A Gidanmu Take Page 1 To 10

Hausa novel by zamgist.com.ng

Barka da zuwa wannan shafin namu inda muka kawo muku littafin a gidanmu take page 1 to 10 wanda Jidda s mapi ta rubuta takuma wallafah

A Gidanmu Take Page 1 To 10

623 1243 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_storywritten by_
_jiddah S mapi_

_Follow me on wattpad_ jiddahpretty

Hi guys this is my first story hope I will have your maximum coop ration

NOTE Banyi wannan littafin sabida wani ko wata ba labarin kirkirrarre ne sabida haka akula sosai

_dedicated to fateemahsardauna_

Page 12

Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba

Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi yana hawaye fuskarshi tayi ja bue baki yayi yanason yin magana amma ya kas sai kuka yake kamar wata mace hadda shesheka dakyar ya iya cewa Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba bacin kai kasan abinda yake damuna idan Banyi kukaba me zanyi Yaare maganar cikin sanyin murya

Gyara zama Habeeb yayi hae da cewa
Addua ya kamata kayi Ahmad domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci

Ya isa haka Habeeb ka yaleni naji da abinda yake damuna bawai ka cikani da surutunka ba sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata rashin daba zan taa mantawa ba tunda narasa FATEEMAH narasa komai
na wulaantata na untata mata nayi mata abinda bazata taa mantawa daniba Ina zanga Fateemah Ina zanji labarinta tana raye ko Tana mace an jinkirtawa da maganan yayi kana ya cigaba da cewa
Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta Ya arashe maganan yana wani irin gunjin kuka

Awannan lokacin har Habeeb baa barshi abaya ba duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye yana me tausayawa abokinnashi

Wai Ina kike ne BINTU kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota

Ina zuwa Sis HABEEBA gyalena nake dubawa ban gani ba Naji wata siririyar murya Tana fada

Kiauki nawa a wardrobe mana bintu Habeeba tafai haka cikin yanayi na osawa

Okay nama dauka ae ganinan Beentu tafai haka tana mai oarin yafa gyalen ajikinta

Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan Habeeba tafaa tana an kallon gefen da Beentun take

Nan naga Beentu na sauowa daga kan step cikin takunta mai auke da nutsuwa Farace sol doguwa siririya tana da manya manyan idanu bakinta dan karami oarin gyara gyallen take tayadda zai zauna akanta

Cewa tayi Haba My Hussaina Kinsan fa bama haka dake kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis

Da ma ay haka zakice kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya to yanzu de muje kinga Mom nata kirana kusan 6 missed calls tayi min Habeeba tafai haka tana mai duban wayarta dake rie a hanunta

Okay to muje Cewar Beentu

A tare suka fito daga falon suna sauri

_see me next page_

Jidderh S Mapi
623 1243 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_story written by_
Jiddah S mapi

_dedicated to fateemahsardauna_

_wattpad jiddahpretty_

Page 34

Suna fita daga falon habeeba ta kwalawa driver Kira yace gani hajiya

tace Ina mommy yace ay hajiya ta dade da tafiya tace bazata iya jiranku ba idan kun gama ku sameta agidan abinci
ok to kaimu driver yace to nan suka shiga motar suka tafi
bayan driver yayi parking naga sun shiga wani waje me kyau Wanda naga maaikata da uniform suna rabawa mutane abinci wasu kuma suna dafawa

Wasu na wanke plates daga gani de wannan gidan abinci ne Wanda yayi suna agarin

ADAMAWA Ina daga kaina naga an rubuta HASSY and HUSSYS KITCHEN

suna fita a motar idanun mutane suka dawo kansu Ana tacewa kaga yan biyun hajiya bada kunku asare

Kuje gida kuce yafadi habeeba ce kadai me cewa sannunku

Samarai barka da war haka ita kuma bintu sai murmushi take nan naga sun nufo wata kykkyawar mata wacce zatakai shekara 40 habeeba tafada kan cinyar matar

Tace mommy shine kikayi tafiyarki kika barmu

matar da aka Kira da mommy naga tayi murmushi nan naga tsananin kamanta da habeeba tace ba dole natafi ba

Kun tsaya kunata shirme kuma kunsan yau ranar biyan maaikata ne

Mommy ai bintu ce ta tsayar damu kinsan yanayinta dayin Abu kamar karkashi

Aa karki sake kizagammin ya zo maya my bintu kizauna anan

Bintu tayi murmushi tace mom inason yau zanyi stew da kaima
Mom tace Haba bintu yazaki gajiyar da kanki kizauna kihuta kinji my bintu

Aa mom kibari zanyi
Toshikenan bazan hanakiba jekiyi

Ahmad dama nayi niyan tafiya yau amma bazan iya tafiya nabarka awannan yanayin ba

Nagode habeeb Allah yabarmin kai dan Allah habeeb ko bayan na mutu idan kasamu my teemah dan Allah ka aureta sabida kai Kadai nayadda dakai Kai Kadai nasan zaka riketa da amana tinda kasan bakar wuyar datasha kasan na zalinceta naci amana dan Allah kayimin wannan alkawarin

_see me next page_
623 1244 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_storywritten by

Jiddah s mapi

_dedicated To fateemahsardauna_

_wattpad_
Jiddahpretty

Page 56

Ahmad kadaina irin wadannan maganganun

Banajin dadinsu Sam meyasa kake maganar mutuwa bayan bakaga fateemahn kaba

Ahmad insha Allah Bazaka mutu ba seka ga fateema

Ka nemi yafiyanta Sannan ku Gina rayuwa me kyau

Kuma inada tabbacin fateemah zata yafe maka

Habeeb bana tinanin my teemah Zata yafemin koda bayan raina ne

Habeeb babu abinda yake damina kamar yanda mommy tadau

Zancennan da zafi ka duba kagani

Yau kusan shekara daya ban sa mommy a idona ba

Yazanyi da rayuwa ta ya karashe maganan yana me hawaye

Abin tausayi

Habeeb kam ba bakin magana

Shi mamaki ma abun yake bashi wai ace yau

Ahmad ne yake kuka yana fada mishi damuwanshi

Shida magana ma be dameshi ba

Gsky dayana da yanda ze taimaka mishi daya yayi

Amma shi besan ma ta ina ze fara ba

Allah ka gaggauta kawo mana karshen

Matsalarnan Ameen

BINTU

Mommy wai meyasa bintu take zubar mana da class ne

Kiduba fa yanzu wajen masu aiki zataje suyi tare

Gsky mom abinda takeyi bata kyautawa wannan aji down ne

Habeeba kibi rayuwa a hankali

Ita duniya a hankali ake binta

Wanda batazo bama Tana jiranshi bale muda muke cikinta

Ni gsky mom kina daurewa bintu gindi dama nasan

Niba sona kike ba

Bawai bana sonki bane beebah babu Wanda ze haifi da

Yakishi sede idan kaddara ne

mom tafada idonta yana cika da hawaye

A hankali tajuya kanta yanda bintu bazata ganta ba ta goge idonta

Bintu kuwa iyayen son aiki tanata girki suna dan hira da ma aikatan

Dan ita ba maabociyar son magana bace

Cikin hiranne wata Wanda suka dan saba da bintu

Take tambayan bintu

Friend dama inason inyi miki wata tambaya

Ok nabeela inajinki

Amma Allah yasa ranki baze baci ba

Aa ba komai yi maganarki ok

Dama inason tambayanki tum bayau ba

Hajiyace ta haifeki

Haba nabeela wannan wace irin magana ce yazakimin wannan tambayar

Bacin kinsan mu yan biyune nice babba

Gsky bintu ba kowane ze yadda ba

Duba da irin yanayinki Kiga beebah mana

Tana Kama da hajiya

Amma ke Sam babu abinda yahadaki da hajiya ta kamanni ko hali gsky akwai abun dubawa anan

