Welcome to Zamgist where you will read hausa novels from different writers, Today we are also here with Auren yarinta page 14&15.
This book was written by the famous hausa novel writer known as Khadija s dogarai.
Auren yarinta page 14&15
Page 14&15
Gabanshi yana duka uku uku ya shiga motar shi ya nufi hanyar gidan su
Yana zuwa yayi horn mai gadi ya wangale mishi gateguri ya samu yayi parking ya fito a bude ya bar motar ya shiga cikin gidan a falo ya same su ganin Nafisa yayi mom din shi sai lallashin ta take yi
Guri ya samu ya zauna
Barka da wuni Dad
In ban wuni ba zaka ganni
Dagowa yayi ya kalli Dad din shi ko baayi masa bayani ba ya san ranshi a bace yake
Allah ya huci zuciyar ka
Aziz bana son iskanci yanzu fisibilillahi haka kawai zaka dauki hannu ka mare diyar mutane
Haba Alhj Meyasa bazaka tambaye shi ba sai ka hau shi da fada ehmm
Hajiya wannan wane irin magani har sai an tambaye shi Ai tunda ki ka ga ya mare ta to a cikin hankalin sa yayi amma tunda kince haka kayi mana bayani meyasa ka mare ta
Sunkuyar da kan shi yayi kasa yana sosa kan shi kamar wanda yayi karya
Uhmm Amm Dad Daman
Nuna shi yayi
kin gani daman nagaya maki ba abunda zai ji haka kawai don jin dadi ya mare ta
Aa Dad laifi tayi min
Don tayi maka laifi sai ka daga hannu ka mare ta Shekara na nawa da Mamar ka ka taba ganin ko a mafarki na daga hannu na da sunan in buge ta
Girgiza masa kai yayi
To meyasa baza kayi hakuri ba kasan da cewa dukan mace ba kyau ko
Ayi hakuri Dad ba za sake ba
Alhj Ni na so ka bariyayi bayani meyasa ya mare ta don da na san ba karamin abu bane
Bisimillah zaki iya tambayar shi
Son ka gaya min meya faru
Amm Mom ina bacci tayi min kwalliya yanda kin ka san aljani kuma ta san da cewa abokaina sun zo ta kyale ni suka tayi min dariya abun ya bata min rai shiyasa na mare ta
Ka gani ko wannan wane irin iskanci ne
Fadan Dad din shi
Shikenan don tayi maka kwalliya sai ka mare ta kuma a gaban abokan ka Wai meke damun ka ne baka san soyayya ba yarinya ce fa dole sai kayi hakuri da ita
Dagowa yayi ya kalle ta ya saka mata wata harara murguda masa baki tayi ta cigaba da wasa da hanunta
Amma dad
Yi min shiru bana son jin shirmen ka Maza ka dauki matar ka ku bani waje
Allah ya baka hakuri insha Allah zan kiyaye
Nafisa ki tashi ki bishi kinji kiyi hakuri
Mikewa tayi tsaye tayi masu sai anjima suka nufa gurin motar shi
Dad ya biyo bayan shi
Shiga yayi ya rufe mota ita kuwa tayi tsaye
Har zai tada mota yaga bata shiga ba
Horn yayi mata alaman ta shigo su wuce amma tayi kamar bata ji sa ba
Ganin Dad din shi yayi ya daure fuska ba don ranshi ya so ba ya fito daga motar bude mata kofa yayi
Ita kuwa ta shiga tana jin dadi Da karfi ya rufe mota sai da ta razana Zagayo wa yayi ya tada mota fuuuu
Muktar kuwa tunda ya shiga dakin sa babu abunda yake tunawa sai abunda Nafisa tayi ma Aziz shima haka zaaye mai
Kawar da zancen yayi ya san suhaila bazata yi yarinta irin ta Nafisa ba
Ko ya zaayi auren a ranshi ya nasa ba zai yi ma Suhaila yanda Aziz keyi ma Nafisa ba
Tunda suka fara hanya ba wanda yace ma wani kala sai wasa take yi da Hannunta
Shikuwa ranshi a bace don ta rame shi ta saka shi cikin kunya kuma tazo ta kawo karan shi.
Auren yarinta page 14&15 PDF Download
Novel Title | Auren yarinta page 14&15 |
Uploaded by | Zamgist.com.ng |
File Size | 490kb |
Hausa Novels WhatsApp Group | Click here |
Telegram Group | Click here |
Novel Price | Free |
Written by | Khadijah s dogarai |
Tags | auren yarinta page 14&15 |
Published date | 02– 09– 2023 |
Karanta:ÂMatar gwamna hausa novel complete pdf
DOWNLOAD NOVEL
Littafin:ÂKarshen Wahala Hausa Novel Complete