Abubuwa 10 Ga Mai Son Dacewa da Lailatul Qadari – Dr Bashir Aliyu Umar

Tsokacin Edita: Watan Ramadana, watan da Allah ya saukar da Al-Kur’ani mai girma wata ne mai falala daga cikin watannin musulunci. A watan Ramadana ne Allah ya kebe ibadar Azumi, wacce ya ce shi ke ba da lada gareta na musamman.
Hakazalika, a watan Ramadana Allah ya kebe wani dare mai daraja, wato daren Lailatul Qadari. Kur’ani ya siffanta daren da kwatankwacin dare 1000.
Daren Lailatul Qadari na zuwa ne cikin goman karshe na watan Ramadana. Hakan yasa hadisai da dama ke magana kan a yawaita ibada da tsayuwar salloli cikin dare domin dacewa da daren Lailatul Qadari.
 
Dr Bashir Aliyu Umar, limamin masallacin Al-Furqan da ke birnin Kano, ya lissafa wasu abubuwa guda 10 da ya ce su ne jagoran mai neman dacewa da daren Lailatul Qadari, kamar haka:
1. Niyyar neman yardar Ubangiji
2. Neman gafara ga Ubangiji kasancewar samun rabauta ya ta’allaka ne ga irin afuwar da Allah ya yi wa dan adam a wannan dare.
3. Wankan tsarki tsakanin Magriba da Isha’i ko kuma bayan Isha’i kamar yadda ya zo a sunnar Annabi Muhammad (SAW). Har wa yau, yana da kyau a sanya tufafi mai kyau domin daren tamkar Idi ne.
4. Tashin iyali domin neman rabauta kamar yadda ya zo a sunnah cewa Annabi SAW duk dare yana tashin iyalansa domin yin ibada.
5. Raya kowanne dare da sallah da sauran ibadu daidai gwargwado ba tare da yin barcin da ya wuce kima ba. Saboda ana son mutum ya kaurace wa makwancinsa a wadannan darare.

6. Mutum ya guji rigima ko musu ko da kuwa da iyalinsa ne domin musu da jayayya na janyo daukewar rahama.
 
7. Yawan yin addu’ar da Annabi ya koya wa matarsa, Aisha wato Allahumma Innaka Afuwun Tuhibbul Afwa Faafu anna.
8. Mutum ya kyautata wa mahaifansa a dukkan dararen goman karshe, abin da zai sa su yi farin ciki da mutum.
9. A kuma yawaita addu’ar neman ‘yantawa daga wutar jahannama.
10. Sannan a yi tawassuli da dararen goma wajen neman Allah ya fitar da Musulmi daga sharrin annobar korona.

0 thoughts on “Abubuwa 10 Ga Mai Son Dacewa da Lailatul Qadari – Dr Bashir Aliyu Umar”

  1. Pingback: Alkawarin da ciwo hausa novel 1 to End - BAKORI TV

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top