Barka da zuwa wannan shafin namu inda zamu kawo muku sakamakon zaben gwamnan jihar yobe 2023 wanda hukumar zabe tariga da ta sanarda Wanda ya lashe zabe.
A ranar asabar aka gudanar da zaben gwanan jihar yobe 2023. A wannan shafin zamu muku sakamakon zaben jihar inda zamu sanar muku waye ya lashe zaben gwamna a jihar ta yobe.
Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Yobe 2023
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato (INEC) ta bayyana Gwamna Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna ta jihar Yobe.
Kwamishinan Hukumar INEC na jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Abdullahi shi ne ya sanar da hakan a dandalin tattara sakamakon zaben dake Damaturu, da daren nan.
Ya ce gwamna maici Buni na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 317,113, fiye da na abokin takararsa daga jam’iyyar PDP, Hon.Shariff Abdullahi, mai adadin kuri’u 104,259, wanda hakan ya tabbatar da Buni a matsayin wanda ya lashe zaben.
===================================
Karanta: Sakamakon Zaben Gwamnan Zamfara 2023
Sakamakon Zaben Jihar Yobe 2023 (Shugaban Kasa)
Sakamakon zabe dai yafara fitowa daga sassa daban daban na yobe inda Atiku abubakar ya lashe zabe a jihar yobe
Ku kasance da wannan shafin namu inda zamu kawo muku cikakken sakamakon zaben dazarar an kammala.
09:48 na safe: Atiku ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Yobe
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu kuri’u sama da 45,000 a gaban abokan hamayyarsa, Peter Obi (LP), Bola Tinubu (APC) da kuma Rabi’u Kwankwaso (NNPP).
Tinubu ya samu kuri’u 151,459, Obi 2,406 sai Kwankwaso ya samu 18,270.
Hotunan sakamakon zaben jihar yobe 2023
Ga wasu kadan daga cikin sakamakon zaben jihar YOBE dake shigowa
Ku kasance da wannan shafin namu inda zamu cigaba da kawo muku cikakken rahoton daga hukumar zabe ta kasa.