What are you saying nabeela

Cewar mom Wanda tin farkon maganarsu takejinsu

Ta taso tambayar bintu kota gama hadin

See me next page

_Wattpad_
Jiddahpretty
623 1244 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_storywritten_by
Jiddah S mapi

_dedicated to fateemahsardauna_

Page 78

A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi

Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani

Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar

Yar da Nina haifeta a cikina shin bakida labarin Akwai yan biyun da Sam basa Kama da juna

meyasa ku mutane
Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Bazaa taba cewa ke kika hada ba saikuma tsaya

Gsky bana son irin wannan tambayar

Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba

Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba inji Nabeela

Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana hajiya ta mayar mata

Bintu wuce mutafi
Tafada cikin bacin rai

To mommy cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma aga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta

AHMAD

Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru

Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame inji Habeeb

Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah inji Ahmad

Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta inji Habeeb

Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe

Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ace

Beebah bataga fuskar tambaya ba

Sai takarasa wajen Bintu tace Bintu yanaga ran mommy a bace

babu komai sis inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata auka da sauki

Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ace

 

Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne Inji Bintu

Ko zaki dake nine to cewar Beebah

Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan Bintu ta mayar mata

Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa inji mommy

Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi an mintuna ba

Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo cewar mommy

Yee mommy dagaske kikcewar beebah

Dama nataba miki karyane

Nan wayan mommy yafara ringing

Yawwa ga shima yana Kira

amsawa tayi takara a kunnenta

Hello my son yakake ok se gobe Amma meyasa yau bazaka dawo ba Ok to Allah yakaimu goben saikuma ta kashe wayar

Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo mommy tafaa musu

Kai amma naji haushi mommy cewar beebah

Mommy tace Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addua Allah yakawo shi lafiya

Ameen cewar bintu

_See me next page_

_wattpad_
Jiddahpretty
623 1244 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_story by_
jiddah S mapi

_dedicated to fateemah sardauna_

Page 910

Washe gari bayan sun gama breakfast ne

Habeeb yake cewa Ahmad

To kaga ni yau zan tafi kuma bazan dawo nan dawuri ba

Saboda wannan zuwanma dakyar mommy tabarni

Acewarta bataso nayi nesa da ita

Dan Allah Ahmad kada kasa tinani a ranka

Sannan kuma karka gaji da Zuwa gidanku neman tuba a wajen

Mommynka

Aa Habeeb bazan iya zuwa inda mom take ba gsky

Sabida mom idan taganni bacin ranta karuwa yake

Har Tana barazanar Zata tsinemin idan harna sake zuwa inda take

Ba tareda Fateemah ba

Kai innalillahi wainna ilaihirajiun abun haryana kai da hakane Ahmad

Wlh Habeeb shiyasa kaga damuwan sunyi min yawa narasa yanda zanyi

Yanzu ma tafiyar da zakayi banso ba

Koba komai kana debemin kewa

Amma yana iya idan kaje ka gaida mommy

Da kannan ka duka
Nagode Allah yabar zumunci

Habeeb yace Ameen

Ahmad yace Kashirya nakaika airport karkayi missing flight

Ok

 

Bintu kinga yau broh ze dawo

Kizo mushiga kitchen dakanmu muhada mishi delicious

Bintu tace Ok sis karki sami damuwa muje

Suka tashi suka shiga kitchen suna ta hira

Mommy Tana kallonsu Tana Mejin farin ciki a zuciyarta

tace Allah yasake hada kanku my twins

AHMAD

Tafiya suke a mota suna hira shida Habeeb

Nan Habeeb yake kara jaddada masa akan yakula da kanshi yadaina yawan tinani

Ahmad yace kaga karka dameni tin jiya kana ta maimaitamin kalma daya kamar karatu

Ohh dama nasan bazaka taba canza haliba Ahmad

Eh naji bazan canza ba

Dahaka har suka isa airport

BINTU

Bintu kuwa anata aiki a kitchen bebba se surutu take zubawa

Banda eh aa to
Ba abinda Bintu take cewa har suka gama hada frid rice da kaji

Bintu tahada sobo me cucumber

Mommy tace yanzu natura driver yaje dauko shi a airport
Wai ya karaso

Yeeeee mommy Aida kin fadamin da tare zamu tafi dashi

Kai Beebah kin fiye gaggawa

Haba mommy yabazanyi gaggawa ba yaufa kusan 2weeks ban ganshi ba sede waya

Bintu kuma murmushi kawai tayi

Horn sukaji abakin gate

Nan Beebah tafita da gudu Tana oyoyo yaya oyoyo

Kafin driver yagama parking harta fara

Bubbuga motan

Seda yafito da sauri yana oyoyo my sis

Nan ta rungumeshi kamkam Tana murna

Yace ina dayarki Tana falo itada mommy

Ok mushiga daga ciki

Suna tafiya Tana rike da waist nashi har suka shiga falon

Tana cewa yaya kadauko tsaraban toh

Mushiga de tukun kinsan tsarabarki ta daban ce

Mommy tace oyoyo my son sannu da zuwa nan itama ta rungumeshi tana murna

Bintu ta tsaya Tana tayi mishi murmushi

Yace kekam meyasa bazaki Waye ba Bintu

kullum kina cikin rashin sabo da mutum

Cheww Allah yakyauta halinnan naki

Kina gani fa yar uwarki tazo tayi min oyoyo

Amma ke kina tsaye

Daga nanne Bintu taje ta rungumeshi

Yahada su duka uku ya rungume sunata murna

 

Ahmad yana komawa gida ya kwanta agado yana tinanin mommynshi
da kanwarshi

Wai yau shine Kanwarshi wanda yafi so aduniya take gudunshi

Yau shine mommynshi take ikirarin tsine mishi

Idan yatuna rayuwarshi na da se yayi kuka

WANENE AHMAD

AHMAD KABEER yarone awajen alhaji kabeer

Alh kabeer shahararren dan kasuwane

Wanda yayi suna a duniya

Alhaji kabeer de dan asalin garin adamawa ne

Shi asalin fulani ne

Wanda yafara harkar kasuwanci tin yana saurayi

Allah kuma ya buda mishi sabida yanda yake da kyauta da taimakon talakawa

Alh kabeer yabude gidan marayu tin yana saurayi

sabida yadda Allah yasa mishi tausayin marayu a zuciyarshi

Dan hakane har yaki yin aure

dan yana gudun kar ya auri matar dazata hanashi taimakon marayu

Iyayenshi ne suka nema mishi aure Agidan marayu Wanda shiya bude da kanshi

Acewarsu zatafi jin tausayin marayu yan uwanta

Inda suka nema mishi wata kyakkyawar yarinya me Suna mariya

Ba matsala a auren mariya da alhaji kabeer sabida mariya Yarinyar kirkice

Bayan shekara hudu Allah be kawo musu haihuwa ba

Har abun yafara damin mariya

Inda alhaji kabeer yake cemata

karki damu mariya haihuwa na Allah ne

Idan ma Allah be bamu b Baga gidan marayu ba semu dau daya murike kaman mu muka haifa

