Barka da zuwa wannan shafin namu, inda muka kawo muku cikakken littafin Hausa novel Mai suna: Kwarton Manya Hausa Novel.
Kwarton Manya Hausa Novel
Wani irin hayaÆ™i ne ya turniÆ™e ko ina na wannan gida , hayaÆ™i mai saka ciwon kai ,can cikin wani kitchen na hango wannan hayaÆ™i na fita ,wanda ko ba’a faÉ—a maka ba kasan icen É—anye take amfani dashi ta damuna”. Zainabu abamu ta Ashirin, Zainabu abani ta goma”. Muryar yara kake ji kowa na faÉ—in Abashi na dai dai kuÉ—in sa, wacce ko aka kira da Zainabu ba abun da take sai aikin goge zufan dake saukowa tun daga goshin ta zuwa wuya”.
Sama’ila ne ya leÆ™o da kansa ta windon lange langen kitchen É—in kamin yace ” TaÉ“ Allah shi kyauta ,mutane na cin DauÉ—a basu sani ba”. Saka luddayin tayi cikin Æ™ullun kalallaÉ“an da take soyawa ,kamin ta buÉ—e murya cike da tsiwa ta hau cewa ” Eh Naji Allah yasa dattin jiki na nake É“anÉ“arowa nayi maggi da gishiri na zuba a ciki duka bai dameka ba , bashi ne dai nace a sana’a ta babu ,baxan bayar ba”. Ke Ni kike faÉ—a mawa wannan maganan??.
Yayi maganan a zafafe dama so yake ta tanka ya buga banza”. Eh na faÉ—a maka ,ai Ni wlh da kowa xanyi faÉ—a indai akan kasuwanci na ne”. Tayi maganan tana juya Æ™ullun kalallaÉ“an nata da gaba É—aya garin matafi na É—ari ba sai sauran cefane da tayi”. Sama’ila ne yayi saurin nufan Ƙofan fale falen kitchen É—in da zumman dukan Zainabu ya buga ya gudu”.
Da Umma Halima sukayi arba,nan take ta É—aure fuska ta mau tana magana cike da faÉ—a ” Tattara kabar gidan ,idan baxaka tafi harkar neman ka ba,to kaje dai ko ma ina ne ,na rabaka da Zainabu kaÆ™i rabuwa da ita dai ko? To bari Malam ya shigo zan sa ayi maku iyaka tsakani”. Cike da cizar yatsa Sama’ila ya juya ,sam bai so zuwan mahaifiyar tasu ba ,yaso ya bigi banza ne kamin ya bar gidan kaman yanda ya Æ™udirta.
Zainabu abani kalallaÉ“a. Wani É—an yaro yayayye yayi mata maganan yana miÆ™a mata kuÉ—in hannun shi ,hannu takai tana amsan kuÉ—in haÉ—i da buÉ—ewa a tunanin ta Æ´an biyar² ne guda biyu ,sai kuma taga É—aya”. TaÉ“ amma wannan Uwar taka taci uwar rainin wayo, banda iskanci nine zata aiko ka da biyar in baka wainar fulawa dashi? To kaci Sa’a yau my temper is Off in maka na turawa, da ba don haka ba ,wallahi yanda ka fito mata kana Annuri da kuka zaka koma mata,don sai na kileka ladon bacin ran da ka sani”.
Fice mun da gani dan Æ™aniyar ka”. Tayi maganan tana cilla Naira biyar É—in a wuta haÉ—i da cewa ” Baxan bada biyar É—in ba na Æ™ona ta ladan É“acin ran danayi”.
Ganin haka yasa yaron ficewa kitchen É—in da gudu yana komar mawa Uwar sa da kuka. Saidai Æ´an sayan kalallaÉ“a kowa yana Son mawa Zainabu magana kan abun da tayi bai kamata ba ,amma kuma suna gudun bala’i ,hakan yasa sai dai su bata kuÉ—i ta sallame su suyi ta kansu. Zainabu kiyi sauri ki gama zan aikeki kasuwar Dole ki Sayo mun Kayan yaji”.
