Welcome ZAMGIST, Where we posted Alkawarin da ciwo complete Hausa novel, Alkawarin da ciwo 18, ALKAWARIN da ciwo 5, Alkawarin da ciwo 24, Alkawarin da ciwo Page 17, Alkawarin da ciwo 30, Alkawarin da ciwo 21, Alkawarin da ciwo book 3 and etc.
Alkawarin Da Ciwo
Asalin iyaye na mutanen katagum ne ta jahar bauchi. Gidanmu babban gidane a garin katagum,kuma ALLAH ya albarkaci daukakain zuri’armu da arziki dai dai misali,sakamakon muhimmaci da iyayenmu suka dora akan harkan noma.
idan ka shiga gidanmu, zaka iske sassa guda ukku, na farko na wan mahaifina ne baba sada da matansa biyu da ‘ya’yansa,sai mahaifiyarsu babanmu itama anan sassan take.
Kana matsawa sassan kanin malam sada ne wanda maihaifina ke bi masa .
Sai namu sasssan shine na karshe a gidan da mahaifinmu malam habibu da mahaifitarmu inna amina, ita kadaice gun mahaifinmu da ‘ya’yansu biyar duk hudun maza ne sai ni kadaice tilon mace a tsakiyarsu.
Ni sunana RAHMA amma yawancin “yan gidanmu sukan kirani da Ramatu amma sam babban yayanmu ya hana a kirani da sunana sai dai RAHMA don kuwa yace shine asalin sunana ko a cikin ALKUR’ani.
Ranar da aka haifeni mahaifina ya shigo gidan ckn murna don kuwa lkncn da aka haihu yana gona sai wani daga ckn yayyena ya hau keke ya garzaya ya shaida masa. Bakin mahaifina bai iya rufuwa ba sai da yazo ya ganni.
Ya dauke ni ya kura min ido tare da tofa min addu’o’i yana mai gdy ga ALLAh DA YA AZUrta shi da samuna sannan gashi na dauko kamannun mahaifiyata, ita asalinta bafaulatanar Ningi ce.
Ana cikin murna ne sai ga babban yayanmu mai suna Aliyu ya shigo dakin cikin hanzarinsa bakinsa washe sbd murna,kasancewar duk gayyar ‘ya’yan gidanmu babu diya mace sai yau akaina aka fara haifo mace.
Mahaifina ya mikowa yaya Aliyu ni ina nade cikin zani , ya amshe ni ckn murna da bata misaltuwa, ya kura min ido na tsawan lokaci yana jinijina irin baiwar kyau da Allah ya bani.
Har kusan awa guda ina rike hannun yaya ALIYU(Babansa shine babban wansu mahaifinmu baba sada kenan).
You may like: Matar Makaho Complete Hausa Novel
Alqawarin da ciwo 2 Hausa novel
Irin dumbin addu’oin da yaya aliyu ya tofa min a wannna lkn basu misaltuwa, mahaifina ya sake shigowa ya iskeni rungume bisa ikin yaya aliyu, ya dube shi yana murmushi yace’A’A alyu har yanzu kana nan gurun jinjira ne?
lallai wannna diya ta iri tuta ta ko dai itace matar?” yayi dryr jin dadi ckn jin kunya aliyu yace “ni wlh baba kyan yrnyr nan har tsoro yake bani, da ace idan ta girma zata yadda da hadin aurenmu ai da sai ince utace natar kawai, don wlh ina sonta babal baba na yayi murmushin gamsuwa da maganar yaya aliyuya dube shi yace” ai shike nan aliyu in dai har kana son diyar nan wlh na dau alkawarin baka aurenta sai dai in kaine da kankakace ka fasa auren amma babu fashi in sha ALLLAHU”
Aliyu yayi murmushi ya sake duba na yace’haba baba duk fa ckn zuri’armu ba a taba haifan wanda ya kama kafarta a kyau ba’baba yayi dry yace ‘ haka dai kake ganmi amma ai kuma kunyo gadon kyau kuna maza n shiyasa kake ganin haka to wanna shine asalin alkawarina ure na da yaya aliyu tun ranar da aka haifeniina ckn tsumma kenan.
gsk na tashi cikin kulawa da shagwaba ta ko wane fanni gun uwa da uba kai da dukkan illahirin zuri’ar gidanmu babu ma kamar gun yaya Aliyu.
Wai shi dole tattali na yake a matsayin matar da zai aura idan mun girma.
Shi yaya Aliyu duk cikin dangin mu shine ya sami isashen ilimin zamani mai zurfi shima a dalilin wani makwabcinmu da ALLAHJ ya hada jinin dansa da yaya aliyu har zumunci mai karfi ya kullu tsakanin iyayenmu.
Makwabcin namu Alhaji yakubu mutum ne mai arziki sai ya zama ya koma da shi garin bauchi sbd a lokacin sun kammala karatunsu na sakandire.
Duk gidanmu dama su kanyi karatun firamare da na sakandire daga nan sai su kama kasuwanci.
Nima ba a bar ni a baya ba na sami yin karatun firamare tare da kulawar Aliyu nake samun daukakar karatuna, don kuwa ya dauki son duniya ya dora a kaina duk zuwan da zaiyi daga bauchi in da yake karatu sai ya siyo min abin da yasan inaso ko kuma wanda zai sani farin ciki. haka kuma baya komawa sai ya tabbatar ya koya min wani abuna daga karatun islamiyyah da boko.
Also Read: Kuruciya Complete Hausa Novel
Alqawarin da ciwo 3 Hausa novel
Tun ina yar shekara goma na iya karatu da rubutun hausa haka nan na turanci na kan iya karantwa ko in rubuta.