Mariya tace haba Alhaji kasan fa akwai banbanci tsakanin a da kuma an riko

Aa mariya a na kowa Ne

Ganin yahau matsifane mariya tayi shiru

To dahakane har Allah yakawo ranar haihuwanta inda aka sha shagali akayi murna

Akasawa yaro sunan baban alhaji kabeer wato AHMAD

Ahmad de yasamu gata dan kota ina anaji dashi

Ahmad kyakkyawa ne

Fari Ne shi dogo da dogon hanci ga karamin baki Atakaicede shi yayi kama da larabawa

Sede kuma matsalar shi nada yawa

Yanada girman kai sosai

Ga kallon banza

Ga zama da abokan banza

Wasu abubuwan dayake yi abokai ne suke zigashi

Sai yayi ta tsula rashin kunya son ranshi

Dafarko yasamu daurin gindi awajen iyayenshi

Se daga baya abun yafara damunsu

bayan wasu shekaru

Dahakane har allah yasake basu haihuwa

Yarinya taci sunan wacce take kula da gidan marayu na mahaifinsu wato FAREEDAH

Fareeda de kykkyawa ce tana Kama da Ahmad sosai

Sannan kuma tinda aka haifi fareeda Ahmad yakara bude sabon rashin kunya

Shi adole yana da kanwa

Bayan haihuwar fareeda fareeda ne Alhaji kabeer yafara diban yaranshi suna zuwa gidan marayu kai tallafi

Acewarshi idan sun girma suma zasu taimaki marayu

Ranar farko dasukaje gidan marayun

Ahmad yasa fararen kaya masu kyau yanata Hada rai danshi beso zuwa ba

Bayan an tara yara ana raba musu kudi ne

Alhaji kabeer yahango wata kyakkyawar yarinya

Tana zaune a gefe tana kallonsu tana murmushi

Alhaji Kabeer yaan tsaya da rabiyar yana kallonta

Se ya yafito ta da hannu yace zo

Yarinyan ta tashi a hankali tana tafiya

Harta iso su seta durkusa tace gani

Alhaji Kabeer yayi mamakin wannan yarinya batafi shekara goma ba

Amma take da natsuwa haka gata dakyau

Shi kuma Ahmad se harara yake tayi wai ana bata mishi lokaci

Alhaji yace ya sunanki

Ahankali tace sunana Fateemah

JIDDAH S MAPI
623 1245 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

Storywritten by
Jiddah S mapi

_dedicated to walidation S mapi_

Wattpad
Jiddahpretty

Page 1112

Wow nice name inji Fareedah

Gsky Daddy yarinyannan kyakkyawa ce gata fara ga ido wow

Daddy yace meyasa ana raba kudi amma baki zo kin kara ba

Tace banada bukatar kudinne shiyasa duk abunda nake so mama tana bani

To ay zaki iya ajiye kudin sabida watarana cewar Fareedah

Shi kuma Ahmad se duba agogo yake yanata tsaki ba abun yacewa Daddy ze tafi ba se harara yake ta bankawa yarinyan Gani yake kamar ita take kara delaying nasu

Daddy ya ciro kudi masu yawa ya bawa yarinyan ta girgiza kai tace aa nagode abawa sauran

Kikara ni na baki ay a hankali tasa hanu ta karba tacenagode Allah yasaka da alheri Ameen

Tin daga wannan rana idan daddy yaje gidan marayu sai yace a kira mishi Fateemah yadau kudi yabata

To fa dahaka suka saba da Fareedah sosai watarana ma Fareedah takan zuwa gidab Marayun suyi ta hira da Fateemah har yazama idan Fareedah bataje taga Fateemah ba batajin dadi a ranta sunyi muguwar shakuwa da Fateemah

Ta angaren Ahmad kuma yana dada lalacewa sabida abokai dayake tare dasu mutane suna yawan kawowa Alh Kabeer karan Ahmad amma baya taa yadda se yace suyi hakuri yaranta ne daya girma ze daina

Abun yana taa zuciyar Mariya taya zaace yarinta bacin yaro yakai shekara 29 ina maganan yarinta anan

yauma kamar kullum Alh Kabeer ne da yaranshi zasuje gidan marayu yayinda Fareedah take ta rokon mom tashirya suje taga kawarta kuma Bestyn ta

To Fareedah naji tashi muje yawwa Mom ko kefah

A hanyarsu tazuwa gidan marayu ne Alh kabeer yake tambayan Ahmad

Wai kai son yaushe ne zakayi Aure Ahmad yahada fuska yana hararan Fareedah wai ana tambayanshi Aure a idon yarinya karama

Ba tambayanka nake ba Am daddy insha Allah very soon zan kawo muku matar dazan Aura

Mommy tace udan ma be kawo ba mu sai mu nema mishiFareedah tace yess mommy nizan nema mishi ma dakaina

Daya juya ya banka mata harara tayi tsitt

Bayan sun shiga gidan marayu ne Fareedah tafara neman Fateemah a inda tasaba ganinta amma bata ganta ba

Ta tambayi wasu yara su biyu suna wasa taceina Fateema

Sukace Fateemah batada lafiya tanata kuka tin azu taki amata allura

A wana aki take cewar Fareedah cikin tashin hankali tayi tambayar muje nakaiki cewar wata yarinya

Suna shiga dakin taga Fateemah tana ta kuka tana rawan sanyi

Da gudu tafita tana kiran mommy

Mommy naganin Fareedah ta fito da gudu tafara tambaya lafiya

Fareedah batayi magana ba se nuna daki take

Mommy tace kiyi magana dakyar tace Fateemah wace Fateeman Cewar Daddy

Nan suka shiga dakin da gudu Suna zuwa sukaga Fateemah bata motsi nan Fareedah ta tsala ihu

Mommy tace kira yayanki awaje Fareedah ta taso da gudu tana kiran yaya yaya

Ya dago kanshi yace ke me haka Kinata kiran sunana kamar wani saanki

Yaya wai kaje inji mommy
Yaja wata doguwar tsaki yace muje

Suna zuwa Daddy yace oya Ahmad dauke ta dawuri mutafi asibiti

Haba Daddy kaduba fa farin kayane ajikina ta yaya zan fara daukanta Dubi jikinta fa duk datti Zaka dauketa ne ko sai ranka ya aci cewar daddy

A hankali yaauketa yana yatsina fuska

Yariketa kamar kashi ya auka sai yayi sauri sauri ya wurgata a motar da iya karfinshi

Har saida kanta ya bugu

Daddy yace shiga mutafi dakyar yadaure yashiga yanata kunkuni

Ita kuma Fareedah sai kuka take tana kiran sunan Fateema tana cewa ta tashi karta mutu

A haka har suka iso specialist hospital Suna zuwa ba ata lokaci aka karbesu

Likitoci suka shiga ciki da ita Ahmad yace dama daddy inason naje wani waje na kari sako babu inda zaka kana gani mun kawo yarinya ba lafiya rai a hanun Allah kace zaka tafi baka da imani ne

Ahmad ya haa rai yasamu waje ya zauna yanata kunkuni me hai na da ita da zaa hanani yin uzirina akanta Yarinya kucaka ma da ita

