Silar Fyade Hausa Novel Complete

A Wannan shafin, mun kawo muku cikakken littafin silar fyade hausa novel wanda shahararriyar murubuciyar nan mai suna ummu maher ta rubuta takuma wallafah.

Silar Fyade Topic Contents

  • Silar fyade hausa novel page 1
  • Silar fyade hausa novel page 2
  • Silar fyade hausa novel page 3
  • Silar fyade hausa novel page 4
  • Silar fyade hausa novel page 5
  • Silar fyade hausa novel page 6
  • Silar fyade hausa novel page 7
  • Silar fyade hausa novel page 9
  • Silar fyade hausa novel page 10
  • Silar fyade hausa novel page 11
  • Silar fyade hausa novel page 12 up to 30.

Silar Fyade Hausa Novel

Bismillahir Rahmanir Rahim

1 & 2

Kuka na ke kamar raina zai fita tsabar tashin hankali,wai yau ni ce agaban gawar mahaifiyata ina kallonta bata numfashi,wani irin ihu na sake sakawa ina girgiza Ummana cikin kuka na ke ce wa”Ummana don Allah ki tashi kada ki mutu,in dai da gaske ne kin mutu to nima tabbas mutuwa zanyi”.

 

“ke wai wacce irin mahaukaciya ce?saboda uwarki ta mutu sai ki saka mutane a gaba kina wani kukan banza?to wallahi ba a gidannan ba,banza karuwa wacce ta bawa wani ɗa namiji jikinta ya yi mata ciki,ai gashinan yanzu kin kashe uwarki da baƙin ciki kinzo kina wani kukan banza da wofi”.

Da sauri na jiyo da idanuwa na da sukayi jawur kamar wuta,tsabar tashin hankalin da na ke ciki bai saka na mayarwa da Maman Nusaiba amsa ba,sai ma ba da ƙaimi da na yi akan kukan da na ke yi,don dole suka fita suka ƙyeleni sai da na yi mai isata sannan na yi shiru,ɗan ciki na naji yana ta motsi kamar zai fito wanda tun da na samu cikin baiyi motsi mai ƙarfi haka ba.

Ina ji ina gani aka fita da gawar Mamana,a duk cikin mutanen da suka zo ta’aziyya babu mai rarrashi na, ni kaɗai na ke kuka na ina share hawaye ranar yini na yi banci ba bansha ba,ƴan uwan Mama na suka kawo abinci katan katan suna ta sha’aninsu ɗaura wannan ɗaura wancen,ni dai ina ɗaki ina tunanin rayuwa ta,a shekaruna da basu wuce 15 ba naga rayuwa kala kala.

Ina ɗaki naji Baba na yana ƙwala min kira,da sauri na fito jiki na sai kakkarwa ya ke saboda rashin cin abinci ga juna biyu a jiki na.

 

“Ke dan iskanci shine ki ka shige ɗaki ki ka ƙwanta uban waye zai yi miki duk wannan aikin da jama’a su ke maza fito ayi da ke,banza ballagaza kawai yaja wani dogon tsaki ya fita.

Ko da na fara aikin wani irin mugun jiri ne ya dinga ɗiba na ina daurewa don nasan halin Baba yanzu zai dawo,a haka har na gama tatar ƙullin kokon,ina tuno da mahaifiya ta ina ta kuka mai ciwo.

 

Girke2 ake a gidan kana shigowa zaka ji ƙamshi ta ko ina,masu aikin gidan kowa da aikinsa,gida ne ƙaton gida mai ƙyau d tsari kana ganin gidan kasan gida ne na masu kuƊi sosai.

 

A tsakiyar garden ɗin gidan an saka wata mat ƙatuwa doguwa wacce zata sada ka da cikin gidan mai ɗauke da sunan,WELCOME MY LOVELY SON.

 

Hajiya Barakat ce ta ke ta zagaya gidan tana ganin irin decoration ɗin da aka yiwa gidan,wanda ya yi tace ya yi wanda baiyi ba ta ce bai yi ba.

 

Da wuri ta saka ƴaƴanta a gaba ƴan mata guda uku masu suna,Zeenat,Rabiat,Aisha,Fatima.

 

Suka tafi taro babban yayan nasu sojan sojoji wato admiral Aliyu Muhammad,A.A M.