To Umma na kusa baifi na soya ta É—ari ba yanxu Æ™ullun ya Æ™are,tayi Æ™are maganan tana karkata kwanon Æ™ullun da baifi kudayi É—aya da rabi ba,nikam nace bala’i wannan wani irin riba Zainabu kebi haka?. Zainabu wai inji maman mu tace ” Kiyi haÆ™uri ki bashi kallaÉ“an ta biyar É—in yaye akayi masa”. Cike da masifa Zainabu ta juyo tana kallon yarinyar da Æ™anin nata da ta cilla biyar É—in sa a wuta ,kana tace ” baxan bayar ba ,ita tana bada bashin kayan sana’ar tane? Ni sai ta nemi cin mun mutumci a nawa ? To na cilla kuÉ—in huta ,Æ™arikon yaye Allah yasa yau ya fito daga ciki duniya”.
Ki fice mun ke dashi kamin na tashi…tayi maganan tana rintse ido na masifa wanda da sauri yarinyar ta tasa É—an Æ™anin ta suka fice. A haka Zainabu tayi ta sai da kallaÉ“an ta gata da jama’a ,amma ba haÆ™uri kamin ta gama tayi faÉ—a babu iyaka. Tana gama kallaÉ“an ko wanka bata tsaya yi ba ,bare wanke fuska ta zura hijab É—in ta iya gwiwa ,yaji dauÉ—an duniya baÆ™iÆ™irin. Umma karo kuÉ—in?”.
Umma ne ta kalle ta sama da Æ™asa ,kamin tace ” Zainabu Bazaki É—an wanke koda Æ™afa ba a haka zaki tafi??. ÆŠan gyara zaman hijab É—in ta tayi kamin tace ” Eh Umma a haka xan tafi , wa’anan mutanen Lagos É—in Æ´an iskan mutane ne,ko wanka nayi naci ado nasa gyale da atampha na fita sunana matan Aure a wurin su…baxasu taÉ“a kira na da budurwa ba indai ba shigar banza nayi ba ,nasa wando 3 quater ,idan kuma shi kikeso nasaka shikenan sai yanxu inna fita na tsaya a Æ´an gonjo na siya da ribar da nasamu ta kalallaÉ“a”.
A’a ina ,maza kinji amsa ta fi ki Sayo mun Kayan yaji komai da komai ta É—ari da hamsin…to Umma sai na dawo “. A dawo lafiya”. Ficewa Zainabu tayi daga gidan tana nufan kasuwar Dole, alhmdullh a wannan karon batayi faÉ—a da tasi’u mai kayan yaji ba ,ta É—auki hanyar dawowa gida ,wanda duk nesan gidan su da kasuwar a Æ™asa take zuwa ta dawo a Æ™asa ,É—an kuÉ—in da aka bata na moto ta riÆ™e tace ” zata jah jarin wani abun ,haka take Zainabu yarinya ce mai zafin nema,tayi wannan sana’a tayi wancenn kuma duka du basu taru sun zama guda ba, yarinya ce fitinanniya ta gaske gata bata da tsoro a ko ina ta shiga ,indai kayi mata sai ta maka ,Æ™arya ne a wuni batayi faÉ—a har da su damme ba ,wanda ita har gadara take da cewa ” bata faÉ—a da yarinya É—aya sai su kai biyu zuwa uku,don idan É—aya ne to tabbas xata mata lahani ,gomma sukai biyu zuwa uku ,to sai ta casusu.
Gata da farin jinin Æ™awaye kowa Zainabu haka matar Aure da yara.amma fa Zainabu bata da mutunci sam….ita idan batayi faÉ—a ba har ciwo ma take cewa takeyi,faÉ—a ya zama mata jinin jiki, gata duk Æ™awayen ta tsoron ta sukeyi ,saboda tana da Æ™arfi kaman Shari’a ,bata taÉ“a dambe ba ita taci nasara akan wa incan ba. Haka xata kama Æ´aÆ´an mutane ta bigi na banxa ,idan iyayen su sun gidan Umma sun kawo Æ™ara. Umma Halima tayi ta basu haÆ™uri tayi faÉ—a ma Zainabu har ta gaji.