Suna cikin zama wata nurse ta fito tace doctor yana magana dakai

Alh kabeer yace to nan yashiga ciki doctor yace kaine baban yarinyan daka kawo Alhkabeer yace eh nine

Ok amma kasan da ciwon dayake daminta Yace Aa

Doctor yagyara zama yace Alh rayuwar yarka tana cikin matsala

Ka taa zama da ita ka tambayi matsalarta Daddy yace Aa

Tofa akwai babbar matsala Am sorry to say yarka tana dauke da ciwon zuciya wanda idan har aka barta cikin tunani tayi nisa zata iya rasa ranta a ko wani lokaci

JIDDAH S MAPI
623 1245 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_story written by_
Jiddah S mapi

_dedicated to my lovly sister walidation_

_ote me on_ _wattpad Jiddahpretty_

Page 1516

Da kyar Fareedah ta janye Fateemah zuwa gefen hanya ta kwantar da ita tace ki zauna anan bara naje na kama mana Napep

A haka ta kama musu Napep ta rike Fateemah suka shiga se gida

Shi kuma Ahmad yana jan motarsa ya wuce carwash yace a wanke mishi ita

Alh Kabeer kuwa da mariya suna zuwa gidan marayu yacewa mama yanason magana da ita
Tace ok ba komai ina jinka Alh

Yace dama so nake na auke Fateemah na an wani lokaci idan ba matsala
Mama tace ba komai Alh Ay duk an zama aya
Da haka suka tafi gida

Shakuwa me tsanani ta shiga tsakanin Fareedah da Fateemah
Dan Fareedah sosai takeson Fateemah har cikin Ranta komai zaa siya mata zatace sai an siyawa Fateemah

Shi kuma Ahmad a duniya babu abinda yatsani gani kamar Fateemah kwata kwata Allah be haa jininsu da ita ba
Ko abinci Fateemah ta dafa baya ci idan har ya san ita tadafa

Yauma kamar kullum Fateemah ce take goge goge a falo
tana kan goge TV ne taji ance mata ke baki da hankali ne ko kin taa ganin inda ake goge TV da tsumma Koda shike ba laifinki bane laifin iyayenki ne dasuka haifeki a titi daga baya suka yadda ki
Nasan da agaban iyayen ki kike dakin iya goge TV Wawiyar banza

Tunda Fateemah take a rayuwarta baa taa faa mata maganan daya ata mata rai irin ta yau ba
Ahmad ne farko yafara kiranta da shegiya

A hankali ta ago kanta tace kayi hakuri zan gyara insha Allah
Ai kuwa yaja tsaki ya fita a akin yanaji kamar ya shaketa ta mutu kawai

Wato yarinyannan duk abunda zaayi mata bazatayi kuka ba saide tayi tabada hakuri kamar marokiya sai nayi maganinta ay

Ita kuma Fateemah yana fita tasa kuka me cin rai
Tana cikin kuka ne taji muryan Fareedah tana Besty ina kike

Ta share hawayenta tace gani nan

Fareedah ta rungumeta tace meya sameki naga kamar kinyi kuka tace Aa babu komai kaina ke ciwo
Ayya sorry kinsha magani
Eh nasha
Ok muje aki to ki kwanta

Da daren ranan Fateemah takasa bacci data rufe ido sai tana tuna maganganun Ahmad na azu
_ba laifinki bane_
_Laifin iyayenki ne_
_Dasuka haifeki a titi_

Wato ni shegiyace A titi aka haifeni To ina iyayena suke Meyasa suka yadda ni
Shine tambayoyin data kasa amsawa kanta
Data kara tunawa seta fashe da kuka
Jikinta yafara zafi tana kokarin ta tsaida kukan amma ta kasa Da haka har tafara tari jikinta yafara rawa taja bargo ta lullua jikinta amma har yanzu tana jin sanyi Tana cikin wannan halinne Fareedah ta tashi zatayi fitsari

Taga Fateemah acikin bargo jikinta yana rawa gashi fuskanta yayi ja
A razane ta iso wajenta tana tambayanta meya faru

Fateemah ba bakin magana se ido kawai
Ta fita da gudu taje akin mommy ta kirata
A tare sukazo da mommy
Mommy tana ganin halin da Fateemah take ciki tace akira mata Alhaji
Ai kuwa Alh Kabeer yana zuwa yace aje akira Ahmad yazo su tafi Asibiti

Fareedah ce taje kiranshi tana zuwa tayi knocking yace yes waye
Tace Yaya Fareedah ce
Yace me kikeso
Tace Daddy ne yace nakiraka
Daddy kuma Meya faru
Nima ban sani ba

Ok ina zuwa
Ahmad yana zuwa Daddy yace oya auke ta da wuri mu tafi Asibiti kar dare yayi sosai

Daddy wani Asibiti
Dama wani Asibiti muke zuwa Inji Daddy

Daddy Ai yanzu dare yayi abari sai gobe mana da safe
Kai Ahmad baka da hankali ne Ko baka ganin halin da take ciki Ko da Fareedah ce zakace abari sai gobe

Yayi shiru dan besan me zecewa Daddy ba ganin yahau 90

A haka badan yaso ba ya auketa yakaita mota
Ji yake kamar ya shaketa tamutu ko ze huta

jiddah S mapi
623 1245 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_storywritten by_
Jiddah S mapi

_dedicated to my lovly sister_
walidation

Page 1314

Alh yarka tana cikin matsala zai fi maka sauki ka kirata ka lallaata ta faa maka meke damunta sabida hakki ne a kanka

To fa nan Daddy yafara share zufa yanason yace ba yarshi bace amma yana tsoron kar likitan yace mishi makaryaci

Yace toh doctor nagode yanzu ya ake ciki Doctor yace a halin yanzu de an aura mata ruwa saura na rubuta muku magungunan da zaku saya

Ahmad kuwa abokanshi sunata kiranshi awaya yana ta tsaki wannan wani irin abune Bamu santa ba Ba dangi ba Ba yan uwa ba Amma ahanani yin komai chewww

Yasake jan wani dogon tsaki ganin ana sake kiranshi

Dan Allah karka dame ni Bash ka kyaleni na huta wannan wana irin Balai ne naji da matsalar Da Daddy yasani yau ne ko da naka ittt ya kashe wayar

Zo nan my son To
Yawwa dama zuwa zakayi ka siyo magunguna acikin asibitin to Daddy ya kari papern yana tafiya yana tsaki

Fareedah kuwa takasa zama da zarar taga likita yana wucewa sai tace doctor ya jikinnata tin suna amsawa har sukayi shiru

Da ahmad yakawo maganin suka unguma gaba aya suka shiga akin suna shiga suka tarar da Fateemah ta farfao Fareedah tayi gudu ta rungumeta

Ita kuma Fateemah ta lumshe ido

Ahmad kuwa yau kamar ido ya fao tsabar harara nace oho de

Ya jikin naki inji Daddy a hankali tace da sauki tom Allah yakara sauki tace Ameen

Daddy Yace idan kika an samu sauki bazaki je gidan marayu ba gida zamu wuce tnx Daddy gaskiya nima nafison taje gidanmu zamufi kula da ita

