Yar Aiki Hausa Novel Complete

Barka da zuwa wannan shafin namu na littafan hausa novels, jnda muka kawo muku yar aiki hausa novel, Yar aikin Uncle Complete da dai sauransu.

Yar Aiki Hausa Novel Complete

Muna mika godiya ga Allah mai kowa mai komai. Tsira da aminci sutabbata ga shugaba kuma fiyayyan hallita wato Annibi Muhammad saw da ahalinsa baki daya.

GABATARWA
Wannan littafin mai suna Yar aiki littafi ne da narubatshi akan wata yarinya mai suna Ummi. wanda iyayanta suka rasu ta fada cikin wata mummunar rayuwa ta kunci da walaha daga hannun matar kawunta sanadiyar maraici. Fatammu Allah yasa musu hali irin wannan su gyara. Allah yasa mudace baki daya.

Yar Aiki Hausa Novel Complete

Part 1

Nafara aiki agidan wata Hajjiya Amina amma anamata inkiya da hajjaju. nafara aikin agidan lokacin Ina da shekara goma sha hudu. tun bayan rashin iyayena danayi a sanadayar wani hatsari da ya afkamusu akan hayarsu ta zuwa kauye ziyara. Mahaifina babban malami a garimmu, domin kuwa yana da dalibai fiye da dari wanda suke koyan karatu awajansa. dalilin haka kowa yake girmamashi da kuma bashi daraja. Kafin mahaifina yabar duniya nasamu kulawa mutuka domin kuwa tunda nafara samun hakalin kaina ko waje bana lekawa balle yawo mara dalilai. idan kaganni awaje saide da babban dalili. sannan haka bani da wata kawa face mahaifiyata.

Koda yaushe ina gida ina karatun alkur’ani da sauran litattafai na addinin musulinci, wanda yasa komai na nema awajan mahaifina baya hanani domin inayin abinda yakeso. wata rana bana mantawa, akwai wani dalibinshi da ya gani yace yana sona saboda tarbiyar da nasumu daga wajan iyayena. Bayan ya nemi izini wajan mahaifina kuma ya amince da shi harma yafara zuwa wajena baiwace kwana biyu dayin haka ba Allah yayi musu rasuwa a sanadiyar wancan hatsarin da ya faru da su lokacin zuwan su kauye.

Bayan anyi sadakar arba’in ne kawuna yadauke ni yakaini gidansa saboda shine kani awajan mahaifina. Saide kuma kashi!! bashi da ilimi irin na mahaifina, Wanda asanadin haka bashi fis balle as agindasa sai yadda matarsa tayi dashi. Nashiga damuwa da tashin hanklin saboda irin abinda natarar agidan kawuna wanda bantaba ganiba tunda nazo duniya, saboda bantaba kaiwa lokacin da nakai awaje ba saida narasa mahaifana, wanda sadiyar haka nayi kuka mara misali. Da farko natsinci kaina a talla wanda da basanshiba, idan nafita tallan kosai tun safe bana dawowa har sai nasiyar, idan kuma bansiyarba nadawo sai duka da zagi ta uwa ta uba, dan adalilin haka ma, ko abincin karyawa baza’abaniba haka zan wuni da yunwa.

Karanta:ÂThe Sexy Boss Hausa Novel By Mamam Teddy

Bayan haka idan rana tayi zan dauki tallan abinci namma ni ce lungu-lungu waje-waje domin nasamu Allah yasa nasiyar nakoma gida da wuri, Duk lokacin da akace abinci bai kareba, tou tsoro da fargaba sune ke kai ziyara azuciyata, saboda fada da duka yazama jikina. wata rana sai nakai har kusan magariba ina talla domin ni ce har cikin tashar mota duk dan nasiyar nakoma gida. Haka kuma idan nadawo akwai kuno da akemin na dare shima bayan nagama talla zan fita da shi bakin kasuwa, wanda shima nakan kai har kusan karfe goma bandawo ba, amma ita ko ajikin ta. Karfa kumanta da cewa duk wani nau’in aiki na gida nace ke yi komai dare idan nadawo sai nayi.

