tasauko daniyar dukanta su hajiya sadiya sukariiketa haba hajia baidace kidaketaba ai labila karamar yarinyace kuruciya ce take damunta

Kotakansu batabiba tahauduba  jakarta”” tadauko sannan takallesu daibayan daya tace naji kuruciya tana damuna amman karani saudubu daku sakarkarun  mataa mstw tsaki taja tafita tabar dakin

        Gabadaya  dakin yayi tsit bakajin motsin komai saina saukewar ajiyar zuciyarasu” labila karamar yarinya amman kullum tasamesu agidan saita soka masu miyagun maganganu

Dasauri tasauko kasan tana rike dajakarta”” sai kutsawa takeyi cikin taron mutane ranta yayi matukar kuna bataso mahaifiyarta tana hulda da wadan nan matan saboda dukansu babu Allah azuciyarsu amman mahaifiyarta batada wasu shakikan abokai bayansu
Wayarta tajawo takamo wata nomber tadanna kirah babu jimawa akadauka”” tayi sallama ya amsa dad dan Allah katuro driver yamiyar dani bazan iyah zama anandinba!!

Ajiyar zuciya yasaukar yace saboda menene labila bazakijirah akawo antyn takiba cikin sauri tagirgiza kai no dady”” dagabaya zandawo inganta yanzu akwai muhimmancin tafiyar tawa gobe munada harda a islamiyya””  amman inshaa Allah idan komai ya daidaita zandawo naga mom din kafin lokacin tazama yargida da murmushi afuskarta tafurta hakan shima murmushi  yayi badamuwa labelaa yanzun bari nakirashi yazo amman nayi kewarki yata gashi zaki tafii amman bamudan zantaba”‘

Tashafo gefen fuskarta bakomai dady zansake zuwa saimuyi firanko?? Yace yauwa yata kikasance cikin amincin Allah

Tasaki sassanyan murmushi tace kaima haka”” inasonka babana  yace nima inasonkii tace bye yace ok bye taciro wayar akunnenta takuramata ido Allah sarki babana”” Allah. Yasa kayi dacen mata Allah yasa daka wannan auren  kasamu kwanciyar hankali wasu sirarun hawayene suka sauko mata tasa gefen mayafinta tashare sake matsawa tayi saboda cinkoson mutane ga shi ankusa la asar”” batawani jimaba driver yazo bayan sungaisa tashige motar suka kama hanyar kano.

KARANTA:ÂJuhud Hausa Novel Complete download Pdf

HATSABIBIN BOKA Page 3-4

By Gentle lady

Sai bayan fitar” labila sannan hajiya lubabatu tasamu tashiga wanka ganin duk jikin kawayen nata yayi sanyi da maganganun da labilar tafadamasu yarinya tamkar banice nahaifeta ba sam bataganin mutuncina
Tayi kwabaa

Batajima dashiga wankaba tafito tasheka kwalliya tamkar wacce zataje gasar sarauniyar kyau” ta chanchade cikin wani tsadadden bugaggen less dan ubansu akalla kudinsa zasukai dubu dari da hamsin””
Tasaka sarkar diamond hannunta yasha awarwaraye na gwal”” nantake tasoma shekii tashi sukayi dukansu suka fara zaga gidan duk indasuka wurga sai anjinjinawa kwalliyarta nikuwa araina nace wato yangulma kikewa kwalliya illai kuwa kwalliya tabiya kudin sabulu dankuwa tayankesu kowacce takoma gidansu tana Allahummar zukuni””

Wani abun saigidan manya bakuga yanda akasoma fitowa dakayan ciye ciyeba bikin gidan masu kudi ko ba agayyacekaba kaje kodakuwa ba asakarmaka fuskaba kakwaso gara””
Dankuwa yanda akacika gidan kaima dagani kasan wadansu abincin kawaine yakaisu “” babujimawa akafara fitoda dakwalen kajiii dakuma babba kakkun raguna masu maiko”” anyimasu gashi Na musamman sunsha shafen barkono saizubarda mai sukeyi saikuma lemuna namanyan mutane wanidinma bantaba ganin irinshiba

Kowa kaganshi rabonsa yake yaga”” masu DJ ne sukafara sakin kidaa bayan suncika tunbinsu””” hajiya lubabatu ce tafara takarawa cikin murna kaikace ba itah za ayiwa kishiyaba babuwanda bata burgeba  wasuma sunata rokon Allah yabasu uwargida maihalinta Sam batadauki kishi abakin komaiba

Kai ranarfa tasha rawa  nikam nace jikinki zaiyi ciwo kuwa””duk wannan bidirinda akeyi banga ma mallakin gidanba””

Yinin ranarfa sunchashe son ransu DJ yakwashi kudii wadanda akaita masu likidasu kasan biki na kusoshin yan duniya wadanda sukarika

Shigar hajiya lubabu goma kowacce shigarkuma saiwanda yaganie komai kuma kalar kayan” anzuba hotona”” magrib tana kawojiki kowa yafara haramar barin gidan”” daki suka sake kowama”” suna nan kowadai saifadin albarkacin bakinsa yakeyi

Karfe takwas mukafarajin dirar motocin amaryaa”” sunata rangada gudaa”” akashigo da itah”” zuwa bangaren uwargida sukashiga da sallama ta amsa dasakin fuska marabanku lale marhabin kuzazzauna mana””
Daga kawayenta harmasu kawo Amarya bakisake suke kallonta sambatada  bakinciki taja hannun amaryar tace zo Kanwata kizauna nan”” cikin jinkunya”” tazauna kanta yanakasa ayanda akebata labarin matarsa babu ruwanta ashema tafiyanda akabata labari””
Take tamike tafara jidomasu kayan makulashe dakuma kayan sha”” da gasassun naman kajie”” bayan sungaisa sukace ga amanar kanwarkinan munkawo maki
Duk dakowa yana shaidunki bakida wata illah Dan Allah kiyi hakuri dahalin kuruciyarta  dan kingirmeta nesa bakusaba idan tayi badaidaiba kiyimata fada””
Tayi murmushi aibakomai abokin zama dadine dashi tadafa kafadarta”” Kanwata nandin kidauka gidane komai yashigemaki duhu karkiji shakkar komai kisanardani nikuma zanwayarmaki dakai

Allah yasa nandin gidan zamankine Allah kuma yasa ace karada akayi Allah yabamu zaman lafiya”” gabadaya aka amsa da amin””
Mikewa sukayi tace yabazaku taba koda ruwabane ai anzama daya nibazanji dadi idankuka kicin komaiba nima idan nazowajenku tareda Kanwata aibazakuji dadiba idan nakishan koda ruwane