A take Ahmad ya ago kanshi yana kallon Daddy yace Daddy wani gida zata wuce

Wani gida kake ciki Cewar Daddy nan yai shiru yana kallonsu

Washe gari bayan an sallamesu ne daddy yace Ahmad ka kaisu gida ni zan wuce gidan marayu nafaawa mamansu nacan bazata koma ba sai ta samu sauki to Daddy

Mommy tace Alhj tunda ga Fareedah me ze hana su tafi tare mu kuma muje gidan marayun tare ok ba matsala ay Ahmad kaisu gida to Daddy

Da kyar Fateemah take tafiya sabida tanajin jiki Fareedah ce ta riketa har suka shiga motan a hankali

Bayan sun au hanya suna tafiya ne Fateemah tafarajin Amai
A hankali tace inajin Amai

Fareedah tace yaya kayi hakuri ka tsaya tanajin Amai yai shiru kamar bai jita ba ta sake cewa yaya Amai takeji nanma shiru ba amsa sema kara gudu dayake

Nan Fateemah tafara sheka Amai kamar ba gobe tofah nan yaja birki ya tsaya

Yace fitah sukayi shiru dan Fateemah ta galabaita ya sake cewa nace kufita

Fareedah tace haba yaya baka ganin Amai take ne kabari mana tagama

Zaku fitane ko sai na ata muku rai ya daka musu tsawa

Fateemah tafara yunkurin tashi Amma ina ba dama da kyar Fareedah ta riketa suka fita suna fita a motar Fateemah ta fai dan bata da karfi ko kaan

Haka yana gani yaja motarsa yabar wajen

_wattpad_
Jiddahpretty

jiddah S mapi
623 1246 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

Storywritten by
jiddah S mapi

_Dedicated to my lovely sister walidation_

ote me on wattpad
Jiddahpretty

Page 1718

Suna shiga cikin Asibiti Likitocin sukayi kansu da gudu suka kare ta sai Emergency Room
Daddy kuwa hankalinshi duk a tashe yanata zagaye Asibitin

Azuciyarshi yana tunanin to me ya tadawa Fateemah ciwon tane haka
Dahaka har likita yafito daga akin yacewa Daddy yana buatar magana dashi
Daddy yace to
Bayan yashiga akinne likita yace mishi Alh idan har kanada daman dazaka Aurar da yarka to kayi mata Aure kaga idan har agidan miji take bazata rina yin wasu tinani barkatai dahar ciwonta zai tashi ba

Daddy yayi shiru yana tinani se daga baya yace to nagode Doctor
Doctor yace yau zamu sallameku sabida anyi mata Allura ansa mata drip idan ya kare zaku iya tafiya

Bayan an sallamesu ne suka koma gida
Daddy ya kira Hajiya Mariya yayi mata bayanin abinda Doctor yace
Yace Mariya bakya ganin kawai mu haa Auren Fateemah da Ahmad
Tunda mun yadda da tarbiyanta
To Alhaji ne dai bani ta taka ba Amma baka tinanin karmu shiga hain yarinya marainiya
Kaga Ahmad shi bawani isashen hankali ne dashi ba kar muzo muyi abinda zai damemu
Haba Mariya shi Ahmad in ba haifanshi akayi ba
Tunda haifanshi akayi ai munada iko dashi
To Alh Allah yasanya Alkhairi cewar Hajiya Mariya

Dahaka Daddy yasanya ranan Auren Fateemah da Ahmad suma kansu basu sani ba

Akwana atashi ba wuya a wajen Allah yau ne Ranan jumaa wanda yayi daidai da yanda Alhaji Kabeer yasa ranan Auren Fateemah da Ahmad
Fareedah da Fateemah sai ganin mutane suke suna shiga gidan suna ta gua Fareedah ta tambayi Mommy meyake faruwa mommy tace ba komai
Shi kuma Ahmad yana wajen Abokansa sunata shashancinsu inda suketa shaye shayensu
Bayan jumaa aka aura Auren Fateemah da Ahmad akan sadaki dubu Hamsin wanda Alh Kabeer ne yabiya
Se dare Ahmad yadawo gida
Daddy ya kira wayanshi yace kasameni a falo

Daddy yacewa Hajiya mariya takira mishi Fateemah da Fareedah
Bayan sun hallara a falonne
Alh Kabeer yayi gyaran murya yace
Da farko dai nasan yau zakuyi mamakin yanda mutane suketa zirga zirga agidannan to yau Aure aka aura
Auren Fateemah da Ahmad

A razane Ahmad yaago kanshi yana kallon Daddy
Ya bua baki zaiyi magana Daddy ya aga hannu yace Banason jin komai daga bakinka kuma babbar kuskuren da zaka aikatamin shine sakin Fateemah ko wulaanta ta
Sannan kuma daga gobe zata tare zuwa side naka
Idan naga yanayin zamanku ba matsala kuma idan kun fahimci junanku saiku koma gidanka na jambutu
Yace zaku iya tafiya

Tofah dahaka suka wuce aki kowa jikinshi a mace
Ita kuma Fareedah murna take kamar me suna shiga akin ta rungume Fateemah tana ta tsalle ita kuma Fateemah shiru kawai tayi ta rasa me zatayi
Dahaka Fareedah tafara haa mata kayanta tana cewa gobe a akin yaya zaki kwana kai ammafa i will miss you
Fateemah shiru tayi batayi magana ba tana ganin anya bazataje wajen Daddy tace a raba Aurennan ba
Kai idan tayi haka kuma batayi daidai ba domin sunyi mata halacci

Azuciyar Ahmad kuwa yanata kulla salon muguntar daze yiwa yarinyan
Lalle zakici ubanki Ai nagodewa Allah ma dayasa babu Wanda yasani acikin abokai na dako nasha kunya
Ina yaro dani ace nayi Aure ay Akwai raini

Haka Fateemah da Ahmad suka fara rayuwa
Inda Ahmad yake mugun takura Fateemah
idan dare yayi sai yayi ta sata tsallen kwao kuma yace idan ta faa saiya kasheta
Haka Fateemah tayi ta hakuri dashi idan Fareedah tashigo saita saki fuska tayi ta dariya idan suna hira
Amma da zarar taji muryar Ahmad tofa zuciyarta tafara tsinkewa kenan

Dahaka Fateemah tayi ta hakuri da Ahmad wulakancin yau daban na gobe daban haka zatayi ta hakuri dashi babban abinda yafi daminta dashi shine shaye shaye dayakeyi tanason tafaa ma Fareedah amma tana mugun tsoronshi dan yace mata idan ta kuskura tafaa wa iyayenshi yana shan abu saiya kasheta

Me karatu Fateemah tasha wahala a wajen Ahmad fiye da misali

Yauma kamar kullum Ahmad ne yashigo gidan A buge yana tafiya yana tangai
Fateemah kuwa tana kitchen tana itada Fareedah suna girki

Kawai se sukaji karan buga kofa Fareedah tayi sauri zata je taduba ko menene Fateemah tayi saurin katseta
Tace ki bari zanje naduba dan ita tasan halin Ahmad may be yaje yasha abune yadawo
Tana lea akinshi taga ya kwanta rub da ciki

Ai kuwa tarufeshi a
Dataje kitche tacewa Fareedah ay ba kowa

Tofah har dare Fateemah kwata kwata ta manta da ta rufe Ahmad a aki haka Har tayi abincin dare ta ci tayi wanka ta kwanta har bacci yafara aukanta amma taji zuciyanta yanata tsinkewa tarinka cewa astaghfurullah