Asuba nayi zantashi nafara shara bayan nagama nayi wanke-wanke nakuma dauki koko nafita talla, Wanda shine akullum dabi’ata ta yau da kullum. Duk lokacin da na tuna da iyayena sai naji hawaye na kwaranya cikin idanuna bamma san inayiba. Wani abimma takaici shine, duk lokacin da akarasa wani kudi acikin kudin tallan babu ruwanta saina nemo aduk inda nasan zan samu. Ahmed wani mutum ne mai kirki kuma mai tausayi duk lokacin da ya ganni yakan siye kunon da koko duk yai sadaka. Abinci kuwa dama kullum ne babu fashi saina kai koda kuwa bazai ciba. Dalilin haka ne muka saba da Ahmed kuma muke mutunci da shi. Dan duk lokacin da yagani cikin damuwa shine ke kwatarmin da hankali da fadamin maganganu masu dadi.

Wani lokacin idan narasa kudi nakanje wajanshi nafadamai abinda yake damuna, Allah sarki haka zai dauki kudi yabani cikin tausayi na. Ahmed mutum ne mai addini ga kuma ilimi, kullum idan kaje shagonshi babu abinda yake face karatun alkur’ani da kuma nazarin litattafai na addinin musulinci, Wanda yasa duk lokacin da nagashi sai naringa tunawa da mahaifina, take wajan kawai saina ji ina zubar da hawaye mara misali acikin idona. Wata rana bana mantawa akwai wani lokacin banasiyar da abinci ba, nayi kwantai sai naje wajan Ahmed nake fadamishi halin da nake ciki, tou ashe akwai wata kawar matar kawun wana taje wucewa taganni awajan atsaye, kafin kace me har tawuce gida takai gulmata akan cewa ta ganni da wani acikin wani shago bisa alamu de akwai lauje cikin nadi. – Yar Aiki Hausa Novel Complete

Ina dawo gida nan tafara zagina da duka da cewa “shegiya daman ashe iskaci kike idan nadauramiki tallan ko? tou shikenan daga yau babu ke babu talla ma, domin baza kije kijawomana bala’iba muna cikin zaman zamummu shegiya mara tarbiya. Tou daga nan ne sukayi shawara ita da kawarta akan kawai nafara zuwa wani gida aiki mana koda ta huta da wannan bala’in? kawarta fada haka. Bayan sun gama shawar kenan sai ga kawun nawa ya shigo namma suka fara fadamishi karya da gaskiya akaina shi kuwa yahau kai ya zauna. Haka de naketa rayuwa cikin takura da kunci mara misali amma kullum addu’ar da nake ita ce, Allah yasa nabi iyayena inda suka je saboda tsananin takura da nashiga. – Yar Aiki Hausa Novel Complete

Wasu Na Karatun:ÂJarababben Namiji Complete Hausa novel

Asabar ita ce nara ta farko dana tsinci kaina agidan aiki, wato gidan Hajjiya Amina wanda ake mata lakabi da hajjaju, nafara aiki ne da shara da wanke-wanke, Wanda daga bisani kuma nakoma cikin wani mahaukacin falo mai mutukar girma, Kai duk wanda ya ga wanan falon, hmm!! abin de ba’acewa koami sai wanda yagani kawai saboda girmansa. Haka kuma falon anzuba gaya nagani na fada amma haka zambi daya bayan daya Ina gogewa kamar baiwa. Bayan nagama wannan kuma akwai dakin Hajjiya da kuma bangaran Alhaji shima yadda nayi a falo haka zanyi asuran dukanin dakunan da suka rake wanda banyiba.

Bayan na kammala duk wannan aiyukan kuma, haka za’a tulamin kayan wanki namma wake na shanya sanan kuma na dushi kicin dan daura kirkin abicin rana da kuma dare. wannnan kullum shine aikina na yau da kullum agidan da aka kaini aiki. Duk lokacin da kaga na zauna hutu tou tabbata dare ne yayi. Kamar yadda Hausawa suke cewa “dare muhatar bawa.” Hausawa sunyi gaskiya a wannan batun nasu wallahi kam. Saide abu guda, duk lokacin da naje kwanciya sai nakaranta alkur’ani kafin nai bacci, ciki akwai Falaki da Nasi da kuma Ayatul Kursiyu domin neman tsari kamar yadda yazo daga shugaban halitta Annabi Muhammad SAW. – Yar Aiki Hausa Novel Complete