Silar Fyade Hausa Novel

Silar Fyade hausa novel 5 & 6

“Me Martaba dafatan mun sameku lafiya”?.inji Salimat ta faɗi hakan tana mai sunkuyar da kanta ƙasa alamar girmamawa.

 

Kallonta Me Martaba ya yi yana yaba hankalin ƴarsa tilo wato Salimat,da ƙer ya buɗe balinsa irin na ƴan sarauta ya ce”lfy ƙlau gimbiya Salima.”

 

shiru Salimat ta yi tana jin kunyar sanar da mahaifinta wannan maganar,gashi kuma babu wanda za ta faɗawa ya faɗa masa don ba ta da uwa araye yau shekarar mahaifiyarta huɗu da rasuwa.

 

Yasan halin Salimat da kunya saboda haka ya janyo abin rubutu ya miƙa mata ya ce”Gimbiya a rubuta mana anan komene ne?”.

 

 

cikin sanyi ta amsa ta rubuta abin cikin kunya ta miƙa masa, hannunta yana ta girgiɗi,sai da ta bawa mahaifinta me martaba sannan ta yi dana sanin miƙa masa wannan takaddar.

 

 

Mamaki sosai Me martaba ya yi,yana kallon Ƴar ta sa cikin nuna kulawa ya ce”a tashi a tafi zamu nemeki”.

 

 

Jiki babu ƙwari Salimat ta tashi kamar zata yi kuka,saboda  yadda Me martaba ya yi magana don kana jin muryarsa kasan a fushi ya faɗe ta,don tasan abinda ta aikata  laifi ne babba a cikin gidan sarauta,kuma gasu fulani kun san yaren fulanj aƘwai kunya,ita dai za ta ɗauki ƙaddarar soyayya don da alama ba tada dacen masoya,ayanzu gimbiya na da shekara 25 aduniya ta ga ƙalubalen soyayya kala2 har kawo i yanzu,saboda wasu don kuɗin mahaifinta suke sonta ba don Allah ba.

 

Kuka sosai su afra suke kuka bayan sun dawo daga boarding skull don yanzu anyi hutu.

 

Ina cikin lallashinsu Khadija ta ce”wallahi Anty Rabiatu baki ƙyautawa rayuwarki ba,da ki ka bawa namiji jikinki ya yi miki ciki,yanzu gashinan kin kashe mana uwa da baƙin ciki”.

 

 

Salimat ma ta ɗora da cewa”Wallahi  Anty Rabiatu na tsaneki tsana mafi muni a rayuwata don wallahi ba zamu yafe miki ba,kin kashe mana uwarmu da baƙin cikin ki.”ta faɗar hakan ta fita tana hawaye.

 

Afra ce kawai ta kalleni ta ce”Anty duk da a yanzu shekaru na basu wuce 15 ba amman nasan rayuwa sosai,duk da na girmi Khadija wacce a yanzu tana da sha uku da rabi 1/3,amman ta gane cewa baƙin cikinki ne ya kashe Umma, amman yana da ƙyau mu tsaya muyi miki adalci ke ma,ki faɗa mana abinda ya faru da rayuwarki don wallahi ba zamu yarda da duk wanda ya lala ta miki rayuwa ba”.

 

 

ƴar dariya kaɗan Rabiatu ta yi sannan ta ce”Afra kenan kina nan da halinki na ƴan jarida?Allah dai ya cika miki wannan burin na ki”.

 

ka saƙe Afra ta yi tana kallon yayar ta cikin tausayi ta ce”Antynmu na sanki da zurfin ciki don Allah ki faɗa min don nima in fita daga sarƙaƙiya please”.ta haɗa hannayenta alamar ban haƙuri.

 

Riƙe hannayen Afrah na yi a hankali na ce”zan faɗa miki Afrah,don hankalinki ya ƙwanta amman a rayuwata ba na son to na asirin kowa,amman ya zama dole shima asirinsa ya tonu”.

 

ina kaiwa nan na tashi na jingina da sip ɗin mahaifiyarmu na fara ba ta labarin.

Labarin ya ɗakko asali ne daga..

 

Silar fyade hausa novel 3 & 4

Cikin ta kunsa mai kyau da tsari ya fara sakkowa a jirgin ,fari ne ƙal kamar zaka taɓa sa kaga jini tsabar farinsa,yana da jiki da kuma tsayi, ƙyaƙƙyawa ne shi ajin  farko,yana sanye cikin wasu haɗaɗɗun ƙana nan kaya,waɗanda suka amsa sunansu ya cire cort ɗinsa ya riƙe a hannu yana gƴara necktail ɗinsa.