Shi kuma Ahmad lokacin da ya dawo hankalinshi yayi wanka yanason yaje club amma me yana bue kofan yaji gumm

Ya rasa yanda zeyi gashi yanajin yunwa kuma ana ta kiranshi awaya club yacika saura shi kawai ake jira
Yadinga buga kofan yana kiran sunanta amma shiru

Haka ya zauna yana tuna abinda zeyi mata yau idan ta bue kofan
Wato raini yafara shiga takaninsu kenan

tana zaune kawai ta tuna yau Ahmad be zageta ba anya lafiya kawai seta tashi tafita tace bara na lekashi nagani
Tana zuwa taga kofanshi a rufe taan buga ofan kaan

Kamar jira yake yace waye tayi shiru yace oya open the door

Sai alokacin ta tuna abundance yafaru da ranata zaro manya manyan idanunta tace kayi hakuri zan bue na mantaka ne wallahi
Cabi ni ta manta

jiddah S mapi
623 1247 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

Storywritten by
jiddah S mapi

_Dedicated to my lovely daughter AFRAH_

_ote me on wattpad Jiddahpretty_

Page 1920

Yace tai ni ta manta lalle zataci ubanta ai kuwa da gudu Fateemah taje taau malullin akin tazo ta baeshi
Tana buewa taji mari tass dan ubanki ni kika manta Gidan ubanki ne Dazaki rufeni kice kin manta yau sena nuna miki kuskurenki

Ya rike hanunta da karfi yana janta Yabi ta kofan baya da ita ya bue motarshi yasata aciki yafita da gudu acikin gidan

Yana gudu tanata bashi hakuri shi kuma hakurin datake bashi yana kara bashi haushi

Dahaka har ya iso wani gida
Tangameme me aton get yayi parking
Yafita agidan da kanshi ya bue get in yashiga cikin gidan yace mata fita
Tafara cewa dan Allah kayi hakuri wallahi mantawa nayi

Yau zakisan kin manta ni
Haka ya auke ta a motan Ya fita da ita

Yana aukan ta be ajeta ako ina ba se a wani bedroom wanda ya kayatu da abubuwan kyale kyale
Haka tana gani yafara yayyaga kayan jikinta tana bashi hakuri amma ina

Haka Ahmad yayiwa Fateemah fyae eh mana ai wannan fyae ne
Haka Ahmad ya auki Fateemah A sume yasata a mota ya kama hanya
Saida yayi tafiya me nisa kadin ya tsaya ya bue motar yana daga ciki ya cillar da ita waje yaja motarsa ya tafi

Bayan Ahmad yakoma gidane ya fara wani tinani me ze faawa Daddy idan ya tambiyeshi ina Fateemah kai anya bazan koma in aukota ba Kodai nabarta ne Nace duk kai kaai

Haka yayi wanka ya kwanta yayi baccinshi
Washe gari da safe Fareedah tazo akin dan takirawa Mommy Fateemah
Tana zuwa tayi knocking
yace waye tace Fareedah ce yace mene ne Tace mommy ce take kiran Fateemah

Dumm yaji zuciyarshi ta buga
Kije ina zuwa tace toh

Yana zuwa akin mommy yace inakwana mommy
Tace lafiya ina Fateemahn
Yace Fareedah fita ki bamu waje
Fareedah tafita yasamu bakin gado ya zauna
Yace Mommy wato yarinyannan ta rainani ne jiy ta kulleni a aki har dare wai ta manta ni
Shine me Inji mommy
Yace shine itama nakaita inda zaa manta da ita
kana hauka ne ko ka fara shaye shaye ne
Yayi shiru
Ina ka kaita
Yace bayan gari
Ji kake tass tass tass Mommy ta wanke shi da mari har sau uku
kayi hauka ko
Yayi shiru ba magana nake maka ba
Shiru har yanzu
Tashi ya tashi Tace muje
Yashiga gaba suka fita Suna fita yaga Fareedah a kwance lub abakin kofa kamar ba Rai
Da gudu Mommy taje wajenta tana kiran sunanta amma shiru mommy ta kwala ihu tana kiran sunanta shi kuma Ahmad ya rikece yarasa me zeyi

Suna cikin haka Daddy ya sauko da sauri yana tambayan meyake faruwa Mommy tace mishi Fareedah ce ta suma Yace wa Ahmad kawo ruwa Ahmad yatashi da gudu ya ebo ruwa aka Zuba mata a hankali tafara bue idonta tace ina Fateemah Da alama taji duk maganganunsu Ahmad yayi shiru Daddy yace wace Fateemah Mommy tace Fateemah ce Ahmad yaje ya yadda ita

Daddy yace what are you saying Mariya Mom tace katambiyeshi kaji mana wai ta kulleshi a aki shine yarama
Daddy ya ago idonshi yana kallon Ahmad
Yace me nakeji

Yayi shiru Daddy yace tashi muje suka unguma duka suka shiga mota

Ahmad yajasu suka tafi sunata tafiya sukaga wajen yayi nisa mommy tana ta Addua a ranta

Har suka iso bayan gari kafin yatsaya Daddy yace ananne
Ahmad yace eh ok ina take yayi shiru
Mommy kuwa tazuba ma wani dutse ido Taga kamar jini ne akai tacewa Alhj kalli can Daddy yana kallo yaga jini ne awajen
Suna zuwa sukaga jini dayawa akan dutsen harya fara bushewa
Daddy yace Wannan jininfa Ahmad yayi shiru Daddy have ba tambayanka Nake ba
Daddy Nina ban Sani ba
Tass Daddy ya wankeshi da Mari

Ina kakai yar mutane Inji Mommy yayi shiru
Ba tambayanka ake ba

Shikamma yarasa ya zeyi idan yayi magana su mareshi yayi shiru suyi ta tambayanshi ya rasa ya zaiyi

Suna cikin dubawa sukaga wani mutum yana zaune dagacan gefe Daddy yaarasa wajen mutumin yace mishi bawan Allah bakaga wata yarinya Acan Akwance ba
Tsohon yacewa Daddy eh ai azu wasu mutane sunzo sun auki wani gawa acan kuma a yadda nagani gawan kamar mace ne

Ai kafin yaarasa Daddy yafai awajen da gudu suka araso wajen suna tambayan tsohon meya faru Yayi musu bayanin komai kafin yakarasa zancanshi ai Fareedah ma tayi asa mutumin yarasa meyake faruwa Mommy tadinga zabga ihu shikuma Ahmad atake jikinshi yafara rawa da yar suka aukesu zuwa Asibiti

Tun daga wannan rana Alh Kabeer yazama bashi da lafiya harya kasance jikin yayi tsanani hawan jini yake daminshi
angaren Fareedah ma bawani lafiyane da ita ba tazama shiru bata da yawan magana Shikuma Ahmad yarasa meyake mishi dai Abu kamar wasa gashi yazama gaske shima yazama shiru shiru dama gashi miskili

Alh Kabeer jiki yayi tsanani yana jinya sosai yau kam jikinma yafi na kullum an kaishi Asibiti rai yayi halinshi saide muce Allah yagafarta mishi da duk musulman da suka mutu Ameen

 

jiddah S Mapi
623 1247 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_Storywritten by_
Jiddah S MAPI