Sukace tayi hakuri akoshe suke ganin tamatsa yasaka sukadan kurba lemun”” tareda itah akafita zuwa bangaren Amarya “””  harkuryar dakin tazaunarda itah yanganin daki Duk suncika dakin”” sunfara tabe tabe”” hajiya lubu tasoma miyarmata”” dakayanda akasoma turewa tadade taredasu sannan tayimasu sallama takoma wajen kawayenta indasuma sunsoma haramar komawa gidan mazajensu”””

Tahadamasu shatara Na arziki tarakasu kowacce takama hanyar gidanta”” bangarenta takoma”” hawa na uku shine Nata nabiyu na Amarya maigidan shine hawana karshe””

Idanzakije bangarensa Mahayar Na ura zakishiga kidanna zuwa sama bàsàikin wahalda kanki wajen taka matakalaba

Tanashiga bangarenta tarage kayan jikinta tahaye saman makeken gadonta tasoma sharar barciii hardà minsharii hankalinta kwancee saijuyi takeyi sànyin Ac yanashigarta tako ina”””

Gabadaya gidan anwatse kowayatafi yana yabon lubabatu da kyawawan halayenta”” karfe shadaya motarsa tashigo gidan”” bayan driver yayi fkng yayi saurin fitowa yabudemàsaa kofaa

Yafito”” yacewa driver n ina” habu driver dubamun   kagani nayita kiran”” wayarsa batashiga labila kuma bata dauki wayarba

Yadan gurfana dasaurii yayi hanyar dakinsu yanakwala masa kirah haryasoma barcii yaji anakiransa firgigit yamike yafito dasaurii taresuka  koma  wajen alhajin””

KARANTA LITTAFIN:ÂTubali Hausa Novel Complete Book 1, 2 and 3

HATSABIBIN BOKA Chapter 5

       By
Gentle Lady

Dukawa yayi yace yallabai andawo lafiya??
Qalau habu tundazu nake neman layinka Amman inajinsa akashe””
Ah yallabai wayarne batada chaji wlh” haba habu yanzu duk wadatacciyar wutar nan da ake sakowa kuma ga gen Amman asamu wayarka babu chaji??? Duk kacinye chajin wajen shiriritaccen cheating dakukeyi kaidai koyaushe  maganata dakai akan rashin wayane
Yasosa kansa yallabai ayi hakuri kuskurene baza asakeba”” murmushi yayi yace hakan kake fada dai kullum”” ya labilar kun isah gidan lafiya ko????

Kai yagyada ah yallabai kafin magrib nihar najuyo tabada sakoma akawo maka”” yana murmushi yace to daukomun””
Dasauri yakoma cikin dakin yadauko key yabude motarda yaje da itah wata katuwar kulace dakuma leda”” yakarba “”
Sukai masa saida safe yawuce cikin gidan kaitsaye hawa nahudu yadosa nikuwa ina biye dashi huhuhu ashe banga komaiba saboda wannan yafi sauran kyau nesa bakusaba

Komai gashinan gwanin sha awa” tundaga flowers da kujerun dakin da center Capet”  green color  ne mai haske” sai makeken TV n bango” saikuma babban agogon bango””
Sai fream da ke dauke da ayatul kursiyyu dayan amanarrasulu gudan lakadja akum”” sai wadansu masu addu.o

Sosai tsarin yaburgeni”” kularda take hannunsa ya aje yakarasa kuryar dakin”” kayan jikinsa yarage yashiga yawatsa ruwa yafito jallabiya yazura yafeshe jikinsa da turare yafito kular yabuda danbun kaxane”” sai babbar ledar gasassun kajine gashin gida harda diminsu kansa yadafe shisam yama manta bairikowa Amarya kazaba shikullum cikin mantawa yake”” yayi murmushi labilaa kenan”” mikewa yayi yabude fridge yadauko madarar yoghurt     yasauko zuwa bangaren hajia lubabatu  da sallama yashiga tayi daidai sai kwasar barcinta takeyi””  ledar hannunsa ya aje yakarasa saman gadon yakura mata ido murmushi yayi yashafo fuskarta shikawai yasan abunda yace azuciyarsa ahankali yasoma tashinta ta ture hannunsa cikin alamun mai barcii kuma yanamata dadi yace  maman laby kitashi kokinyi sallah??? Cikin barci tace ah nayifa alhaji harkadawo???

Yace gashi kinyi barci bazaki rakani gun kanwar takiba murmushi tayi wlh nagaji alhaji baxan iyah zuwa ko inaba saida safe tasake juya kwanciya
Murmushi yasakeyi

Yaja bargo yarufemata jikinta  yafito zuwa bangaren Amarya Yanashiga  daddadan kamshi yadaki hancinsa yalumshe ido sannan yabude ahankali yafurta Alhamdulillahi ala ni imati”
Yataka harcikin dakinta tana zaune tsakiyar gado yadine sanye ajikinta “” dashikuma akarufe mata kanta dashi””

Ahankali yataka yazauna saman gadon yayimata sallama ta amsa ahankali””  hannunsa yasaka yadage mayafinda akaimata rufadashi

Murmushi tasakarmasa takanne ido daya”” wani dadi yaji yamamayeshi yana tunanin zaihuta sosai ajikin habiba dantunkafin ya aureta yagano macece mai yawan sha awa shine dalilinda yasaka hartarabu damijinta Wanda tafara aura””

Mayafin yasaukar yace Amarya bakya laifi”” koda kinkashe Dan masu gida”   tayimasa fari”” da ido””   yasaki fara a tashi muyi sallah mugodewa Allah””  mikewa” tayi daga kan gadon tashiga tayi alwala tafito tasamu yashimpida abar sallah yanagaba yajasu sallah bayan sun idar yagabatar masu da kajin da labiba ta aikomasa dasu kitchen dinta yaje yadauko plate yajuye masu naman yakalleta yace bisimillah cikin jinkunya tace nakoshi

Yace wasa kikeyi nasan bakici komaiba hidimar buki nima kaina yunwa nakeji kodai nabaki abakine?? Yayi maganar yana jawota tanarke ajikinsa tashagwabe murya nakoshi my love

Yace nifa banyardaba kokadanne saikinci  ahakan yadibo yanufo bakinta cikin kissa take karba harsaida yatabbatar takoshi shima yaci yasha madarar””
sannan sukafara wasanni

Ganin kasan bazaimasuba sukakoma saman gado yatashi zaikashe masu wutar dakin koda yadawo yasameta sai munsharii takeyi abunyabashi mamaki matuka dagazuwa kashe wuta wane irin barcine zaidaukeka kuma ayanda takeyin barcin kamar tadade dafarashi”” baikawo komai aransaba duk da amatseyake yauyaso more Daren amarcinsa da Habiba jiki asanyaye yaja bargo yarufemata jikinta yamiyarda kayansa”” yakwanta gefenta ido yakuràmatÃ