Ina dada girma kyauna yana kara fitowa sutura sai wadda na zaba nake sanyawa kuma iri iri masu tsada shiyasa na fita daban da sauran kawayena,ko kudin scholarship yaya aliyu ya samu duk a kan hidima ta suke karewa.
Ina yar shekara goma sha daya yaya aliyu ya kammala karatunsa na jami’a digiri guda biyu ya samu. Ba tare da wani bata lkc ba ya sami aiki a lagos kuma mukami mai girma ya samu.
Nan da nan ALLAH ya daukaki yaya aliyu ga mota sabuwar yayi ya saya sannan ya gyarawa iyayenmu gidan da muke zaune komai dai yaji a gidanmu.
A wannan lokacin da daukakar yaya aliyu tayi kamari shekaru na sha biyu amma zaka dauka na kai sha biyar sbd girman jiki. shi kam maihaifina har ya fara shakku akan al’amarin aurenmu da aliyu sbd yadda yaga yanayin da aliyun ya shga na azurcewani kuma gani ba wani girma nayi ba duk da yake a cewar baba ba zan wuce shekaru sha biyar ba za’ayi aurenmu da yaya aliyu, akwai wani zuwa da aliyu yayi daga lagos lokacin ina zaune a sassan mahaifan aliyu a dakin kakarmu ina ninke mata kayan sawanta kawai sai ganin mu2um nayi yayi sallama ya shigo ckn dakn.
sanye yake cikin lallausan bakin boyel sai kyalli yake yi, habawa ban san lkcn da nayi wurgi da kayan dake hannuna ba nayi tsalle na rungume shi tare da fadin “lah! yaya aliyu oyoyo”.
shima cak ya daga ni sama ya rungume sannan ya sauke ni kasa muna kyalkyala dry ya dubeni fuskarsa cike da fara’a yace,”rahama naji kin kara nauyi ne me su inna suke baki ne idan bana nan?” nayi dry nace,”Allah yaya aliyu duk kayan dadin da kake kawo min ne daga lagos suke sani yin kiba”, yayi murmushi yace,”zo mu zauna ki gani ga wasu na siyo miki” muka zauna bisa gadon gwaggo(kakarmu kenan), ya dubeni yace”ina gwaggo ne? nace, “tana bayi yanzu ta shiga” yace” ok, ai na aza ta tafi anguwa ne’ ya fiddo min da kwalayen biskit zuwa su chakulet da wasu irin gwangwanaye na biskit wasu na sansu ya saba siyomin irinsu wasu kuwa ma ban taba ganinsu ba, ya bude biskit din kwali yace,” bude bakinki kiji irin wannan akwai dadi”, ba bude bakin ya bani na gutsura ina ci tare da gyada kai alamun yana da dadi ko?” na gyada kai nace, “wlh very sweet”.
yayi dry tare da ja mini labba yace,”uhm rahaman kwadayi”, muka saka dry. nima na dauko biskit guda daya nace,” nima yaya aliyu bude bakin ka in baka”,ya kuwa bude bakin na bashi muka yi ta dry.
ya sauko cakulet yana saka min a baki kenan gwaggo tayi slm ta shigo.
hannunsa na bisa baki na muka tsayamuna kallon gwaggo, ta duni aliyu tace,” yauwa ka dawo har ka fara sangarta ta ko? sai ka tafi ka barmu da jijalin shagwaba, ka riga ka shagwaba ta da bata abinci a baki shi yasa idan ka tafi take zama da yunwa” ya fiddo ido cikn mamaki yace “ashe zama da yunwa kike yi rahama? to daga yau na daina baki abinci a baki” gwaggo tace”ah! to ku dai kuka sani yrnya 2un tana karama ka koya mata dabi’un turawa ai in agama an kusa ayi aurenku mu huta ku tafi can ku karata”.
ya ware ido cike da mamaki yace ” wana irin aure gwaggo? shekarun rahama fa sha biyu ko kin manta ne? haba ai ko za’ayi aurenmu sai ta kai shekaru sha bakwai zuwa sha takwas”.
gwaggo tace” ba dai a gidan nan bane za mu bar rahama ta kai shekaru sha akwai tsanani sha biyar, to ba ga sa’anninta ba nan duk an yi musu baiko wasu ma har an sa musu rana” yayi ajiyar zcy a ransa yana tunanin ALLah dai ya taimake shi su bar rahama ta dad girma kafin ayi auren su.
tabbasa yasan rahama yake so har kn ransa to amma aurensu ba yanzu ba duk da yake ko sun yi aure ba zama zata yi ba cogaban karatunta na sakandire zata yi har zuwa jami’a maganar haihuwa ma in sunyi aure in sha ALLAHu BABU ITA SAI AN KAMMALA KARATU.
GWAGGO TA KATSE MASA TUNANI da cewa, “ali ko dai ka canza ra’ayin aurenka akan rahama ne? naga daga yin maganar auren ka canza fuska kwata kwata” yayi ajiyar zuciya yace ” wlh ban canza ra’ayina game da aurenta ba, ai ko don in faranta maku rai zan yarda in auri rahama balle ma har ckn raina ita nake so”
gwaggo ta saki wani murmushin jin dadi dangane da maganar yaya aliyu tace, ” to Allah ya nufe mu da ganin lokacin auren” yace “amin ba wai na dauke shi da muhimmanci bane, illa dai kawai na kanji dangi nace min matar aliyu nima haka na dauka wani lokacin har baba aliyu na kance masa amma sai inji yace kar in kara kiransa baba sai dai yaya.
bayan sun gaisa da gwaggo suka dan taba hira ya kawo irin turarrurrukan da ya kan siyo mata a lagos masu kamshi da tsada ya bata sannan ya riko hannuna muka baro dakinta tana ta shi masa albarka.