Saran Boye Complete Hausa Novel
Tags: Saran Boye Complete Hausa Novel: saran boye 70,saran boye 72,saran boye 65,saran boye 62,saran boye 73,saran boye 60,saran boye 67,saran boye 50,saran boye 76,saran boye hausa novel,saran boye audio,saran boye abokiyar hira,saran boye the end,saran boye book 2,saran boye book 1,saran boye by billyn abdul,saran boye complete hausa novel,saran boye chapter 1,saran boye chapter 22,saran boye document,saran boye complete document,saran boye complete document download,saran boye end,saran boye 1 to end,saran boye facebook,saran boye page 1 facebook,saran boye hausa novel complete,saran boye hausa novel wattpad,saran boye littafi,saran boye last page,saran boye littafin hausa,saran boye novel,saran boye na bilyn abdul,saran boye na billyn abdul,saran boye on wattpad,saran boye page one,saran boye page 1 on facebook,saran boye page 1,saran boye page 30,saran boye page 23,saran boye 51 to 60,saran boye 21 to 30,saran boye wattpad,saran boye wattpad 1,saran boye hausa wattpad,Saran boye
Saran boye | Complete |
Uploaded by | zamgist.com.ng |
File Size | 1.8mb |
Hausa Novels WhatsApp Group | Click here |
Telegram Group | Click here |
Novel Price | Free |
Novel Author | Billyn Abdul |
Tags | |
Published date | 26 – 09 – 2022 |
Read: Littattafan hausa novel complete guda 500
DOWNLOAD
Karanta Kadan daga cikin Saran Boye Complete Hausa Novel
Tun a farkon shigowa anguwar zaka shaida lallai ana biki, musamman da gidan da ake taron ya kasance shine na biyar a farkon shigowa layin.
Cike titin layin yake da yara da ƴammata harma da manya maza da mata. Musamman a cikin babban haraban massalacin dake manne da katafaran gidan da tun daga kallon gate ɗinsa zaka san ya wuce raini a gine da yalwar girma.
Rumfunane guda uku a tsaye, waɗanda gaba ɗayansu an cikasune da fararen kujeru bisa tsari. Rumfar farko cike take da manyan malamai masu faɗa aji a ƙasar dama wasu ƙasashen ƙetare musamman na musulmai. Rumfa ta biyu kuwa matane zalla a cikinta tundaga ƙanan har zuwa manya. Rumfa ta uku mazane suma manya da yara.
Babban abin birgewar da ƙayatarwar shine shigar kamala da mutunci dake tattare da jama’ar wajan. Duk da taron bikine kowa ya suturta jikinsa, babu wani mai shigar ALLAH wadai ta nuna tsiraicin da ake laɓewa da sunan biki.
Duk da cikar da wajen take da shi hakan bai hana yawaitar mutane a cikin gidanba shima. Lallai da gaske gidan babban gidane, dan a kallo ɗaya zaka fahimci gidan family house ne, dan kuwa yafi ƙarfin mallakar mutun guda kai tsaye. Daga jikin gate ɗin gidan zaka iya ganin dukkanin yawan ɓangarorin gidan da aƙalla zasu iya kai sashe biyar zuwa shidda, ginin iri ɗaya ne babu wani banbanci game kallo da ga nesa, saika shiga daga cikine ka fahimci kowa da kalar tsarin da yafi buƙata a nasa sashen.
Lokacine bana banbance minene a cikiba, ko mi aka tsara. dan haka nabi ayarin mutane masu kai kawo zuwa sashe na biyu da yafi ɗaukar jama’a. Kasancewar duk mutane na a harabar masallaci wajen da za’a gudanar da walima ya bani damar kutsa kai har cikin ɗakin da naji ana masa ishara da amarya na ciki.
Ƴammata ne da a ƙalla zasu kai goma zuwa sha a ciki, kowacce nata ƙoƙarin ƙimtsa jikinta dai-dai buƙatarta cikin doguwar riga milk color mai adon golden ɗin furanni da aka ƙawata da stones a gabanta da ƙarshen hannun. Hirarsu suke da dariya har baka iya jin mi wani yake faɗa.
“Oh ALLAH, Aure mai saka kowa hankali. Su o’e tunkan Yah Ab.. Yaci ƙaniyar bakin harya mutu haka?”. Ɗaya daga cikin ƴammatan dake naɗa ƙaramin golden veil a kanta ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya. Kusan a tare duk suka juya suna kallon wadda ke kwance saman gado ita kaɗai ta juya musu baya, kwance take rubda ciki da ɗaurin ƙirji sai ƙaramin hijjab a jikinta. “Hhhhh! Wlhy kuwa Iman, kinga dai bakin tsiwa tun jiya ya mutu”.