KARANTA:ÂLittattafan Hausa Novel Complete Guda 500
Hee heey Madam for ur babies”. Nan Zainabu taji Muryar wani inyamuri yana katseta da cewa ” For your babbie ,yana É—aaga mata gonjon bby suit na yara”. Wani irin fusata Zainabu tayi a zuciyar ta tana cewa ” Wa’annnan inyamuran kullum iskanci Æ™aruwa yake yi”. Bama baby ba a’a yanxu babbie take dasu. Kai kalle Ni da kyau Dan Uwar ka kaga nayi kama ma da wacce take da Aure har da yara??. Shegu Æ´an iskan mutane kawai ,wato sai na fitar da tsaraici ne sannan nake budurwa a wurin ku ko? Wanda sukayi sabo da ganin tsaraicin mata,shiyasa shekaru Æ™alilan ido ya makance”.
Inyamuri ne ya kalle yaya kallon ta kusa dashi haÉ—i da ware ware yana cewa ” what is she saying?. Eiyee kana nufin ma baka san me nake cewa ba?”. Kamin ya Æ™ara mawa Zainabu magana ne nan yaga ta É—aga hannu tassss tana wanke fuskar sa da mari”. What of now? Nace yanxu fa kaji me nake cewa ko sai na Æ™ara wanke fuskar ka da wani marin?. Cikin tsoro da rawar jiki inyamurin yace Sorry my friend sorry pls.
Yanxu kayi magana tayi maganan tana wuce shi da mutanen da suka fara taruwa tana tafe tana cigaba da zage zagen ta”. A wurin ba inyamurin kaÉ—ai ba ne ya tsorata da Zainabu kusan duka inyamuran sun kasa mata mgn ,basu taÉ“a ganin yarinya wacce ashekaru ba zata haura sha takwas 18 ba Æ´ar bala’i kaman Zainabu ba…wannan yasa su kasa yi mata haÉ—in kan da suka saba ,suci mawa bahaushe mutunci. Haka suna kallon ta ta É“ace ,sauran ko hausawa sai dariya sukeyi ,suna jin daÉ—in abun da Zainabu tayi…………
Ƙwarto Æ™warto manya naji wurin ya É—auka ,waigawa nayi don ganin waye ake kira da wannan suna haka?? Amma sai dai nakasa fahimta a cikin su huÉ—un waye ke da wannan suna,kasantuwar dukkanin su Kaki ne jikin su ta Sojoji. ÆŠayan su na gani wanda shi gaba É—aya su hankalin su ke akan shi….idon shi a lumshe suke bai buÉ—e su duka ba, hannun sa riÆ™e yake da Sigari yana busawa haÉ—i da fitar da hayaÆ™in ta baki da hanci irin na tatattun Æ´an duniya…a sojojin ma shi É—in Zakka ne cikin su a tachewa”.
Irin jijjiga jijjagan mazan nan ne ,don sun wuce akira da ingarma,ga tsawo ga Æ™iba…. Fari ne tass wanda yafi kama mun da ba cikakken bahaushe ba ruwa biyu. Wata Æ™il É—aya ciki daga iyayen sa ba É—an Africa bane ba duba da yanayin zubin sa..Æ™ara sa sigari yayi yana zuÆ™ar ta da Æ™arfi yana furxarwa cike da tacewa t Æ´an duniya,wanda anan ne na kuma Æ™are masa kallo ,hulan kansa na gani yasha ban ban dana Sojojin dana saba gani.
Domin kuwa tasa jah ne,wanda yasani jah baya ina naÉ—o maku rahoton baya baya kasantuwar fahimtar wani soja ne a gaba na… Soja ne militry Army wanda idan sojoji suka ga É—ayan su gudu sukeyi ,su ba’a yar je masu faÉ—a da soja É—aya ba ,sai idan sun kai goma zuwa sha biyar ,saboda idan suka ce zasu ba Soja horo ko duka zasu kashe shi zuwa É—aya”. Wannan yada su Bama ka ganin irin su masu jan hula , a ko’ina suna killace sai wani irin babban É“araka ko yaÆ™i ya tashi a Æ™asa ake fito da irin su kaman goma,to duk girman runduna sai sun gama da ita”. Habab naji an kira sunan shi”……………..
Wasu Na karatun:ÂSakon Barka da Juma’a and Barka da Juma’a Messages