Kamar maison tunawani Abu”” munshariii takeyi tamkar gurnanin zakii yayita juyi Sam barci yaki daukansa”” haryasoma jantsaki   karshedai mikewa yayi yakullemata kofar dakin yakoma bangarensa

KARANTA:ÂKyawuna Jarabta ta Hausa Novel

HATSABIBIN BOKA Chapter 6

     By
Gentle Lady

Dashigarsa dakinsa bai tsaya ko inaba sai akan makeken gadonsa “” yazube tamkar gajiyayyen mutum wanda yayi tafiyar yini guda cur batareda ya hadiye kwayar  hatsi acikin saba” gabadaya damuwa ta mamaye zuciyarsa

Take yafara sake sake acikin ransa” wai me wannan takenufine??? Kowacce matar dazan aurah salonta daban yake itakuma wannan natasalon yaudarar abarci zata fake?? Yayi kwaba bakomai komai daren dadewa aizankaigaci inhar tasan wata aibatasan wataba lallai inkere nayawo zabo nayawo babu shakka saisun hade

Inma makircine irin nasu namata zanganota idan yanzu tayi makircin barci saina gani idan darana zatayi hakan”” yayi tsaki maganar banzama  yau Allah kadai yasan bururrukan dasuke cikin raina awannan Daren Amman komai yarushe nakoma tamkar wandama baitaba aureba “” ina amfanin dukiyata??? Kansa yadafe Wanda yaji yanayimasa barazana tamkar zairabe gida biyu saigashi yana kuka da idanuwansa hawaye wadansu sunabin wadansu””

Waini saiyaushe zansamu kwanciyar hankali??? Wacce irin rayuwace nakeyi?? Duk irin tarin dukiyarda nakeda itah nakasa samun abunda nakeso saboda duka matan bakin halinsu dayane kowacce zan aura sainaga salon cin amanarta yafigaban kwatance

      Yashafe dakiku arba in yanata kuka shikadai batareda mai rarrashinshiba  daga bisani mararsa tasoma ciwo wanda wannan ciwon kusan yazame masa tamkar ibada  yadade agun yana mirgina tareda addua sannu ahankali ciwon yasoma sauka tamkar yanda ruwa suke sauko wadaga sararin samaniya “”  yana nan agun bai motsaba saida sanyin alfijir yasoma bugomasa yatashi””alokacin yaji jikinsa yakoma daidai tamkar wani Abu baisameshiba

Kaitsaye bandakinsa yashiga  yawatsa ruwa sannan yadauro alwala yashinfida  abar sallah yafara sallah””
Saida akayi kiran asalatu sannan yasauko da charbinsa  ahannu yanufi bangaren lubabatu hawana uku kamar yanda yabarta da dadaren hakan yasameta saidai wannan karon zaninda yakejekinta tuni yakoma gefe tamkarma tunfarko batareda  shidin takwantaba”””

Bayan under dayake saye ajikinta da tinbir zatakasance gashi tatara taiba sai kirjinta dasuke manya manya kowanne daya yayi girman kofin roba

Gefe da gefe nacikinta amurde yake alamar jindadi dakuma Hutu sunkwanta akan lafiyayyar fatar jikinta tamkar irin dika dikan matan yarbawa hakan take

Yaduka ahankali yadauki zanen yarufamata ajikinta daga bisani yasoma tashinsa ahankali”” yadade yana tashinsa sannan tabude idonta”” yace tashi kiyi sallah”” murmushi tayi tasake juya kwanciya tace hutunake “” batareda yace komaiba yawuce zuwa bangaren habiba cikin yanmintuna kalilan Na urar tasadashi da bangarenta  dakin yashiga tanakwance takama filo tarungume kamar wacce tasamu jariri””  haryanzu lullube take ciikin zanen gadon”” yataka kusa da itah yasoma bubbugarta ahankali yanakiraan sunanta”” tasoma juyi cikin barcinta maidadi tasoma bude idonta  ahankali tadorasu akan mijinta tasakarmasa  murmushi maikamada tusar jaki”” tabude bakinta daniyar magana tuni yakawarka fuskarsa sakamakon wani mugun doyi dayafito acikin bakinta tamkar gawar mushe ya tunkari kofofin hancinsa” cikin sauri yajuya yayi taku biyu tareda toshe hanchin nasa sakamakon yankayan cikinsa dayaji suna hautsinawa  cikin sauri yace  sauri nake kitashi kiyi sallah”” baijirah Jin amsarda zatabashiba yayi waje haryacin tuntube

Sam habiba batakawo komai arantaba saitadauki hakan amatsayin yanasaurine karyarasa jam i saboda falalarda kecikin sallar asubah acikin jam”i

Shiru tayi nawani lokacin tana tunanin daren jiya”” Sam tamanta abunda yafaru tayi iya kokarinta kozata iya  tuna abunda yafaru bayan hawansu akan gado damijinta Amman takasa tunawa datamatsà datunani saitaji kanta yasoma ciwo take tayi saurin fatattakar tunanin daga zuciyarta tamike tadaura zani takarasa bayin domintayi wanka

Shikuwa dafitarsa yasoma saurii haryana waigen dakinta haryanzu dayan hannunsa yanakan hancinsa yadadeshi kyam  yace aransa waiii wannan wane irin warine naji tamkar rubabben mushe”” wannan warin daidai yake da aturmuya kanka acikin shadda wacce taikwana shida arufe itakuwa wannan dawanne kalar mangoge hakorah take amfani dashi kodai rashin wanke bakine??? Idankuwà hakane akwai matsala dankuwa bazan iyah kusan tartaba muddin inajin wannan doyin

Dawannan tunanin yasauka kasa yasoma tashin ma aikatan gidan domin wucewa masallaci dama al adarsa kenan bayazuwa masallaci sallar asuba batareda yatada dukan ma aikatan gidanbà wannan dabiar tashi tanamatukàr burge yaran gidan asanadin hakan drivernsa  Sunday yakarbi addinin  musulunci Wanda yanzu akekiransa da Abdullahi

Sosai halin maigidàn nasu yana burgesu basu kadaiba hatta makotansa Dan mutunne Wanda yasan hakkin makotàka sautari idansukàje masallaci inyaga ankusà tàda sallah wani makocinsa baishigoba dakansà yake zuwa ya bugamasa duk da shidinfa maikudine Amman Sam dukiiyarsà batasakashi yazama maigirman kaiba

HATSABIBIN BOKA Chapter 7

    By
Gentle Lady

Sautari talakawan anguwar suna matukar mamakinsa saidai shi Sam baidauki wai girmankai yadorawa kansaba girmankai Wanda mafiyawan masu kudi suka sakawa ransu”  dazaran sunyi kudi zasufara daukar kai Sam sumanta da lokacinda suke fakiransu  gabadaya  abokanansu nabaya saidai idansuka wulgo cikin mota sudagamasu hannu wanikoma dagahannu bazaiyiba yama manta dayataba zama wata majalisa”” dazaran yaga Wanda yasani talaka saiya saki gilashin motarsa yakauda kai gefe tamkarma baiga mutumen ba