Wata tabama mai maganar amsa tana dariya itama da ƙarasawa jikin gadon, yayinda suma sauran suke dariya suna nufar gadon. Sai da suka zagayeta sannan suka haɗa baki wajen faɗin “Gobe zata fashe!!!” tare da ƙyalƙyalewa da dariya suna tafawa.
Ƙaramin tsaki wadda ke zaune can gefen mirror tana kwalliya taja tare da taɓe baki, taɗan hararesu idanunta cike da ƙwalla, cike da fushi ta ajiye hodar da take shafawa ta fice daga ɗakin.
Bama susan tanayiba, dan sukam hankalinsu nakan amarya suna cigaba da mata ihun “Gobe zata fashe!! Gobe zata fashe!!!”.
Faɗi suke da ihu sosai suna dariyar tsokana irinta ƙawen da ƙuruciya ke ɗawainiya da su, dan gaba ɗaya yarane ƙanana da bazasu wuce 16-17 ba.
Hawayen da tun ɗazun take haɗiyewa ne suka silalo saman kumatunta a hankali. Bata motsaba, kamar yanda bata buɗe ido ta kalli ƙawayen nata dake mata shaƙiyancin ba. Ita kaɗai tasan mi takeji a ranta tun daren jiya.
Tabbas wannan ranace data daɗe tana fatan zuwanta itada masoyinta Yah Abdallah tun bata gama sanin ciwon kanta ba. Sai dai batasan miyasa tunda aka shiga satin bikin jikinta yay sanyi ba kuma.
Tasan hakan bazai wuce nasaba da sabuwar rayuwar da zata wayi gari a cikinta gobe idan ALLAH ya kaimu ba. Ta sake matso hawayen masu zafi tana jan ajiyar zuciyar da har jijiyoyin wuyanta saida suka miƙe………..
“Ya salam! Yaran nan lafiyarku kuwa!!?”. Akafa faɗa a bayansu da ƴar kakkausar murya.
Tsitt ɗakin yayi, duk suka juya suna kallon mai maganar. Ta sake tafa hannayenta tana riƙe haɓa.
“Oh ku ɗin nan, yanzu nan bama ku sakata ta shiryaba kuka zauna shiriritar da kukafi ƙwarewa akai?”.
“Afuwan Addah”. Ɗaya ta faɗa tana ɗan sosa bayan wuya na alamun jin kunya. Girgiza kai Addah tayi tana ƙarasowa gaban gadon, “To naji, ku fita ku bani waje na kimtsata”.
Ɗai-ɗai suka ringa fita suna ƙananun ƙunƙunai na alamar ba haka sukaso ba, amma sanin yau Addah babu fuskar wasa tattare da ita yasa babu wanda ya iya cewa komai.
Ita dai bata kulasuba, dan yau babu ƴan wasan a kanta.
Kamo ƙyaƙyƙyawar budurwar tayi ta zaunar tana faɗin, “Tashi kinji dear, kukan ya isa haka, kefa amaryace, amaryarma mai tsada ga ƙyaƙyƙyawan miji irin Abdallah.
Ko bakison auren a fasa ne?”.
Baki budurwar ta tura gaba tana sake matso hawayenta, sai kuma ta faɗa jikin Addah ta sake fashewa da kuka. Karan farko Addah tai dariya tana shafa bayanta.
Tace, “Oh Rabbi, yau ga Nu’aymah shugabar tsiwar gidanmu tayi laushi darajar aure”.
Ita dai sakema ƙarfin kukanta tai tana narkewa jikin Addah. Sunja kusan mintuna huɗu a haka kafin Addah ta ɗagota tana sake faɗaɗa fuskarta da murmushi, zaunar da ita tai sosai ta kama bakin mayafinta ta share mata hawayen fuskarta tas duk da wasu na silalowa kaɗan-kaɗan.
“Haba Nu’aymah’n Abbah kukan ya isa haka mana, ko an miki wani abune?”. Kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya a jajajjere. “To wani waje ke miki ciwo ne?”. Nanma ta girgiza mata kai. “Ikon ALLAH, to minene ya sakaki kuka irin haka? Keda zakiyi auren soyayya Nu’aymah?.
Ki duba kowa a family ɗin nan cikin tsantsar farin ciki yake da auren nan naku, dangi ta ko ina sun iso gobe idan ALLAH ya kaimu kawai ake jira. Umm. Hajjo, su Abbanki damu baki ɗaya kowa yana cike da farin cikin wannan alkairi. Ɗazun nan mukai waya da Angon shima jirgin ƙarfe uku zasu biyo daga Abuja, yanzu hakama sun taso inaga shi da abokansa.
Ai nazata yau ranar farin cikice a gareki mara misaltuwama Nu’aymah. Uhhmm?”.