 

 

Ayshe ta fara hangosa ta ce”Hajiya ga yaya cen yana sakkowa,gaskiya yaya ya daɗa ƙyau wallahi gaskiya Hajiya yaya ya fimu Ƙyau”.

 

 

Rabiatu ta ce”ke kuma kina kishi ko?ke dai wallahi aisha kishi ne da ke wallahi,ke ce ki ka yo dangin Papa shuwa arab kishi ne dasu”.

 

 

Hajiya ta ce”kuyi wa mutane shiru zaku fara halin ko?”.suka ja bakinsu suka yi shiru ita daman Zeenat da Fatima miskilanci ne dasu irin Yayansu.

 

 

Zeenat tana da shekara 25,sai Fatima 22,sai Rabiatu shekara 19,sai Fatima auta mai shekara 17.

 

shi kuma babban gogan yana da shekara 35 a duniya,Har hajiya ta fitar da ran haihuwa sai kuma ta dawo ta haifi mata har huɗu.

Da sauri Hajiya ta ƙarasa ta rungume ɗanta cikin so da ƙaunarsa duk da sojojin da ke bayansa,shi kuwa jan zaki Aliyu Haidar kunya ce dashi sosai,don haka cikin kunya ya rungume ta,shi daman tun yana yaro kunya ce dashi,tun yana shekara 4 ya daina yadda mahaifiyarsa na yi masa wanka,sai dai ya rufe gabansa ta yi masa,haka har ya girma shi mai kunya ne.

 

 

 

Yana cikin cin abinci wayarsa ta kama ringing ɗin wayarsa,ya ƙi ɗauka Hajiya Barakat ta ce”haba son ka ɗauki wayar mana kaji ko menene?”.ta faɗi hakan cikin yaran yarbanci,shima cikin yaran ya ce “to momi”.

 

“Haba A/D ka tausayamin ka dinga ɗaga waya ta,kasan dai babu ƙyau wulaƙanta ɗan adam, please ka yadda ina sonka tsakani da Allah”.

 

“oky”.

 

kawai ya ce mata ya kashe wayar.

 

Salimat ta goge hawayen da suka zubo mata don matuƙar ba ta auri admiral ba komai zai iya faruwa,ya zamar mata dole Ƙara Ƙaimi wajen yin addu’ah don komai yazo da sauƙi,tana cikin wannan tunanin ta tashi ta shiga bathroom ta ɗauro alwala ta fara yin sallah tana kai kukanta ga mahaliccinmu subhanahu wata ala.

 

 

 

 

 

 

 

***       ***      ***

 

yau aka yi 7 ɗin mahaifiyata dangi duk sun fara tafiya,har yanzu mutuwar mahaifiyata tana cikin ƙoƙon zuciyata,na share wata ƙwallar da ta cukomin ƙwarmin idanuna,na gogesu ina cigaba da ƙara tsanar wannan bawan Allahn da ya yi sanadin rugujewar rayuwar a halin gidanmu.

 

Ƙannena uku ne duk suna bording skull,Salimat,Afra,khadija.

 

 

Har lokacin kuma ba a gaya musu rasuwar mahaifiyarmu ba,ko ya ya zasuji idan suka ji mahaifiyarmu ta cika oho?.

 

 

ina cikin wannan tunanin naji an watsomin ruwan kanzo mai sanyi,don alokacin safiya ce,na waiga don ganin maiyi min wannan izayar,mmn nusaiba ce da kuma Hafsatu,wacce ta  kasance ƙanwa awajen mahaifina.

 

Suna ta kumfar baki wai na iya munafunci na shiga ɗaki na ƙi fitowa don nasan na yi abin kunya.

 

 

 

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara fitomin a ƙwarmin idanuwa na,na gogesu na fita don yin aikin da suka ce zuciyata tana yimin ƙuna.

Karanta: Hariji Hausa Novel Complete

Silar fyade hausa novel 7 & 8

“Wata rana Umma ta aiki ni gidan Baba Na sidi sai akai rashin sa a ranar anyi ruwa kamar da bakin Ƙwarya,har Mama Khaltum tace in ƙwana na ce mata ai ban tambayi Mama ba,babu yadda bata yi dani ba nace ni tafiya zanyi haka na biyo hanya ga dare ga komai haka na fito ina ta tsare motoci amman babu wacce ta tsaya.