Wannan girman Kaine kuma duk Wanda yakedashi yasani yakama hanyar halakarsane saboda abunda kesauran halakarda bawa girman Kaine dagahakan zakafara hassada kanadaukar kanka wata tsiya bakaso wani yayi kudii kamarka kasani ko shaidan abunda yasakashi hassada girman Kaine haryakaishi ga fadawa halaka
.              Allah yaciremana girman kai dakuma hassada acikin rayuwar mu Ameen”” saida yajirasu dukansu sukayi alwala sannan yawuce suma suka Mara masa baya “” zuwa masallacin unguwar

Babu nisa Dan gabangidansa kadan akagina masallacin Ku San babu kwadagar kowa wajen ginin shine yadauki nauyin komai masallacinda aka kawatashi ko acikin manyan unguwanni saikayi dakyar kafin kasamu mai kyansa”” Dan asalin wajen wata tsohuwar ginace akazagaye korufin kwano babu akarosheta akagina wannan masallacin  Wanda fankoki da ac kamar suyi magana idan kashiga kamar karka fito sannan gatarin littafai nan idan kanason karantawa”” bayan an idarda sallah”” yakoma gefe yasoma karatu inda sauran ma aikatan wajen sukasoma karatun zuwa adanjima sukafita zuwa wajen aikinsu””

Dai daikun jama ar wajen suka soma fita ahankali haske yanagama wartsakewa shima yatashi yakarasa wajen liman sukai musabaha sannan yafita zuwa gidansa tun a hanya suketa gaisawa da  makotansa haryakai gidan dashigarsa yasamu ma aikatan gidan sungama aiki shikawai suke jirah bayan sungaisa yawuce cikin gida sukuma sukawuce

Dayake yauranar lahadine babu aiki duk da yakeshidin dankasuwane  yanada campani masu yawan gaske Amman yanayin tsarinsa tamkar aikin gomnaty dashi da ma aikatansa
Basazuwa aiki asabar da lahadi acewarsa takasance ranar Hutu gakowa saboda idan sukaje takwas nasafe basa tashi sai karfe takwas darabi

Ranar lahadi da asabar taxama ranar Hutu kowanne magidanci yafuskanci iyalansa yaji damuwarsu””  idankuma marar aurene yaje wajen budurwarsa idankuma yanada wata lalurah yayi koyayi ziyara”” musamman jumua dan ranar juma.a karfe hudu aketashi

Shikuma ranar asabar inhar yashiga gidansa bayafitowa bayan zuwa masallaci yanatare da matansa yakasance lokacinsune komai sukeso kosunada damuwa saisufadamasa duk da kafinsu kwanta kowanne darema suna ganinsa

Kaitsaye bangarensa yanufa yasakeyin wanka  yakwanta kasancewar barcin jiya Yana nan a idonsa take barci yayi awon gaba dashi

Hajiya lubabatu ce tashigo dakin cikin takun kasaita balaifi yautayi kwalliya dass da itah fuskarta saifitarda sihirtaccen murmushi takeyi ahankali tataka zuwa saman gadon taxauna hannu tasaka tanashafo lallausar sumar kansa Wanda takwanta luf gwanin sha awa hakika tana matukar son mijinta dakuma kishinsa fiye da tunanin mai karatu hakaxalika tana mutuwar kaunarsa da begensa fiye da tunanin duk wani mai tunani taja gauron numfashi” atake talulaya wata duniyar daban

Sai farkawa yayi yasamu hajia lubabatu tasakashi gaba hannunta yanakan gashin kansa  idanuwanta suna kallon saitin drawer yayi kuru yana kallonta daga bisani yasaka hannu yashafo fuskarta tadan zabura sannan tasaki murmushi hannu tasaka tajawo hannunsa daga kan fuskarta tace harkatashi ???

Murmushi yasakeyi akaro nabiyu yace ah tunanin mekikeyi??? Taware ido waini batunani nakeba
Yace bayan Wanda nagani”” tayi murmushi ah ah alhaji wai shin inakabar Kanwata??? Tayi saurin kawarda zancen dawannan tambayar”” yace tanadaki tanabarci mana””

Cikin zolaya tace barcin gajiyako nasan halinka basauki jiya bakabarta tahutaba duk da take yarinya batasaba sosaiba
Yayi murmushi yace kinfara ko lubabatu yayi kyau inhar nakama ki akoma zakiyi bayani

Aransa kuma yace hmm inakikasani saida ta talemun kaza tacinye sannan tasoma barci kamar kasa yayi maganar yana mikewa daga kan gadon yashiga toilet domin watsaruwa

HATSABIBIN BOKA Chapter 9

      By
Gentle Lady

Bazato kawai saiyafara jin amai”” dasauri yasauko zuwa bayin dakin dagudunsa yasoma kela amai tamkar zai amayarda kayan cikinsa yayi matukar galabaita”” take yazube acikin toilet din yana hakii tamkar wanda yayi gudun tsere da kartii goma””

Tsayin mintuna talatin yana wajen sannu ahankali yasoma samun natsuwa mikewa yayi yasakarwa wajen ruwa yawanke bakinsa sannan yafito kallo daya yamata yadauke kansa wasu hawayene suka sauko akan fuskarsa harzai wuce saikuma yadawo tareda saka hannu ya dade hancinsa zuwa saman gadon” yaja abun rufa yarufe mata jikinta sannan yawuce dasauri

       Dayake akwai yalwatattun dakuna abangarensa tamkar wani babban gidane ahawan wani bangaren yashiga”” jiki sanyaye yakarasa bayin yayi wanka yadauro alwala domin koda yakwanta bazai iyah barciba

Washe garin ranar Sam fuskarsa batada wani walwala dankuwa alal hakika wannan lamarin yasoma kaishi bango yanaji yanagani zai halaka kansa”” ko lunch dasukayi sama sama yaci daga bisani yamasu sallama yawuce ko rakiyar bainemaba dama dai yau rakiyar habibace Dan haryanzu hannunta yake

Saida akayi kwanaki uku cur kamar yarda addini yasimfida budurwa sati daya bajawara kwana uku Amman harzuwa wannan lokacin baisamu kwantawa da itah ba”” gashi hargirki yadawo akan hajiya lubabatu””
Dadare suna zaune akan kujerah sunashan kayan itatuwa habiba tana barin gefensa nadama hajiya lubabatu tana barin hagu kokadan ayanzu bayajin warinta koda tabude bakinta”” aransa kuwa yana ayyana damacen muguntane bataso yakusanceta akwai abunda take sakawa ajikinta duk lokacinda tasan zaizo mata””” ahankade yake kallonta

Bayan sungama Shane yayi gyaran murya yasoma yimasu nasiha akan zamantakewar aure daga bisani yace  kamardai yanda kukasani yaudai kwanana uku dakin Amarya danhaka yau za araba kwana kwana biyu kukeso ayi ko daya daya???