_dedicated to my daughter Afrah_

_ote me on wattpad Jiddahpretty_

Page 2122

Tun daga Wannan ranan Hajiya Mariya tadaina yiwa Ahmad magana Fareedah ma ba magana take mishi ba ko yayi musu magana auke kai kawai suke Abun duniya yayi mishi yawa ya rasa ina zesa kanshi shi fa a Azuciyarshi yanaji bata mutu ba Haka yazama kamar wani mahaukaci duk inda yaji ance Fateemah saiya juya yaga meshi abokansa sun kasa gane kanshi baya zuwa club yadaina bin mata ko ankirashi awaya baya auka sai shaye shaye yake kamar mahaukaci

Akwai wata rana daya kira Fareedah yace tazo tasaya mishi magani Fareedah batayi magana ba sai yaga kamar ta rainashi ne haka yarike Fareedah yayi ta dukan ta
Mommy tana dawowa taga Fareedah jiki a fashe tace meya sameki Fareedah tace Ahmad ne ya daketa Mommy tafita a akin taje ta sameshi a kwance kan gado mommy tace Ahmad bazaka kashe yar mutane ka kashe mahaifinka sannan kazo ka kashe anwarka ba baka isa ba kayi kaan
Katashi kabar gidannan cikin minti goma idan kasake dawowa saina tsine maka AlbarkaAhmad yabue baki zaiyi magana amma Mommy tace idan ya kuskura yayi magana Allah ya isanta haka ya tattara kayanshi yabar gidan

Ahmad ya rame bashi da tinani saina Fateemah a halin yanzu yafara tuninin yana son Fateemah ne idan ya tuna da hakurinta da juriya Sai yayi ta kuka kamar me haka Habeeb yazo ya tarar dashi haka
Yace meya sameka Ahmad yayi mishi bayanin duk abinda yafaru

cigaban labari

Yaune ranar zagayowar haihuwan Bintu da Beebah an haa party wanda kawayensu na makaranta dayawa suka hallara inda Bintu da Beebah suka sa anko na skirt pink da top black suka aura kai da black na ankwali Fain yanda sukayi kyau ata lokaci ne domin yau yan biyun Mommy sunyi mugun kyau kamar asace a gudu kawayensu kuma sunsa dogon riga baki sunyi kyau suma sosai an yanka cake ansa waa a speaker Inda Beebah tayi ta dansewa ita da awayensu Bintu sai video kawai take yi musu tana dariya

Habeeb kuwa ya kira Beebah yace mata sweet sis ki hau watsapp kituramin hotonan da kukayi yau zansa a status ina tom broh bari na bue Data

jiddah S mapi
623 1247 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

Storywritten
By jiddah S MAPI

_dedicated to my daughter AFRAH_

_follow ne on wattpad Jiddahpretty_

Page 2324

Beebah ta bue data ta turawa Habeeb hotonan su da videos in dasukayi habeeb yana ganin videon yace mata wow sweet sis kunyi kyau gaskiya tace thank you broh
Se mangariba dab suka gama partynsu suka raka duk awayensu kowacce tashiga motarta suka tafi Bintu ce ta kwashe musu gift dasuka samu daga wajen awayensu tashiga musu falon mommy dashi

Ahmad yau ya tashi da tsananin ciqon kai inda yayi ta birgima yana rie da kanshi dakyar yasamu yasha magani yaan samu saui ya zauna a gefen gado yana tinani azuciyarshi yace da ace my teemah tana nan data bani magani da kanta nasha komai nayi mata zatayi hakuri dani wayyo my teemah ina kike dan Allah ki bayyana min kanki nasan kina raye baki mutu ba Ki fito dan Allah naganki zan nuna miki soyayyar dabaki taa jin labarinshi ba ko a Novel

Haka ya karashe tunanin shi ya tashi ya shiga wanka bayan yafito daga wankane yashafa mayukanshi masu kamshi ya taje gashin kanshi me laushi kamar na indiyawa ya bue wardrobe nashi yaauko wani riga pink colour da bakin wando ya auko picap baki yasa ya dubi kanshi a madubi yaga ya rame sai de yayi fari sosai a hankali ya rufe idonshi yace oh god help me out

Habeeb bashi da damuwan daya wuce damuwar abokinshi Ahmad kullum idan ya zauna sai yayi tagumi yana tinanin ta ina zai fara taimakawa Ahmad har Mommy tagano yanayin shi da daddare suna zaune a falo suna kallo Bintu tana an danne danne awaya ita kuma Bebbah ta kwantar da kanta akan cinyar Habeeb tana mishi rigima wai sai yayi mata tsifa Mommy tace Habeeb inason in tambayeka wani Abu mana Yace to Mom ina jinki Mommy tace meya sameka ne naga tin ranan daka dawo daga Kaduna kashiga damuwa ko wani Abunne yasamu Ahmad

Habeeb yace gaskiya mom Ahmad yana cikin matsala nan yafara faa mata duk abunda ya faru Amma ya oye mata yanda Ahmad ya yar da Fateemah
Ba Mommy ba har yan biyu saida sukayi hawayen tausayin Ahmad Mommy tace yanzu shi Ahmad in yana ina Habeeb yace yanzu de yana gidanshi acikin kadunan Amna yace min bazai iya zama a Kaduna ba gaskiya ze tafi Dubai yayi zamanshi acan Mommy tace to yayi Aure mana wata kila idan ita Hajiya Mariyan taji zata yafe mishi Habeeb yace gaskiya mom Ahmad A halin yanzu ko yayi Aure to matar daya Auran agaskiya GANGAR JIKINSA TA AURA dan zuciyar Ahmad tana wajen Fateemah

mommy tayi shiru tana tunani

jiddah S mapi
623 1247 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

Storywritten by
Jiddah S mapi

_dedicated to Eeshart_

KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION

_united We stand and succed our ambition is to Entertain motivate the mind of readers_

WATTPAD
Jiddahpretty

Page 2526

Bayan wasu lokutane Mommy ta ago kanta tace da yayi Aure dayafi dai Habeeb wata kila ta yafe mishi idan taga yayi Auren musamman idan yaje mata da jika toh fa kunji mommy da zance Habeeb yace ok mommy baradai nagwada yi mishi maganan ko zai yadda to Amma mommy idan ya yadda wa zai Aura sabida kinsan bashi da budurwa Mom tayi shiru daga baya ta nisa tace ga Habeeba saina bashi ita ya Aura Habeeba tayi shiru atake zuciyarta ta tsinke To Shikenan mom bara zanyi mishi maganan anjima inji Habeeb

Ahmad yana kwance ciwon ciki ya dameshi yasha magani ma ba sauki da kyar ya au wayarshi yakira abokinshi Bash

Hello Bash dan Allah kana inane Bash yace kanada matsala ne Ahmad yace eh akwai matsala ok kana wani club ne Bash bana club Ina gidana na anguwar sarki kazo ka sameni ok
Bayan wasu mintuna saiga Bash

Bash yana shiga akin yaga Ahmad a kwance yanata murkususu ya arata akin da gudu yana tambayan Ahmad meya faru Ahmad baya iya ko magana sai rike maranshi dayake Meya sameka A hankali yace cikina Bash yayi shiru yana tinani can yace Haba gaye meyasa zaka cutar da kanka ga yammata a club kala kala ya zaka zauna da ciwon ciki kamar mace Haba mana gaye karka bada ni mana Aa Bash nadaina bazan sake kusantar wata mace ba a duniya na riga nayi Alkawari idan ba my Teemah ba saide ciwon cikin yakasheni to Amma ai saika an sha ko kwalba ayane inji Bash Ahmad yace nasha nasha banga anfaninshi ba sai ma aramin cuta dayake to Shikenan saika kashe kanka