Yadda naga dare haka zanga rana saboda wuni nake a gida tamkar matar kulle, dalili kuwa ko waje bana lekawa saide idan zanje kasuwa kuma shima tare muke zuwa da direba muje mu dawo, duk lokacin da muke tafiya da direban sai yaga nayi shiru bana magana nayi tagumi, kullum haka kullum haka, kai wata rana saike tambayata “baiwar Allah ke kuwa meke damunki haka kullum kina cikin tunani haka, Allah yasa lafiya? ” Nayi shiru nace, Ehmm!! lafiya kalau. kafin narufe baki sai hawaye shar-shar nasuba idanuna. Inda ya kallen yace” tou Allah ya kyauta.

Shi kuwa Alhaji koda yaushe idan yawo gida yana gani, yana kuma kallan irin yawan aikin da nake sha a gidan, tun bayamin magana harma yakasance idan yadawo yaganni sai yacemin “sannu da aiki ko”. Yauwa Alhaji Barka da zuwa. ita ce amsata agareshi. Haka de alhaji ya cigaba da yamin harma Hajjiya ta fahinci cewa mijinta ya fara min magana. Wata rana naje bangaran Alhaji domin yi masa gyaran daki Kamar yadda nasaba, Ina zuwa sai yace” Kinga yau kibar wannan sharar sai da yamma domin naga aikin gidan yamiki yawa ke daya, dan haka kibarshi kawai sai anjima kinyi. Tou shikenan alhaji nagode nan cikin sauri da juya baya da murmushi na. – Yar Aiki Hausa Novel Complete

Wani lokaci ina zaune nayi tagumi ina sake-sake da tunawa araina, can sai nace “yau kimanin shakarata guda da fara aiki na, amma ko fallan zani bani da shi balle kuma turmin atamfa, sakamakon ko biyar bantaba ganiba a kudin aikin nawa, balle ma nasa rai da siyan wani abu mai amfani da kudin. Kwatsam wata rana alhaji yayi tafiya ya dawo, sai yakawowa hajiya kaya nagani na fada, inda ni ma yakira ni yabani wata babbar atamfa nayi muna mukuta da cewa” yau wacce rana Alhaji yamin kyauta naita murna da jindadi. Saide kashi!! taleko ta koma hajjjiya ce ta biyuni har daki takwace atamfar da mijinta yabani da kuma fadin cewa” tou makira anje wajan boka ko za’a rabani da mijina tou wallahi baki’ isaba sha-sha-sha kawai.

Hausa novel:ÂZaki Hausa Novel Complete

Dalilin haka kwana biyu banje bangaran Alhaji ba domin yi masa shara Kamar yadda nasaba. Alhaji kuwa da ya ga haka sai ya nufi falon Hajjiya domin jin meke faruwa, zuwan shi keda wuya ya iske Hajjiya zaune a falon tayi tagumi alamun akwai damuwa. Alhaji nashiga yayi sallama amma Hajjiya tayi shiru har saida ya je kusa da ita yace “Hajjiya lafiya kuwa naganki acikin irin wannan yanayin?” Budar bakin hajiya fara cewa ita fa gaskiya agidan amfara mata dauke-dauke kuma gaskiya abin yana bata mamaki mutuka, saboda ita da agidan nan duk abinda na ajjiya baya bata sai yanza, tabbas alamu sun nuna cewar masu halin bera agidan nan tabbas. – Yar Aiki Hausa Novel Complete

Budar bakin alhaji cikin fushi yace” Ni ba wannan ce takawoniba ina Ummi yar aikin gidan dan yau tsawan kwana biyu bataje tayi sharaba, wai mai yake faruwa ne haka?” Rufe alhaji keda wuya Hajjiya tafara fada ” Ni gaskiya bangane ba, ta yaya yarinya zata ringa shisshikemaka kamar ma ita ce mai gidan ko na cewa wadda ka aura.” Nan fa rikice ya balle tsakanin Hajjiya da Alhaji akaina. – Yar Aiki Hausa Novel Complete

Kubiyoni don jin yadda takaya tsakanin su akashi na biyu.

Copyright
Sagiru Bn Abdul Aziz

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top