Hajiya lubabatu ce tayi saurin tarar numfashinsa tace maigida nidai kasan banda wata matsala amatsayina na antynta nidai nayafe nawa kwanakin nabaku watadaya kumore amarcinku

Jiyayi tamkar yafasa ihu
Dasauri yabude baki daniyar yin magana ta dakatàr dashi tahanyar rufe masa baki dahannunta tana girgiza kai cikin murmushi tace karkadamu basaika godemun ba nimaisonkace

Inason duk wani farincikin ka ninasan amarcin nan bai ishekaba”” bazan cutuba harcikin raina nabar maku zuwa watadayan saika rabamana kwana

Gabadaya jikin habiba yayi sanyi son hajia lubabatu yashiga ranta lalai kowa da irin halinsa bata taba ganin macenda batadau kishiya abakin komaiba kamarta Allah yabarmu tare hajia

Al amarin alhaji kuwa sandarewa yayi awajen saboda kaduwa dajin furucin lubabatu anyakuwa tasan masifarda nake fuskanta???

Yanisa aransa batasaniba nasan datasani dabazataso incutuba”” yanda takesona fiye darayuwarta “” kuma haramun ne kasanarda matarka sirrin abunda ketsakaninka da dayar matarka dasaina fadamata”” yaja dogon nunfashi yace shikenan mungode hajiya yanayin yanda yayi maganar kaida ganinta kasan ba cikin dadin rai yayiba”””

Basuwani jimaba hajiya lubabatu tayimasu saida safe tawuce bangarenta”” shima hakan yasaka yamike zuwa dakinsa hakama habiba”” sosai yau taraya aranta zatafaranta ran maigidanta domin samun abunda yakeso

Bayan tayi wanka tashirya cikin shigar kayan barci farare masu sharara tafeshe jikinta da kalolin turarukka”” kaitsaye bangarensa tanufa

Tasameshi yayi shirin kwanciya yana ganinta gabansa yafadiii yaukuma meyakawota alhalin bankirataba ????

Batareda tanemi iso daga gareshiba tayi saurin fadawa jikinsa””” ’’kafin yayi kokarin tureta daga jikinsa hartafara aikamasa dasakonni tako ina”””

Takesuka zube akan gadon tunbaya maida martani haryasoma maida mata da martani””” abukamar zaitafi ahakan sannu ahankali yasoma jin doyin tunyana daurewa tareda toshe hancinsa saiyaji abun kamarma karoshi akeyi  kusamma doyin yafi nakoyaushe

Bashiri yahankadata gefe yamatsa baya dasaurii””” itakuwa alokacin hartayi barci abunta saitasake gyara kwanciya

Gefenda take yakuramata ido tamkar maison tunowani abun dagakarshe wanka yashiga koda yadawo baisametà dakinba tafita

Tsaki yayi damashi yasan komai takeyi dagangan takeyi kawai danyanason hakkinsa tana nema takasheshi indai Dan wannan ne bazansake nemantaba

Darenkuwa daciwon ciki yakwana”” tundaga ranar kullum idan sukatashi don su kwanta”” saikawai yarufe dakinsa kuma koda tabugàmà  bazai budeba Amman Sam bayanuna komai idansuna tareda lubabatu ahakan har akacinye watadayan da hajiya tabasu

HATSABIBIN BOKA Chapter 8

     By
Gentle Lady

Tabishi da kallo dawani boyayyen murmushi Wanda itah kadaice tasan ma anarsa”” tana nan akan gadon haryafito yana daure da towel

Yadauki comb yana   taje sumar kansa””  saida tayi luf sannan yadauko turarukka yasoma fesawa ajikinsa”” yafesa akalla turare kala biyar sukahadu sukabada wani kalar kamshi na daban kaisaikace ma aiikatar turarece tayi ambaliya

Wata bugaggar shadda ja wacce taji aikin hannu da zare jinin kare maiduhu dinkin tazarcene daidai wandonsa bataja kasaba kamaryanda wandonsa baiwuce idon kafarsaba”

Yadauko hukarsa kube maikalar kayansa hatta Zanen hular tamkar tarema aka kerasu”” yadaidaita tsayin hularsa sannan yajuyo wajen hajia lubabatu yasakar mata murmushi yace mujeko dannafarajin yunwa yayi maganar yanashafo cikinsa

Batareda tayi maganaba tamike sukajerah zuwa kasa kowannensu  fara a kwance akan fuskarsa”” aka idar sa falon kasa yakeyin break saboda masu aikine sukeyin komai shiikuma  bayason masu aiki suhau saman sa inhar ba matarsaba babu Wanda yataba shiga saman””

Kaitsaye saman dinner suka nufa yaja kujerah yazauna tadubeshi tace bari nakirah Kanwata ko batareda yakalletaba yace ok”

Kaitsaye tasake hawa mahayar zuwa bangaren Habiba””  bakin kofar dakin tatsaya tana kwankwasawa cikin dakin akace waye shigo” taturah kofa habiba tana ganinta tasaki faraa danta shaidata tace Anty kece inakwana

Tamayar mata da martanin murmushinta tace lafiya qalau Amarya yakwanan amarci ya kuma bakunta?? Murmushi tayi kawai tadone kanta kasa””

Hajia lubabatu tace hmm kunyata kikeji Amarya nifa antynkice kinga taso muje mukarya nasankema kinajin yunwa””

Batareda tace komaiba tamike hajia lubabatu tanagaba tanabayanta itakuwa saikada mazaunai takeyi kamkar randar ruwansha

Harsukakai kan dinner din itah ta gabatar masu da abincin sukaci sukai hamdala sannan suka koma cikin falon suka zauna sukasoma firah

Dama ankusa azahar bayan yayo sallah yasake dawowa falon alokacin duk basanan”” baijima daxamaba hajia lubabatu tafito tanaganinsa tawashe baki harkadawo yace ah wlh kusadashi tazauna

Yace inakuma habiba??? Tasake murmusawa tace banda abunka alhaji kasan kunya takeji bata sababa nidai nayafe hirar kakoma bangarenta zakufi sakewa kudarji amarcinku

Murmushin yake yayi yace hakane kuma kinkawo shawara mai kyau yamike yana gyara tsayuwar rigarsa yayi hanyar mahaya itakuma takoma bangarenta

Kofar dakinta yatsaya yana sake sake aransa karshedai kawai yayi kundun bala yaturah kofar tareda sallama tana zaune cikin katon falon tana kallo tadago cikin fara.a ta amsa masa” dannesa da itah yaxauna yana Dari Dari yace kallo kike???