Yanzu me kake so Nayi maka Ahmad yace mommy zaka kiramin awayarka inason naji muryarta dana Fareedah Bash yayi shiru dan ya tuna Mommy tahanashi tafiya da Ahmad idan tagansu tarema hararanshi takeyi Mommy taki jininshi amma bari dai ya gwada

Yacewa Ahmad bani numbanta Ahmad yamishi nuni da wayarshi Bash ya auko wayar yaau numban Mommy yakira ta da farko kamar bazaa aga kiranba sai daga baya aka aga

mommy tace hello baayi magana ba Tanata hello hello anyi shiru Bash yakasa magana sai can yace hello momsy ya gida Mommy tayi shiru tsabar taaici tarasa me zatace mishi dan tagane muryanshi azuciyarta tace wannan Bash in da kanshi kamar sandan mopping sainayi maganinshi
Tace meke tafe dakai Yace am dama momsy Ahmad ne Mommy tace dakata banason shashanci komai Ahmad yayi a duniyarnan dasa hannunku aciki sabida ku abokanshi ne ku kuke bashi shawara mara kyau mom tafashe da kuka tace Allah ya isa tsakanina daku Bashir kun atawa ana rayuwa nabarku dashi nikam na yafe Ahmad duniya da lahira kuma idan kasake kirana to hukuma ne zasu rabamu dakai
Mommy takashe wayar tana kuka me cin rai

Bash yayi shiru yana kallon Ahmad wanda yake ta kukan dana sani Yace haba gaye ya zaka tsaya kana kuka akan maganar tsohuwa kasanfa tsofinnan surutun balai ne dasu ka manta kawai kaansha ko kwalba aya ne idan babu kuma a frij in zan iya saya maka da kuina

note
ana cewa aboki baya ata aboki wannan magana ba gaskiya bace wani abokin ma ze iya kashe ko nawa ne dan ganin kaima ka ata rayuwarka kun zama daidai akiyaye abokai da bakai ba gindi ko kawayen dabasu da natsuwa Allah yatsaremu Ameen

Ahmad yace Aa akwai a frij aukomin kwalba aya da Bash yaga Ahmad ya shanye kwalban giya me tsada aya sai ya ara auko waniyabashi haka Ahmad yayi ta urawa har bacci yaaukeshi
Da Bash yaga Ahmad yayi bacci saiya fita a akin yakira numban wata yace hello polinah kina inane Ok kizo anguwar sarki yanzu kisame ni yabata numban gidan

Polinah wata sheaniyar yarinya ce wanda ta ware a bariki sau da dama Bash yanayiwa Ahmad tallanta amma yaki itama polinah tanason Ahmad sosai kamar ranta yau ta samu dama

jiddah S mapi
623 1248 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

_Storywritten by_
jiddah S Mapi

_Dedicated to my lovly friend ELHAM_

KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION

United we stand and succed our ambition is to entertain motivate the mind of readers

Page 2728

Bayan wasu mintuna Bash yaji aran tsaiwar motar polina ya tashi ya fita a falon yaje yaaraso da polina cikin akin polina Big girl ce ko ta ina ta hau tana da shape wanda ake kira cocacola shape
Tana shiga akin tahango Ahmad kwance agado yana bacci Alaman ya sha abu sosai
Bash yacewa polina Babe nasan ke kaai zakiyi mishi maganin abinda yake daminshi polina tace that way i love you Bash kai kaai kake gane damuwata har kayi mini magani kuma zanyi mishi magani yanzu yanzu ma kuwa kai dai kawai ka jiramu a falo
Bash yace nabarku lafiya ita kuma polina ko kunya babu tafara kwae kayan jikinta jikinta har rawa yake

angaren Mommy kuma tinda Bash yakirata taji hankalinta yatashi idan Ahmad yamutu ya zanyi Nayi rashin mahaifinshi yanzu kuma in rasa shi Kai anya kuwa abin zaiyi Baradai nakira Bashir in na tambayeshi awana gida Ahmad yake ay hanunka baze taa ruewa ka yanke ka yar ba duk maganannan Azuciyarta takeyi sai kawai taau waya takira Bash tace kai Bashir awana gida Ahmad yake Bash yace a gidanshi na unguwar sarki Mommy takashe wayar taau hijabinta da makullin motarta tayi gaba

Bash yana gama wayar yatafi siyan musu abinci a restorant
Polina kuwa tana bedroom ita da Ahmad sunata aikata mashaarsu duk da Ahmad baa hankalinshi yake ba

Mommy gidan Ahmad ta nufa tayi parking na motarta awaje
Tanata sallama baa amsaba tarina kiran Bashir taji shiru atake taji zuciyarta ta buga saita shiga cikin falon tana sallama babu wanda ya amsa tace Allah yasa lafiya takama hanya zata tafi taji muryan mace asa asa tana cewa i love you so much my Ahmad tafara addua aranta kawai saita kama banyan bedroom Ahmad kuma alokacin yafara dawowa hankalinshi yafara kiran sunan polina polina mom taji muryan Ahmad yana cewa polina Ita kuma polina tana cewa Ahmad I love you so much da polina da taga Ahmad yana son yadawo hankalinshi saita haa bakinsu wuri aya alokacin mommy ta bue kofa sai kawai taga Ahmad da mace kwance kan gado ba kaya bakinsu ahae ay kawai saita zube awajen

Muje zuwa

jiddah S mapi
623 1248 PM Ummi Tandama
A GIDANMU TAKE

Storywritten by
jiddah S Mapi

_Dedicated to All my fans_

WATTPAD
Jiddahpretty

Page 2930

Polina tana ganin mutum ta bue ofa kuma ta fai kasa take sai kawai tadiro akan gadon ta tsala ihu
Alokacin Bash yadawo daga siyan abinci yaji ihun polina amma shi yazata iskanci ne kawai

Polina takara zabga ihu tana cewa azo ataimaketa Bash yatashi da sauri yaje bedroom in yaga mom akwance asa kamar ba rai ai da gudu yaje frij ya auko ruwan sanyi yazo wajen datake kwance

BINTU

Bintu ce kwance akan gado tana chatting awayarta kirar samsung yayinda Beebah take kwance agefenta tana bacci
Bintu ce tanaawa Beebah duka tace ke tashi kiga nayi saurayi sabo Haae Beebah ta tashi tana matsifa

A Gidanmu Take Page 1 To 10  Complete
Uploaded by Zamgist.com.ng
File Size 730kb
Hausa Novels WhatsApp Group Click here
Telegram Group Click here
Novel Price Free
Novel Author Jidda s Mapi
File format Txt
Published date 18 – 03 – 2023

 

Download Novel

KARANTA WASU LITTAFAN

Ribar Kishi: Hausa Novel Complete

Jarababben Namiji 51 Romantic Hausa Novel

Jarababben Namiji 1-2 Hausa Novel

Tsintacciya COMPLETE hausa novel pdf

Jarababben Namiji Littafi na 2

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*