 

Na yi tagumi kamar zanyi kuka wata ƙyaƙyawar mota ce naga ta shawo ƙwanar titin,banji tsoro ba haka na tashi naje tsakiyar titi,ina tsayar da motar da hannuna,baiyi niyyar tsayawa ba amman sai da na tsayar dashi,sauke glass ɗin ya yi,kansa a ƙasa bai kalleni ba ya ce”come in”.

 

 

da sauri na shiga ina ta raba idanuwa,ban kalli mai motar ba shima bai kalleni ba,da alama bashi da lafiya don naji yana ta numfarfashi ni kuwa tsoro na ya ƙara ƙaruwa sosai jin wani baƙon al’amari yana ta ziyarta ta,shima a nashi ɓangaren haka wannan abin ya dinga faruwa.

 

 

 

In ta ƙaice miki a wannan dare ne abubuwa da dama suka dinga faruwa,na samu kaina a mai ƙin hanashi duk abinda ya ke son faruwa,tun abin yana tafiya gentle gentle har dai ya yi tsanani,ban san me ya faru dani ba?ban taɓa jin tsananin feelings ba sai aranar,a wannan dare komai ya faru kuka na ya tsananta sosai.

 

Shima hankalinsa ya tashi sosai da sosai,don ina jin gunjin kukan da ya ke yana cewa Allah ka sani ban taɓa zina ba,ban taɓa kusantar ta ba sai yau ya Allah idan mafarki na ke ka farkar dani ya Allah.

 

A matuƙar hargitse na fito daga cikin motar ina ji yana ta yimin magana don shima har fitowa ya yi,amman na fizge hannunsa na tsayar da wata adaidaita kamar ƴan party ya ɗebo,akayi sa a unguwarmu ɗaya don haka muka tafi.

 

 

Ina dawowa Baba yana kiciniyar kulle gida don sun san tunda na kai yanzu to sai gobe zan dawo,mamaki Baba ya yi na ganina amman bai ce komai ba ya matsamin na wuce,kai tsaye ban ɗaki na wuce ina kuka haka na cire sutura ta,kamar a mafarki haka na ke ganin komai yana dawomin,to me ya faru dani haka na bada kaina ga wani wanin ma ban sanshi ba.

 

Kaca kaca siket ɗina ya yi da jini ina kallonsa na saka wani ihu a banɗaki,Baba da ya ke a tsakar gida hankalinsa ya tashi yana tambaya ta lafiya,shiru na yi ina rufe baki nan ina kuka don tabbas na cigaba da kukan to kaina xan tonawa asiri.

 

Don wannan abin ba dole ya yi min ba,ban san me ya shiga brain ɗina ba,Rabiatu me addini me kishin musulunci,me girman kai awajen wasu saboda kamun kai to me ya sakani aikata haka kuma?.

 

 

Ina fitowa ina ɗingishi na hango Baba da Mama suna tsaye cirko2  suna kallo na na sunkuyar da kaina zan shige ɗaki,Mama ta daka min tsawa ta ce”aiken ne sai yanzu?Kuma me ya samu ƙafarki ki ke ɗingishi”?.

 

wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riskeni,gaba na yana dukan uku uku na buɗe bakina daƙer na ce faɗuwa na yi Mama,ba tare da ta ƙara cewa koma ba ta shiga ɗaki ita da Baba.cen kuma ta fito a lokacin ina zaune na yi tagumi da hannu bibbiyu ga ƙasa na kamar zai tsage saboda tsananin zafi.

 

“Rabiatu ina saƙo na”?.

 

sai alokacin na hau dube dube don sai yanzu na tuno na barshi a motar wannan azzalumin mutumin.

Anan zan tsaya saboda matsalar chagi.

Karanta Wasu littafan hausa novel damuka dora:

Kusauke Littafin Izuwa wayarku domin cigaba DA karatu.

Silar Fyade Hausa Novel Complete Document Download

Title Silar hausa Novel Complete
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 498kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author Ummu maher
Tags Silar fyade
Published date 18 – 09 – 2022

Download Txt

Dafatan kunji dadin wannan littafin? Kuci gaba DA ziyartar wannan shafin domin samun Sabbin littafan hausa novel.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*