Tace ah kanta yanakasa yace dakyau”” dagahakan baicekomaiba”” saidai yanata satar kallonta takasan ido haryana hadiyar yawu kafin cikar mintuna ashirin yaji baxai iyah dakatarda kansaba cikin kasalarlar murya yakirah sunanta ahankali ta amsa yayimata nuni akan tazo babu musu kuwa tataso

Al amaridai anan yasauya yafara aikamata da sakonni dayake yanayi yana kauce hancinsa dankarya shakomasa abunda yafi karfin Tunaninsa tsayin mintuna goma yasunkuceta zuwa kuryar dakin

Abun mamaki yana ajeta akan gadon yajitafara wani minshari arazane ya kwalalo ido cikin kaduwa yace barcin kuma???? Waimeke faruwane kodai yarinyar nan aljanun barcine da itah?? Kuma dantsabar shakiyanci ace barcin bayazuwa sai idan nazoda bukatata”??? tsaki yaja yamike akan dagon yafita abunshi zuwa bangarensa

Saida akayi la asar yafito da mamaki yasameta cikin falon kasa da itah da wata kawarta”” kallo daya yamasu yadauke Kansa yawuce fuuuu tamkar kububuwa dansosai amaryar  nan tasa tasoma batamasa rai jiyajiya dakawota jifa dazun barcitake haikam Amman gashi kawarta tazo tawartsake tamkar batayi barciba
Anjima nasan mezanyi
Dawannan yakawarda tunanin yakarasa masallaci””

Habiba kam tacika da mamaki duk da bata nunawa kawarta dakwai wani abuba Amman tanacikin damuwa tarasa meke faruwa aduk lokacinda zaitara da itah batakoma sanin meke wakana saidai tafarka taganta itah kadai idan kuma tamatsawa kanta da tuna abunda yafaru saitaji kanta yasoma ciwo

Har da dare taresukai dinner sukadan taba firah tayi masu saida” safe tayi bangarenta” batajima datafiyaba hajia lubabatu tamike tayi hamma”” tace nizan kwanta” alhaji saida safe”
Shima yamike yace kenan duk kunwatse kunbarni””anan kamar tsinkàkken silifas”” bakomai muje inrakaki” tayi murmushi tayigaba””   yana bayanta saida yarakatà har bangarenta”  saida takwanta sannan yarufemata kofa Yakoma bangarensa yayiwanka

Yayi shirin kwanciya wannan karon kiranta yayi awaya tasameshi bangarensa””cikin shigar kayan barci masu sharara dukkan halittar jikinta ta bayyana” take Yakama zumudi jikinsa yasoma karkarwà tamkar zakinda yakwana biyar yanajin yunwa aganinku mezaifaru idanyayi arba da abinci

Ahankali ta takazuwa wajensa”” babuwani   bata lokaci sukafara faranta ranjunansu”” kafin wani lokaci sunkai saman gado kamar almara saigashi tasoma barci

Ganin hakan yasa yaji haushi aransa yace kobarcin mutuwane bazai hakurabà saiya Kore kishinsà yanata”” kokarin biyan bukatarsa tasoma gurnani tanabude bakinta wani”” mugun doyi yana fitowa babu shiri yasa hannu daniyar rufemata bakiii yajikamar yataba wasu hakorah zagan zagan”” take Kuma zuciyarsa tasoma tashi

HATSABIBIN BOKA Chapter 10

      By
Gentle Lady

Alokacinne akaraba girki” yakoma hannun lubabatu””
Habiba Sam takasa gane wanne irin aurene tayi gatadai batadawata makusa wacce zatasa namiji yaji baya sonta”  batada matsala tabangaren kishiya saidai tabangaren miji”” sosai yakesonta kafin auren ammankuma gashi tunda tashigo gidan komai yadargwaje tarasa gane kuma dalilin yinhakan gashi tanada tsananin bukata zuwa yanzu tarame tafige tafita hayyacinta”””

Kwance take cikin falonta kasancewar yauma ranar hutuce yanagida Amman takasa fita domin ganinsa kawai zaisake tasomasa da bukatarta wacce tasan bazata samu maganintaba “” lallai tayarda akwai abunda yajefaruwa da itah cikinta taji yasoma juyawa tafara murkususu””

Tun tana kankujerah hartafado kasaa wata irin kara ta kwallah daidai shigowar hajiya lubabatu tazo kiranta suci abinci dasauri takarasa arude tadagota tana tambayar lafiya kafin tarufe bakinta jinine yasoma zubowa dakarfiii ta gabantaa””

Cikin tashin hankali lubabatu tace habiba dama bakida lafiyane???ina habiba tamatukar galabaita bata iyah kodaga kanta dasauri hajiya lubabatu ta kwantarda itah tafito dasauriii zuwa kasan

A firgice tana kuka yana ganinta yamike yana tambayarta lafiya hajia??? Cikin kaduwa yaji meyafaru tace munshiga uku habibace ba lafiya

Kafin tarufe bakinta tuni yahaurah saman baimabi takan na urarba tasaman benen yataka tuni hajiya lubabatu tabi bayansa koda suka karasa hartasuma ga jininan yanata malala”” gakuma wata karamar halitta wacce batawuce girma Dan kadan gareba””  take jikinsa  yahau rawa duk da abunda yagani Amman hakan baisa yadamuba ya ciccibeta  duk dajinin dasauri yasauko kasa hajiya lubabatu tana bayansu sai kuka takeyi

Tunkafin yafita yasoma kwalawa driver Kira”” dasauri yafito jinkiran jikinsa yanarawa Dan dagajin kiran yasan ba lafiyaba”” ganinshi damaidakinsa ahannu yasaka yabude masu Mota dama ashirye take”” akasakata taresuka dunguma  har hajiya lubabatu zuwa hospital””  emergency akawuce da itah kaitsaye bakin kofa aka dakatar dasu aka hanasu shiga”””

Dagashi  har hajiya kaikawo sukeyi awajen kowanne kagani kasan yanacikin tashin hankali tsayin awanni biyu likitan yafito dasaurii alhji yatareshi “” saidai yadagamasa hannu yawuce haryana hadawa dagudu””

Zuwacen yadawo yashiga dakin”” ansake shude wasu awannin saigashi yafito
Alhaji yatareshi tareda hajiya lubabatu harsuna hadabaki wajen tambayar yamaijikin???