Hannu tasa ta share hawayenta, cikin rawar murya tace, “Addah wlhy inajin tsoro ne?”. Da mamaki Addah tace, “Tsoro kuma Nu’aymah? To tsoro akan mi Uhhmm?.
Ko wani abune ya faru dake bamu saniba?”. Nanma kanta ta girgiza mata tana haɗiyar zuciya dajan numfashi.
Addah ta sauke nishi tana girgiza kai, hannu ta ɗaura kan haɓarta ta ɗago fuskarta. “Kalleni Nu’aymah”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launinsu ya koma Jaa, gashi sun kumburo saboda kukan data sha ta saukesu akan Addah”.
“Kukan ya isa haka kinji daughter, kicire komai a ranki babu abinda zai faru sai alkairi, duk wani tsoro da kikeji ki ciresa a zuciyarki, kiyi farinciki dan gobe ranarki ce idan ALLAH ya kaimu, fatanmu ALLAH ya sanya albarka a al’amarin ya baku zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, ALLAH yasa wannan haɗi ya zamewa family ɗinmu alkairi duniya da lahira”.
A zuciyarta ta amsa da amin, a zahiri kuwa sai tai ƙasa da idanunta alamar jin nauyin ta. Lura da hakan yasa Addah yin murmushi da lakace dogon hacinta. Tace, “Yauwa tagaban goshin Hajjo tashi ki shirya gashi can har an fara walima babu amarya”.
Ɗan murmushin yaƙe kawai tayi da miƙewa bisa umarnin Addah. Dama tayi wanka tuni, dan haka ta sake wanko fuskarta yanzu kawai ta dawo inda Addah ke jiranta.
Ƴar kwalliya taimata da bazata takurataba, kafin ta sata ta shirya cikin atanfa zani da riga pitch da ratsin Maroon. Ɗinkin yay mata ɗagwas ajiki kasancewarta mai murzajjen jiki, dan sam Nu’aymah ba siririya bace, badai za’a kirata mai ƙiba ba, amma jikinta a mulmule yake babu alamar rama sam duk da kasancewarta yarinya ƙarama sosai.
Baƙar riga mai zubin alƙyabba da tasha ado da pitch zare aka bisa da stones ta saka mata, da ɗan turare kaɗan, ta bata flat takalmi baƙi ta saka wanda yayma farar ƙafarta data sha ƙunshi jaa da baƙi ɗas.
“Masha ALLAH amaryan ɗana Abdallah” Addah ta faɗa tana mata alamar tayi ƙyau da hannu. Ɗan murmushi tayi da maida kanta ƙasa na alamar jin kunya.
Yarinyar ɗazun dake jikin Window a laɓe tana kallonsu ta share hawayen da take faman yi tun ɗazun, duka maganar Addah da Nu’aymah akan kunnenta da idonta suka faru, ta taune leɓenta da ƙarfi tamkar zata hudashi tana ƙoƙarin danne kukan dake neman kufce mata da ƙarfi…
Babu ɓata lokaci Addah ta taimaka ma Nu’aymah suka fito harabar gidan, inda sukaci karo da wasu tsoffin mata su kusan biyar. Da ɗan faɗa farar ciki ta watsa musu harara tana faɗin, “Wai mi kuke da amaryar a cikin gida da har yanzun an gaza kaita wajen walima Fauza?”. Cike da girmamawa Addah tace, “Ayi haƙuri Hajjo, mun tsaya shirine shiyyasa”.
To wane shiri kuma nikam kamar wadda za’a kai ɗakin miji yau, kinga taho Zainabu”. Tai maganar da kama hannun amarya Nu’aymah. Babu musu Addah ta sakar mata ita tana murmushi da binsu da kallo har sai da suka isa gab da gate sannan ta sauke ajiyar zuciya. Yunƙurawa tai zata bi bayansu itama………
Caraf aka riƙe hannunta. Juyawa tai da sauri, sai dai ganin wadda ta riƙotan yasa taƙi cewa uffan. Kallon gefe da gefe tai, ganin mutane nata ɗan kai kawo yasa ta sake tsuke fuska tana kallonta…….
“A’ah! Adawiya lafiya kuwa? Fauza mi akai mata haka?”. Firgigit Addah tai da ture hannun Adawiya daga kan nata tana harararta, sai kuma ta kalli mai maganar fuska a narke.
“Umm bar wannan ƴar taki kinji, bansan mike damun kansuba daga ita har Nu’aymah, canfa na iskesu sun haɗe kai a ɗaki sunata dirzar kuka ko shiryawa basuyi ba, ni wannan shaƙuwa tasu har tsoro take bani wlhy, gashi kuma mai rabawa yazo….” ta ƙare maganar da sharce hawaye tana kallon Adawiya dake jikin Umm tana kuka tamkar ranta zai fita.
YOU MAY LIKE:
Good