Zufan kansa yashare yace kukwantarda hankalinku insha Allah zatasamu lafiya”” yanzudai muna bukatar jini cikin gaggawa”” kafinma yarufe bakinsa yace muje a auna idan nawa zaiyi”” hakan kuwa akayi saidai jininshi baiyiba

Adole akakirah yan uwanta mahaifiyarta “” dakuma yayyunta””” su ukune kowanne akadibi gorah biyu ajikinsa”” take akajonamata anasaka jini jinin yanafita”””

Harzuwa dare babuwani haske hakazalika  sunkasa tsayarda zubar jinin”” yanda yakezuba zuba banawasaba hakan yasaka sukanemi Karin wani jinin”” duk dayana fita idan ansakamata””

Yan uwanta basuda wadataccen jinin gashi har andibi gorah biyu dagahakan baza sake dibaba”” gashi duka jininta ya tsiyaye”” hajiya lubabatu sai kuka take tace aduba konata zaiyi itakam bataso tarasa kanwarta

Likitan yatausaya mata sosai yace saidai hakuri hajiya ba adiban jinin mace”” cikin karaji ta chakumo wuyansa tace inaruwanka jininka konawa

Tasakeshi cikin kuka tahada hannuwanta gida biyu Dan Allah doctor kataimaka mana wlh koda zanrasa raina tasanadin dibar jinin nawa”” wlh nayarda Amman banaso kanwata tamutu

Jiki asanyaye yagyada kai ganin kowanawajen yazubamasa ido”” take aka auna jininta baidakomai”” akasoma diba  anasakawa Habiba”””likitàn yafita mahaifinta dawani kaninsa sukabishi abaya”” zuwa office dinshi”” mahaifintane yasoma tambayarsà meyakedamuñ yarsa???
Yayishiru dagabisani yace  barine tayi” cikin kaduwa mahaifinta yace barin lafiya watadaya da aurentafa??? Yajinjinà kai tareda turomasa takarda gabansa yace sakamàko yanuna tanashañ kwayoyin zubarda cikine babisa ka idaba shine yajawomàtà wannan matsalar

Kafin yarufe bakinsà alhaji yashigo dasauri yace doctor kataso jinin ya facce kusan taresukà mike dasauri zuwa dakin harsunà hadawa dagudu

Sannu ahankali tabude idonta takurawa gadonda hajiya lubabatu take kwance ido sirarun hawaye suka saukomata

Take tasoma Kalmar shahada”” idanuwanta sukai sama take Na urah tasoma kara”” daidai shigowar su doctor yakarasa wajentà yayi yan aune aunendà zaiyi yagirgizà kai

Yacire abun Karin jinin tareda Na hajiya lubabatu yarufe mata idonta yaja kallen yarufeta”” gabadaya dakin shisuke kallo Dan haryanzu basu fuskanci meyafaruba

Yajuyo dakallonsa wajen alhaji yace saidaifa kuyi hakuri Allah yakarbi abarshi””

Daga haka yajuya yafita hajiya lubabatu tasoma kururuwa tana wayyo itah tabani mahaifiyar habiba saman gadon lubabatu takoma tanabata hakuri suka rungume juna sunata kuka””” akarasa Wanda zai rarrashi waniii

Tsayin mintuna talatin mahaifin habiba dasauran yan uwa da sukazo dakyar akasamu su hajiya lubabatu sukai shiru

Kanin Mahaifiyarta yakalli alhaji yace waimenene musabbabin ciwon nata””??? Kodama tadade batada lafiya???

Ciikin sanyin murya yace shima baisaniba yadaifàdamasu iyah abunda yasani  ahakan”” mahaifinta yace sai asamo mota suwuce gida babu wani bata lokaci akadauki gawar zuwa gidan iyayenta””

HATSABIBIN BOKA Chapter 11

      By
Gentle Lady

Gabadaya gidan iyayen nata akanufa harda Alhji”” saidai dare yayi Dan lokacin andade dayin sallar isha I”” hakan yasa akaimata wanka aka suturtata” zatayi kwanan keso washe gari sai akaita gidanta na gaskiya
Cikin Daren su labila sukasamu labari anasanarda itah tarabka salatiii kukane yakwace mata taruga cikin daki waisaiyaushe mom zatadaina kashewa dad matane???

Meyasa haryanzu nakasa sanardakowa abunda take aikatawa??? Ninasan koda nafadadin babu Wanda zaiyarda dani ganin irin yanda take nunarashin kishi akan matanda yake aurah

Ya Allah ka gaggauta tona mata asiri”” wasu hawayene suka sauko akan fuskarta tashare””” tundaga bangaren lubabatu har alhaji babu Wanda ya runtsa acikin Daren sai rarrashinta yakeyi washe gari labila  abdulmajed da hajiya da kannen alhaji hafis da kubra suka kamo hanyar kaduna

Koda sukashigo kaduna bakwai darabi”” alokacin har anyimata sallah antafi Kaita makwancinta”” su hajiya gidan su habiba aka kaisu sukayiwa iyayenta gaisuwa””
Harda hajiya lubabatu sukaje idanuwanta sunyi suntul saboda kuka kowayaganta saiya tausaya mata”” iyayenta Kansu basuyi kuka kamar yanda tayiba”” labila Kuwa dage take kallonta dankuwa tasan aikintane””
Ahakan akayi zaman makoki akawatse “” Dan babanta yace bayason wani zama saidai kowa yabita da addua”” aranar kowa yawatse anayiwa habiba Neman gafarar Allah
Kowa yazo gaisuwar dole yakoma dason lubabatu acikin ransa ba alfahariba ko mijinta baikaita nuna bakincikiba””
Ahakan akayita lallashin juna”” aranar sukadawo gidansu

Hajiya lubabatu harda karamar jinya tayi tarashin kanwarta adole alhaji yabar aikinsa yatsaya jinyarta”” su hajiya kwanansu hudu sukajuya suka koma””

Bayan satii daya darasuwarta yan uwanta sukazo gidan suka kwashe kayansu”” ranarma Ku San kukanda sukayi dasu da lubabatu tankar yafi naranar rasuwarta wata kanwar Innar habiba harcewa tayi da alhaji yanason yarta ai wlh databashi Dan sosai sunason lubabatu kamar yanda takesonsu””

Bayan sungama yan koke kokensu tarakasu sukawuce takoma cikin gida””tasheke dawata mahaukaciyar dariya””” tasoma tafawa lallai kimabashi yarki??? Aikuwa dakin yankarwa yarki ticket din zuwa lahira barganina ahakan  bakar kunamaçeni🦂 “nidin damoce Amman nafi maciji hadarii

Babu wata wacce ta isah nayi kishi da itah ba ahaifetaba””” idankuwa tsautsayi ya saka wata tashigo gidan nan tabbas tasoma kididdigar ranar mutuwarta tasake shekewa da dariya tawuce saman

*WADANSU SHEKARU BAYA*

Alhaji adamu yunusa”” wani gawurtaccen maikudine kudikuma bana wasaba”” attajiri wanda yakrtashen kudi yanada mata biyu hajiya binta itace uwargida yayanta uku Usman hafis da kubrah”” sai Amarya hajiya hannatu yayanta biyu duk maza kabeer Ahmad”” Alhaji adamu irin mutanen nan ne wadanda sukeda kudi kamar hauka Amman ba agane hakan ajikinsu kokuma asuturansu domin bayaci kuma baya bawa iyalansa komai nagidan kwab kwab akedashi acewarsa aidukiya tattali take so” idan bahakaba tawargaje😂

Sam yan uwansa abun yanabasu haushi barinma hajiya hannatu dankuwa itah macece maison karya danuna isah

Abudayane bayawasa karatun yaransa danyafison kowanne yayi karatu yanemi nakansa dankar zuciyarsa  tamace akan na mahaifinsa””

Usman tunda yatashi Sam dukiyar mahaifinsa bata burgeshi tunda yasoma karatu yamaida hankalinsa wajen karatu”” harya kammala degree dinsa fannin kasuwancii””

Alokacin babansu yabasu jari Usman da kabeer dankusan taresuka kammala karatu””
Usman yanada farinjini hakazalika akwaishi  dason mutane babu ruwansa dashiga harkar dabata shafeshiba   yanada wani aboki akaduna sunansa abdullahi shine kawai abokinsa baban abdullahi dankasuwane shima yakarfafamasu guiwa akan suyi karatunsu bangaren kasuwanci

  Alokacin da mahaifinsu yabasu kudi yanunawa mahaifiyarsa tasanya masa albarka ranar yakirah Abdul yasanardashi””

Yace gobe zaizo kaduna hakan kuwa akayi mahaifin Abdul yahadashi damanyan yankasuwa yafara sana a

Cikin yan shekaru Allah yasakawa dukiyarsa albarka”” alokacinne hajiya binta tafara masa maganar aure”” damakuwa yadade yanason wata ameena wacce take tuyar awara alayin gidansu Abdul
Ameena marainiyaçe mahaifiyarta tarasu tuntana yarshekara hudu aduniya”” babu kalar wuyarda bataciba wajen matar ubanta huwaileDuka kuwa dayunwa dasuna kashi datuni sunkashe ameena

Mahaifinta yanasonta sosai Amman dagabaya da akaci karfinsa yakoma da itah dababu itah duk daya gashikuma itace kawai yarsa

Huwaile tasoma dauramata talle kuma baburuwanta nairah inhar tayi ciwon kai ajikinta Zata debe tashayi mata tsarki da attarugu tawanke mata daruwan zafiii

Azaba iri iri babuwaççe ameena batashaba”” tunlokacinda taga tasoma kirgan dangi saitafàra yimata awara tana toyawa alayinsu

Dayake unguwar kowayasan mahaifiyàrtà babu Wanda yatabajinta tayi sa insa da makota bakamar huwaile ba harfada takeyi da kartii idansunçi bashinta basu biyaba babu ruwanta dawai itah matar aurece!!!

AishaâœðŸ¼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*â˜

Chapter 12
By
Gentle Lady💃ðŸ½

Malam garba kuwa dashi da babushi duk daya kobanza yana bala in tsoronta tunda ba banza tabarshiba””
Duk saurayinda yace yanason ameena har gigi yakaishi kofar gidansu huwaile ce zatafito tazageshi ta uwa ta uba”” hakan bazai ishetaba saita samu iyayensa tayi masu Tass kuma tace sujawa dansu kunne kartasake ganinshi kofar gidanta dayawa samari sunason ameena Amman balain huwaile suke gudu””
Tunranarda Usman yaganta yaji takwanta masa arai barinma lokacinda Abdul yasanardashi ainahin tarihinta saiyaji babu matarda yakeso aduniya sama da itah”””

Lokacinda mahaifiyarsa tayimasa maganar aure saida yafara neman shawarar abdul akan yasanarda itah”” dariya yasoma yimasa yace zakafara wautar taku ta yayanfari tomenene dankafada mata kokunyarta kakeji””

Dariya yayi yace wacce irin kunya Abdul tunani nayi yarinyar nan bataSanniba kawai dai saninda tamun inazuwa cin awararta lokacinda nake karatu” atunaninka itah zatasoni??? Nifa banaso nacutarda itah

Abdul yasake kwashewa da dariya yace kwantarda hankalinka mutumina indai ameena ce wlh bakada damuwa kasan sarai itama kamar akan kayatake agidansu yanda aka azabeta nikam hakan yayima kaga huwaile Batasan da soyayyar kuba ballantana ta fatattakeka

Tare suka kwashe da dariya yace fatattakadai abokina aitasan wadanda zatayiwa hakan sudinma rainasu tayi kodayake hakan datayi alhairi ne agareni dayanxu banine zansamu wannan kyakkyawarba”” sosai Usman yarude akan sonta cikinwai ma bata kwalliya Dan huwaile batabari waidan kartasamu samari

Ranarda yasanarda mahaifiyarsa tafadawa alhaji adamu yayi murna sosai Amman kafin yanema masa auren saida ya tabbatarda kasuwancinsa dayanda yasamu riba sosai fiye dakudinda yabashi

Bawani batalokaci yasanarda limamin unguwarsu dawasu abokansa sukaje kaduna sukanema masa auren ameena awajen mai unguwa

Saboda Usman yafadamasu komai akan matarsa””mai unguwa yaji dadi sosai yasa akakirah malam garba” agabansa akayi komai sunbada harda kayan nagani inaso dakuma kudin saka rana ahakan alhaji   adamu yace asaka biki kusa kusa kumashi yaron yace basaitayi komaiba shizaimata kayan daki dakomai malam garba kam yayi murna duk dakasan zuciyarsa halbawa yakeyi shikawai yasan fitinarda zaihadu da itah agida”” mai unguwa yace totunda har hakane mezaihana adaurah auren ayanzuma idan ashirye kuke”” hakan bakaramin dadi yayiwa alhaji adamu ba babu bata lokaci yakirgo kudi dubu hamsin amatsayin sadakii

Goron saka rana shi akayita   mikawa mutane mai unguwa shiyazama waliyin Amarya”” take akadaurah aure jama a suka shaida bayan yan gaishe gaishe”” alhaji adamu da tawagarsa suka kama hanyar kano cikin farinciki

Malam garba yanarike da sadakin ameena dagoro yatunkari kofar gidansa gabansa yanafaduwa”” yadade bakin kofar gidan dagabisani yashiga da sallama
Ameena tana tsakar gidan tana darzar wankin huwaile da fa Iza ” ita kuma uwar ikon tana inuwa zaune tanayiwa fa Iza tsifar kaiii”” fa iza yartace Amman batareda  malam tahaifetaba bayan tahaifetane tarabuda mahaifinta saita auri malam

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top